← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 176

Sashe 33

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tasha ajiye masa litattafai da suke magana akan illolin zina kowacce iri,tasha zaunar dashi ta masa wasu tambayoyi da yakanji kunya qwarai.....amma daga sanda ya soma mallakar hankalinsa......daga sanda ilimin addini ya ratsashi sosai sai ya fahimci yadda zai bawa kansa kulawa,yadda zai kare kansa daga kowacce irin illa ta zina.

Tun daga sannan.....tun daga wadannan shekarun ya tsaya akan azumin litinin da alhamis.....tun daga sannan ya sake nesanta kansa da kalar kowacce mu'amala data hada da mata a ciki,kowacce iri ce idan bata zama dolen dole ba. Daga sannan ya maida kansa busy sosai akan aikinsa......akan komai da yasan zai dauke masa hankali daga kowanne tunani na diya mace.

Ya sake cusa kansa akan cases masu hadari da wahala sosai a national intelligence security service saboda ya samu ya nisanci kowanne tunani. Yana da burikan da yakeson cimmawa tukunna.....yana da tsarika masu yawan gaske da barin mace ta shiga rayuwarsa a wannan lokacin karyewarsu ne kawai.

Bai taba ganin halittar kowacce d'iya mace muraran irin haka ba kaman yau......shi daya yasan da yadda yayi controlling qafafunshi suka dawo dashi daki.....shi daya yasan da yadda yaketa kokawa da numfashinsa.....idanunsa da yakejin wani abu ya cika masa su.

Ya isa gaban dressing table din dake dakin,ya xube dukka hannayensa akai gami da sadda kansa yana qoqarin daidaita nutsuwarsa da numfashinsa dake masa wani wahalan zuqa da daidaituwa cikin hunhunsa.

Idanunsa a lumshe suke sosai,saidai still hotonta gake gani a ciki,ya dunqule hannunsa guda daya ya daki dressing table din yana kiran sunan Allah. Ji yake kaman hankalinsa zai rabu da gangar jikinsa.....ji yake kaman ya koma.....kaman ya koma ya sameta.....ya rungumeta cikin jikinsa da yanayin da zata mannu sosai a qirjinsa. Ji yake kaman yaje ya kamota cikin jikinsa ta kuma tabbata cikin jikin har sai abinda yakejin ya lafa.

A daidai wannan yanayin da yake ciki ta fado fadin. A gigice take,gigicewar da bata barta ta lura da halin da yake ciki ba,sai kawai qoqarin riqo hannunsa da takeyi tana magana a rude.

"Falaak......falaak tace zai kasheta.....don Allah ka taimakeni muje....kada wani abu ya sameta". Duk da a rude take amma shi a tsaye yake cak......a tsaye yake cak yana binta da kallo,a tsaye yake kaman an dasashi yana bin sassan jikinta da kallo,yadda take maganan tana girgiza hannunsa sai ya zamana kamar suna suna motsawa ne don su nuna motsin da take ya isa har inda suke.

"Ya salam.....ya Allah.....wai bata gani ne ba?,bata fahimta?" Ya fada yana jin 'yar guntuwar nutsuwar daya soma kokawar samowa tana silalewa.

"S’il vous plaît(please)" Ta qarasa fada tana riqe hannunsa da kyau har tana shigewa jikinsa ba tare data ankara da abinda takeyi ba.

"Najiiiiiii" Ya fada yana fusgar kalmar da qyar gami da dan tureta kadan daga jikinsa yana jin kamar zai zauce tafukan hannunsa akan kunnensa duka biyun kamar wanda numfashinsa ke shirin daukewa.

_busy,sorry please_🙏🏽

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 31*

Turetan da yayi sai ya sanya taji a ranta kamar yanaso ne yaqi kaita. Tsoro takeji sosai......zuciyarta bugawa takeyi,tana tsoron wani abu ya samu falaak. Falaak ce fa?,jininta,ita kadai ta rage mata a yanzun,bata da wani makusanci kamar falaak din a yanzu.

"Pleaaaaaaaseeeee" Ta sake fada hawaye suna gangaro mata tari da sakewa hannunsa mugun riqo tana kuma shigewa jikinsa,duk a qoqarinta na amintar dashi ya kaita.

"Sub.....hanallah" Ya furta labbansa suna motsawa,numfashinsa yana fita a rarrabe. Kusancinta a gareshi wani irin sake haukatashi yakeyi. Wai ita bata gani bane?,bata gani?,bata lura da idanunsa?,iya idanunsa kadai shi kansa yasan tarin fitina ce da babu ruwan kasheta a nan kusa.

"Don Allah" Ta fada a wani irin narke daidai da yadda takejin zuciyarta ta karye.

"Kisa fa......kasheta tac......"

"Nima kasheni kikeyi........kasheni kikeyi biftuuuuuu" Ya katse numfashinta da maganar da batakai ga qarasawa ba da wani irin birkitaccen sauti tana riqe fuskarta cikin dukka tafukan hannayensa gami da matso da fuskokinsu dab da juna.

Cak zuciyarta ta dakata da bugu na wucin gadi kafin ta koma aikinta da wani mahaukacin gudu na wuce sa'i. Wani zazzafan numfashi da yake sauke mata saman fuska shine abu na farko daya fara sanyata dawowa cikin hayyacinta.

"Kina kasheni nima......don Allah......" Sai kuma ya kasa qarasawa saboda hannuwanshi da suka dauki rawa. Blue eyes dinta ta fiddo waje,har yanzu tunaninta baikai can ba,saidai wani yanayi na tsoro daya d'arsu a ranta jin yadda tafukan hannuwanshi ke rawa jikin fuskarta. Hannunta daya ta dora saman nashi tana riqewa sosai.

"Me nayi maka?,......ban maka komai ba....Allah ban......"

"Kinmin biftuuuuuu......kinyimin mana" Yayi maganar da sound na rada,yana sake kusanta fuskarta da nashi fuskar,sannan ya hade fuskokin nasu guri daya ta hanyar hade goshinsu da hancinsu guri daya,ya saka daya hannun nasa ya riqe bayan wuyanta sosai yadda ba zata iya qwacewa ba,sannan ya riqe qugunta da daya hannun yana son matso da ita jikinsa ya hade kusancin dake tsakaninsu.

Sai a sannan jikinta ya dauki kyarma,kusancin ya fara mata yawa......iya numfashinsa da suke musaya ta bashi nata ya bata nashi kadai sai ta jishi da wani irin nauyi da girma ba. Ba wannan ba......sanda taji lallausan tafin hannunsa saman fatar cikinta......wani irin zabura tayi,zaburar data raba fuskokinsu saidai bata kawo tazara ko qanqanuwa a tsakaninsu ba.

Still bai saki wuyanta ba,hannun nasa tayi caraf ta riqe,sannan ta daga idanunta tana duban qwayar idanunsa. Wani irin abu taci ya hautsina cikin kanta ya daki zuciyarta,wani irin mamaki da tsoro,wadannan manyan fararen idanuwan......wadannan idanun dake da wani irin haske da girma,a yanzun basu taki gani ba. Qananun idanuwa da suka qanqance..... Masu launin ja da wani irin abu a cikinsu daya cikasu taf.

Kai yake juya mata a hankali kamar meson yayi magana amma ya kasa,kaman yadda itama ta matsa qaimi gurin riqe hannunsa cikin nata tana juya masa nata kan,sannan ta fusgi.kalmar

"A'ah.....a'ah" Dukkanin ilahirin jikinta itama yana kyarma. Idan ta fuskanta,idan kuma ta gane yanason yayi sama da hannayensa ne ta qasan rigar. Saman da zaiyi dasu din kuwa daidai yake da ya sanya hannunsa tsakiyar dukiyar fulaninta?. Wannan gurin?,wannan muhallin da take matuqar tattalinsu?,muhallin da tun daga fara tsiruwarsu bata sake bari koda idanun mammina bare hadimanta yakai kai ba yau shi can yakeson isa.

"Aah" Shima ya maimaita fadi mata......kamar akwai abinda yakeson cewa amma bakinsa ya sarqe.....kamar akwai abinda yakeson ya fada amma sam harshensa yaqi bashi hadin kai.

Jin yadda ya zame hannunsa a haukace yana ci gaba da tafiya dasu zuwan saman ya qarasa birkitata.

"Don Allahhhhhh....." Ta furta tana barkewa da wani irin kuka me dauke da siririn sautin daya dace da lallausar muryarta.

Kuka.....wani abu guda daya dake da tasirin karyashi,wani abu daya da baya qauna sam game da diya mace......a yanzun a hankali ya daki kunnensa ya fara karya duk wani lagonsa.

"Why?" Ya fada can qasa da wani irin sauti daba lallai ka gane ba sai idan labbansa da sukayi jaa ka kalla.

Kamar an yashe tunaninsa da komai nasa completely haka yakeji,baisan yadda akayi ba yadaiji ya fusgota jikinsa sosai,ya mata wani irin mugun riqo,sannan a zafafe ya lalubi bakinta data soma masa wannan kukan dashi ya riqe lips dinta da wani irin salo me taushi amma tafe da zafin nama.

A hankali ya soma zagaya lips dinta da harshensa. Yanaso ya dainajin wannan sautin kukanne.....yanaso ta daina cika masa kunne da kukan da tuni zuciyarsa ta yanke kukan sakalci ne. Abinda ya qara adadin yawan rawar da jikinta yakeyi,tayi qoqarin zamewa amma bai bata wannan damar ba,don gaba daya ya sake manneta a jikinsa,ya kuma tura harshensa kai tsaye zuwa cikin bakinta ya fara sauke mata wasu abubuwa dashi kansa baisan yadda akayi ya iya sauke mata su hakanan da zafinsu ba.
.
Matsanancin tsoro ya dirar mata a sanda shi kuma hankalinsa yayi nisa. Kamar zai hadiye dukka bakin dama komai da komai da yake cikinsa haka yakeji. Yana tunanin samun relief ne......amma sai ya zame masa kamar iza wuta yakeyi da makamashin kara me saurin kunnuwa. Wani irin sound yake sauke mata daya sake rudata ya sanyata tsananin firgicewa. Kuka takeson masa da qarfinta amma bai bata wannan damar ba saboda yadda yake sarrafa bakinta kamar abinda aka halicceshi yayi kenan a duniya. Tsoro ya hanata iya tsaiwa da qafafunta.....yanayin daya shiga ya zare Shima duk wani kuzari nasa,sai gasu suna shirin zubewa qasa warwas,abinda ya taimaka gurin kado da hankalinsa kenan ya sake mata baki da wani irin yanayi me matuqar zafin da idanunsa suka birkice gaba daya kamar ba nasa ba. Sakin da ya yi mata na sakanni su suka bata daman fashewa da kuka tana jin wani abu yana shiga zuciyarta a hankali bayan tsoron.

Ta dauka zai saketa ne........amma sai ya hade jikkunansu guri daya da wata irin wawiyar runguma kamar zai ballata gida biyu. Rungumar data bashi daman jin saukar duk wani tudu da kwari na jikinta daya tsone masa idanu......yaji saukarsu sosai a kowanne sashe na jikinsa,abinda ya sanyashi jan waga doguwar ajiyar zuciya kamar zai hadiye zuciyarsa gaba daya sannan ya saki wani irin numfashi kamar zai fidda hunhunsa gaba daya,sannan jikinsa gaba daya ya bada wani reaction kaman an girgizashi kafin yayi collapse a jikinta,kaifi da qarfin rungumar da yayi mata ya soma sassauta a hankali,saidai duk da haka bai saketa ba gaba daya ba. Abinda yayin sai ya d'arsa tsoro a zuciyar akhnan da idanunta suke jage jage da hawaye. Kada taje ko shima ya mutunne ace itace ta kasheshi?. Ta tattara dan qwarin gwiwarta ta motsa labbanta da takejinsu kamar ba'a jikinta ba ta furta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Chapter 33 · 0% Book details