Sashe 58
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya amsa kamar zai yi kuka. Numfasawa Abba ya yi ya sake buɗe idanunsa akansa, a hankali kuma ya kai hannunsa na hagu wanda aka maƙala masa canola ya shafa fuskarsa yana murmushi ya ce
“karka damu kaji, I'm fine”
“you are not Abba. Kalleka fa, baka da lafiya Abba, dan Allah ka daina damuwa kaji. I'm promise, I already promised cewa zan dawo da Nana. Zata dawo gida Abba!”
Ya yi maganar hawaye na kawowa cikin idanunsa.
Lumshe idanu Abba ya yi wanda ya bawa hawayen dake cikin idanunsa damar sakkowa kan fuskarsa, ya girgiza kansa a sanyaye ya ce
“bana son ganin Nana Abdul. Bana son ta dawo, just leave her, bana son na sake ganinta har abada!”
Da wani irin mamaki Abdusammad ke kallonsa, lokaci ɗaya ya shiga girgiza kansa kafin ya ce
“a'a Abba. A'a, zaka sake ganinta, zata dawo gida. Komai zai shige kamar bai faru ba”
Shiru Abba ya yi yana kallon gefe, dan ko kaɗan baya son magana akan Nana. Idan ya tuna ta zuciyarsa zafi take masa, dan haka ya fawallawa Allah komai zai kuma manta da ita, duk da ya san hakan ba ƙaramin abu bane.
A tare suka shigo ɗakin bakinsu ɗauke da sallama, Abdusammad ya amsa a sanyaye dan babu lallai ma sun ji. Papa ne ya tsaya a gefensa a sanyaye ya ce
“Ahmad!”
Ɗago kansa ya yi ya kalleshi sai kuma ya sakar masa murmushi, Papa mai yi mamakin haka ba dan ya san halin Abba, da wuya ka gane halin da yake ciki. Da wuya ka gane asirin zuciyarsa, duk abin da ya kai shi ga barin a gane damuwarsa to ba ƙaramin abu bane, yana da zurfin ciki fiye da tunani, wannan dalilin ya sanya Nana ta yi gadonsa. Baka taɓa jin damuwarsu cikin sauƙi.
Murmushin Papa ya mayar masa kafin ya ce
“stop pretending Ahmad, ya jikin naka?”
Lumshe idanunsa ya yi ya buɗe ya ce“Alhamdulillahi”
Papa ya jinjina kansa sannan ya ce“Allah ya ƙara sauƙi, ya kuma kiyaye gaba”
Amin duka suka ce. Sannan suka yi masa ya jiki suma, ya amsa a sanyaye.
Kallon Sultan ya yi wanda ke tsaye kusa da Hamid ya ce
“Sultan zamu iya tafiya gida ko?”
Girgiza kai ya yi ya ce“a'a Abba. Har yanzu baka da lafiya fa, kawai kana daurewa ne, ba za'a iya sallamarka ba”
Abdusammad ya jinjina kai ya ce“Eh. Sai ka samu sauƙi sosai Abba”
Shiru Abba ya yi yana kallonsu sai kuma ya ce
“Alright but you have to go, Kun bar matayenku a gida”
Girgiza kai Hamid ya yi ya ce“idan muka tafi kai fa Abba?”
Murmushi kawai ya yi sai kuma ya ce“ba komai. Ku je kawai”
Girgiza kai Abdusammad ya yi ya ce
“A'a ku kawai ku tafi. Zan zauna dashi”
Da sauri Abba ya kalleshi sai kuma ya girgiza kansa ya ce“a'a ku je duka”
Shiru Abdusammad ya yi dan ba tafiyar zai ba. Papa ya ce su tafin tun da jikinsa da sauki, suka yi masa sallama sannan suka tafi.
A can estate kuwa, Amma ce zaune gefen gado Aunty Ramlah na gefenta sai kuka take ƙasa-ƙasa. Aunty Ramlah ta sauke numfashi sannan ta ce
“Dan Allah Yaya ki yi haƙuri. Kaddara ce kuma ta riga da ta faru, babu wanda zai sauya hakan, ki yi haƙuri kin ji”
Cikin kuka Amma ta ce
“Ya zan yi na yi haƙuri Ramlah? Nana fa bata nan. Kuma kin ga hotunan da ake dangatawa da ita, har mahaifinta ya yarda. Ya za'a yi na samu natsuwa, ina so naga Nana, ina son na tambayeta ta faɗa min gaskiya”
Dafata Aunty Ramlah ta yi tana jin wani irin tausayin ƴar uwar tata ta ce“ki yi haƙuri Yaya. Na sani abu ne mai wahalar yarda amma ki sani duk abin da ki ka ji ko kika gani to gaskiya, don nima kaina na san yaron”
Da sauri Amma ta kalleta sai kuma ta riƙe hannayenta duk biyun cikin kuka ta ce
“Da gaske? Kin san shi Ramlah?”
Gyaɗa mata kai Aunty Rahmah ta yi. Amma ta matse hannayenta ta ce
“to kai ni wajensa dan Allah, kai ni na tambayeshi meyasa zai yiwa Nana haka. Kai ni na tambayeshi ina ƴata take!”
Kasa masa Aunty Ramlah ta yi sai kuka da take a hankali, ta rungumeta cikin shessheƙar kuka ta ce
“Ki yi shiru Yaya, in sha Allah komai zai shige”
Amma bata sake cewa komai ba sai kuka da take a hankali.
****
No. 045 Sultan road,
Kano State.
A hankali ta tura ƙofar ɗakin bakinta ɗauke da sallama, Zaune ta same su gefen gado. Ta ƙarasa ciki tana kallonsu, Babbar mata ce da zata yi kaiwa 50 to above ɗin nan, fara mai ɗan jiki. Ta zauna ɗan nesa dasu har sannan idanunta na kan su,ganin yanda suka riƙe hannun juna sai kuka suke a tare. Ta ɗan numfasa sannan ta ce
“Nana”
A hankali ta ɗago idanunta ta kalleta, Mami ta yi mata alamar da ta zo da hannu, ta saki hannun Khadijah sannan ta tashi a hankali ta ƙarasa gabanta. Zama ta yi gefenta, Mami ta jata ta rungumeta tana shafa kanta, Ji tayi kamar a jikin Amma take dan haka ta sake fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Mami ta yi shiru ba tare da ta hanata ba. Khadijah sai kallonsu take tana kukan itama.
Above 5mins kafin ta ɗago kanta jin har sannan bata daina kukan ba, ta goge mata hawayen duk da wasu basu bar zuba ba ta ce
“Ya isa haka Nana. Kar wani abun ya sameki”
Sake shigewa jikinta ta yi cikin kuka ta ce
“Mami Ammata, Abbana.”
Sosai ta bawa Mami tausayi dan tun da ta zo babu abin da take cewa daya shige wannan. Ta shafa kanta a sanyaye ta ce
“Zaki koma kin ji, zasu ganki”
Girgiza kanta ta dinga yi tana cewa
“A'a Mami, ba zan iya ba. Ba zan iya komawa wajensu ba, na tozarta Abbana! Na wulaƙantashi gaban mutane, na san yana can hankalinsa a tashe. Gara na mutu Mami! So nake na mutu!”
Ta ƙare maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan. Kasa cewa komai Mami ta yi, dan ta san ko ta faɗa mata ba zata fahimta ba yanzu. Ita kanta bata ji daɗin guduwar da ta yi ba, sai dai idan ta tuna abin da ta faɗa mata sai taji sam bata da nutsuwa. Sai taji gara da ta bar gidan akan rashin son aure da ace an fitar da irin hotunan wanda zasu iya tarwatsa zuciyar duk wata uwa ko uba. Ganin ta fara rage kukan yasa ta ɗagota ta ce
“Ya isa haka tashi ki ci abinci sai ki kwanta” girgiza kanta ta yi ta ce“na ƙoshi Mami”
Mami ta yi shiru tana kallonta,can kuma ta mike tana kallon Khadijah ta ce“zo ki karɓar muku abinci” a sanyaye ta ce to sannan Mami ta fita. Ta tashi ta dawo gefen Nana ta riƙe hannunta cikin kuka ta ce
“Nana ki daina kuka kinji. In sha Allahu sai Allah ya saka miki”
Tari ta fara yi tana dafe saitin zuciyarta, lokaci ɗaya ta nemi fita daga hayyacinta. Da gudu Khadijah ta tashi ta fita tana kwalawa Mami kira, Mami dake tsaye a corridor ita da Adeel ta kalleta da mamaki ta ce
“Mimi lafiya?”
Girgiza kanta ta yi tana nuna mata hanyar dakin ta ce“Nana! Nana Mami”
Da sauri Mami ta yi hanyar ɗakin, Khadijah ta jawo Adeel da ke tsaye ta ce“Yaya zo muje kai ma”
Bai mata musu ba ya bi bayanta suka nufi ɗakin.
Tsaye suka tarar da Mami gabanta ta riƙeta ganin yanda take aman jini, suna shigowa ta kalleshi hankali tashe ta ce“Adeel zo ka ɗauketa mu kaita asibiti”
Shi kansa sai da hankalinsa ya tashi, ya dinga kallonta ganin how weak she's yasa ya ƙaraso ya ɗauketa sannan ya yi waje da ita da sauri.
****
Washegari da sassafe around 8:00 Aunty Khadijah ta shigo parlon, zaune ta samu Zahra ta zuba uban tagumi. Kayan jiya ne a jikinta. Ta ƙarasa ta zauna kujerar dake facing tata tana kallonta ganin yanda ta fice hayyacinta, gaba ɗaya ta zama kamar ba ita ba, fuskarta ta wani irin zugewa. Idanunta sun kumbura, har wata ramar tashin hankali ta yi daga jiya zuwa yau, musamman daya kasance babu kowa a gidan dan tun jiya take zaune jiran Abdusammad ya shigo amma babu shi babu alamarsa. Noor kuma tana apartment ɗin Hajiya Babba. Numfasawa Aunty Khadijah ta sai kuma ta girgiza kanta ta ce
“Zahra! Zahra!”
Shiru babu amsa, dan babu alamar ma taji shigowarta. Dan haka ta taso ta dawo inda take ta zauna sannan ta ɗan jijjigata ta ce
“Zahraaa!”
A firgice ta kalleta, sai kuma ta sauke numfashi ta ce
“Aunty”
Kallonta Aunty Khadijah ta yi ganin duk ta birkice kanta ta ce
“mene ne haka? Ba cewa nayi ki bar damuwa ba?”
Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da fingers ɗinta lokaci ɗaya kuma wani kuka ya tawo mata, ta dinga rerashi ba tare da ta ce komai ba.
Kusan mintuna biyar kafin Aunty Khadijah ta ce
“yanzu kukan za ki ci gaba ko kuma shiru zaki yi mu san abin yi?”
Kallonta Zahra ta yi sai kuma ta fara share hawayenta da hannunta ta ce“na kasa haƙura ne aunty. Zuciyata ta kasa jurewa, ji nake kamar ba gaske ba, ji nake kamar zuciyata zata fito daga ƙirjina. Ya zan yi aunty?”
Dafata Aunty Khadijah ta yi sai kuma ta ce
“Dole akwai abin da zamu yi. Ba dai yarinyar bata gidan nan ba yanzu?"
Gyaɗa mata kai Zahra ta yi, ta numfasa ta ce
“To ba zamu bari ta dawo ba. Ta tafi kenan!”
Da mamaki Zahra ke kallonta sai kuma ta ce
“amma Aunty ban fahimceki ba.”
Dan murmushi Aunty Khadijah ta yi ta ce
“Cewa nayi ba zata dawo gidan nan ba. Koma ina ta tafi ba zamu bari ta dawo ba, ballantana har ta tare a matsayin kishiyarki”
Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“ni dai babu ruwana Aunty, kada ki saka a yi mata wani abun. Babu ruwana wallahi!”
Tsaki Aunty Khadijah ta yi ta miƙe tsaye tana kallonta ta ce