← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 176

Sashe 63

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bawai ya samu dukkanin nutsuwa bane.....amma yana qoqarin kame kansa ne kawai. Mamaki ne can qasan ransa. A shekarunta?,a wayewarta?,tana nufin bata da masaniya akan irin wannan abun?.

Kamar bazai gamsu da haka ba.....amma wani halint guda daya tal na fadi da yin abu kai tsaye ya sauya akalar tunaninsa. Ya tuna yadda ta sauyawa falaak bayan ta tabbatar da abinda ya faru,t juya kaman haushinta takeji......wannan duka yana cikin tarko da plan din mammina?,ko tsabar yadda ta killacw rayuwarta take sarrafata cikin tafukan hannayenta ya kawo mata wannan naqasun?.

Baida amsa sam,don haka ya mirgina da sauran kuzarinsa don sauka yayi wanka,don a lokacin yanayin duhun magariba ya tabbatar masa an riga an kammala sallar magariba din.

Miqewar da yayi yaji mararsa a qulle sosai. Zafin ya ratashi sosai,yasan hakan zata iya faruwa,don lokaci lokaci yana fuskantar irin wannan issue din.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 57*

Duk da haka ya taka a nutse yana wucewa bathroom. Ta mirgina tana sake qudundunewa cikin duvet. Da gaske kuka take,tana jin ranta yana baci,ba wani d'a namaji daya taba ganin koda singalilin hannunta,amma shikam yanzu ba inda hannunsa baikai a jikinta ba sai gu d'aya tak.

"Dama shima haka yake?" Ta fada can qasan ranta tana tuna falaak. Falaak din da har yanzu take mamakinta,don zuwa yanzun ma ba'asan a wacce qasar suka yada zango ba,don ba'a maganan zuwansu Ethiopia yanzu.

Motsin fitowarsa ya dawo mata da tunaninta,ta daga idanunta a sace ta qasan duvet tana satar kallonsa,saidai ba shiri ta zuqe kanta ta.maidashi cikin duvet din jikinta na rawa.

Towel kawai ya dauro,towel din da ya fara ne kawai daga qugunsa ya rufe iya shafaffen cikinsa. Dukka muscles din da suka lullube jikinsa a bayyane suke,wani siffan qarfi sosai da dama koda ta cikin jallabiyyarsa kana iya ganin alamun hakan.

"Zaki iya tashi?,ko kina buqatar taimako?" Ya fadi sanda ya kammala maida kayansa neat,saidai kuma bai saka 'yar saman suit dinsa ba,hakan ya sanya kana iya ganin dan squeezing din rigar tasa tayi. Yayi maganan ne yana tsaye daga can gefe,ya saba 'yar saman suit din nasa a kafada.

Zabura tayi da maganan da yayi,tana tuna wancan ranar da yaso daukarta cak ya kaita bathroom din,saita tattare duvet din yana rinjayarta tayi bathroom din.

Murmushi kawai yayi,wani kalan murmushi dake qunshe da manufofi da dama. Akwai wasu abubuwa masu yawa tattare da ita......wasu suna bashi mamaki ne suna kuma sauya akalar tunaninsa a kanta,wasu kuma sanyashi suke yana tantamar anya itace?.

Ta jima sosai a bandakin,ita daya tana kumbure kumbure gami da share hawaye. Itakam inda tasan haka yake da bata yarda ta biyoshi ba,koda meye sultane zaiyi kuwa. Yanzu da wanne ido zata kalli sultane?,me zatace dashi?. Ba sultane kadai ba,kowa ma gani take zai iya ganin komai a jikinta.

Amma abun haushin,abun takaicin,maimakon taji tsanarsa a ranta ko haushinsa.....saita laluba zuciyarta taji babu ko daya,sai alamun saukar hannuwansa a jikinta da takeji tako ina,kamar a yanzu komai yake faruwa.

Ta fito daga wankan bayan dadewar da tayi,tanaso ya tafi ne don batasan da wanne ido zata kalleshi ba. A yau dai kam bata da wannan juriyar.....bata da wannan zarrar da zata iya hada idanu sam dashi.

Knocking da akayi na qofar ya saka gabanta faduwa,ba'a shigo ba,saidai taji sautin muryarsa daga waje.

"Idan kin gama shiryawa ki fito,lokacin sallah zai wuce". Baki ta tura gaba,me yasa bazai tafi ba?,wai me yasa ma bayajin kunyarta ne?,sai ya gama lalubeta hankali kwance kuma yaci gaba da harkar gabansa hankalinsa kwance?.

Da qyar ta kammala shiryawa cikin wata yalwatacciyar abaya royal blue data haska fatarta sosai. Kamar me tsoron haduwa da wani abu take kowa inda yake.

Yana zaune very calm,kamar ba shine ya danneta dazu dazun a daki ba ya gama lalube komai nata ba. Coffee yake sha cikin wani mug,idanunsa suna kan wayarsa daya ajiye a table din gefansa,batasan abinda yake kalla ba.

Narkakkun idanun nan nasa ya dago ya zuba mata,ta janye dubanta da sauri. Me yasa a duk sanda ya gama mata wannan abun maimakon taji ta tsaneshi.....ko tana jin haushinsa.....ko girmansa da kimarsa sun zube saidai taga ya sake mata wani kwarjini na musamman?.

"Bismillah" Ya fada yana hawa saman lallausar abar sallar dake shimfide tana fuskantar alqibla.

Wata irin nutsuwa,wani irin kwanciyar hankali taji yana ratsata sanda yake rera karatun alqur'ani a duka sallolin. Har taga kaman ma yayi saurin idar da sallolin gaba daya,duk da bayan sun idar ta duba agogo sai taga mintunan daya dauka sun ninka adadin mintunan data saba yi idan zatayi sallarta ita kadai.

Wani irin shuru ya ratsa gurin,tayi qasa kawai da kanta,tanason miqewa ta wuce ciki amma zuciyarta ta gaza bata wannan qwarin gwiwar,kawai sai ganinsa tayi ta juyo yana fuskantarta,ya kuma zauna sosai saman dardumar.

Dukkan idanunsa ya zuba mata,a hankali kyawawan labbansa suna motsawa yana karanta azkar din bayan sallame sallah. Kafin ya kammala azkar din ya sanya zuciyarta tana dab da rikicewa,ya shafa addu'ar sannan yaci gaba da kallonta kamar abinda yazoyi duniya kenan.

"Me yasa kike fushi?" Yayi tambayar kansa tsaye yana tsareta da idanu. Da sauri ta daga kanta sai kuma ta sauke,batason ko yaya ta bashi qofar karantarta,don haka ta tattara dukka qwarin gwiwarta tace.

"Fushi?....."

"Karki qaryata.....kada ki musa,na gani a idanunki" Ya furta can qasa yana sake dafata da idanunsan nan masu tarin dafi da wani magnet me qarfin gaske.

"Ba zaki iya kokawa da abinda yake cikin zuciyarki ba.....amma idan zaki iya na baki dama" Ya fada yana miqewa tsam yana gyara daurin agogon hannunsa.

"Gobe zakiyi baqi" Maganansa na yanzun ya sakata daga kanta badon ta shirya ba,sai shima akayi sa'a idanuwanta yake kalla.

"Mama na.....mamana zatazo" Idanun ta sauke qasa a hankali. Sai taji wani abu me nauyi yana ratsata,wani yanayi da ya saukar mata da tsananin kewar mahaifiyarta lokaci daya.

Ashe yana da uwa?,yana da mahaifiya?. Haka kawai saita samu kanta da son ganin mamarshi,idanu da zuciyarta suka shiga wassafa mata yadda take a cikin tunani da hasashenta.

"Ba wani abu.....bakya buqatar komai?" Ta tsinci muryarsa dab da ita. Kadan ta motsa baya tana lumshe idanunta bugun zuciyarta yana son canzawa. Kai ta girgiza masa,saidai har lokacin tana jin alamunsa a kusa da ita,har lokacin bataji alamun ya janye ba

"Goodnight" Taji ya furta a hankali da yaren France da yake sake fusgar hankalinta dashi.

Bata iya bude idanunta ba har sai data daina jin alamunsa. Ta waresu a hankali tana sauke dubanta akan hanyar daya wuce din. Zuciyarta ta matse kadan sanda take raya mata ya fita.....ya fita daga gidan,wani fili taji zuciyarta tayi,wani sarari da zuciyartata take raya mata kamar akwai wani abu da yayi nesa da zuciyarta.

Abubuwansa da yawa mamaki suke bata......amma irin wannan abinda yake matan.....baya masa nauyi?,bayajin kamar be kyauta ba?. Wa zata kira tayi maganan dashi?.

"Falaak" Wata zuciyar ta gaya mata. Shuru tayi tana juya abun a ranta

"Eh falaak.....itace ta biyo ta hanyar" Zuciyarta ta sake jadda mata. Amma ta yaya zatayi irin wannan maganan da falaak din?.

"Ita kadai ce zata fahimta" Wani sashe na zuciyarta ya sake bata amsa.

Wayarta ta jawo,ta bude watsapp dinta da takan kwana biyu bata hau ba. Wancan satin kaman taga saqon falaak din ta watsapp ta sabuwar number da bata tsaya tantance code din wacce qasar bane,tayi copying number din ta dawo wajen kira ta dora number din sannan ta kirata.

Tayita ringing ba'a dauka ba,sai dab da zata katse sannan taji an dauka,saidai maimakon muryar falaak ita kadai,sai muryoyinsu a cakude ita da maleek da suka fara shiga kunnenta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Cikin shagwaba take masa magana shi kuma ya lalace yana rarrashinta. Gaban akhnan ya tsinke ya fadi,ba shiri ta kashe wayar. Kunnuwanta ba zasu iya jin abinda suke fada ba,maganganu ne masu nauyi sosai,da alama ma batasanma ta daga wayar ba gaba daya. Jefar da wayar tayi gefe tana jan siririn tsaki,yaushe falaak ta lalace haka ne?. Yaushe falaak ta koma haka?. Ba doguwar mu'amala bace a tsakaninsu......amma ta sani ba haka halinta yake ba. Ta lumshe idanunta ta budesu a hankali,ya tafi ya barta da qamshinsa,ya tafi ya bar mata memories masu yawa a tare dashi.

"Girmama na gaba.....girmama baqo" Ta tuna daya daga cikin lesson data dauka a zamanta cikin gidan. Ta bude idanunta a hankali,dole kenan tayi practicing daya daga cikin abinda ta koya kodon ta samu a kammala wannan zaman waqafin na rules din rayuwar masarautar da har yanzu ita batasan a wanne matsayi take ba.

~Ta cikin motar da yake tafiya idanunsa zube kan hasken farin watan daya haske sararin samaniya. Baisan murmushi yakeyi ba,baisan murmushi bane akan fuskarsa ba sai da yakai hannu ya shafa fuskarsa a hankali.

Ya tsinci abubuwa da yawa da baiyi zatonsa ba tattare da ita. Quruciya.....zallar quruciya take gwadawa da suka sanya ya sake raina shekarunta. Iya yadda takeyi kawai ya tabbatar masa quruciya ta mata yawa,kuma ba kowa zai.gane hakan ba sai wanda zama ya hadasu kaman hakan. Kwarjini kawai takewa mutane.....wannan izzar da sarautar dake jikinta mutane ke mata kallon girma da manyance.

"Da gaske batasan komai ba?" Ya sake tambayar kansa da kansa cike da mamaki still. Inda ace ya aureta ne kawai fa don sha'awa?,inda ace ya aureta ne don ya biya buqatar ransa a kanta fa?. Lallai inda hakanne da babbar matsala za'a samu.
Chapter 63 · 0% Book details