← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 125

Sashe 33

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ganin irin kallon da suke mata ba tare da sun bata amsa ba ya sanya ta ɗan yi murmushi tana basarwa ta ce“daman zan ɗan amshi saƙo ne a hannunsa” jinjina kai Maimoon ta yi kafin ta ce“eh Yaya Safwan yanzu ya dawo daga office na san, maybe yana apartment ɗin Hajiya Babba, tun da ba'a fara kiran sallah ba, yana ma can” ta ƙare maganar tana bata tabbacin inda yake, faɗaɗa murmushinta ta yi ta ce“okay na gode sosai bari naje can ɗin” to kawai Maimoon ta ce sannan ta bi bayan Nana wadda ta yi gaba abin ta, Siyama ta juya ta sake bin su da kallo sai kuma ta yi murmushi a fili ta ce“nan gaba kaɗan zaku fara girmamani” ta ɗan yi dariya sai kuma ta bar wajen, Maimoon ta dinga kallon Nana sanda ta tsaya a balcony nasu kafin ta ce“wai me ya sa baki bata amsa ba?” taɓe baki ta yi ta ce“ke ni bata min ba wallahi, rannan na gansu a Apartment ɗin Aunty Zahra, kawai na tsaneta” murmushi Maimoon ta yi tana miƙa mata tata ledar ta ce“ji min baƙin hali kawai sai ki tsaneta, to Allah ya kyauta miki” karɓa Nana ta yi ta ce“ki gaida gida” okay kawai ta ce sannan ta nufi nasu gidan, ita kuma ta juya ta murɗa handle ɗin ƙofarsu.

****
Zaune suke cikin ɗaya daga cikin sorayen gidan guda biyar, wanda kuma shi ne ya kasance na huɗu a lissafi, gabansu wani mutum ne ya durƙusar da kansa yana dube-dube, wuyansa rataye da ƙaton carbi irin mai dubun nan, Mutumin ya yi gyaran murya ya ɗago mummunar fuskarsa irin ta gardawan tsangaya ya kallesu, Kaddu dake zaune kusa da Auntt Khadijah ta ce“Malam ya ake ciki?” atishawa ya yi kafin ya ce“wannan aikin naku zai yiwu, amma domin samun biyan buƙata dole ana da buƙatar juyar da tunaninta” Kaddu ta ce“wace Malam?” sai da ya sake wata atishawar sannan ya ce“ita yarinyar, dole ne a juyar da tunaninta ta dawo ɓangaren ku, dole ne ta sanya baki cikin maganar auren, domin ta haka ne za'a iya jawo hankalin sa har ya fara sonta” Aunty Khadijah dake saurarensa tun ɗazu ta ɗan zaro idanu kafin ta ce“wai kana nufin Zahra za'a juyarwa da tunani?” gyaɗa mata kai ya yi, ta ɗan girgiza kanta ta ce“a'a Malam idan kuma ba'a yi nasara ba fa?” tuntsirewa ya yi da dariya sai kuma ya ce“da baki yarda da aikin namu bane? To idan har ki ka ga an samu matsala sai dai inda ba yanda na ce ku yi ba ku ka yi, dole ne a sauya tunaninta, ta dawo bayanku ta shiga cikin maganar auren, daga nan sai ta jawo hankalin yaron ta hanyar abubuwan da zamu dinga yi, shi kuma a gefe ɗaya zamu yi aiki a kansa, daga nan komai zai zo da sauki zai auri yar ki ya dawo yi miki biyayya kamar ke ce uwar da ki ka haifesa!”.

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 21...

Aunty Khadijah ta dinga murmushi ba tare da ta ce komai, Kaddu ce ta kalleshi ta ce“tom malam yanzu nawa za'a bada?” girgiza kansa ya yi sai kuma ya ce“a'a ba zan karɓi komai daga hannunku ba, amma nima ina da abin da za'a yi min kamar yanda ki ka sani” Kaddu ta jinjina kanta dan daman ta san da hakan, lokaci ɗaya ta juya tana kallon Aunty Khadijah da ke kallonsu a hankali ta ce“muje ki ji” okay kawai Aunty Khadijah ta ce sannan suka miƙe a tare suka nufi ɗaya soron.

Wani irin kallo ta dinga yi mata kafin a ɗan fusace ta ce“Haba Kaddu ya ma za'a yi na yarda da wannan ƙazamin mutumin? Ta ina? Gaskiya ba zan iya ba, idan yana son kuɗi kawai a bashi” tsaki Kaddu ta yi tana jan hannunta ta ce“ashe ba biyan buƙatar ki ke so ba, to mene a ciki dan dai sau ɗaya, daga wannan fa shikenan ba sake neman wani zai yi ba” shiru ta yi tana tunani, Kaddu ta ɗan yi murmushi ta ce“muje dan Allah” girgiza kai Aunty Khadijah tayi ta ce“kai Kaddu! Kai! Gaskiya bana jin zan iya wata mu'amala da wannan mutumin, to wait idan ma na yarda dashi aka zo aikin bai yi ba shikenan ya cuceni kenan?” harararta ta yi ta ce“kin ga ni ba zaki ɓata min rai a banza ba wallahi tallahi, ya ina ƙoƙari akan ki kuma bakya gani, kin san aikin nasa ne? Wane ya ce miki idan aka yi za'a iya rashin nasara? To ki zauna, idan bakya so kawai mu shige mu tafi daga nan” furzar da iska ta yi daga bakinta tana tunanin abin da ya kamata ta yi, ta yarda dashi ta bashi kanta domin biyan buƙatarta? Ko kuwa ta yi tafiyarta ta nemi wani?.

****
Sati ɗaya a tsakani lokacin shirye-shiryen biki ya kankama, ranar wata Litinin ta kama ita ce ranar da aka kai wa kowace yarinya kayan aurenta, dan haka estate ɗin a cike take da yan uwa da abokan arziki. Zahra ce ta buɗe ɗakin tana kallonta ta ce“Nana har yanzu baki tashi ba?” tana kwance kan gadon ta juya mata ba, ta sanya hannunta ta share hawayenta sannan ta ce“na tashi Aunty”

“to ki fito ki yi breakfast kin ji” toh kawai ta ce, Zahra ta juya ta fita, sai a sannan ta tashi zaune tana sake fashewa da wani sabon kukan, she just can't believe ace aurenta nan da one week, auren ma kuma bada Junaid ba, da Yaya Safwan wanda ko a mafarki bata taɓa tunanin irin haka zata kasance a tsakaninsu ba, ta goge hawayenta sannan ta janye duvet ɗin data rufa dashi ta sakko daga kan gadon, gaban dresser ɗin ɗakin ta tsaya ta dinga ƙarema kanta kallo a jikin ƙaton madubin, ta rame sosai, idanunta sun firfito har ɗan duhu ta yi wanda yake nuni da rashin kwanciyar hankalin da take ciki. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta bar wajen ta shige toilet, after 20mins ta fito ɗaure da towel, ta ƙarasa press ɗin Aunty Zahra ta buɗe, wata simple gown ta ɗauka mara nauyi ta saka, ta shafa mai a jikinta sannan ta ɗaure kanta da mayafin rigar ta nufi hanyar fita daga ɗakin.

Hayaniyar data dinga ji a parlon shi ne ya hanata ƙarasowa, ta maƙale jikin benan tana kallon su ɗaya bayan ɗaya, Aunty Khadijah ce sai Siyama da Safeena sai kuma wata wadda bata taɓa ganinta ba amma bata fi girman su Safeenan ba.

“Laa Nana ki ƙaraso mana”

Safeena ta yi maganar sanda ta lura da ita, gaba ɗaya suka kalli wajen da taken, ta ɗan sunkuyar da kanta sannan ta ƙaraso a hankali ta ɗan durƙusa tana kallon Aunty Khadijah ta ce

“ina yini?”

Babu yabo babu fallasa ta ce“lafiya sannu” daga haka ta ɗauke kanta, ita ma Nanan bata damu ba ta mai da Idanunta kan Safeena ta ce“sannu sister ya ki ke?” washe baki Safeena ta yi ta ce“Alhamdulillah kefa Nana? Ya shirye-shirye?”

“Suna nan muna fama” Nana ta yi maganar a sanyaye, sai kuma ta kalli Zahra ta ce“aunty bari naje” harararta Zahra ta yi ta ce“ki je ina Nana? Shiga kitchen ki ɗauka breakfast ɗin ki har kusan 1pm baki karya ba” langwaɓar da kai ta yi ta ce“a'a ai zan karya a wajen Amma” girgiza kai ta yi ta ce“ban yarda ba ɗauki ki koma sama ki ci idan ma zaman nan ne baki so” babu yanda ta iya dan bata san musu da Zahra yasa ta tashi ta nufi kitchen ɗin, ba'a jima ba ta fito hannunta riƙe da plate ɗayan kuma ta riƙe mug ta nufi sama da sauri, da idanu suka bita har ta ɓacewa ganinsu sannan Siyama ta taɓe baki ta ce“wai ita wannan yarinyar wace ce a gidan nan? Naga ta fiye girman kai, can you imagine rannan nazo ina musu magana ko kallona bata yi ba” ɗan murmushi Zahra ta yi ta ce“ayyah ai daman Nana bata da magana sosai, in dai bata sanka ba, ba zata taɓa sakin jiki da kai ba, yar ƙanin babansu doctor ce” Aunty Khadijah ce ta ce“har da ita a waɗanda za'a aurar ɗin ne naji Safeena na cewa ya shirye-shirye?” gyaɗa mata kai Zahra ta yi kafin ta ce“eh mana, ai ita ce zata auri Safwan!”

Da wani irin mamaki suka dinga kallonta duka, barin ma Aunty Khadijah da hankalinta ya tashi matuƙa, ta buɗe baki a hankali ta ce“kenan dai ita ce zata fasa aurensa Siyama ta aureshi” Zahra ta kalleta amma bata ce komai, Ɗayar wadda tun zuwansu bata yi magana ba ce ta ce“to ba dolenta ba, ai wallahi sai Siyama ta yi aure s cikin gidan nan!”

Safeena ce ta kalleta sai kuma ta ce“ke Amal me ke damunki ne? Wai mene haka?” harararta ta yi ta ce“bansani ba, wallahi ke duk abin ki sai ta aure shi, to mene amfanin arzikin idan ba'a ci ba, yanzu duk inda ta aureshi mun zama muna da mutum biyu namu a family ɗin nan, nan da wani ɗan lokaci sai ki ga mun mamaye dangin”
Chapter 33 · 0% Book details