← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 160 OF 176

Sashe 160

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiye abun hannunta tayi ta tako tana marabtar akhnan din. Cikin kunya ta zame mata shirin gaidata amma saita rungumeta tana tambayar lafiyarta.

Tare suka baro kitchen din,nanay na mata tambayoyi game da lafiyarta. Sai data duba komai nata,tare suka zauna zaman cin abinci,wanda sai da suka zauna din sannan taji qarar da wayarta takeyi. Koda ta duba haisam ne. Ya tara mata messages da miscal saboda jinta shuru suna tsaka da magana,sai kawai tabi kiran.

Bugu daya ya dauka kaman daman jiran kiran yake daga gareta.

"I can't wait my princess,on my way,nan da fifty minutes zan qaraso" Tadan fidda idanunta tana mamaki,kafin ta sauke wayar sanda ta jishi ya yanke kiran.

Ga mamakinta,adadin wadannan mintunan su ya dauka taji shigowarsa shida guard dinsa. Ta lumshe ido a hankali sannan ta bude tana jin kamar wani sashe na jikinta ke dawowa gareta.

Sanda ya shigo nanay ta tayar da sallah bata parlor din. Ya bude hannayensa yana dubanta gami da jiran isowarta jikinsa kamar yadda suka saba. Sai ta noqe kafada,wannan ya sanyashi jefo qafafunsa da sassarfa yana fadin.

"Ba lokaci my princess......bazan iya jiran wannan jan ajin naki ba yau" Ya qaraso kusa da ita ya sanya dukka hannayensa yana shirin dagata

"Nanay" Ta fada da sauri tana zaro idanu waje,daidai sanda nanay din ke fitowa,sai yaja da baya yana shafa sassalkar sumarsa idanunsa a qasa.

Da wannan dabi'artata ta ta gani amma kaman bata gani ba ta zauna. Ya zauna qasanta yana gaidata cike da kulawa.

Su danyi hira kadan kafin ya miqe yana duban akhnan din.

"Ku jirani na fito sai muci abincin tare nanay idan ba damuwa" Ya fada idanunsa akan akhnan.

"Na kusa tafiya....amma idan baka zauna ba zaka sameni" Ta fadi tana duban agogon hannunta.

"Okay.....yanzun in sha Allah" Ya fadi idanunsa da fatansa dukka akan akhnan. So yake ta taso.....so yake ta biyoshi. Yanason yaji dumin jikinta,yana so ya aza hannunsa saman cikinta yaji tudin ajiyarsa. Yanaso ya shanshanata,ya shanshana qamshin nan nata. Yayi missing nata ba dan kadan ba.....yayi kewarta kaman ya dauki wasu kwanaki ba tare da ita ba. Amma har ya soma takawa zuwa ciki akhnan batayi niyyar wannan ba.

Koda ya shiga dakin sai ya kasa komai,ya cire socks dinsa da cufflinks dinsa,amma duka sai ya jefar. Yaji sam bashi da wani energy. Ya tako a hankali yana komawa bakin qofar dakin ya bude a hankali ya tsaya ta inda zai iya ganinta. Hankalinta kwance a gaban nanay,ya saki qofar ya koma da baya yana sauke numfashi. Daga ita har nanay kaman suna mantawa dashi idan suna tare,ya rasa wanne irin wariyar launin fata suke masa haka.

Sake takawa yayi ya koma bakin qofar,wannan karon kai tsaye ya kirata.

"Akhnan"

"Na'am" Ta amsa tana waiwayowa,suka hada idanu amma sai ta basar. Duk da tana jin kewarsa itama,duk da tanason zuwa gareshi,amma kunyar nanay takeji

"Ina kika ajiyemin kayan nan da na bari a gefan bedside" Da farko ta shiga tunanin wadanne kaya?,amma daga bisani data dago maganan da kuma yadda ya zuba mata ido sai dariya ta kusa zuwar mata.

"Suna inda ka ajiye....."

"Giiftii" Nanay ta kira sunanta.

"Na'am"

"Tashi kije gurin mijinki" Ta fada a nutse don ta fahimci komai ita. Sai data dan dakata kadan,sannan ta miqe a kunyace tana takawa zuwa dakin.

"Ki kula da kanki" Nanay ta fada a hankali,kalmar data saka akhnan ta kusa nutsewa a gurin.

Tasan yana kusa....amma bata dauka yana kusa da qofa haka ba,sai ji tayi ya jawota a tausashe cikin jikinsa.

Juyo da ita yayi suna fuskantar juna,idanunsa sunyi wani irin laushi cakude da gajiya da wani irin shauqinta da kewarta. Ya motsa labbansa a hankali da zummar yin magana.....amma saita hana masa wannan damar ta hanyar hade bakunansu guri daya.

Wani irin fitinannen kiss take ajiye masa wanda ya qarasa cakuda hankalinsa gaba daya,ya sake ingizashi wata duniya data sanya ya gaza komai,har sai daya dauketa cancankat dinta ya maidata saman bed din.

Zazzafar maraba ya samu da wata irin tarba ta musamman data sanyashi jin kamar sannan komai yake wakana bayan kammaluwar lamarin. Baisan kowacce mace a duniya ba sai ita....a kanta ya fara sanin me ake kira da wannan abun....amma shi kansa ya tabbatar yayi imani ita din ta musamman ce. Ya sani ba shakka samun irinta cikin mata kadanne.

Tasa hannu kaman zata tsone masa idanu saboda yadda yake faman qare mata wani narkakken kallo sanda kawunansu ke saman pillow daya suna huce gajiya.

"Nanay tayi kuskuren fahimta......ina jinta tana cewa ki kula da kanki.....batasan yaronta ba,Allah sarki,yanzu ya zama salihi......diyarta ita ce fitinanniyar" Yadda yayi maganan dole ya bata dariya. Ta cusa kanta cikin pillow tana qyalqyalawa.

Ita kanta da farko abun yayita bata tsoro,har ta kaita ga yin binciken dalilan dake sawa buqatar mace ta qaru. A cikin jerin sawun taga harda pregnancy saboda sauyawar hormones,hauhawar wasu daga ciki.

"Shikenan.....yallabai yarimana ayi haquri,yanzu dai kada na takurawa ya sheikh,ya kamata na tafi hutu koda na sati biyu ne....."

"Wallahi baki isa ba...." Ya furta yana cafkota sanda take qoqarin sauka daga gadon ba tare daya bari ta gama furta abinda zata fadi ba.

Dariya sosai ta saki,saboda yadda yayi wata sufa yana kamota. Sai shima daga baya abun ya sanyashi sakin tattausan murmushi me qaramin sauti.

"Wannan tsarin shine daidai na.....ta yaya zakimin qauro?" Ya fada yana matseta cikin jikinsa.

*_BAYAN WATA BIYAR_*💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 147*

Sannu a hankali kwanaki ke juyawa suka bada wadannan watannin. Watannin da suka maida cikin akhnan ya zamana wata takwas daidai da wasu 'yan kwanaki.

Cikin 'yan biyu ne kaman yadda scanning ya nuna musu,amma yayi wani irin girma daya sanya haisam ya sake maidawa gami da tattara dukka hankalinsa a kanta.

Komai kusan da wahala yake zuwa mata.....amma duk da wannan wahalar abubuwan sai suke juye mata da sauqi saboda kasancewar jajirtaccen namiji a gefanta. Uwa uba kuma taimakon amintattunta irinsu birra,wanda numfashi ne kawai basu da ikon suyi mata,amma komai da take buqata saidai idan bata nuna hakan ba.

Yayin da cikin ke qara girma wata bayan wata,cikin zuciyar Haisam ma wani abu ke sake canzawa.

Ba soyayyarsa ga Akhnan ce kawai ke qaruwa ba......Aah,wani irin girmamawa yake mata ta musamman. Tattalinta da tattalin dukka al'amuranta.

Musamman da aka wayi gari akhnan din ta zama cikakkiyar mace a gareshi.

Bata damu da nauyin da take dauke dashi ba......bata damu da irin matsayin da Allah ya bata ba. Bata kuma damu da gidan data fito ba.....shi MUHAMMAD HAISAM shi dinne kawai a gabanta. Ta yaya zata faranta masa?. Ta yaya zata kula dashi?. Musamman data fara fahimtar irin yawan matan da zuciyoyinsu ke yawo a kansa. Yawan matan da burinsu a ko yaushe shine yadda zasu mallakeshi da komai nasa.

Tun daga rainon cikin ta sake jin wata sabuwar soyayya da qaunar mahaifiyarta. Tun a sannan ta sake ganin kimar morsa safiyya....nanay....dama duk wata uwa da zata bude ido ta ganta rungume da yaronta.

Ta shiga wani sabon yanayi gaba daya. Wasu kwanaki tana cike da kuzari.
Wasu kwanaki kuma tana gajiya da qananun lalure lalure.

Amma duk da hakan,ta zabi ta zama jarumar uwa. Ta zabi ta zama jajirtacciyar mata me tsananin kulawa da mijinta da komai daya shafeshi.

A irin wadannan lokutan haisam ya koyi abu guda daya. Biye mata da kuma lallashinta cikin kowanne yanayi.

Ta zama wata mafadaciya me saurin fushin da babu dalili,takan iya sanya masa kuka haka siddan ba tare da yasan yayi komai ba. Duk lokacin da ta ce

"Ban san me yasa nake kuka ba." Sai kawai ya jawota jikinsa.

"To ki yi kukanki.....yi kukanki yadda zaiyi miki"

"Ba ma san dalili ba fa." Takan maimaita fada wani lokaci cike da tsoron kanta da kanta na yadda komai da komai da yadda yanayinta yake sauyawa.

"Ba lallai sai kin sani ba." Zai sake amsa mata da kulawa a tausashe. Hakanan sai ya zauna yana lallashinta,tsadaddun lokutansa duka ya sarayar mata har sai ta gama.

A gefe guda kuma duk wasu harkokinsu basu fasa garawa ba. Kamfanonin su na ci gaba da bunqasa.....kasuwancin na wani irin habaka daya bawa haisam mamaki cikin watannin.

Sau daya ya taba jin wani yana fadin,wani lokaci wani arziqin silar aure Allah yake sake bude maka shi. Baisan adadin abinda ke shiga account dinsa ba kullum rana. Sabbin yarjejeniyoyi na shiga. Sabbin cinikayya na budewa.

Sau tari ana iya samun Haisam a babban conference room yana tattaunawa da manyan shugabanni. Yana yanke shawarar da zata iya motsa miliyoyin daloli.

Amma a tsakiyar meeting wayarsa zata yi haske,message daga giiftii dinsa zai shigo. Ko yaya ya fita suna tare akan waya. Tun tana cewa ya maida hankalinsa kan ayyukansa idan ya fita harma ta daina ta biye masa. Haka kawai tsakiyar meeting yana iya daukan break,kowa sai ya jira,yakan shiga rest room ya zauna ya kira takanas don yaji muryarta da lafiyan yaranshi. Yaran da tun kafin suzo duniya batasan irin soyayya da mutane da dama ke gwada musu ba.

Duk muhimmancin meeting idanunsa basa gaza sauka kan message dinta. Murmushi yakan bayyana a gefen lips dinsa.

Abin da ma'aikatansa suka daina mamaki da gani,wannan murmushin da idan ka ganshi saman fuskarsa to tabbas yana da alaqa da princess dinsa.

Su kansu yanzu sun sani......CEO dinsu ya zama mutum daban idan maganar matarsa ta shiga.

Sannu a hankali akhnan ta fara shiga wasu daga cikin ayyukan kamfanoninsu daga gida. Ba wani dogon stress ko aiki me wahala ba. Saboda Haisam ya hana ta wahala sam sam.

Tana bibiyar reports,tana ba da ra'ayinta akan abubuwan da suka shafi gudanarwa,tana shiga online meetings idan tana da kuzari.

Da wani yammaci suna zaune a library na gidansu.

Takardu ne a gaban haisam,akhnan kuma laptop.

Yayi nisa qwarai cikin lissafin ribar da sahel couture ke kawowa,wata irin riba me ban mamaki cikin watanni kadan da ci gaba da gudanar da kamfanin wanda akhnan ke jagoranta daga gida.

Da tare suke aikin,sai yace ya bata break,ta zauna tayi relax kawai na wasu mintuna. Sai data huta sannan ya kalleta.

"Time up" Ya fadi yana dubanta,sai ta dage girarta tana murmushi. Sai da yaga taci gaba sannan ya maida hankalinsa ga takardun da yake lissafin.
Chapter 160 · 0% Book details