← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 176

Sashe 117

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*BOOK 03///PAGE 105*
___________________________
https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee*
___________________________

Sosai ya sake riqeta cikin jikinsa yana sake jera kiran sunanta,idanunsa a kanta.

"Alhamdulillah" Ya fada sanda numfashinta ya tsaya,saidai kuma cike da rauni. Ta ware idanunta fes a kansa,wadannan blue eyes din da suka sake wani irin haske dake birkice da tsoro da fargaba.

"Alhamdulillah" Ya fada yana taba qirjinta yanason jin yanayin bugun numfashinta.

A hankali komai ya dawo mata,tamkar mutumin da ya farka daga wani mummunan mafarki bayan dogon lokaci.

"Bappi...." Ta furta a raunane hawaye suna sake wanke mata fuska.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.....Allahumma ajirni fi musibati,wa'aklifny khairan minha" Ya soma maimaitawa a hankali,ba tare daya kula da kukanta ba.....ba tare daya tsaidata ba....ba kuma tare daya hanata yin komai ba. Ya hade yatsunta cikin nasa yana bata support a hankali da wani yanayi da yake kama da yanason dora harshenta da zuciyarta a ambaton Allah.

A hankali bakinta ya kama innalillahi din,taci gaba da maimaitawa tare dashi ba qaqqautawa.

Bai motsata ba,bai hanata kukanta ba bai kuma tasheta zaune ba,ya barta a jikinsa sunaci gaba da maimaitawa istirja'in a tare. A haka ta soma jin wannan dutsen me nauyi da qarfi daya tokare mata numfashin yana narkewa yana buda mata 'yar siririyar hanyar da zata iya zama.....siririyar hanyar da zata iya numfasawa adadin kwanakin da takeji sun rage mata.

"Da gaske kenan.....bappi na ya mutu?,sultane ya mutu?" Ta fada kanta kwance saman qirjinsa,hannunta na riqe da rigarsa kamar tana tsoron duniya gaba daya.

Shi kansa zuciyarsa tana nauyi da ganin halin da take ciki.

Muryarsa ta zama calm,soft,cike da nutsuwa. Sai yadan shafa kanta a hankali.

"Akhnan" Ya kirata yana qoqarin danne nauyin yasa zuciyar.

"Ki saurareni" Ba zata iya amsa masa ba......amma kunnuwanta shi suke saurare. Fatanta daya yace mata abinda taji kawai ba daidai bane,fatanta kawai tace masa sultane bai mutu ba yana raye.

"Mutuwa wajibi ce akan kowa" Sai ya dakata a tausashe.

"Kuma babu wani rai da Allah ya halitta wanda bazai d'an d'ani mutuwa ba"

Hannunsa ya sanya yana dago fuskarta daga qirjinsa,yana bin hawayen dake sake ambaliya suna wanke mata fuska da kallo. Yatsansa ya sanya yana dauke mata su.

"Nasan akwai ciwo"

"Musamman mutum ya rasa wanda zuciyarsa take qauna" Sai ya danyi qasa da kansa yana kallonta.

"But akhnan"

"Qaddarar Allah bata tabayin kuskure" Ta lumshe idanunta da qarfi saboda zafin da ke zuciyarta.

"Amma na barshi.....shima kuma ya tafi ba tare da mun yiwa juna bankwana ba" Ta fadi tana jin zuciyarta kamar zata tsage.

Hannunta ya riqe cikin nasa a tausashe,yana matsawa a hankali cikin nuna rarrashi.

"Kada ki azabtar da zuciyarki da abinda baya hannunki.”

" Allah ya fimu sonshi.....kuma wataran muma zamu bishi,zamuje inda yaje" Sake matse hannunta yayi da salon bata qwarin gwiwa.

"Ki tuna...."

"....Duk addu’ar da zaki yi masa yanzu zata isa gare shi.” kai take gyadawa a hankali,duk da ta kasa magana sai hawaye kawai dake zuba.

"......Kuma idan ya kasance uba nagari gare ki…” ya saki siririn murmushin da bashi da alaqa da farinciki.

"Then the greatest gift da zaki masa yanzu…”

"…shine ki ci gaba da zama d'iyar da zai yi alfahari da ita.” kai ta sake jijjigawa da qarfi,sai wani kukan ya sake qwace mata. Wannan karon....kuka ne dake sauke mata gami da rage mata nauyin zuciya.

Jawota jikinsa yayi a tausashe yana bata kyakkyawar runguma.

"Kiyi haquri saboda Allah"

"Ki karbi qaddara saboda Allah" Shuru ya sake ratsawa tana jin yadda maganganunsa ke samun muhalli me kyau cikin zuciyarta suna kuma saukar mata da nutsuwa kadan kadan.

"Duniya gaba dayanta tafiya ce akhnan...."

"Wata rana muma zamu koma ga Allah" Ya sanya idanunsa cikin nata a tausashe.

"So while we are still here…” ya jijjiga kansa.

"…let us hold onto faith.”.

Maganganunsa wadansu taskoki ne masu tsada a tare da ita,wasu taskoki ne masu nauyin da idan aunasu za'ayi cikin ma'auni zasu rinjayi komai dake kanta.

Wani irin tauhidi....imani......haquri da karbar qaddara ta gaskiya ta saukar mata. Da taimakon kalmomin nan guda biyu....masu nauyi da tsada da ya maidasu suka zama abun saurarenta daga sanda aka fara shirya private jet dinsu na tafiya agadez har aka kammala.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Da kuma

"La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimeen" Daga baya ya surka mata da.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel". A dukkan awannin.....awanni masu tsananin gaske a cikin rayuwarta.....awanni mafiya jirkicewa rudewa da fuskantar ibtila'in da bata taba ganin makamancinsa ba.....hannunsa yana cikin nata. Idan har ya zameshi ko ya sakeshi to sallah zasuyi shi da ita.

Bai bari su shehnaz sun ganta da wuri ba sai bayan wasu awanni. Batasan yadda yasha kansu ba.....amma dukkanunsu sunyi qoqarin zama cikin nutsuwarsu,saidai ba wadda idanunta ya dakata daga zubda hawaye.

Ba shakka sultane uba ne.....ubane har uba game uba da mara ubanma. Bai taba nuna banbanci gazawa ko kasawa ba tsananinsa da akhnan da kuma falaak ba.

Sai zuwa dare sannan private jet din ya samu daman tashi dasu.

Shuru ne ya sake wanzuwa cikin jet din,sai sautin engine mai laushi da kuma dim golden lights dake cikin cabin.

Tana zaune kusa da window ne kawai,amma idanunta basa kallon komai. Ko daga nesa kana iya ganin yadda idanunta suka kumbura da kuka,kukan da haisam yace tayi idan tanaso.....amma karta fadi karta bari zuciyarta ko bakinta su furta abinda Allah bai yarda dashi ba.

Tun bayan tashinsu daga Dubai,bata iya zama lafiya ba. Zuciyarta wani zugi take mata,fargabar da batasan ta meye ba tana sake mamayeta.

Kowanne minti zuciyarta tana tuna Sultane ne.....kalaman Mammina .......da kuma yadda bata yi bankwana da mahaifinta ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Haisam kuwa yana zaune kusa da ita. Ba aiki ba kuma danna waya kwata kwata,gaba daya attention d'insa yana kanta. Kowannd motsi idanunsa suna kanta,yana jin yadda tausayinta ke narkar da zuciyarsa.

A yau duk wani tausayi nata da yakeji a baya.....sai yaji ya ninka kansa ninkin baninkin,tausayin daya sake narkewa da wata mahaukaciyar soyayyarta da baisan qarfinta yakai haka ba sai yanzu.

A hankali sai ya lura hannayenta suna rawa kad'an. Ya motsa a hankali ya dauki gorar ruwan dakr gabasa ya tsiyaya a cup ya miqa mata

“Drink something.” ya fada idanunsa cikin nata a tausashe. Ta girgiza kai cikin karaya.

“Bana so…” Sai ya matsa kusa da ita kad'an.

“You haven’t eaten either.” ya fada da kulawa sosai,bai jira amsarta ba ya d'ora

“Your body needs strength.”

Ta lumshe ido tana qoqarin hana sabon kukan fitowa. Bata jin a wannan yanayin da take ciki,banda iska akwai wani abu da zai samu daman wucewa ta maqoshinta.

Sai kawai ya cire belt d'insa ya matsa kusa sosai,kafin ya jawota jikinsa cikin tausasawa.

“Come here.” Ba musu ta kwanta a jikinsa. Bango take buqata a yanzu,majinginar damiwarta. Ta lumshe idanu cikin gajiya da ciwon da zuciyarta take mata. Sai ya rufe ta da soft cashmere blanket,hannunsa na shafa bayanta a hankali cikin kwantar da zuciyar dake cike da firgici

“Sleep a little.” ya fada kaman me lallashin jaririn goye,yayi kissing nata a hankali

“I’m here" Ya sake fada yana matsa kafadarta cikin bata assurance.

Tafiyar awa biyar zuwa shida tsakanin dubai zuwa agadez. Duk lokacin da ta farka cikin kuka sai ta sameshi still a gefanta,still yana riqe da hannunta.....sannan still calm
Kamar baya son ta ji tana ita kad'ai. Bayason yaga wannan kewar.....wannan kadaicin cikin idanunta. Inda yana da dama.....inda ya isa tabbas da zai kauda mata wannan quncin da taketa fama dashi,wannan quncin da take kokawa dashi.

*A G A D E Z*

*Mano Dayak International Airport*

Gaba daya yanayi da atmosphere ya bambanta tsakanin Dubai da agadez.

A idanunta sai taga sararin samaniya tamkar ya dusashe.

Iskar hamada na busowa a hankali,kunnuwanta suka jiye mata wani irin shuru da agadez din tayi.

Daga can nesa tana iya jin sautin karatun qur’ani daga masallatai mabanbanta mallaki qasar agadez din daga kowanne sashe nata.

Motocin masarautar agadez ne sun cika wajen. Hadimai bayi da masu tsaro. Royal convoy sosai duk saboda taronta.

Amma duk fuska d'aya,yanayi daya zaka gani saman fuskar kowa da zaka kalla a gurin.

A hankali take takowa matattakalar tana saukowa,da wani irin kasala da mutuwar jiki cakude da matsewar da zuciyarta takeyi. Tazo step din qarshe saita tsaya cak zuciyarta na wani irin bugawa.

Karo na farko kenan.....karon farko da ta dawo Agadez ba tare da jin wanzuwar mahaifinta cikin qasar ba. Karon farko data shigo agadez taga ta mata baqi.....ta mata duhu. Wata agadez da a yanzu ba sultane a cikinta....sultane din da zuwa yanzu yayi kwana d'aya cikin qabarinsa. Wata agadez daban take gani cikin idanunta ba wadda ta saba gani ba.

Hannuta ya riqe yana sake matsawa softly cikin yanayin bata qwarin gwiwa.

"La haula wala quwwata illa billahil aliyyul azeem....Allahumma ajirni fi musibati,wa'klifni khairan minha" Ya fada cikin taushi. Hawayen nan dai da suka kasa yanke mata,sune suka ciccika idanunta,ta motsa labbanta a hankali tana maimaitawa tare dashi,saita fara takawa suna nufar motar dake bude tana jiran isowarsu.
Chapter 117 · 0% Book details