Sashe 18
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ta kalleshi fuska a ɗan kwaɓe ta ce"eh mana, just tell me wane ne"
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce
"Hajiya Babba ce!"
Saurin rufe bakinta ta yi tana girgiza kai, ta sake shi tana murmushi ƙasa-ƙasa, kamo hannunta ya yi ya ce"ina kuma zaki, ki ka ce za ki yi faɗa da koma wane?"
Zaro idanunta ta yi tana faɗin "Allah na tuba, ban san Hajiya Babba ba ce, Allah ka yafeni"
Ta yi maganar tana daga hannunta sama alamar roƙo. Dariyar da bai yi niyya ba ya yi kafin ya ce"ashe? Daman ba za ki iya tsayawa mijin naki ba ko?"
Jan kumatunsa ta yi tana murmushi ta ce"zan iya mana, amma ban da akan Hajiya, in dai akan Hajiya Babba ne to sai dai na kwanta maka"
Janye jikinsa ya yi yana dariya ya nufi hanyar fita daga ɗakin yana faɗin "ina Noor?"
"Ta yi bacci"
Zahra ta bashi amsa tana bin bayansa.
****
Around 11pm tana kwance tsakiyar gadonta ta yi nisa cikin karatun littafin HASKEN CIKIN DUHU wanda Nanameera ta rubuta kira ya shigo wayarta, ɗan tsaki ta yi dan ji take kamar an katse mata jin daɗi, ta kalli numbern sai kuma ta ɗaga ta yi shiru. Daga ɗaya ɓangaren Junaid na zaune tsakiyar parlon da ke apartment ɗinsa idanunsa bisa tv yana kallon game ya ce
"Nana"
Murya can ƙasa ta ce
"Uhm"
"Kin yi bacci ce?"
Girgiza kanta ta yi kamar yana gabanta ta ce
"A'a ban yi, kawai I'm doing something ne"
Junaid ya rage sound ɗin tv jin ana ihu kafin ya ce
"Me ki ke yi da daren nan?"
Kamar ba zata ba shi amsa ba sai kuma ta ce
"Karatun novel nake"
Gyara zamansa ya yi yana faɗin
"Ashe? Wani novel ne haka da har ya hana ki bacci da wuri ke da ki ke kwanciya da wuri Nana?"
Ƙaramin yatsarta ta sanya a baki tana taune farcenta ta ce
"Karatun ne yake min daɗi"
Junaid ya jinjina kansa yana murmushi ya ce"lailai, kina jin daɗin ki, to ki bani labarin littafin"
Murmushi ta yi tana tashi zaune a kan gadon ta ce
"Toh kana ji"
Shiru ta ji ya yi, ta ɗan kwaɓe fuska a shagwaɓe ta ce"ba ka ji ne?"
Yana sake jingina da kujerar da yake kai ya ce"ina jin ki fa"
Murmushi ta yi ta ce"to sunan jarumar Salma, shi kuma jarumin sunansa Zayyad, Yaya Yad me paracetamol, ita ƴar talakawa ce shi kuma ɗan masu kuɗi, yana da girman kai kuma baya ji, sai yake zuwa garinsu a lokacin tana sai da lemo a bakin kasuwa suka fara haɗuwa ya mata rashin mutunci ta masa rashin kunya..."
Ta tsaya tana dariya a hankali. Dariyar shi ma ya yi ya ce"ina jin ki"
"To sai wata rana ya taimaketa wasu sun biyota, shikenan ya kai ta gidansu, ta fara zama yar gayu za'a sakata a makaranta kawai sai aka masa asiri ya haukace, kuma aka ce ita ta haukatashi dan haka tare zasu tafi duk in da zai je, abun tausayi, ta dinga wahala dashi ta samo masa abinci, ta basa kudi, ya daketa ya shaketa a haka har ya samu lafiya. Aka musu aure, kawai! Kawai sai iyayensa suka zo tafiya dashi ya ce wai ya saketa..."
Ta fashe da kuka tana jan numfashi, da sauri Junaid ya ce
"A'a Nana sorry kin ji, bar bada labarin haka kin ji"
Gyaɗa masa kai ta yi tana ci gaba da kukanta, ya kwantar da murya ya ce"nace ki yi shiru ko, ki kwanta sai da safe"
Toh kawai ta ce sannan ta kashe kiran, ta juya ta kwanta tana ci gaba da kukanta har bacci ɓarawo ya saceta.
**** Kusan sati biyu kenan, abubuwa sai kankama suke a cikin estate ɗin, ana ta shirye-shiryen biki wanda za'a yi nan da wata ɗaya da rabi. Duk yanda Abdusammad ya so ya sauya lamarin abun ya ci tura, dan Hajiya Babba ta hana shi magana a kai, dan haka dole ya saka ido kawai ba dan ya so ba. A ɓangaren Sultan kuwa kullum cikin damuwa yake, shi ma tun bayan da Ummi ta ce kar ya yi magana bai tada zancen ba, amma ko kaɗan bai ji wani abu ya ragu a zuciyarsa daga son da yake wa Nana, sai ma wani sabbin abubuwa dake son bijiro masa. Dan yanzu baya iya yini ɗaya bai sakata a idanunsa ba, ko dai su haɗu a Apartment ɗin Hajiya Babba, ko kuma ya je gidansu da sunan gaisar da Abba.
Tana zaune gefen famfon tana wanke inner ɗinta Amrah ta ƙaraso wajen hannunta riƙe da ƙaramin bucket, zama ta yi gefenta ba tare da ta ce komai ba, ita ma kallonta kawai ta yi sai kuma ta ci gaba da abin da take, ba'a fi 2mins ba Maimoon ta ƙaraso wajen ita ma hannunta riƙe da nata bucket ɗin, ta zauna itama ta zuba uban tagumi, Nana ta ɗan kallesu ganin yanda suka yi sai kuma ta ce"ina Hamida?"
"Mama bata barta ba ina ga"
Cewar Maimoon hannunta tallafe da haɓarta, numfasawa ta yi sai kuma ta ce"to ko muje gidansu ne?" girgiza kai Amrah ta yi ta ce"idan muka je can ba zamu sake ba, that's why yasa nace mu zo nan ɗin ma" Maimoon ce ta ce"eh nima haka nake tunani, wai yanzu da gaske auren nan za'a yi?" murmushin takaici Nana ta yi kafin ta ce"gashi kuwa, ni yanzu kullum hankalina a tashe yake, ji nake kamar wani abu mara kyau zai faru dani ɗin nan wallahi" tsaki Maimoon ta yi ta ce"ki ci gaba da ɗaukan haka, sai ki ga ya faru"
Kallon Amrah ta dinga yi ganin yanda ta ƙura masa idanu bata ko kiftawa, sam ba kula dasu ba dan haka ya yi shigewarsa. Nana ta janyo hannunta tana faɗin"keee wannan kallon...."
Maganar ta maƙale ganin yanda hawaye ki biyo kan fuskarta kamar an buɗe famfo, suka dinga kallonta da mamaki kafin Maimoon ta yi ƙarfin halin cewa" lafiya dai Amrah?"
Cikin shassheƙar kuka ta ce
"Kowa yana faɗar abin da ke ransa dan yaji daɗi, dan haka nima gara na faɗa ko zan samu sauƙi, wallahi tallahi ban taɓa son Yaya Sultan ba, ban taɓa masa kallon wanda nake so na aura ba, kullum zuciyata da tunanina suna wajensa, kullum fatana ya dawo ƙasar nan a haɗani aure dashi, kullum dashi nake kwana da shi nake tashi, ina sonsa! Ina son sa tun ina ƙarama wallahi!"
With so much confused suke kallonta, Nana ɗan girgiza kanta tana faɗin"ban gane ba? wane? Wa ki ke so?"
Ta jera mata tambayoyin a lokaci ɗaya tana mai da kallonta dan jiran amsar da zata bata. Amrah ta sauke nannauyan numfashi hawaye na sake zubowa fuskarta ta ce
"Uncle Abdusammad mana! Ina son shi, ina ƙaunarsa wallahi, ko mai ya yi birgeni yake, ko faɗa yake kyau yake, ina sonsa! Shi nake so na aura ni! Shi nake so Nana!"
08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*
Page 12...
Yan channel ɗina masu quality ❤️ This page na dedicated to guys, na bar muka kayanku, ku yi sama dashi abin ku, Nanameera heart u guys💃.
Tuntsirewa da dariya Nana ta yi tana yin baya, ta yi zaman dirshan a wajen, Amrah ta kalleta sai kuma ta sunkuyar da kanta hawaye na zubowa kan kuncinta, Maimoon ce ta kalleta ganin how serious she's ta ɗan taɓa Nana a sanyaye ta ce"me ya sa ki ke dariya ne?" Ba ta ce komai ba sai ci gaba da dariyarta da tayi kama zararriya, suka dinga kallonta baki buɗe. Sai da ta yi mai isarta sannan ta tsagaita tana ƙoƙarin saita nutsuwarta. Sai dai bata san sanda ta sake tuntsirewa da wata dariyar ba da suka haɗa idanu da Amrah, duka Maimoon ta kai mata tana tsaki ta ce"wai ke baki da hankali ne?" girgiza kanta ta dinga yi bayan ta rufe bakinta da hannunta ɗaya gudun kada ta sake dariyar.
"Wai me ki ke wa dariya to?"
Maimoon ta sake tambayarta a dame, gyaran murya ta yi fuskarta a sake ta ce"wai uncle take so, uncle fa, wannan tsohon, ya fa girmi duk ya'yan Hajiya, taɓ subhanallahi..."
Ta sake tuntsirewa da wata dariyar, a fusace Amrah ta mike tsaye tana kallonta rai ɓace ta ce"ke ki ke ganinsa a matsayin tsoho, amma ni bana masa wannan kallon, kuma kin san yafi kowane mutum a gidan nan daraja da martaba. Saboda ya fi kowa kyau, ya fi kowa kuɗi, ya fi kowa ilimi, sannan yafi kowa sanin abin da ya dace!. Ke bari ki ji ma ko Yaya Safwan ɗin da zaki aura a karkashinsa yake, daga jikinsa suke samun abin da suke yiwa kan su buƙata. Rabin arzikin wannan estate ɗin nasa ne, ke bama rabi ba, kusan duk arzikin nasa ne! Dan haka ki iya bakin ki wallahi tun kafin ran ki ya ɓaci!"
Wani irin kallo Nana ta dinga mata sai kuma ta yi shewa cike da ƙwarewa a masifa ta ce"banza kawai! Au she daman ba shi ki ke so ba, arzikinsa ki kewa. To sai me dan ya fi kowa kuɗi? Ke kudinsa ya dama, dan da alama abin da babanku yake baki baya isarki, domin da yana wadatarki da ba zaki taɓa zuwa kina faɗar irin waɗannan maganganun ba, da kin godewa Allah da ni'imar da ya yi miki. Amma da yake son zuciya ki ke sa a gaba har kin gano cewa yafi kowa arziki, to ina ruwana da arzikinsa? Mene abin da ya shafeni dashi, ni abin da ubana yake min shi ne abin tunƙawona ba wai wani can ba, banza kawai me son zuciya!..."
Cikin tsananin ɓacin rai Amrah ta jawota ta shiga faɗin"ke har kin isa ki zageni? Dan kin ga ina zama tare da ke? Ni sa'ar wasarki ce?"
Cikin azama Maimoon ta ƙarasa gabansu tana faɗin"mene haka? Sai wani ya zo shigewa ya gan ku, ke Amrah cikata mana"