← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 176

Sashe 93

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*_kuna zaton shurun haisam game da lamarin mammina na lafiya ne?_*

*_Fatan alkhairi_*

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 83*
_________________________
https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee*
__________________________

Wani iri nauyi taji yana mamayarta,wani irin abu yana taba zuciyarta.

"Ya aikata kenan" Abinda ta fadi a zuciyarta jikinta yana wani irin sanyi. Hannu tasa ta maida duvet din tana rufe gurin. Kawai sai taji a yau ita ke kunyar akhnan,ba akhnan kawai ba,hatta da jinin kunyarsa taji tana ji. Shi yasa wannan uban zazzabin ya rufeta?,bai kuma kira kowa ko ya yiwa kowa magana azo a taimaka mata ba?.

"Bazaiso ki gani ba....bake ba,kowa ma bazaiso ya gani ba,qilan yanaso ya dawo ya gyara abinsa da kansa ne" Wata zuciyar ta gaya mata saboda sanin haqiqanin halinsa.

Ta sani,tabbas inda yasan zata shigo har dakin taga abun bazai taba fita ko nan da can ba. Ta miqe a hankali jikinta yana wani irin sanyi,tausayin akhnan yana saukar mata. Tasan irin yadda yanayin yake da girma da wahala a gurin kowacce d'iya mace......tasan yanayi ne me radadi qwarai.

Amma kuma ta wani Fannin wani irin sanyi ne yake ratsata,qauna girma da soyayya mara misali ta akhnan tana ratsata.

"Alhamdulillah" Ta fadi can qasan ranta,tabbas safeena tayi haihuwa me kyau.....morsa safiyya tayi halin qwarai da suka iya tsaiwa kan tarbiyyar d'iyarsu har takai budurcinta inda ya kamata a karbeshi.

Batasan me ta nanay ta gani ba,saidai kawai taji kalaman bakinta sun yanke,idanunta ta maida ta lumshe,sai kuma taji muryar nanay din a tausashe tana fadin.

"Sannu giiftii" Sake bude idanun nata tayi tana dubanta,haka kawai sai taji gabanta ya karye da irin kallon da ta gani cikin idanun nanay din. Kallo ne na jin nauyi hade da tausayi,ba irin kallon data gani dazu bane.

"Zaki iya tashi?" Ta tambayeta a tausashe. Da sauri ta daga mata kai gabanta yana faduwa. Ko da ba zata iya ba to tabbas zata tattara dukkan qarfinta ta miqe din don kada nanay din ta gano komai.

"To bismillah" Nanay din ta fada tana ja baya kadan ta bata guri. Ta qyaleta ne saboda tanaso ta miqe din taga iya adadin b'arnar da yaro nata yayi.

Ta tattakura kuwa cikin gwaninta da jarumta ta tashi daga kwancen,sannan ta fara yunqurin miqewa,saidai tuni ta koma ta zauna tana cije lebe gami da riqe
"Wayyo Allah" Da taso fada.

"A hankali mana.....karki qarawa kanki ciwo" Nanay data zaburo cikin zafin nama ta fada tana qarasowa gami da riqe akhnan.

"Bakiga yadda jikinki yake bane?" Nanay ta sake fadi tana janye duvet din da zai iya hardeta.

Tayi qasa da idanunta,tana jin kamar nanay din tana fahimtar komai,saidai kafin takai ga sauke idanunta gaba daya,idanun suka fara haska mata yadda gurare da yawa suka baci jikin farin zanin gadon.

Wata irin faduwar gaba ta saukar mata,taji kamar tana daga zaunen jiri zai kayar da ita.

"Meye wannan?" Ta fadi cikin sakalci da rashin sanin komai,saidai tana dire tambayar kwanyarta ta dauko mata falaak a wancan ranar.

"Innalillahi......na shiga uku" Ta fara maimaitawa a ranta tana curewa guri daya.

Itama saida yayi mata irin na falaak din?,tana yabonsa salla ashe alwala ma ya kasa yinta?. Wanne irin babban tashin hankali ne wannan?,Me yasa zai mata haka?,me yasa zai kira mata nanay?,wanne irin tonon silili yayi mata haka?.

Ya tsallake hasnaaa ya tsallake rumaisa ya tsallake dukkan hadimai ya kira mata nanay?. Batasan me yasa bayajin nauyin wasu abubuwa ba.

Hawaye kawai ya balle mata sabo,ita yanzu da wanne ido zata kalli nanay?,ba zata sake yarda da ita ba.....zataga kaman duka laifinta ne. Don idan bata manta ba ai tace mata ta kula da kanta,ashe abinda take nufi kenan?.

Kallo daya kawai tayi mata ta fahimci yanayin data shiga. Ta sani,ko wacece dole a irin wannan yanayin kunya ta dabaibayeta. Ta kasa koda motsa yatsanta,ta wani cure guri daya tana hawaye kamar ta kashe dan mutum.

Tausayinta da qaunarta suna sake narkar da zuciyarta,sai kuma murmushi ya subucewa nanay din mara sauti. Murmushin alfahari da ita.....murmushin nasarar samun suruka irinta. Ba shakka kunya wani abu ne.....kunya adon diya mace ne.....kunya tana burgeta idan ta ganta tattare da d'iya mace.

Hannu tasa ta cire cliff din da aka riqe zanin gadon dashi na gefe guda,ta sanya hannun ta tattareshi can bata iya inda akhnan din bata zaune a kai.

A tausashe ta kamo hannunta ta riqe cikin nata,abinda ya sake yawaita kukan akhnan din harda dan sauti.

Shuru ya ratsa tsakani,har yanzu dariya akhnan din ke bata,murmushi take me gauraye da tausayinta.

"Ai kukan ya isa haka ummm takwara?" Ta furta a tausashe.

"Karki kuka da yawa,kanki zaiyi ciwo......kiyi haquri a madadina a madadin muhammad haisam.....muna nema masa afuwa" Wannan maganar data fada ta qarasa sanya akhnan ta narke gaba daya,wani sabon kukan ya sake zuwar mata.

Shikenan.....ya fadawa nanay din ma,bashi da kunya ta rantse baida kunya,a yanzu ta sake yarda da haka ta kuma sake tabbatarwa.

A nutse nanay ta janyota cikin jikinta ta rungumeta sosai,kuma bata sake cewa komai da ita ba ta barta sai dataji sautin kukan ya sassauta sannan ta fara magana cike da dattako da nutsuwa,har a sannan tana rungume da ita.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Wajibi ne akan dukkan macen data kawo mutuncinta gidan mijinta ta fuskanci irin wannan wahalar daga farko.....duk da tana wucewa ne a hankali kamar bai taba faruwa ba......akwai wahala,amma alfarmarki kenan......alfarmar diya mace kenan da bata da kamarshi har abada. Alfarmar da ba wadda zata sameta......martabar da babu wadda zata sameta sai wadda ta kaiwa mijinta halalinta wannan budurcin. Wani alfahari guda daya da koda bayan shekara dubu ne zaki iya kallon qwayar idanun mijinki ki goranta masa.......kiyi wannan alfaharin ki sake maimaitawa. Koda ya musa komai daga gareki,koda ya musa dukkan alfarma a nan bashi da abun cewa. Ki godewa Allah daya sanyaki cikin matan da suka rabauta da wannan DARAJAR da ALFARMAR......" Sai tayi shuru tana sauke numfashi.

"Alhamdulillah" Ta samu kanta da fada can qasan zuciyarta.

Wani irin kwantar mata da hankali maganganun nanay sukayi,wannan shine yake bata tabbacin abinda ya fada a jiya. Kowanne miji da mata da gaske sunayi kamar yadda yace da ita a jiya. Kenan kowa boyewa yakeyi yana shuru?,kuma haka kowacce takeshan wannan wahalar amma taga sunci gaba da zama shekara da shekaru da mazan?. Kamar nanay din tasan abinda take tambaya a kai tace.

"Wannan wahalar.... Wannan tsananin na dan lokacine,kada ki damu,zaki daina jin komai.....kinsan me nakeso dake?" Ta fada tana dago akhnan din daga jikinta tana duban fuskarta.

Kanta ta girgiza a hankali ba tare data iya yarda ta kalli idanun nanay ba.

"Ki dauka a ranki safeena da safiyya ne dukka a nan" Ta furta tana nuna qirjinta.

"Duk da ban rayu dake ba,amma nima kamar uwa nake a wajenki.....da wannan idon nakeso ki kalleni,da wannan zuciyar nakeso ki saki jiki dani. Zan miki abinda zanwa su rumaisa da Aanani,don baki da maraba dasu a gurina. Ni ba surukarki bace daga yau.....ni mahaifiyarki ce......uwa nake a gareki" Kanta ta gyada a hankali,tana jin wani irin nutsuwa da gamsuwa suna mamayarta.

Wayarta taga ta dauka,tayi kira hadi da yin waya na duka duka mintinan da basufi biyu ba sannan ta ajiye. Riqeta tayi ta sauka daga kan gadon,ta maidata saman sofa ta zaunar da ita a hankali tana bibiyar yadda taka taku a hankali,abinda ya sake ninka tausayinta cikin ranta kenan.

Tana zaune daga saman sofa din kanta a qasa tana kallon yadda ta tattara zanin gadon da kanta,ta bincika ta samo wani cover me zip me kama dana bedsheets din ta turashi a ciki tayi zipping nasa sannan ta dauko wani sabo.

Batakai ga shimfidawa akayi ba akayi knocking qofar. Kai tsaye ta bada damar shigowa.

Dattijuwar macace sosai,wadda tana dan yawan ganinta a sassan nanay sosai. A shekaru zata bawa nanay din shekara kusan biyar,saidai duk da yanayin tsufanta jikinta ya nuna qaqqarfa ce,irin tsufan nan me kyau da yake nuna lallai mutum yana gyara kanshi da jikinsa.

"Qaraso mama" Nanay ta fadi tana buda mata qofar,ta shigo da sallama.

Koda nanay bata gaya mata ba tasan akwai aminci da kusanci sosai tsakaninsu da matar. Daga gidan sarauta ta fito,ta san duk wanda zaa budewa qololuwar daki irin haka ya shigo tabbas amincin yakai qarshe.

Wata leda ta karba daga hannun mamar wadda take ta yiwa akhnan sannu lokaci lokaci,sannun data sanya take sake jin nauyi kamar ta narke a gurin.
Chapter 93 · 0% Book details