Sashe 119
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da wani irin mamaki Anty Khadijah ke sake buɗe idanun ta, Ji ta yi kunnuwanta na neman jiye mata wani tashin hankali, Ko dai ba Kaddun data sani ba ce? .
Malam Garba ya girgiza kansa yana wata irin muguwar dariya, Lokaci ɗaya kuma ya tamke fuska ya ce
“Dani zaki ja? Me ki ke tunani? Na saka kin min aiki akan Khadijah saboda na biya ki da wanda take shirin aure?.” Ya tuntsire da dariya sannan ya ci gaba da faɗin
“Har abada ba zaki aure shi ba, Ke bama zaki yi aure ba. Haka zaki yi ta gararamba a gari, Shi kansa barikin sai an daina nemanki. Kuma babu abin da ki ka isa ki yi min, Ni Garba ni ne me abin yi, Idan na so a yau sai nayi abin da zai sa ba zaki kwana da rai ba!”
Wata irin shewa irin ta yan bariki Kaddu ta yi ta tafa hannu sannan ta ce
“Ai ko zan nuna maka wace Kaddu! Zan shayar da kai mamaki! Wallahi ina da bokayan da sai sun kashe min kai! Kuma ka jira abin da zai biyo baya. Zaka gani!”
Tana gama faɗin haka ta zura takalmanta ta yi waje ko mayafin bata yafa ba, Ban da dariya babu abin da Malam Garba ke yi, Ya dinga girgiza kansa yana daga zaune. Juyawar da zai yi suka haɗa idanu da Anty Khadijah, Ya tashi tsaye yana kallon ta a ɗan daburce ya ce
“Kkk... Khadijah!”
Girgiza kanta ta dinga yi hawaye na zubowa akan fuskarta, Ya tako har gabanta yana kallonta ya ce
“Kina ji”
Anty Khadijah bata ce komai ba ta juya ta nufi hanyar daƙinta, Tana kai wa bakin ƙofa ta faɗi a ƙasa Sumammiya. Malam Garba ya yi kanta da gudu yana kiran sunanta.
****
Zahra na zaune kan kujera a parlour tana danna wayarta aka buɗe ƙofar dakin, Shigowa suka yi bakin su ɗauke da sallama. Ta amsa da fara'a tana fadin
“Laaa Yaya sannun ku da zuwa”
Babban ciki ne ya amsa da
“Yauwa Zahra'u”
Suka zauna kan kujera ta miƙe tana fadin “Bari na kira Umman” To kawai ya ce sannan ta nufi sama da sauri. Buɗe ɗakin Umma ta yi ta shiga, Ta sameta zaune kan dadduma tana jan carbi, ƙarasawa ta yi ta zauna gefen gadon tana kallon ta ta ce
“Umma kin yi baƙi”
Sai da ta ƙarasa lazumin da take ta shafa sannan ta juyo ta kalleta ta ce“Su wane?”
“Yaya Bashir ne, Da Kamal ƙaninsa”
Da ɗan mamaki Umma ta ce
“Ikon Allah yaushe Bashir ya dawo?”
“Kamar rannan naji a group ɗin gida an ce ya dawo"
Sai da ta miƙe ta naɗe daddumar sannan ta ce
“Allah sarki bari naje mu gaisa”
To kawai Zahra ta ce, sannan ta kwanta gefen gadon, Ita kuma Umma ta fice daga ɗakin. Wayarta ta ɗauka ta shiga gallery tana kallon hotunan Noor, Can kuma ta kai kan wani hoton Abdusammad wanda yake zaune cikin office ɗin sa, Sanye da suit, Bai ma san ta dauki hoton ba sanda ta taɓa zuwa asibiti wajen sa. Iyaka kyau hoton ya yi kyau musamman yanda ya yi murmushi yana ƙoƙarin mata magana, Ji ta yi wani iri a jikinta, Ta yi saurin ajiye wayar a gefe, Cikin yan mintuna sai ga hawaye na zubowa gefen idanunta. Tabbas ta yi kewarsa, tana kan yi kuma, Kullum sai ta tuna shi, Idan ba shi ba to Noor. A duk sanda ta tuna shi sai taji ina ma ta tashi ta bi shi, ina ma bata dawo ƙasar nan ba, Ina ma ƙaddara bata rabata dashi ba, Har yanzu bata daina sonsa ba. Kamar yanda ta san shi ma bai daina sonta ba, Kawai dai yana ƙoƙarin mantawa da ita ne. Haka ta dinga tunanin sa a wajen tana sake-sake a zuciyarta, Can kuma ta ɗauki wayar kamar wadda aka yi wa dole haka ta hau dialing numbern sa. Ganin har ta katse bai ɗauka ba ya sanyata ajiye wayar, wasu zafafan hawaye suka ci gaba da zubowa kan fuskarta. Daga karshe ma tashi ta yi ta fice daga ɗakin ta koma nata.
****
New York.
Nana na zaune kan sofa tana kallon tv kasancewar ranar Saturday ne babu lecture taji wayarsa na ringing, amma har ta katse bata tashi a inda take ba. Tunawa ta yi da chocolate ɗin ta ta jiya da suka siyo ta miƙe ta nufi cikin ɗakin ta, Ledar gaba ɗaya ta dauko ta dawo parlour, Samu wayar ta yi tana ci gaba da ringing. Ta ajiye ledar kan kujera sannan ta nufi inda wayar take, Kafin ta ɗauka ta katse, Ta ɗan yi tsaki sai kuma ta koma ta zauna da wayar a hannunta, kasancewar ta san password ɗin ya sanya ta cire dan ganin wanda yake kira. Koda ta shiga call log ɗin sunan Buddy ta gani a sama, Ta taɓe baki tana ƙoƙarin ajiye wayar idanunta ya sauka akan sunan dake ƙasan na Aliyun.
“Zahra!”
Ta faɗa a fili tana sake ware idanun ta kan screen ɗin, Mamaki ne ya kusan kasheta, Duk da ta san da ba haka ya yi saving numbernta ba. Amma ta san bashi da wata mai irin sunan, Dan haka ta danna kira dan ganin wacece. Har ta gama ringing ba'a ɗauka ba, Tayi kamar ta ajiye wayar sai kuma ta sake danna kiran, Sai da ta kusan katsewa sannan aka ɗaga, Daga ɗaya bangare Zahra ta ce
“Hello, Salamu alaikum.”
Wani irin abu ne ya zo ya tokarewa Nana a ƙijri, Ta kasa koda haɗiyar yawu, Jin ba'a yi magana ba ya sanya Zahra ta yi ƙasa da murya ta ce
“Docco... Doctor!”
“Algunguma! Muguwa azzaluma, mai kashe mutane! Uban me yasa ki ke kiran sa? Me zai miki? Ko shi ma kashe shin zaki yi? To wallahi Uncle yafi karfin ki! Banza kawai, Dangin masu kisa!”
Da mugun mamaki Zahra ke sauraren kalaman Nanar, Dan bata yi tunanin ita ce ta ɗaga wayar ba, Ta kasa cewa komai tana jin wani irin zafi a zuciyarta. Cike da masifa Nana ta ci gaba da faɗin
“Na rantse duk ranar da ki ka sake kiran mijina sai na yi miki abin da ba zaki manta dani ba! Banza kawai masu kashe mutane! Dangin da babu Allah a ransu!”
“Nana!”
Ya kira sunanta a tsawace. Kallon sa ta yi ganin yanda ya yi tsaye a wajen yana kallonta da mamaki, Kafin ya ƙaraso ya karɓe wayar yana faɗin
“Ke dawa? Wa ki ke zagi haka?”
Ƙoƙarin fizge wayar ta fara yi tana cewa
“ni ka bani, Ka bani na zageta! Kwartuwa mai kiran mazajen mutane!”
Wata irin tsawa ya daka mata wadda ta sanyata shiga cikin hankalinta, Ta tsaya tana kallon sa. Sai a sannan ya kalli screen ɗin ya ga sunan wadda ke kiran, Bai ce komai ba ya juya ya bar wajen da wayar a hannunsa. Nana ta dinga bin sa da kallo kamar wata zararriya, Tama kasa gane abin da ya yi. Shi ko cikin ɗakin ya koma sannan ya kai wayar kunne muryarsa a nutse ya ce
“Zahra lafiya dai ki ka kirani?”
Zahra da taji wani irin abu ya tsaya mata a ƙirji ta kasa magana, Sai shessheƙar kuka da take. Ya gyara tsaiwarsa ya ce
“Subhanallahi lafiya dai? Ko wani abun ya faru?”
Girgiza masa kai ta yi tana ƙoƙarin ɓoye kukanta ta ce
“Doctor ba komai, kawai kiran ka nayi na gaishe ka”
Ta ƙare maganar hawaye na yar rige-rigen sauka kan fuskarta. Jinjina kansa ya yi dan yana da fahimta ya ce
“Allah sarki to ya ku ke? Ya Umma?”
“Tana nan kalau"
Ta bashi amsa a sanyaye, Ya gyaɗa kansa kafin ya ce
“To ki gaishe min da ita. Na gode, Sai an jima”
Ji ta yi kamar kar ya katse wayar, Amma ta dake ta ce
“Tom in sha Allah, Na gode.”
Daga haka ta kashe wayar. Ajiyar zuciya Abdusammad ya sauke sannan ya girgiza kansa, Ya zura wayar cikin aljihun trousern da ke jikinsa sannan ya fito daga ɗakin. Durƙushe ya samu Nana a wajen sai kuka take, Ya yi kamar ya wuce sai kuma ya nufi inda take. Tsayawa ya yi a gabanta yana kallonta fuska babu walwala ya ce
“And this should be the last time da za'a kirani a waya ki ɗauka, Koma wane kar ki sake ɗaga min waya. Sannan kada ki sake zagin wani tun da bake ya kira ba, Bana son tashin hankali. Ki nutsu ki kama kan ki! Idan ba haka ba sai na ɓata miki fiye da tunanin ki wallahi!”
Ya ƙare maganar a ɗan zafafe, Ita dai ko ɗago kanta bata yi ba, Ya ja tsaki sannan ya juya ya fice daga parlon. Sai a sannan ta ɗago idanun ta wanda suka yi jajur, Ta kalli hanyar ƙofar sai kuma ta fashe da wani raunataccen kuka.
08106608363
Nanameera.*Page 70.*
Yinin ranar Nana a ɗaki ta yi shi ko parlourn ƙasa bata sakko ba, Shi ma bai sake shiga harkarta ba har dare. Around 9pm ya shigo ɗakin cikin shigarsa ta ƙananun kaya hannunsa na dama riƙe da wayarsa yana dannawa, Tana kwance kan gado ta yi nisa cikin tunanin da take. Ya tsaya gefen gadon ya zura wayar a aljihu yana kallon ta ya ce
“Ki tashi ki ci abinci”
Ko daga kanta bata yi ba ballantana ya saka ran zata kula shi, Ya ɗan yi jim kafin ya sake cewa
“Nana baki ji bane? Tashi nace!”
A fusace ta tashi zaune tana kallon sa tana huci ta ce
“To ba zan ci ba ɗin, Ina ruwanka dani ko dole sai na...”
Saukar marin da taji ya sanyata haɗiye ragowar maganar tata, Ta sanya hannunta na hagu ta dafe kuncin daya mara tana kallon sa, Kuka take son yi amma ta kasa. Fuskarsa a haɗe babu alamar wasa ya ce
“Duk ranar da bakin ki ya sake kuskuren ɗaga min murya sai kin gwammace baki sanni ba!”