← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 176

Sashe 26

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu tasa tana duba kayan daya bayan daya,ranta ya baci,taja qaramin tsaki. Wanne irin shirin kaya birra tayi mata?,bataga under wears ba banda guda daya. Ba rigar bacci sai guda daya qwal......bata saka mata kayayyaki da yawa ba daya kamata ace suna cikin kayanta,kayan da da yawa birran ce take da alhakin hadasu,ta kuma saba,ya zame mata jiki,don ko tafiya tsakanin agadez da Niamey da takeyi a baya duk qarshen sati birran ce ki shiryawa da tsara komai,ba'a kuma taba samun akasi ba,to a yanzu batasan sanadin wannan mantuwar ba.

Hakanan ta zaro daya daga cikin abayas din da sukafi yawa a kayan nata. Sakakkiya ce sosai,wadda bata nuna shape dinta kwata kwata. Saidai kuma yadin wani irin yadin silk ne me asalin tsada dake wata irin walqiya yana sauya launi. Duk da maroon ce amma idan haske ya haska wani gurin a maimakon maroon din sai ya koma kaman baqi.

Wani irin mugun kyau da dacewa da launin fatarta tayi,wani irin ado ke jikin abayar da shi kadai zai gaya maka tsadarta.

Gashinta kawai ya rage ta daureshi,saidai tayi iyakar yinta ta kasa,har tsintsiyar hannunta tana riqewa saboda yadda tayita kokawar tajeshi ta matseshi yadda birra ke mata.

Tilas ta sakeshi tana yarfa hannu kaman zata saki kuka. Bata saba ba,ba ita kewa kanta ba kuma zata iya ba,dole ta jawo Malaysian hijab baqi da yazo maqale da abayan,wanda bayansa yafi ko ina tsaho a jikinsa ta zura,take wannan kyakkyawar fuska ta fito sosai da wani irin haske me jan hankali ta tsakanin fuskar hijab din.

Tana zura wani designer snickers taji ana knocking a tausashe. Ta qarasa saka takalmin tana jin yadda ta gaji gaba daya sannan ta miqe tana nufar qofar.

KAMSHINSA.....shine abu na farko daya fara marabtarta.....qamshinsa dinnan data gama aminta shine JARRABAWARTA a tattare dashi.....jarrabawar da take fatan ta zama ita daya ce inde a tare dashi ne......kada ta kasance me abokiyar tafiya.

A nutse ta daga blue eyes dinnan nata tana saukewa a kansa. Yana tsaye gaban kyakkyawan fridge din yana tsiyaya ruwa me madaidaicin sanyi cikin glass cup din daya dora saman fridge din.

Idan tace bataji zuciyarta tayi rawa ba a lokacin ta sani.......tabbas ta gunduma qarya.......ya fita sosai a GIANT dinsa......tsaho da kaurinsa da murdewar muscles dinsa da suka bayyana ta hanyar kafadarsa guda daya dake waje.

Komai nasa fari qal......a yau da yake sanye cikin ihram komai nasa ya canza. Wani irin sanyi....wani irin nutsuwa da wata irin kwarjini ta cikin fuskarsa dake nuna zallar nutsuwa da muhimmancin ibadar da ya dauki niyya.

A hankali take tana qafafuwanta.......kafin ta samu kanta da tsaiwa cak tana kasa ci gaba da daga qafarta. Yau din kamar an sauyashi,ainihin tsarin halittarsa tana cika idanunta. Ya mata wani irin kwarjini daya daki zuciyarta. Ba luxury......ba jubah......ba cloak thobe......sai lallausan qamshinsa da a yau takejin ya qara taushi kamar an surkashi da wani abu daban. Fari kawai.....tsarki kawai.....nutsuwa kawai.....sai taji wani abu ya motsa zuciyarta.

"Me yasa yafi kyau a haka?" Ta tambayi kanta kafin zuciyata kwabeta,ta kuma tattara komai ta watsashi a gefe.

Daidai sanda ya kammala shan ruwan,ya ajiye cup din ya juyo da nutsuwa sai idanunsa suka sauka a kanta. Ta bada baya ne.....wannan ya bashi daman ganin doguwar sumarta me sulbi data jera tsaho da tsahon hijabin jikinta.

Idanunsa ya lumshe sannan ya bude,yana jin Allah ya taimakeshi daya gani,inda bai gani ba a haka zata fita......a haka zata ratsa mutanen da basu da qayadadden adadi.

"Akhnan...." Ya kirata a karon farko da wani irin sautin daya sanyata taji wani abu yana ratsa qashin da qafafuwanta gaba daya.

Waiwayowa tayi tana dubansa ba tare data iya sake takawa ko motsawa ba,saboda har cikin b'argonta kiran ya kutsa yana ajiye mata wani yanayi a dukka sassan jikinta.

Takowa yaci gaba dayi ba tare daya dauke idanunsa daga saman lips dinta ba,lips din da sai yau yaga ainihin color dinsu. Wai irin glowing suke,sirara dasu wanda ko baka taba ba kasan zasuyi laushi sosai.

Dab da ita ya tsaya,ya kuma zura hannunsa ta bayan hijab din a hankali yana kama gashin. Gashin da ya masa wani irin santsi a hannu har yasa tsigar jikinsa tashi.

"Ki rufe" Ya fada yana zare hannun nasa a hankali.

"Ban iya ba" Ta fada a wani mugun narke kamar qaramin yaron dake jin rigima. Yanayin ya sanyashi tsaiwa cak.......sannan ya zuba mata idanu yana jin wani abu yana sauka a sassan jikinsa. Tayi maganan ne har ga Allah kuma kanta tsaye,saboda wani mugun gajiya da takeji hannuwanta sunyi,ta kuma sani,babu ta yadda zata iya taje kan nan ta daureshi koda shigen yadda birra take mata ne ballantana irinsa. Batasan tone dinta ko mode dinta ya sauya zuwa kalan shagwaba ba.....shagwabar da sultane da mammina kawai take yiwa ita. Gefe guda har yanzu tana masa wannan kallon.....wannan kallon tuhumar....wannan kallon rashin amincin....wannan kallon na waye kai?....wannan kallon na ban aminta dakai ba.

Numfashinsa ya dinga zarowa daga tsakiyar qirjinsa da qyar kamar wanda aka saka wani abu aka matse masa shi. Yau yaga wani side......wani side da yake mutuwan so tattare da mace. SHAGWABA the only thing daya fara banbanta halittar mace data namiji kenan.

Baice mata komai ba sai taga ya juya yana komawa dakinsa,bai kuma dauki lokaci ba ya fito hannunsa dauke da wani comb. Ajiyewa yayi,ya daga manyan fararen idanunsa yana kallonta.

"Essaie un peu" Ya furta a nutse yana sanya idanunsa cikin nata. A hankali ta zare idanunta tana jin wani iri,kasheta yakeyi.....kasheta yakeyi da wani irin emotions a duk sanda yayi mata magana da French,tana jin kamar a bakinsa aka halicci yaren.....tana tsoro ta jarabtu da son yaren a bakinsa kamar yadda turarensa ya zame mata jarrabawarta.

Cikin zuciyarta take ayyana ta yadda zata zare hijabin a gabansa......amma kafin takai qarshen tunanin sai taga ya juya a nutse yana tattakawa zai fice.

"Me yasa yake hukunci da wuri?" Ta tambayi kanta. Kamar fa yanzu ita takeson space,ya bata space din kuma me yasa takejin wani iri?.

"Sai ya jira.....ya jira na fada masa ya fita mana" Ta fadiwa kanta da kanta,saita samu kanta da hararar qofar daya fice din. Hijabin ta zare,sannan ta dauki comb din ta soma gwada tajewar.

Bashi da tauri sosai,amma yana da tsaho sosai da cika,don idan ta wareshi duka zai maka wahala kaga fuskarta.

Jefar da comb din tayi saboda da gaske ta gaji,ta dakata tana maida numfashi kafin ta soma hade sumar,saidai sau uku tana hadewa yana wargajewa,sai kawai taji kuka yana zuwarmata,ta saki gashin tana zama saman stool din dake dab da conceal mirror din dake gurin.

A nutse ya buda qofar yana shigowa,idanunsa suka sauka a kanta sanda take dora tafin hannunta tana rufe fuskarta dasu. Kukanta wani private abune da ba kowa take bari ya kalla ba,taji kuma shigowarsa,bataso kuma yaga hawayenta. Gajiya takeji yau daya da duk wata hidima,bata saba ba,ba ita takewa kanta ba.

Kamar ya fahimci hakan,sai ya tako a hankali yana zaro wayarsa dake aljihunsa. Kadan yayi danne danne sannan yayi kira ya kara a kunnensa.

"Ishee ergi" Ya fada a taqaice sannan ya maida wayar aljihunsa. A nutse tsaf ya zauna yana qare mata kallo. Dole saita boye rauninta.....dole saita bayyana qarfinta da jarumtarta,bayan rauninta a bayyane yake.

Murmushi kadan ya subuce masa sanda yake tunawa. Ranar da zai cewa nanay dinsa ga jinin safeena dinta......ranar da zai cewa nanay safeena tabar tsatsonta har uku a duniya. Tunaninsa ya yanke saboda izinin shigowa da ake nema daga waje,sai ya miqe yana takawa zuwa bakin qofar ya bude.

Birran ce.....birran da yace a turota,taja baya cikin girmamawa ta rusuna tana gaidashi.

"Kuyi saurin fitowa lokaci ya kusa qurewa" Ya fada yana fita a dakin.

"Allah ya taimakeki" Birra ta fada murmushi na fita saman fuskarta. A duniya wani irin farinciki takeji ida taganta tare da sheikh haisam. Wani dadi takeji idan taga rayuwarta daure data sheikh haisam din. Saboda abune sananne ga duk masoyinta......tayi tsintuwar wani kebantaccen LU'U LU'U ne me girman darajar da har yanzu me yiwuwa bata ganeshi ba. Tana zaton iya TAGULLA ne kawai yasashe mara daraja.💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 25*

Da sauri ta sauke hannunta,ta kuma jefawa birra harara da jiqaqqun idanunta. Kafin tace komai birra tayi qasa da kanta.

"Don Allah kiyi haquri,ba laifina bane,yallabai ne ya tsara tafiyar kowa da masaukin ya zama daban daban.....muna qarqashin kulawar yaranshi"

"Yaranshi?" Ta furta tana duban birra. Kaman zata sake cewa wani abu da ita sai kuma tayi shuru tana dauke kanta miskilancin ya motsa,wannan ya bawa birra daman matsowa ta soma gyara mata gashin kamar yadda ta saba,wanda cikin minti biyu ta hade mata shi tsaf,ta kuma daureshi cikin madaidaicin ribbon,sannan ta miqa mata hijab din ta zura.

"Ina falaak?" Ta tsinci kanta da tambayar birra.

"Suna nasu hotel din a masaukinsu" Birran ta amsa mata. Mamaki kadan ya kama akhnan,wato ita hankalinta kwance?,yarinyar bata da hankali,haka kawai tabi wani namijin hankali kwance ba kuma wanda take nema?.

A qasa ta sameshi har ya sauka zuwa babban reception na hotel din. ya kalleta sau daya saidai bai soma tafiya ba har sai da tazo dab dashi.

A hankali suke takawa,cikin wani yanayi daya sanyawa zuciyarta nutsuwa. Iska me kyau....haske me haskaka zuciya dama gangar jiki.....kai kawo na mutane dake cike da nutsuwa da yanayi na ibada,bautar Allah cikin sakankancewa.....nutsuwar ruhi dama ta gangar jiki gaba daya.

Wani abu ya sake daukar hankalinta yayin shigarsu haram. Kebantacciyar mashigar da tunda take zuwa bata taba shiga ta gurin ba,bisa jagorancin mutum ukun da suke sanye da uniform na ma'aikatan dake kula da haram baki daya. Tun takowarsu gurin suka iso su uku

"Barka da zuwa sheikh" Suka fada cikin girmamawa. Murmushi ya saki a nutse,murmushin dake sake cika haibarsa da kamalarsa,yake sake fitar da sirrin kyansa. Sai ya miqa musu hannu sukayi musabaha.

"Sheikh yasir addosary ya sanya hannu kan takardar zamanku......amma ba shine zai jagoranci sallar isha'i ba,sheikh abdurrahman assudais ne....saidai yana gurin,zasu dan zauna a tsakaninsu,lokacin kamar zai isa ka kammala umararka ku zauna dasu" Yayi maganan cikin harshen turanci wanda hakan ya bawa akhnan damar jin dukkan abinda ya fadi din.
Chapter 26 · 0% Book details