← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 176

Sashe 38

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaban sultane ya matsa kansa tsaye ya zubesu yana zazzage ledar. Idanu sultane yabi kayan dashi zuciyarsa tana bugawa,Alhaji nasiruddeen ya koma da baya a nutse ya zauna yana fuskantar sultane.

"Bincike ya kammala......kuma zarginmu ya tabbata......ga irin nau'in kayan da muka samu cikin dakin". Zuciyar sultane tayi wani irin nauyi,ba jiya yau ko dazu dazu yasan Alhaji nasiruddeen ba. Mutumne daya qware gurin aikinsa,cikin tarin gaskiya da amana. Uwa uba qasarsa ta niger qasace da take da tsauri akan sha'anin cin hanci da rashawa. Babu ta inda za'a shirya komai saboda cin hanci ko toxarci. To amma abin yazo mata wani iri,ta wata sigar daya kasa yarda dashi.

"Ayimin afuwa Allah ya taimakeka......inaso a bani daman yi mata wasu tambayoyi a nan....idan kuma hali yayi zamu wuce da ita zuwa office dinmu" Maganan ta zowa mammina a bazata,wanne office?,ita din zasu dauka don tuhuma?

"Na baka nasiruddeen" Sultane ya fada kansa tsaye a sanyaye. Bashi kadai ba,hatta da morsa safiyya a sanyaye take kallon komai. Tafi kowa sanin wacece zaituna kaf fadin agadez,bata tunanin akwai wani wanda zai gaya mata wacece ita......amma wannan lokacin abun ya girme mata itama.

"Ranki ya dade......wadannan qwayoyin da hodar iblis......"

"Ba nawa bane" Ta amsa kai tsaye tun kafin yakai qarshen tambayar tana qoqarin cusa nutsuwa cikin maganganunta da reaction dinta. Shuru ya ratsa bayan amsar data bayar. Shurun ya zarce na wasu sakanni,sannan ya sake magana.

"Amma an samesu cikin dakinki".

"Eh ba nawa bane" Ta sake maimaita amsa daya dai. Dole akwai wani yanayi na aiki,da muddin ya biyo ko ta kan waye a danne sanayya,banda ita dince.....ba wanda za'a kama red handed da wadannan kayan a tsaya masa tambaya cikin gida.

"Bedroom dinki......dakin kwananki,waye yake amfani dashi?" Yayi tambayar yanayinsa yana nuna mode na aiki ya shigeshi. Idany ta zuba masa itama sosai,tamkar tana gargadarsa,tamkar tana gaya masa cewa.

"Kabi a hankali.....ina da hadari sosai".

"Nice" Ta amsa kai tsaye.

"To me yasa suke cikin dakin?" Ya maimaita. Shuru ya ratsa na sakanni,sannan ta amsa

"Ta iya yuwuwa wani ya saka saboda ya batamin suna kamar dai haka"

"Wani?.....kamar wa kenan?" Ya sake tambaya yana dubanta ta tsakiyar idanunta. Duk amsar data kamo sai taji ta subuce,akwai sunaye da yawa da takeso ta furta amma sai koda qwaya daya yaqi fita a bakinta,wannan ya sake bada shuru me nauyi,har sai daya sake magana.

"Sun kasance cikin wani irin boyo na sirri,da dukkan alamu dake nuna ba'a son kowa yasan dasu,da dukka wata kalar dabara dame laifi yake iya boye kayan laifinsa...."

"Kana zargina kenan yanzu?" Ta fada fushi yana nunawa saman fuskarta. Idanu ya zuba mata,yana karantar muddin akaci gaba a nan,muddin yaci gaba da biye mata zata nannade tabarmar kunya da hauka ne,kuma ya tuna,wannan umarnin da aka ruba masa shi da manyan baqi BA'A GABAN SULTANE KOMAI ZAI KASANCE BA. sai ya tausa muryarsa

"Ba tuhumarki nake ba.....tambaya ce kawai". Kalmar tasa ta qarshe ta danneta,shurun da yayi mata nauyi da yawa ya biyo baya,kamar an daure harshenta,kamar an daure kowacce kalma daga bakinta,tana jin sanda ya juya ga sultane.

" Ayimin aikin gafara ranka ya dade,a bani dama mu wuce da giwa zuwa hukuma mu qarasa bincikenmu a can,idan komai ya daidaita zamu dawo da ita har gida in sha Allah". Tayi zaton zataji muryar sultane yana fadin bai yarda ba,ta dauka zaice sam sam,amma ga tarin mamakinta sai taji muryarsa cikin rauni yana cewa.

"An baku izini".

" Muhammad?" Ta kira sunan sultane kai tsaye idanunta kafe cikin nasa. Yadda ta kirashi gatsal din ya jawo hankalin kowa da kowa a gurin hatta dashi sultane din. Zare idanunta tayi ta maida kan ma'aikatan daidai sanda sultane yake cewa Alhaji nasiruddeen su dan basu mintuna biyar. Ba musu dukka suka juya suka fice,gurin ya rage daga ita sai morsa safiyya sai sultane din,morsan da sam mammina ta manta da wanzuwarta a gurin saboda tsananin rudewar da taketa pretending tana boyeta.

"Kai da kanka ka miqa matarka inda za'a wulaqantata?,da kanka ka amince wasu jami'ai su tafi dani?". Idanunsa ya lumshe sannan ya bude lokaci guda.

" Ba tozarci ko wulaqanci bane.....haka tsarin yake,dokar ce a haka,muke gyara doka da bayar da ita.....ba zamu taba zama masu karyata ba.....idan na hana su tafi dake ashe bamu da gaskiya kenan?, a duk inda kake gaskiyarka ce take fidda ka,ita take kunceka ta dawo dakai mataki da matsayinka" Maganan ya mata kama da jirwaye me kama da wanka. Har ta bude bakinta zata sake magana sai idanunta suka sauka kan morsa safiyya,abinda ya sanyata shanye duk abinda take da niyyar fada,ta maye gurbin abinda yake kan fuskarta da murmushi

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Na yarda dakai,na amince ba zaka taba sakin hannuna ba a sanda nafi buqatarka. Ko waye ya qulla wannan abun zai warware in sha Allah.......rabuwarmu ko toxartata saidai a jira" Idanu morsa safiyya ta kawar kawai,can qasan ranta abubuwa da yawa suna kai kawo. Ta sani.....zaituna nada wani irin hatsari.....ta sani,zaituna din wata halitta ce da komai akace zata aikata zai farun,sai abinda Allah ya tsare kawai,wadannan maganganun duka ta sani tana yinsu ne saboda ita.

Ita da sultane din duka sukabi zaitunan da kallo sanda take ficewa gurinsu Alhaji nasiruddeen.

Motarsu suka bude mata,don baya cikin doka mutum ya tafi a motarsa kaman yadda zaituna taso tayi da farko. Inda tuhuma ce kawai ba'a kamata da komai ba ana iya bata wannan damar. Da farko ta tsaya kai da fata bata shiga motarsu saidai ta taho a tata motar,duk da tasan cewa doka bata bata dama ba. Amma sai tawagar 'yan jaridar da sukayo kansu.....'yan jaridar da basusan waye ya kirasu ba suka sanyata da qafafunta ta shige motar,musamman da idanunta suka sauka kan biyu daga cikinsu. Suna cikin 'yan jaridar wancan ranar......suna cikin 'yan jaridar da suka yada labarin takardunta na wancan ranar,har abun yake neman zame mata barazanar da a yanzu ake d'ari d'arin karbar taimako daga gurinta daga kowanne asibiti ko gidajen marayu da sauransu.

"Da gaske ne an samu qwayoyi a tare dake......da gaske ne tafiya zakuyi don tuhuma?" Tambayoyin da suka ratso glass din window din da take zaune suka isa ga kunnuwanta,tambayoyin da suka tilasta mata runtse idanunta tana jin zuciyarta da idanunta suna zugi.

"Ina tafisu da nace zamu tafi tare?"

"Ba'a ganta ba......amma ko daga baya ne zata iskemu a can" Driver din motar ya bata amsa yana tayar da motar.

*S U L T A N E*

Idanu morsa safiyya ta zubawa sultane,wanda tun bayan tafiyarsu mammina bai sake cewa komai ba banda shurun. Koda ba'a gaya mata ba tasan yanayinsa,tasan kuma halinsa,alamu ne na zurfafa cikin tunani,tunanin data tabbatar baida fa'ida gareshi da lafiyarsa,musamman yanzun da yake yawan qorafi akan yanayin qarfi da lafiyar jikinsa.

"Bappin akhnan" Ta kirashi da sunan da tasan yana masa dadi sosai. Kansa ya daga yana dan sake mata murmushin qarfin hali.

"Nace ko zaka tafi ka kwanta ne?,zuwa anjima qilan idan ka samu kayi bacci zakaji dadin jikin naka?" Kai ya daga mata a hankali,shi kansa baya marmarin ci gaba da zaman. Wani irin abu yakeji yana taso masa game da mammina. Wani irin yanayi da yafi kama da zargi rashin yarda da rashin aminci. Ya sani,gidansa cike yake da tsaron da ba wanda ya isa ya keta sassan matansa ta sauqi haka har yayi ajiya makamanciyar wannan,ballantana sassan mammina din,da kusan ko sashensa bazai nuna masa tsari tsaro da kulawa ba.

"Muje" Ya fada yana yunqurin miqewa. Koda ya miqe sai yaji kamar ana jijjiga jikinsa da qafafuwansa. Sai yaji kamar komai yana shirin bace masa a lissafinsa,kafin ya iya yin komai wani jiri ya debeshi.

Salatin morsa safiyya da hailalarta kawai ya iyaji,yana jin sanda ta tareshi amma bata da wannan qarfin,dole ita dashi din duka suka zube a qasa.

Da wani irin tashin hankali take kiran sunansa tana tattaba fuskarsa ganin idanunsa suna komawa gami da rufewa ruf. Iyakar yadda zatayi ya gagara,sai ta miqe a birkice tana kama sunayen duk wani hadimi da tasan za'a sameshi a kusa dasu.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 36*

"Ba numfashi a jikinsa kwata kwata" Daya daga cikinsu ya fada yana duban morsa safiyya gumi yana yanko masa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" Ta samu kanta da maimaitawa sau babu adadi,ya sulale tana zama dab dashi tana riqe hannayensa sosai cikin nata.

Safeena ce take dawo mata cikin kanta....wancan ranar da ba zata taba gogewa cikin kanta ba,har sai ranar da tata ta sameta.

"Karka tafi ka barni kaman yadda safeena tayimin" Ta motsa labbanta tana fada a hankali tana jin kamar hankalinta yana neman gushewa daga jikinta.

"Likita ya iso Allah ya baki nasara" Taji muryar daya daga cikin hadiman,kai ta daga tana dubansa kamar bata ganewa,sai kuma ta sake matsawa kusa da sultane din da har yanzu ba wani abu nasa daya motsa,kamar tana gaya musu bazan iya tashi daga nan ba.

★★★

*M A D E E N A*
_ALMUNAWWARA_

*_InterContinental Dar Al Iman Madinah(presidential suit)_*

Cikin lallausar jubah yake sanye wadda aka samar da ita da zare da auduga me darajan gaske. Fara ce tas me wani irin daukan idanu saboda tsadajajjen silk material me asalin tsada da aka maida audugar zuwa ga saqarsa.

Yana tsaye bakin babban glass window din,wanda kai tsaye idanunsa suke kafe akan haram na masallacin ma'aiki S A W.

Tunda suka zo baya gajiya da tsaiwa a gurin......baya gajiya da kallon gurin da yake fata ruhinsa da gangar jikinsa watarana su dawwama a gurin. Koda zai mutu kuma ya zamana yana da rabon qasarsa ta kasance cikin garin me tsarki.
Chapter 38 · 0% Book details