← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 176

Sashe 156

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi ya sake bude mata motar, ya zagayo ya riqe hannunta yana fiddo da ita, sannan suka fara takawa zuwa cikin gidan yana amsa gaisuwar bayi da hadimai da wani irin yanayi dake nuna asalin izza da sarautar dake yawo a jininsa.

Faluka bayan faluka suka dinga ratsawa shida ita. Tako Ina gaisuwa ce cikin girmamawa suke karbarta shi da Akhnan din.

Sanda suke isa sitting room na qarshe da zai sadasu da inda nanay tafi zama,a daidai lokacin take shigowa itama ta daya qofar da ahalin gidanne kawai suke using wannan qofar, Kamar yadda yake akwai kebantattun gurare da iyasu dinne kawai ke da access da gurin.

Ganin farko data musu taji wata matsananciyar faduwar gaba ta saukar mata. Wani irin kyau suka mata me daukan hankali. Kwarjininsu,da kalar matching din da sukayi da juna abune da idanu ba zasu iya kaucewa a kansu ba.

Har tayi taku daya baya,amma wata zuciyar me cike da kishi ta bata shawarar dawowa. Ba musu ta tako a hankali zuwa gabansu.

"Barka da shigowa obbo" Ta fadi da wani yanayi na girmamawa sosai cikin muryarta,da kuma nuna kulawa. Yanayin daya tafi a hankali,kai tsaye kuma ya sauka a zuciyar akhnan.

"Yauwa" Ya fada a taqaice idanunsa suna kan hanya. Ta dan saci kallon akhnan. Ko yaya tana so tayi abinda zata qona mata rai,tanaso ko yaya ta motsa wannan izzar tata.

"Kamar nanay tasan zakazo,tace na hada mata coffee me yawa na kawo mata" Ta fada da murmushi a fuskarta tana dubansa. Abun yadan masa banbarakwai,amma hankalinsa sam baya ta gurin,sai ya waiwaya yana duban akhnan din.

"Mu qarasa?" Kai ta gyada masa a nutse,sai ya sake ware hannayensa yana sarqesu da nata kamar wanda akace za'a qwacewa ita.

Akan idanunta yayi hakan,bata sare ba ta murmusa kadan.

"Idan ba damuwa na maka iso,kaman ta zauna zaman addu'a" Ta fada da girmamawa,amma yadda tayi gaba ba tare data damu da miqa wannan girmamawar ba yaja hankalinsa.

"Saamee" Ya kirata kai tsaye. Har cikin ranta taji saukar sunan,wani abu me sanyi ya lullubeta,don ta manta yaushe ne na qarshe da taji ya kira sunanta. A ladabce ta waigo tana amsawa.

"Wannan ya zama karo na qarshe da zakiga matata ki wuceta ba tare da kin gaidata ba.....ina fata baki manta hukuncin dake kan duk wanda ya aikata hakan ba". Wani irin qasqanci zallarsa taji yana mamayarta. Wannan maganar tasa tana daidai da tuni daya mata gami da maidata asalinta na DIYAR BAYI. kenan....hakan na nufin ba'a canzawa tuwo suna?. Hakan na nufin ita ba diyar kowan kowa bace har yanzu ba abinda ya shafe wannan?.

"In sha Allah" Ta fada a sanyaye,sannan ta waiwaya sashen akhnan.

"Barka da isowa"

"Na gode" Akhnan din ta amsa still ba tare daya dubi sashenta ba.

Wani abune ya mata tsaye a zuciyarta,wasu irin dabi'u take karanta tattare da saame wadanda suke bata haske kan inda ta nufa.

"Ba buqatar kiranta....zan qarasa da kaina" Akhnan tace da saamee sanda take shirin isa ga nanay ta sanar mata isowarsu. Saita tsaya cak tana jin kamar an sace mata gwiwa,sannan taja baya a hankali sanda akhnan ke tattakawa riqe da hannun haisam ba tare data sakeshi ba.

Dole taja gefe ta basu hanya,sannan ta koma da baya a hankali tana barin gurin.

Suna shiga ta zame hannunta daga nasa,saita ja baya kadan tana duban idanunsa. Haka kawai ta samu kanta ta watsa masa harara.

"Ban yarda kowa ya shiga tsakanina da sultane ba.....wai har don saboda inason ganin mahaifina sai anmin iso.....haka yake game da nanay. Ban gayyaci kowa gurin neman iso kan ganin mamana ba" Ta qarasa fada tana sake miqa masa wata hararar sannan ta fara takawa.
call

"Tun wuri ka gaya mata. Bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane....idan da wani tunani da take dashi a kanka,ka gaya mata ta daina,tun kafin ta shiga inda ba zata iya fitowa ba" Ta dan matsa kusa da shi, idanunta cike da kishin da take qoqarin boyewa.

"Tana kirawa kanta tashin hankalin da mutane duniya duka basu isa mana sulhu ba"

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"ni khadeeja muhammad hammud ba sa'ar kowa bace". Wani lallausan murmushi ne yake fita ta gefan bakinsa,idanunsa zube fes a kanta. Idan tana nuna kishinsa irin haka,shi kadai yasan yadda abun ke burgeshi,shi kadai yasan yadda abun ke masa dadi. Hararsa ta qara yi,yanayin daya sanya idanunta suka masa kyau.

"Kaima kada ka sakemin wannan murmushin"

"Which smile?" Ya tambaya cikin nutsuwa kuma kai tsaye still yana kallonta.

"Wanda yake nuna jin dadin abinda nake fada" Ta sake fadi wannan karon harda murguda masa wannan qaramin bakin nata. Dariya ta kusan subuce masa,yadda ta koma me tsiwa sosai cikin lokaci kadan. Wannan tsiwar da yake hange daga nesa.....yau gata kusa dashi ana gwada masa.

"You're jealous" Ya fada murmushinsa yana qara fadada. A hankali ta bude bakinta don ta musanta,amma saita kasa hakan,ta kauda kanta gefe tana tura baki gaba.

"Duk yadda ka dauka" Sai ta fara takawa zuwa ciki.

"Akhnan." Ya kirata yana jin yadda idanunsa suke narkewa a kanta. Ba tare da ta juyo ba ta amsa.

"Me kuma?"

"Kin makara." Ta hade gira.

"Makaran me?" Ya jingina da bangon dake kusa dashi yana kallonta

"Da wannan kishin." A hankali ya qara da fadin.

"Da kin zo shekaru da suka wuce,da kin samu abin kishi." Sai ya girgiza kai.

"Yanzu kuwa..." Ya dakata na dan sakanni.

"Babu wanda nake gani sai ke." Akhnan ta ji yadda zuciyarta ta yi wata irin bugawa,amma duk da haka ta qi ba shi nasarar gani a fuskarta. Sai kawai ta sake jefa masa harara,wacce a wannan karon ta fi kama da murmushi fiye da fada,ta kuma juya abinta tana shigewa zuwa ga nanay.

Cikin nutsuwa ta yiwa nanay cikakkiyar sallama,nanay din dake saman abun sallah rumaisa a gabanta da alama magana suke ta amsa tana d'aga kanta zuwa ga akhnan din.

Wani faffadan murmushi me cike da qauna da soyayya ya kubcewa nanay din.

"Giiftii.....fitowa kikayi?,haisam bai gaya miki zanzo da kaina na ganku ba?" Nanay ta fada cikin kulawa tana duban akhnan da tarin soyayyar da irinta takewa mahaifiyarta safeena.

Qasa akhnan din tayi da kanta,tana jin wata matsananciyar kunyar nanay da bata taba jin irinta ba. Haka kawai takejin all over her body nanay na ganin komai. Komai da sukeyi ita da haisam din,dama yadda haisam din ya lalatata a kwanakin nan. Ashe haka surukutar take?,take tambayar kanta sanda takejin ba zata iya hada idanu da nanay ba sanda nanay din ta miqe da kanta tana marabtarta.

"Maraba da diyata" Nanay ta furta tana budewa akhnan hannuwanta don ta rungumeta.

Idanun nanay din a kanta sanda take takowa,mamaki kadan yana kama nanay din da yadda akhnan din ta wani bude lokaci guda tsakanin tafiyarsu da dawowarsu. Ta sauya gaba daya kamar sai a yanzunne mijinta ya santa diya mace.

Wani abu ya d'arsu a zuciyar nanay din sanda take rungume akhnan a jikinta.

"Barka da warhaka nanay" Ta fada tana rusunawa cikin jikin nata. Riqeta tayi sosai a jikinta.

"Banason ganin wanna surukutar cikin idanunki giiftii.....ke din kamar rumaisa kike ko Aanani,matsayinki ma a zahiri ya d'ara wannan" Ta fada tana dagata daga jikinta gami da mata mazauni saman shimfidarta data tashi a kai. Rumaisa na zagayowa tana zama gefan akhnan din gami da leqen fuskarta sosai. Ita kanta mamakin sauyawar giiftii din tasu takeyi,wani ajiyayyen kyau tayi me matuqar daukan hankali duk da tarin kyan nan nata.

"Giiftiin Captain.....kina kallon madubi kuwa?,anya captain sheikh zaici gaba da barinki fita koda tare zaku fita din?" Ta tambaya da gaskiya cikin muryarta.

Ture hannunta kadan akhnan tayi cikin jin kunya tana mata nuni da nanay da idanu. Nanay din da tayi kaman bata ji ba,saidai zuciyarta tayi nisa a wani tunani.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 143*
________________________
https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa ameen*
__________________________

"Ina ya tsaya shi muhammad din?" Nanay ta tambaya tana zama sosai saman shimfidartata,saidai tana sauke maganan muryarsa ta bayyana.

"Yaya za'ayi ki ganni nanay.......gani nan a tsaye kusan minti nawa.....amma nanay wai baki ganni ba tambayata ma akeyi" Ya fada da wani yanayi daya sanya rumaisa sakin boyayyar dariya. Murmushi nanay ta saki,tasan kishinsa da yadda bayaso a shiga tsakanin soyayyarta da shi.

"To qaraso mana" Ta fada tana daga masa hannu. Kafada ya maqale yana komawa wani kalan tausayi.

"Alqawari nanay......nima na cancanci a marabceni" Murmushi tayi ta kauda kai.
Chapter 156 · 0% Book details