← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 125

Sashe 56

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗauke kansa ya yi yana kallon mutanen dake ta faman kai koma a compound ɗin sannan ya ce“ba zaka fahimta ba” taɓe baki Aliyu ya yi ya ce“da ka fahimtar dani ai” kallonsa kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba. Sultan ya ƙaraso wajen hannunsa riƙe da babbar rigarsa wadda ya daɗe da cirewa. A gefensu ya tsaya jiki a sanyaye ya ce

“Yaya”

Kallonsa Abdusammad ya yi ba tare da ya ce komai ba. Cike da damuwa Sultan ya ce“Yaya Nana fa? A ina za'a ganta?” numfasawa Abdusammad ya yi sai kuma ya dafa kafaɗarsa ya ce“za'a ganta kaji” daga haka ya kalli Aliyu ya ce“bari naje wajen Abba”

“muje tare”

Aliyu ya faɗa yana tattare babbar rigarsa. Ok ya ce sannan ya yi gaba Aliyu ya bi bayansa. Sultan ya jima tsaye kafin ya sauke numfashi ya nufi hanyar apartment ɗinsu.

****
Fitowa ta yi daga kitchen hannunta riƙe da plate tana murmushi ta kalli su Aunty Khadijah dake ta faman dariya ta ce“yau dai murna har kunne” Aunty Khadijah ta gyara zamanta tana kallonta ta ce“ai yau ko bacci ban jin zamu iya. Wannan abu. Kai Allah na gode maka”

Ta ƙare maganar tana ɗaga hannunta sama alamar godiya ga Allah. Murmushi Zahra ta yi bayan ta zauna ta ce“amma tafiya zaku yi ko? Tun da kun ga yanzu ku surukai ne” jinjina kai Siyama ta yi ta ce“eh fa Aunty. Gara mu tafi, to amma ke naga baki damu ba”

Taɓe baki Zahra ta yi ta ce“akan me zan damu to? Yarinyar da aka aura masa bagidajiya ce, ke bayan haka ma anan zata zauna mu kuma US zamu koma. To kin ga ba zan kirata kishiyata ba ai”

Gyaɗa kansu suka yi sai kuma Aunty Khadijah ta dafata ta ce“koma tare zamu zauna ai ba zamu bari ta yi nasara akan ki ba. Mu da muke da malamai” shiru Zahra ta yi can kuma ta janye hannunta daga jikinta ta ce“a'a Aunty ni babu ruwana da bin malamai ko bokaye. Kawai dai na san ba zata zama kishiyata ba” ta ƙare maganar tana haɗe rai. Murmushi kawai Aunty Khadijah ta yi dan ita yanzu bata da wata damuwa. Safeena da ke zaune tun ɗazu ba tare da ta ce komai ba saboda takaici ta miƙe tana ɗaukan jakarta ta ce“ni zan yi gaba”

“ba zaki bari mu tafi tare ba?”

Amal ta tambayeta da mamaki. Gyaɗa mata kai Safeena ta yi fuska babu walwala ta ce“a'a tafiya zan yi, ni ba zan zauna ba” daga haka ta juya ta nufi hanyar fita daga parlon. Taɓe baki Siyama ta yi ta ce“ni na rasa abun da ke damunta wallahi.” Aunty Khadijah ta bita da harara sannan ta ce“Allah ya raka taki gona”

Suka tuntsire da dariya a tare. Ban da Zahra wadda lokaci ɗaya taji lamarin auren ya dameta.

****
Tura ƙofar ɗakin ya yi bakinsa ɗauke da sallama, cikin tashin hankali ya ƙarasa gaban gadon ya dafashi yana faɗin

“Subhanallahi. Abba! Abba!”

Ya ɗago shi ya jingina shi da jikinsa, ban da tari babu abin da Abba ke yi, idanunsa a rufe jikinsa sai wani irin rawa yake. Aliyu ya ƙaraso ciki hankali tashe ya ce

“mene ne? Me ya same sa?”

Girgiza kai ya yi bayan ya miƙe riƙe dashi ya ce“i don't know bari muje asibiti” daga haka ya fice daga parlon da sauri. Aliyu ya dafe kansa a sanyaye ya ce“Ya Allah” sannan yabi bayansu da sauri.

A hankali ta fara buɗe idanunta wanda suka yi mata nauyi, ta dinga kallon ɗakin da take kwance, Lokaci ɗaya kuma ta tashi zaune a ɗan firgice. Da sauri Mama ta riƙeta tana faɗin

“kin tashi”

Amma ta dinga kallonta, can kuma ta saki wani kuka tana fadin “Mama Nana, me ya sa Nana zata yi haka? Wane ne wanda ta yarda dashi haka! Mama zuciyata zafi take min. Innalil lahi wa ina ilayhi raji'una”

Amma ta yi maganar tana sake rushewa da wani kukan. Sake riƙeta Mama ta yi cike da tausayinta ta ce“yi haƙuri Rabi'ah, ki yi haƙuri dan Allah” cikin kuka ta kalli Mama ta ce“to ina take? Yanzu shikenan ba zata yi aure ba? Babu wanda zai aureta. Wallahi ban bar Nana tana fita ban sani ba, ban santa da yawo ba, ban san yaushe haka ta faru ba. Iya kar ƙoƙarina ina yi akan tarbiyyarta. amma me yasa? me ya sa zata yi mana haka? Me yasa zata yi fatali da tarbiyyar da muka bata..”

Mama ta yi shiru tana sauraren sautin kukanta. Ta san tabbas ba ƙaramin abu ne, ba abu ne wanda zuciya zata iya dauka ba, ace yarka daka haifa aka samu da irin wannan ƙazaman hotunan. Garin ya ya? wane ya yaudari Nana har ta yarda dashi haka?. Mama ta sauke numfashi sai kuma ta mai da idanunta kan Amma a sanyaye ta ce

“ki bar zubar da hawayenki, domin shi ɗin masifa ne gareta. Addu'a zaki yi mata, kuma ki yi mata fatan Alkhairi”

Amma ta jinjina kanta wasu hawayen na sake zubowa ta ce“ina son na ganta. Ina son naga Nana Mama, ina so na tambayeta meyasa ta yiwa rayuwarta haka? ina son ta faɗa min dalilinta na tafiya ta bar mu. Ina son na ganta Mama...” ta sake fashewa da wani raunataccen kukan tana ɗora kanta a cinyar Mama. Kasa cewa komai ta yi dan tasan dole ta yi kuka, ta dinga shafa bayanta a hankali.

****
Ana kiran sallar la'asar Ummi ta shigo ɗakin, ta dinga kallonta ganin yanda take kuka kamar ranta zai fita. Tun bayan da aka gama ɗaurin aure bata yi shiru ba, dan haka ta saki ƙofar ta ƙarasa ciki tana ci gaba da kallonta. Zama ta yi gefen gadon ta riƙo hannayenta a sanyaye ta ce

“Maimoon”

Ɗago kanta ta yi a hankali tana kallon Ummi, gaba ɗaya idanunta sun kumbura sun yi jajur dasu. Har wani janyewa sukayi saboda azabar kuka, Ummi ta girgiza kanta sai kuma ta shiga share mata hawayen tana faɗin

“kukan ne har yanzu? me ki ke wa kuka kuma?”

Samun kanta ta yi da faɗawa jikin Ummin ta sake fashewa da wani sabon kukan, Ummi ta dinga kallonta ba tare da ta ce komai ba. Above 5mins kafin ta fara rage sautin kukan dan kanta. Sai a sannan Ummi ta ɗagota tana murmushi ta ce “Shikenan ya isa haka, ki tashi ki yi wanka ki ci abinci, sai ki je apartment ɗin Hajiya Babba”

Gyaɗa mata kai kawai Maimoon ta yi dan ita sam ba wannan ne ya dameta ba. Ummi ta tashi tana cewa“bari na kawo miki abincin” da sauri ta mike ita ma tana ƙoƙarin yafa mayafinta ta ce“a'a zan je gurin Hajiya Babba” Ummi ta yi shiru can kuma ta ce“abincin fa?”

“na ƙoshi”

Ta ce a sanyaye. Ummi bata sake cewa komai ba barta ta fita, dan ta san daman ba lallai bane ta iya cin abincin a sannan.

Tafiya ta dinga yi tana kuka, ta rufe fuskarta da mayafin kanta ko gabanta bata gani. Ji ta yi an riƙeta tayi saurin ɗago kanta ba tare da ta buɗe idanun nata ba, Aliyu ya dinga kallonta ganin tana shirin faɗuwa. Hannunsa ya sanya ya janye mayafin ya dawo goshinta, sai a sannan ta kalli fuskarsa, ta yi saurin sunkuyar da kanta. Kallonta ya dinga yi can kuma ya ce

“ki kula kar ki faɗi”

Gyada masa kai kawai ta yi ya saketa ta yi gaba da sauri. Da idanu kawai ya bita sai kuma ya juya ya nufi inda ya yi parking motarsa dan komawa asibitin.

Ta ƙofar wajen kitchen ta shiga gudun kada ta haɗu da mutane, sai dai ga mamakinta Safwan ta gani tsaye a wajen ya jingina da jikin flowers da alama tunani yake yi. Ta dinga kallonsa cike da tsana sai kuma ta juya zata bar wajen, kamar daga sama taji ya ce

“Maimoon!”

Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba, ya ƙaraso gabanta ya tsaya ba tare da ya ce komai. Ganin mintuna biyu sun shuɗe bai yi magana ba ya sanya ta ratsa ta gefen shi zata shige, ya yi saurin riƙe hannunta kafin ya ce

“Wait pls!”

Tsayawa ta yi har sannan bata kalleshi ba, ya numfasa sannan ya ce“na san zaki ce ban yi dai dai ba. Wallahi babu yanda na iya ne Maimoon, ban so na faɗawa kowa ba, amma ina son Siyama, ina son na aureta. Ba zan iya bari na rasata ba, kin ga...”

“Ya isa haka Ya Safwan! Ya isa!”

Maimoon ta faɗa a mugun tsawace, wanda ya tilasta shi yin shiru ba tare da ya gama faɗar abin da ke bakinsa ba. Ta dinga wani irin huci hawaye na zubowa kan farar fuskarta, lokaci ɗaya kuma ta cakumeshi cikin ɓacin rai ta fara faɗin

“Kai mugu ne! Kai azzalumi ne Yaya Safwan! Ka cuceta. Ka cuci rayuwarta! Wallahi ko wanda ya sanya aka yi hotunan na bai kai ka lefi ba. Akan me zaka yaudareta? Akan me zaka sa ta bar gida? Akan me zaka yi mata alƙawarin rufe sirrinta sannan kuma ka buɗashi a gaban kowa? Me ya sa zaka tozarta ta?. Me ya sa? Me yasa Yaya Safwan?”

Ta ƙare maganar tana fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi. Kasa magana Safwan ya yi, sai hawaye da yake zubowa daga idanunsa. Har sannan Maimoon na rike da kwalar rigarsa. Suka dinga kuka a tare kamar ƙananun yara, shi kansa bai san dalilin daya sanya ya fito da hotunan ba, dan bai manta alƙawarin da ya yiwa Nana ba. Bai manta sanda ta tsaya a gabansa ba tana kuka ta ce

“Yaya Safwan zan tafi, zan haƙura da komai. Zan bar gidan nan kuma ba zan sake dawowa ba, zan tafi kamar yanda kace, zan ɗorawa kaina laifin cewa ni ce bana son aurenka. Amma dan Allah, dan Annabi kada ka bari kowa ya ga hotunan, ka ƙonasu kamar yanda kace, kada ka bari Abbana ya gani, kada ka bari dan Allah...”
Chapter 56 · 0% Book details