Sashe 69
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Labari take mata kala kala,saidai,muryarta qasa qasa sannan cikin nutsuwa. Ko a tafiya motarsu daya da noorah da nanay da akhnan din. Aanani tayita mita zatabi motarsu,amma dole haka ta haqura kaman yadda sauran suka haqura,kowacce ta shiga asalin nata motocin suka harba zuwa masarautar.
Wata DUNIYA take hange daga nesa bawai masarauta ba,manyan katangun da sune suke fara marabtar dukkanin mutumin dake tahowa zuwa ga masarautar. Kafin kuma ya iso dab da ita hasken wadansu irin fitilu su cika idanunsa. Fitilun da duk me kallo cikin nazari da fahimta zai gane cewa ba fitilu bane kawai na ado,ba fitilu bane na banza,fitilu ne dake gaya maka cewa ka kusanto wata duniya dake cike da IKO da QASAITA.
Wasu irin hasumiyoyi ne dake nuna tsananin qarfin tsaro na soji da dakarun da masarautar ke dashi,suna nesa da juna amma kuma abun mamakin cikin tsari suke.
Yadda jerarrun alatun fitilu suka cika hanyar masarautar,hanyar data miqe dodar har zuwa bakin babbar qofar da tafi kama da qofar shiga wata duniyar.....haka dakaru da masu tsaro kowa ke tsaye akan tsari,a muhallinsa cikin uniform launi da dinki iri daya.
Fitilu iyakar ganinka da asalinsu na tagulla ne da zinare,wanda aka sarrafasu da wani irin yanayi me daukan hankalin me kallo. Ba don haske kawai ba,don su nuna alatu gado ne ma masarautar aba jifar......don su nuna girman arziqin da qabilar oromo dukka ke taqama dashi.....sannan su nuna girma da daukakar masarautar ibraheem aba jifar.
Da wani irin tsari motocin suka jera kansu,suka kuma fara shiga ta babbar qofar,jerawar bawai don gudun matsewa ba....aah,hasalima sama da mota ashirin na iya shiga ta qofar idan an budeta a lokaci guda. Jerawar na nuna irin tarbiyyar ta tsaro da suka samu wanda ba tsoro sam a cikinta.
Daka kalli qofar zakasan itama mix ne na zinare da lu'u lu'u da aka yafasu jikin sassaqaqqen dutsen da yake wani irin qyalli,a jikin qofar zane ne na sarauta dawakai da kuma rubuce na nasarorin masarautar da yaruka har guda uku,hakan sai ya sake zama wani ado me daukan hankali matuqa da gaske.
Masu tsaron cikin gidan sun banbanta dana farko da suka tarar. Wadannan tufafin jikinsu silk ne,suna tsaye cikin tsari da wata cikakkiyar nutsuwa kamar masu tsaron wani rufaffen sirri,su suka sanya hannu suka bude qofar gaba daya da sassarfa bayan da suka fahimci sheikh muhammad haisam aba jifar da mama oromo ne ke shigowa masarautar da kansu.
"Barka da dawowa ya me daraja" Abinda ta iya fahimta suna fada kenan a duk sanda motor haisam dake bayansu zata gifta daya daga cikinsu,cikin wani kalan rusunawa da girmamawa.
Idanu ta janye zuciya da hankalinta gaba daya a jagule,wani tashin hankali yana sauko mata. Abinda take gani a yanzu ya girmi hankalinta,abinda take gani a yanzu yafi gaban tsoro shakka ko kokwanto,yafi mata kama da ALMARA irin wadda hankali bai taba kawowa ba.
"Wacce irin masarauta ce wannan?" Ta tambayi kanta tana jin dukka wani qoqarinta yana zagwanyewa. Ta gama sallamawa,wannan mutumin,ta gama miqa wuya wannan shiekh din ba shine sheikh din da suka taso dashi daga agadez ba. Kwanyarta ta gaji da tambaya da tuhuma,ta gama saddaqarwa ba zata taba sanin wayeshi ba sai sanda yaga daman gaya mata da kansa,ko Allah yasa taji.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Amma wanne girman matsayi yake dashi a nan din?,wacce irin masarauta ce me girman iko haka?" Ta fadi daidai sanda motocin suke sake kutsa kai cikin gidan,tana kuma ci gaba da ganin abubuwan almara.....yadda alatu yake magana da kansa......yadda MULKI DA IKO suke aiki ba tare da anyi magana ko an bada umarni ba.
"Kin shirya muna iya fita?" Nanay ta fadi a nutse,kalmar data jawo hankalinta daga duniyar tunanin data tafi. Kanta a qasa,jikinta a mugun sanyaye ta gyadawa nanay kai,kaman ana jiran hakanne aka buda mata murfin motar,sannan aka buda ta bangaren nanay din.
"Barka da shigowa masarautar oromo.....barka da shigowa ahalin oromia.....jini mafi girma da daraja jinin aba jifar" Wata mata data zube a gabanta kaman yadda sauran matan suka zube ta fadi kanta a qasa sai kace bishiyar da aka dasata bata da niyyar motsawa.
"Muna farinciki da kasancewarki macen da yarimanmu me jiran gado ya mallaka.....muna alfahari da wannan d'iyar sarkin agadez". Wani irin tsalle zuciyarta tayi cikin qirjinta sannan ta samu guri ta dire. Maganan matar ta qarshe tana maimaita kanta cikin kunnuwanta,
"Matar yarima me jiran gado?,wanne yariman?,an sauya mata wani da haisam ne?,ko kuwa shi dinne?,idan shi dinne ta yaya hakan zai buya a gareta tsahon zamansu?,tsahon wannan lokaci?,tsahon kasancewarta da 'yan uwansa?.
" Yau masarauta zata kwana cikin farinciki mara misaltuwa,zukatanmu cike suke da fatan alkhairi a gareku,tare da fatan samun zuriya me albarka tsakaninki da yarimanmu.....yarima sheikh muhammad haisam,jinin oromiyawa" Matar dake duqe har yanzu a gaban akhnan ta fadi,sannan ta yaye wani farantin silver da yafi kama da farantin azurfa
Komai da yake kan farantin na zinare ne,sai abu guda daya da haskensa ya dara na komai da yake kai. Qafar akhnan daya ta riqe a hankali ta dora saman cinyarta,a yadda take tsugunnen,ta saka hannu ta ciro wata sarqar qafa me bala'in qyalli da daukan idanu,ta bude marufin sarqar,ta soma sakata a tsintsiyar qafar akhnan din.
Wani irin numfashi me tauri samee dake can gefe ta shaqa ta kuma furzar. Wannan sarqar me daraja ce,tsananin daraja kuwa a fadin tarihin qabilar oromo,ba kowanne gida bane.....ba kowacce masarauta bace,ba kuma kowacce suruka bace ake iya mallaka mata ita. LU'U LU'U ne wato zallar diamond,ta dade tana bincike akan tarihinta da asalinta,kasancewarta mutum me yawan bincike akan abinda ya shige mata duhu. Darajar sarqa tana ganin tafi gaban a mallakawa akhnan din ita,amma saidai kuma,ana azata saman qafartata kyanta da darajarta ya sake fitowa,tamkar don saboda akhnan din kawai aka qerata.
"Kina cikinmu yanzu,cikin qauna da aminci" Ta fada matar da harshen girmamawa.
Miqewa matar tayi da farantin azurfar a hannunta,saidai bata iya tsaiwa gaba daya a gaban akhnan din ba,wata irin tsaiwa ce ta nuna girmamawa.
Ta bude wani turare,ta zuba a wani qaramin abu tana miqawa akhnan din. Ta fahimci me take nufi,don haka ta bata dukka tafukan hannayenta ta zuba mata shi. Tun batakaishi jikinta ba ta gane turaren,da sauri ta maida dubanta ga kwalbar. Turaren nan ne dai.....turaren da ya riga ya zame mata jarrabi....turaren nan da tayi nemansa harta gaji.....turaren data dinga nema kamar tayi hauka?,ya akayi suka sameshi?.
A sannan ji take kaman ta miqa hannu ta daukeshi,a sannan tanajin ko nawa zata iya bayarwa a batashi.
"Mun tsarkake miki guri,mun karbeki da hannu bibbiyu tamkar dama daga cikinmu kika fito" Ta sake fada da murmushi akan fuskarta.
Maganar ta sake dokawa cikin kunnuwan saamee,maganganun matar kamar gugar zana sukeyi mata,maganganunta kamar suna fadin cewa.....akhnan ta cinye gurin.....ba zasu sake karbar wata matar daban bayan ita wa sheikh haisam din ba.
Wani qaramin kofin azurfa ta sake dagawa ta miqawa akhnan din wanda yake dauke da sassanyan ruwan zamzam,hannunta ta miqa ta karba,amma saita gaza sha.
"Sha diyata.....addu'o'in tsari ne daga dukkan abunqi da mugun ido" Nanay tace da akhnan qasa qasa,saidai duk yadda tayi qasa da muryarta hakan bai hana saamee jin abinda nanay din ta fada ba.
A nutse idanunta suka fada kanshi,yana tsaye nesa kadan dasu,nesa kadan din da take jin ita kadai take iya ganinsa.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 63*
Kamar an sauyashi daga bakin qofar gidan zuwa shigowarsu ta yanzun da tsaiwarsu. Wani mutum daban take sake gani.....cikin suturar oromo data maidashi wani kamilin matashi. Zaki take gani wanda qananun namun daji sukewa hidima,don ko a yanzun tana hangen yadda hadimansa ke gyara masa zaman rigarsa cikin tsananin kulawa da girmamawa
Fuskarsa a tsuke,da wani irin qarancin fara'a daya sanya gabanta tsananta faduwa,qarancin fara'ar kuma daya qara adadin yawan kwarjinin dake shimfise akan fuskartasa. Sannan ya sake kawo wani kwantaccen kyau ya zube a fuskarsa gaba daya. Kaman an ninka kyansa....kamar an ninka kwarjininsa.......hakanan kamar an ninka haiba da kamalarsa.
"Yarimanmu me jiran gado" Kalmar ta sake dawo mata cikin kunnenta,saita sake aza idanunta a hankali akan fuskarsa. Tantama take......komai nasa ya sake canzawa daga taku daya tak da tayi zuwa cikin gidan?,komai yanayinsa ya sauya?,anya shine?,shine kuwa?.
Firgigit tayi saboda magana da yayi mata,bada bakinsa ba don ko motsawa wani sashe na jikinsa baiyi ba. Da idanu da kuma girarsa kawai,kaman yana cewa.
"Kisha abinda suka baki,mutane ne kewaye dake suna jiranki" Sai ta sauke idanunta da suka raunana sosai,suna jinta ta koma wata maqasqanciya,ba kuma don an tozartata ba ko an durqusar da matsayinta ba,aah......sabda cin karo da tata izzar da tayi da IKO da yafi nata tsananin qarfi.
Tayi bismillah ta kurba,ta daga kanta a hankali sanda take ajiye cup din saman tray din tana maida idanunta inda yake dazun,saidai a yanzun bata da damar ganinsa.....a yanzu baibaye yake da dogaransa ma'abota fararen kaya,zagayeshin kuma da sukayi ya hana mata daman koda ganin wadannan idanun nasa masu qyalli.
Wani bracelet ta miqa mata,na azurfa wanda akayi dukkanin adon jikinsa da qananun duwatsun lu'u lu'u.
"Wannan girmamawa ce daga yarima muhammad haisam....." Ta fadi tana miqata ga akhnan. Sake kallon gurin tayi,still bata iya ganinsa,tasa hannu ta karba bracelet din daketa sheqi yana daukan mata idanu,sai jakadiyar ta janye farantin baya,sannan ta soma komawa da baya da baya ba tare data juya ba. Ta fahimci al'adarsu ce haka,sanda duk zasubar gaban me iko basa juya masa baya,saidai suyi qasa da kansu,su kuma janye da baya da baya har su bacewa ganinsa.