← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 125

Sashe 19

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ƙare maganar tana ƙoƙarin janye hannun Amrah daga jikin Nana, tureta Nana ta yi tana faɗin"Eh na faɗa ɗin, ko ba banzar bace? Ai duk wanda ya ga abin da ki ka yi zai tabbatar da cewa ke banza ce, irin banzar ma da bata san abin da take ba! Saboda haka..."

Cikin zafin nama Amrah ta sauke mata mari a kuncinta na dama, wanda ya sanya ta yi shiru ba tare da ta ƙarasa maganar data fara ba, ta ɗora hannunta kan fuskarta tana faɗin "ni ki ka mara?"

Amrah ta ɗora hannunta a ƙugu tana faɗin "an mare kin ko zaki..."

Ko gama maganar bata yi ba Nana ta sauke mata wani lafiyayyen mari itama. Da sauri Maimoon ta rufe bakinta da hannunta tana kallon Nana da ke faman huci kamar ƴar damisa, Amrah ta dafe kumatunta tana gyaɗa kai, kwafa ta yi kafin ta yi wani kukan kura ta janyo Nanar ta shaƙeta tana faɗin

"Ni zaki mara? Ni sa'arki ce! Ko dan kin ga ina miki wasa?"

Ita dai Maimoon tsayawa ta yi a wajen tana kallonsu tana girgiza kai, ganin da gaske faɗa suke ya sanya ta ƙarasa tana ƙoƙarin janye Nana da ke kai mata duka ta ko ina ta ce"ke Nana sai na faɗawa Abbanki ba zaki bari ba!"

Hannayenta biyu ta sanya ta ingiza Maimoon tana faɗin "dallah can rabu dani!"

Daga haka ta mai da hankalinta kan faɗan da suke.

"Ke!! Kee!!"

Safwan ya yi maganar yana ƙarasowa wajen, da mamaki ya dinga kallonsu kafin ya janye Nana da sauri a ɗan tsawace ya ce"mene haka? Ba zaku bari ba!"

"Ni rabu dani, ba zan bari ba ɗin, wallahi ba zan bari ba!"

Nana ta yi maganar tana ƙoƙarin sake jawo Amrah, daka mata tsawa Safwan ya yi, kawai sai ta fashe da kuka ta juya ta bar wajen tana ihu kamar wadda aka daka. Da idanu ya dinga bin ta har ta sha kwana kafin ya dawo da idanunsa kan Amrah rai ɓace ya ce"mene ne haka Amrah? Da hankalinki?"

Cikin shassheƙar kuka ta ce"wallahi Yaya bata da kunya ne, marina fa tayi"

"Mari kuma?"

Safwan ya faɗa da matuƙar mamaki. Gyaɗa masa kai kawai ta yi tana ci gaba da shessheƙar kukanta, ajiyar zuciya ya sauke kafin y ce"to ki yi haƙuri kin ji, kar ki ɗaga maganar dan Allah" sake gyaɗa masa kai ta yi ya kalli Maimoon ya ce"ke kuma kina kallonsu ba zaki raba su ba?"

Marairaice fuska ta yi ta ce"Yaya nima fa tureni suka yi" taɓe baki ya yi sai kuma ya juya ya bar wajen ba tare da ya sake cewa komai. Ƙarasowa gabanta ta yi ta riƙe hannunta tana faɗin "ki yi haƙuri kin ji, zo mu tafi"

Fizge hannunta ta yi ta ce"rabu dani wallahi ba zan yarda ba na rantse da Allah!"

Da mamaki Maimoon ta ce"to sake kamata za ki yi da kokawar? Kina dai gani tafi ƙarfinki, ji yanda ta yakushe miki fuska"

Sai a sannan Amrah ta kai hannunta gefen fuskarta ta taɓa, jini ta gani a hannunta ta sake fashewa da kuka tana fadin"shegiya mayya, na rantse ba zan yarda ba sai naje na faɗawa Abba"

Girgiza kai Maimoon ta yi ta ce"ke kar ki yi haka, kin dai san halin Abba ko? Ki yi haƙuri kawai" tsaki Amrah zaka ta yi ta juya ta bar wajen kamar zata tashi sama. Numfashi Maimoon ta sauke sannan ta nufi hanyar gidansu da sauri dan daman ba'a san ta fito ba.

****
Amma ta kafeta da idanu ta ce"ba magana nake da ke ba?" shiru ta yi tana sake murza hannunta dake kan idanunta, a tsawace ta ce"ba zaki faɗa min da wanda ki ka yi faɗa ba Nana har ki ka yi squeezing da kayanki haka?" Cikin shessheƙar kuka ta ce"babu kowa fa" daga haka ta nufi daƙinta da sauri. Da idanu kawai Amma ta bita sai kuma ta girgiza kanta dan tasan ƙarya take ta ce babu kowa dole faɗa ta yi da wani. Komawa ta yi ta zauna tana jiran ta fito ta sake tambayarta.

Ƙarfe 6:30 na yamma ta fito tana sanye da hijabi, ko gida bata shiga ba tun bayan abin da ya faru dan ta san Mami ba zata barta ta fito ba. Dan haka ta yi zamanta a Apartment ɗin Hajiya Babba har yammar ta yi. Ta kusa apartment ɗin su Nana ta gamu da Hamida tana tafe sanye da hijabi har ƙasa, ta dinga kallonta sai kuma ta ce"Amrah lafiya? Me ya sami fuskarki?"

"Babu komai"

Ta ce a takaice sai kuma ta yi gaba abin ta, Hamida ta sake juyawa tana kallonta kafin ta numfashi ta ce"Allah ya kyauta" daga haka ta juya ta ci gaba da tafiyarta. Cikin Sa'a ta tarar da motar Abba a compound ɗin gidan da alama dawowarsa kenan daga wajen aiki, Amrah ta ja ta tsaya a balcony jar ya fito ya nufo wajen, yana zuwa gabanta ta durƙusa har ƙasa murya a sanyaye ta ce"Abba sannu da zuwa" fuska a sake ya ce"Yauwa Mamana sannunki" daga haka ya juya zai ci gaba da tafiya, da sauri ta ce"Abba!" Cak ya tsaya ya juyo yana kallonta ya ce"lafiya dai?" sai a sannan ya lura da fuskarta ya sake cewa"subhanallahi, meya sami fuskarki haka?" madadin ta bashi amsa sai kawai ta fashe da kuka tana murza idanunta, ya girgiza kansa yana faɗin"faɗi mene ne bana son kukan nan" cikin shessheƙar kuka ta ce"Abba Nana ce ta mareni" da wani irin mabayyanin mamaki ya dinga kallonta kafin ya ce"wace Nanar?"

"Nana dai, kawai dan nayi mata magana shi ne ta dinga zagina ta ce min banza mahaukaciya, wai bana son iyayena bana ganin girmansu, kuma Daddyna talaka ne bashi da komai, Abbanta yafi kuɗi, shi ne dan na mareta ta rama, kuma ta kama ni da kokawa ta dinga dukana har sai da ta yakushe min fuska"

Amrah ta ƙare maganar tana wani irin kuka, Kallonta kawai Abba ya dinga yi fuskarsa ta sauya kala daga fara zuwa ja, jijiyoyin kansa sun firfito ko ba'a faɗa maka ba kasan ransa ya yi masifar ɓaci.. Bai ce mata komai ba ya juya ya nufi cikin gidan da sauri, Amrah tana ganin ya shiga ta sauke hijabinta tana murmushi a fili ta ce"yauwa! Yau na nasan sai kin gane kurenki yarinya!" Daga haka ta bar wajen ranta fes.

"Nana! Nana! Nana!"

Abba ya dinga kiran sunanta yana tsaye a tsakiyar parlon, Tashi Amma ta yi tana kallonsa ganin yanda fuskarsa take a ɓace ta ce"lafiya dai yallaɓai?"

"Ina Nana take?"

Ya tambayeta a fusace, da hannu ta nuna masa daƙinta ya yi gaba da sauri ya bar ta tsaye a wajen. Tana zaune a gefen gadonta hannunta riƙe da wayarta tana game ya turo ƙofar ya shigo, da sauri ta ɗaga idanunta tana kallonsa ganin yanda ya shigo a fusace yasa ta ce"sannu da zuwa Abba..."

Ko rufe bakinta bata yi ba ya sauke mata wani zazzafan mari har sai da ta tafi ta faɗi ƙasa, ihu ta saki wanda ya yi dai dai da shigowar Amma, ya ƙarasa ya fincikota yana mata wani irin kallo ya ce"wato kin dawo da halin ki ko? Wane sa'anki a cikinsu da har zaki dinga faɗa dasu? Har ki iya zaginta, sannan bayan ita ki iya haɗawa da babanta! Yaushe ki ka dawo da wannan mummunar ɗabi'ar taki?!"

Tafa hannaye Amma ta shiga yi tana salati kafin ta ce"ni daman na san tun da na gan ta ta shigo a birkice to magana ta dauko ashe kuwa haka ne, da wa ta yi faɗa kuma?"

Abba bai tsaya bata amsa ba ya zare belt ya dinga dukan Nana kamar Allah ya ai ko shi, ban da ihu babu abin da take, ta dinga kiran sunan Amma ta taimaketa amma ta mata banza. Sai da ya yi mata lilis sannan ya wurgar da belt ɗin yana kallonta ya ce"daga yau ko kallon banza ki ka sake wa wani wanda ya girmeki a cikin gidan nan zaki ga yanda zan yi dake!"

Daga haka ya juya ya fice daga ɗakin rai ɓace. Amma ta tsaya a wajen tana kallonta ganin yanda take kuka, duk ta fice hayyacinta dan ba ƙaramin duka ya yi mata ba, ta sauke numfashi sai kuma ta juya ta bar ɗakin..

Tsaye ta same shi a ɗakinsa ya dafa study table, ta ƙarasa ta tsaya daga bayansa tana kallonsa a sanyaye ta ce"amma yallaɓai dukan nan bai yi yawa ba? She's too small fa, beside ma kasan ba lafiya ne da ita cikakke ba!"

Kamar ba zai magana ba sai kuma ya juyo yana kallonta da idanunsa wanda suka yi jajur ya ce"kenan na barta ta dinga dauko mana magana? kin san wannan faɗace- faɗacen nata shi ne dalilin daya sanya na kai ta boarding school ba, to akan me zan bari ta dawo ta ɗora daga inda ta tsaya. Amrah fa mara! Sa'arta ce?"

Numfasawa Amma ta yi kafin ta ce"haka ne, amma dai bai kamata ka mata irin wannan dukan ba gaskiya, nayi shiru ne kawai saboda a gabanta ne, da ba zan barka ba wallahi, ka dinga tunawa da ita kaɗai muke da, duk abin da ya sameta mu ne a ciki!"

Ta ƙare maganar jiki a sanyaye, Abba kallonta kawai ya dinga yi sai kuma ya juya ya shige toilet ba tare da ya ce komai ba, itama bata damu da rashin maganar tasa ba ta juya ta fice daga ɗakin..
Chapter 19 · 0% Book details