← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 176

Sashe 3

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba haka ya zata ba,bama shi kadai ba.....dukkan wanda yasan da aikin......dukkan wanda yasan da aikin yana hasashen farincikin nasarar haisam a ranar zai zama na dabanne.

Yatsunsa ya murxa kadan,baisan me zaice da bobbo da zai gane.....baisan da wanne yare zaiwa bobbo bayani ba,bashi kadai ba harda su omar. Abu daya ya sani wani qatoton abune yake a tsaye a wuyansa a yanzu haka idan ya tuna shirin mammina mafi muni,shirin halasta haram tsakanin muharraman da tafi kowa sanin girma da nisan haramcin dake tsakanin AHMED da KHADEEJA.

"Akwai sauran bayanai" Bobbo ya fadi kansa tsaye yana duban haisam. Sai a sannan haisam din ya dawo da dubansa ga fuskar bobbo din,ya gyara zamansa da yanayin zamannan dake cike da qasaita wanda ya zame masa jiki,ko a office ko a taro koma a inane,wanda yawancin lokuta baimasan yana yinsa ba.

"Akwai" Ya amsawa bobbo a nutse da muryar nan tasa da nutsuwa kewa ado koda yaushe.

"Ina saurare" Bobbo ya fada shima yana tattarawa haisam dukka nutsuwarsa.

"Asalin sunan ZEENATU ne.....zaituna sunan aminiyarta data salwantar da ita ne bayan ta tabbatar a duniya itace kadai ta rage halittar datasan kaf sirrikanta.....ta taho da jaririn ajaani xuwa niger.......ta kuma dauki jinin sultane muhammad hammud ta maidashi tantirin dan shaye shaye bayan ta bayar da kyautarsa ga magajiyar karuwai.....kyautar da an shiryata ne da nufin za'a waiwayeta bayan wasu shekaru saboda cika wasu munanan qudure qudure da muradi na hada haramtaccen aure tsakanin 'yan uwan da aure tsakaninsu ya haramta har gaban abada.......khadeeja diyar sultane......da ahmed babban d'an sultane daya kamata ace yana rayuwa a fada yanzu kaman sarki,.......wanda ya kamata ya karbi sunan MAGAJIN SULTANE a yanzu haka" Ya qarashe maganan yana jin wani d'aci yana ratsashi tun daga zuciyarsa har izuwa harshensa.

Shuru ya sake wanzuwa,girma bayanan da haisam yaci gaba da bashi yana ratsa bobbo. Girman rashin imani.....zallar zalunci da BAQAR SHUKAR zaituna yana ratsa zuciyar abbo din.

"Lokaci yayi muhammad.....a yanzu ka lalata komai,ka kuma bata dukkan wani shaida makama ko hujja tata,......ka saare dukkan wani qarfi da takejin tana dashi,na baka dama a kanta a yanzu" Bobbo muhammad dawud ya fada shima yana jin wani irin abu me nauyi yana sake sauka a zuciyarsa.

Wani kalar murmushi ne ya subucewa haisam din yana murza tafin hannunsa da yatsunsa,wani kalan murmushi da baida alaqa da jin dadi ko walwala ko kadan.

"Taci bulus kenan bobbo" Ya furta calmly,saidai wutar dake ruruwa me girma ce.

"Zunubin zama a qasar AGADEZ,cakuduwa da mutane masu aminci,da kuma ha'intarsu kadai....iya wannan zunubin yafi qarfin a kama zaituna cikin girma......dole ta rasa wannan GIRMAN data dade tana tattalinsa.......dole kuma ta zama mutum ta farko da zata fara tonawa kanta da kanta asiri........inaso a gaban idanunta AHMED ya zama magajin sultane....... Inaso akan idanunta abinda take jayayyar hukuncin Allah a kansa ya faru alhalin bata da yadda zatayi....."

"Sultane fa?" Bobbo ya fadi yana duban tsakiyar idanun haisam,yana kuma karantar zurfin bacin ransa.

"Za'a yi komai yana nan......saidai zai dan kwanta ya huta da kalar hutun da zai zame masa sassauqa.....hutun da zai hanashi ganin wasu daga cikin tashin hankulan da suka durfafoshi suka durfafo iyalinsa,suka koma durfafo masarautarsa......na shirya kawai bobbo.......idanu da kunnuwanka kawai nakeso ka kulle......a yanzu na shirya kowa yasan waye sheikh muhammad haisam ibraheem aba jifar......"

"Al_saamit?.......the silent one?" Bobbo ya fada da wani kwantaccen kuma sauqaqqan murmushi kan fuskarsa. Ya sani,tsokanarsa bobbo yake,wata tsokana cikin girmamawa wadda haisam ya riga ya saba da ita.

"Na kulle muhammad.......na damqa maka dukkan wata dama kuma dari bisa dari.....na zare hannuna na baka wuqa da dama......ka qarashe wasan da dukkan salon da kaso" Idanunsa haisam ya lumshe yana kuma budesu dukka lokaci daya.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

09166221261
KO
08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

09166221261

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
09166221261

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 03*

"Na gode" Ya furta yana kuma qoqarin shutting down system din.

"Salaana ya fito da mota" Haisam ya fadi yana qarashe kasheta ba tare daya dubi omar da yakeson yayi tambayoyi wa haisam din ba.

*M A M M I N A*

_"Kwanciya ba taki bace zaituna........ki tashi zaituna.......ki tashi ki nuna ma koma waye da yake wasa da rayuwarsa cewa yana kutsawa sansanin mutuwa ne yana yin wasa da ajalinsa......ki tashi zaituna kada ginin nan na shekaru masu yawa da kika jima kina yi ya fado ya danneki.....ki tashi zaituna!!!.....kada ki bari akhnan ta fahimci komai.....kada ki bata qofar da zatayi nisa dake da burikanki ba tare da sun kammala cika ba"_

Ire iren wadannan maganganun sune abinda taji zuciyarta na rad'a mata har cikin kunnenta a sanda take kwance da tarin zazzabin da ya dinga kadata kamar zata datse harshenta da haqoranta.

Wani irin wuf tayi ta tashi.......ta kuma buqaci maganin da zai warkar mata da zafin zazzabin cikin mintuna goma ko ashirin. Ta karba ta kuma sha,sannan kuma ya sauka kamar yadda tayi buri,ta shiga tayi wanka,sannan ta buqaci abinci wanda ta zauna ta cishi sosai ba tare da tana banbance d'and'anonsa ba. Tana cine kawai saboda tana buqatar energy sosai a tattare da ita,tana cine saboda tana buqatar aga confidence da cikakken karsashin nan da aka santa dashi,tanaso ta fito a giwarta sak,batasan komai nata ya nuna karaya ko rauni.

Ta sani......indai cimmawa ne an riga da an cimmata.....ta sani,jikinta kuma yana bata akwai tarin baqin fuskar dake rayuwa cikin gidan.....akwai tarin inuwoyin da suka saje da duhun katangun gidan,suke rayuwarsu suna kuma farautarta ba tare data san hakan ba,saidai koma waye.....koma meye tana bawa kanta tabbacin indai itace wannan zaituna din.......indai itace zeenatu to sai ta sanya nadama a zuciyar dukkan wanda yayi gigin ketawa ta cikin shirin ta......rayuwarta dama dadadden burinta.

SHIEKH MUHAMMAD HAISAM sunan da yake kwance a ranta......sunan daya zame mata tamkar wani jarrabawa. Dashi take kwana.....dashi take tashi.......tare da dukka tsare tsaren yadda zatayi dashi,ta yadda ba wani malami da zai sake mararin shigowar masarautar AGADEZ yace zai rayu ba tare da amincewarta da samun dama da dukkanin goyon baya daga gareta ba.

"Ki aika saima....ta duba cikin bangaren suturu mafi zama alfarma ta bani daya" Tayi maganar da d'aya daga cikin hadiman da ita ke biyewa yalwa a matsayi a gurinta. Har hadimar ta fice idanunta yana kallon sashe daya,lissafinta akan toshewar kowacce qofa da zata bada makama akan batan yalwa takeyi. Ba yalwa ba dalilinta,saidai ba wani abu da zai alamtawa kowa b'ata yalwan tayi,b'atan nata yabar tarin hujjojin da duk wanda ya kalla zaice yalwa ta zabi ta tafi da qafafunta bawai da sunan b'ata ba.

Ta sani......ta kuma tabbatar da cewa. Bata yadda za'ayi yalwa ta zabi tafiya daga gareta,bata yadda za'a yi yalwa ta zabi tafiya daga masarautar agadez. Tafiyar yalwa din wani SHIRYAYYEN ABU NE da mutane irinta ne kadai zasu gane hakan.

Tsaf ta shirya cikin ire iren shigar dake nuna zallar alfarma alfahari da kuma izzar da takejin tana da ita. Ba kwanaki ko shekaru qalilan ba........a dukka tsahon shekarun data kwashe qasar agadez ta samu wani irin girma da ba wata halittar diya mace data sameta. Girmamawa da tarin darajtawar da ita ta nemeta.......ita ta siyeta.......ita kuma take tattalinta har kawo yanzun da takejin ba wani.....ba kuma wani abu daya isa ya rabata da wannan izzar tata,izzar da itace MAKAMINTA izzar da takejin zatayi dukkanin me yuwuwa gurin adanata da kyau har zuwa sanda numfashinta zaibar gangar jikinta.

"Ina fatan akhnan na cikin gida?". Kai ta gyada mata cikin maqurar ban girman nan da suka saba bata.

" Eh tabbas.......ance ta fita zuwa dakin karatun me martaba"

"Dakin karatu kuma?" Mammina tayi tambayar tana zubewa hadimar tata idanu.

"Eh Allah ya baki yawan rai" Shuru ya ratsa kadan,mammina din tana juya zoben dake yatsar hannunta. Wani abu ne yake harbawa cikin kanta da saurin gaske yana sake nauyayawa da kuma zurfafa tunaninta.

Zuwa dakin karatu baya cikin dabi'a ko al'adar akhnan din kaf tsahon rayuwar data raineta a kai,idan dan zamanta dashi ne fa?......idan dan kebancewar da tayi dashi ne wanda duka duka idan aka lissafesu guri daya ba zasu haura kwanaki biyar ba fa?. Hakan na nufin zai zamemata wani sabon aikin kenan wajen kawo qarshen alaqarsu da aurensu?. Ya kamata ta bari irin hakan yaci gaba da wanzuwa?,har takai sun fara musayar wasu dabi'u a tsakaninsu ita dashi?.

"Inason magana da ita.....zan isa zuwa dakin karatun inaso kuma kowa ya sani"

"An gama" Ta fada cikin girmamawa ta juya ta ficewa.

A yau fitar tata ta zama cikin salon da takanyi amfani dashi lokuta da dama. Wata irin tafiya tsakanin sassanta zuwa dakin karatun sultane din. A kowanne taku da zata gamu da bayi ko hadiman gidan kyauta ce take yinta. Kyautar kudade ga duk wanda suka hadu a hanya dashi. Wannan salon yana daya daga cikin wani hanya data bata daman mallakar zuciyar mutane da yawa dake rayuwa cikin masarautar,alkhairinta kuma ya danne na kowa........sai d'ai d'aikun da har a lokacin alkhairin nata ya gaza saya mata matsugunni a ransu ba tare da suma sunsan dalili ba.

*_SHEIKH MUHAMMAD HAISAM_*

Cikin lafiyayyar motar Mercedes Maybach S_class suke tafiya zuwa killataccen gidan dake cike da tarin tsaro. Killataccen gidan da almaz ya dade a cikinsa.......JINJIRI da har yanzu baida cikakken suna kuma D'A ga ajani ya zama cikon na biyun.

Yana zaune d'ai d'ai saman lausassar kujerun alfarmar da motar ta mallaka,yayi relaxing sosai cikin kujerar,dukkanin idanunsa a lumshe suke qasa qasa,zaka iya dauka bacci ne yake shirin saceshi. Sau uku omar yana daga idanu yana dubansa,sai ya bari ba tare da yace dashi komai ba. Iya yanayinsa kadai ya gaya masa 'yan miskilancinne suka motsa,dukkan alamu sun nuna bayason magana me zurfi....kaman yadda yake ganin alamun akwai wani kwantaccen fushi qasan ranshi.
Chapter 3 · 0% Book details