← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 176

Sashe 166

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eheennn" Ya sake fada yana dubanta. Ya jima yanaso yaga yadda take shayar da yaran,amma saidai ko sau daya a kwanakin bata bari ta basu a gabansa ba,tunda ana hada musu da madarar yara kafin jikinta ya qara daidaita.

"Haisamm" Ta fadi ganin yana matsowa dab da ita ya miqa hannu yana qoqarin zuge zip din gaban rigarta.

Idanu ya zuba mata yana kallonta,saidai kafin yace komai ta zame hannunta daga saman nashi a hankali,ta rufe idanunta tana jin yadda iska ke ratsa fatarta alamun ya zuge zip din gaba daya.

Sai da yaji wani abu ya tsarga masa tun daga tsakiyar kansa zuwa tafin qafarsa sanda idanunsa ke sauka a kansu. Farare tas sun cika sosai,suna tsaye kuma kamar yadda ha sansu. Ya lumshe idanunsa a hankali sannan ya budesu,ya matsa yana dora mata shi saman cinyarta ta hannun damanta ya sanyata ta daidaita zamanta.

Tana jin sanda ya saka hannu ya ciro masa ya saka a baki,tana jin yadda yaron ke cin abincinsa.....tana kuma jin sanda ya koma kawai ya zauna ya zuba mata idanu yana kallonta ita da yaron gwanin sha'awa.

"Me zai hana.....kowanne shayarwa kimin alfarma" Sai ta bude idanunta a hankali a kansa.

".....kiyi alwala kafin kowacce shayarwa" Ya qarasa maganan da alamun akwai abinda yakeson ya sake cewa. Amma bai samu wannan damar ba,noorah da tunda akayi haihuwar ta tare a asibitin ita da camera dinta tayi knocking. Ya bata izinin shigowa,ta shigo da lallausan murmushin nan nata tana cewa..

"Obboo.....yaa maleek......ya khadeem......"

"......da omar" Ya qarasa mata. Kanta ta gyada da murmushi,sai ya miqe a nutse yana duban akhnan.

"Birra zata shigo,ki shirya please,banason kowa yaga komai.....inkin kammala shayar dashi ki fadamin sai mu shigo" Sai ya matsa yayi kissing goshinta yana janyewa da baya a hankali idanunsa a kanta ita da yaran gaba daya,sai kuma ya juya yana ficewa da wannan takun nasa me cike da qasaita yana daga wayarsa data fara ruri,wanda da alama kira ne daga su omar din dake waje suna jiran a musu iso.💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 153*
_________________________
*_INGANTACCEN MAGANIN SANYI NE SADIDAN,WANDA BA'A CAKUDASHI DA KOMAI BA SAI ZALLAR SASSAQE DA ITATUWA MASU AMINCI_*

*_KAYAN GYARA MASU INGANCI DA WARWARE MATSALAR MATA TA FUSKAR CIWON SANYI WANDA YA KASA JIN MAGANI_*

*_GARZAYA A SIRRANCE KI WARWARE MATSALARKI,KI TUNTUBETA TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE_*

+234 810 914 9876
__________________________

Ajiyar zuciya ta sauke a hankali,ta maida idanunta saman fuskar yaron dake shan madararsa a hankali. Ga mamakinta kamar yasan fuskarshi take kallo sai ya riqe yatsanta gam cikin nasa da nata yatsan. Ba shiri murmushi ya subuce masa,ta zuba masa idanu tana kallon yadda hankalinsa ke kwance a jikinta.

"Ko yaya sunanshi?" Ta tambayi kanta,daidai sanda birra ta turo qofar dakin tana shigowa. Fuskarta dauke da murmushi,idanunta akan gadon yaran kamar kullum kafin ta dauke idanunta ta maida kan akhnan.

"Yarima yace nazo na gyaraki....akwai baqi zasu shigo" Ta fada da girmamawa da kulawa.

"Bari na kammala bashi tukunna" Matsowa tayi daura da akhnan din,tana kallon babyn dake kan cinyarta. Duk bayan sakanninsai ta gyarawa akhnan daukan yaron,idanunta da hankalinta dukka suna kansu. Ta daga kai ta kalleta sanda take karbarsa daga hannunta ta dorashi a kafada don yayi gatsa.

"Birra" Ta kirata wanda ba Kasafai take hakan ba.

"Na'am" Ta amsa tana dubanta.

"Inaso ku fitar da miji ke dasu buhaina......aure zan muku" Ta fada kai tsaye.

"Aure?" Ta tambaya tana fidda idanu waje.

"Eh aure,yara mata ne ku da kuke da chance na aure da haihuwa kamar kowacce diya mace,bai kamata ku zauna kawai rayuwarku ta qare a haka ba". Wata kunya ta gani cikin idanun birran,sai ta sunkunyar dakai tana takawa zuwa gadon da sauran 'yan uwanshi suke ta kwantar dashi a cikinsu,sannan ta dawo ta taimakawa akhnan din ta rufe jikinta da wata kyakkyawar after dress mara nauyi. Ta juya ta fita don sanarwa da haisam sun kammala.

Tun daga nesa ta fara jiyo muryoyinsu,daura da dakin da 'yar tazara kadan.Tun daga corridor din,dariya.....tsokana.....hayaniyar tsaffin abokai da wani irin aminci da yarda da juna da kuma shaquwa me zurfi suka shiga tsakaninsu.

Muryar omar tafi ganewa,don muryar tasa ma tafi ta kowa fitowa.

"Move" Taji Omar din yace.

"Kai.....kabi guy dinnan a hankali,yanzu ya fika matsayi.....he can throw you out ya hanaka ganin babies dinka".

Tuni akhnan ta fara murmushi,Saboda ta san wadannan mutanen,wadannan 'yan shidan....kullum idan suka hadu zaman lafiya kuma ya qare. Sun yita dauki ba dadi a tsakaninsu. Ba can baya da suke zamartaka ba,har yanzun da kowannensu ya zama mahidanci ma,gashi har sun fara tara 'ya'ya.

Qofar ta bude a nutse,kaman ba sune take jiyo hayaniyarsu daga corridor ba. Haisam ne a gaba,kamar wanda ke jagorantar wani taro na musamman. Idanunsu suka hadu da nata,murmushinta ya qara fadada. Yau kam zata ga yadda zaiyi.....mutumin da baison cikakken hayaniya ko doguwar magana. Yau ga 'yan shida ciwon kansa kenan,batasan ya zasu qarke ba.

Maida mata yayi,ya mata magana da ido dake nufin

"Bari kiga wannan rigimar"

"Behave yourself" Yayi maganan yana shan mur.

"We're not children fa captain sheikh....."

".....gaya masa,speak for your self captain" Dariya yayi,irin boyayyar dariyar nan da saidai tasa fuska kawai ta washe.

Daya bayan daya suka fara shiga,dukansu cikin tsari....classy...legant. Da wannan nutsuwar da kamar dukkaninsu sun samu tagomashinta. Kana kallonsu kaga matasan dake tafiya kafada da kafada da nasara. Irin matasan da sukasan kansu suka kafa duniyarsu arziqinsu da komai nasu da ilimi nutsuwa da halal cikakkiya.

Kowanne sai da yayi sallama sanda suke shigowa. Haka ta amsa musu daya bayan daya suna neman sofas din da aka ajiye daga can gefan dakin saboda zuwan baqi irin haka.

Daya bayan daya suka gaidata,abin daya sanyata jin nauyi da kunya kenan. Su kam wai suna mantawa ne da matsayin da suke dashi a idanun duniya?. Me yasa suke da sauqin kai har haka dukkaninsu,wanda idan daga nesa ka kallesu sam basuyi zubi ko kama da mutane masu sauqin kai haka ba.

Ta dauka zata ga su khadeem dasu shehnaz,tunda tunda ta haihu wayarta na ajiye,amma sai ta kasa tambaya.

Omar ne kawai basu gaisa ba,don haka ya matso gaba kadan.

"Sannu da jiki, Princess." Akhnan ta amsa da murmushi.

"Nagode." Ta furta da murmushi tana tuna wasu abubuwa. Tana tuna sanda ta fara sanin da zaman sheikh haisam cikin masarautar agadez. Tare ta sanshi da omar. Omar din kuma shi kadai ne take ganin wargi wani lokaci a idanunsa,amma badai haisam ba.

"Wallahi ka bamu tsoro." Mutallab ya fada yana,nan take Haisam ya daga ido ya kalle shi. Daga hannuwansa mutallab din yayi.

"I'm serious!" Ya fadu kansa tsaye sannan ya kalli Akhnan.

"Mutumin nan ya hana mu sakat." Akhnan ta dan yi dariya tana aza idanunta kadan kan mutallab. Ya tsare mutallab din da ido,saidai a yadda ta fahimta sai mutallab ya gama fadin albarkacin bakinsa bazaiwa haisam shuru ba kaman yadda yakeso.

Omar ya gyada kai.
"Three days." Ya nuna haisam.

"Three days yana kiran likitoci fiye da yadda yake kiran mu?." Dariya duka suka sanya masa,akhnan ma tayi qasa da kai tana boye tata.

"Harda ke?" Ya fada da sigar tambaya yana dage dukka girarsa sama hannuwansa harde qirji.

"No....ba laifina bane..." Ta fada tana qoqarin hadiye dariyar.

"Wait....." Amjad ya fadi wanda tuni yakai bassinet din da yaran ke ciki. Juyowa yayi garesu,sannan ya maida dubansa still cikin bassinet din. Ya sake juyawa ga haisam dai.

"Three?"

"Yes." Haisam din ya amsa masa yana hade gira,don yasan halin Amjad da b'allo magana.

"Three actual babies?"
Haisam ya kalle shi.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Do they look imaginary to you?"
Dariya ta kaure a dakin. Har da haisam din,har Amjad dinma da saboda dariya sai daya dafa kujerar kusa dashi.

"Bance haka ba.....amma sun shammaceni ne. Kasan naje Amsterdam.....daga can na biyo flight muka hadu da naseeb,basu gayan triple bane wallahi.....amma dai" Sai ya tsaya yana duban fuskokin sauran.

"Nikam daga yau na sallama.....you're a true hero.....a shekara daya three babies?.....congratulations to us" Ya fada yana miqawa haisam hannu

Haisam ya kalli hannun da amjad ya miqa masa,sai ya sauke idanunsa kan jariran,sannan ya dawo da kallonsa kan Omar.

"Congratulations to us?" Ya maimaita cikin nutsuwa. Duka dakin ya fashe da dariya. Amjad kuwa bai janye hannunsa ba.

"Of course, us."
Ya amsa da cikakken qarfin hali.

"Ka manta shekaru nawa muke tare? Wannan nasara ce ta qungiya." Ya fada yana shan mur saidai yanayin tsokana a fuskarsa yana nunawa sosai.

Khadeem ya ballawa amjad harara sannan ya yi qwafa.

"Ka ji dan rainin wayo ko." Amjad din ya nuna shi da yatsa.

"Kai ka yi shiru kawai. Kai ko cat ba zaka iya raino ba." Akhnan ta kasa hana kanta dariya,don bata taba ganin wannan game din nasu har haka ba irin yau.

Dole ba yadda haisam zaiyi da halin Amjad,a qarshe ya miqa masa hannu suka yi musabahar.

"Thank you." Haisam din yace. Amjad ya dan tsaya,saboda ba kasafai Haisam yake fadin irin wannan kalmar ba. Ya sani,tunda ya fadi masa hakan zasu hadu ne a gaba. Amma ya maze yana boye dariyarsa.

"You're welcome." Ya amsa masa.

"Wallahi da gaske har yanzu ban gama yarda ba." Omar ya fada yana duban haisam. Ya nuna na ukun.

"Wannan fa daga ina ya fito?" Nan take nurses din da suka shigo don ajiye sauran magungunan akhnan suka saki dariya. Kunya ta kama akhnan ta rufe fuskarta da tafin hannunta saboda dariya. Kau da kai haisam yayi gefe yana cije lips dinsa. Wato sun shirya cakar dashi ne kawai,tunda yaqi basu fuska suci namansa yadda sukeso sanda ya dauke akhnan suna yawon qasashe. Sunyi timing masa tsiyar da Allah ne yasan iyakarta,amma ya hana musu fuska,shine duka suka tattare zasu fanshe a yanzu. Dama ya sani,tunda sukayi shock sanda yace musu triple yasan yau sai yasha maganin ciwon kai saboda iskancinsu.

Omar kuwa ci gaba yayi hankalinsa kwance yana tsaye kusa da bassinet din ya kasa matsawa,hannunsa riqe da qugunsa.

"Ni da Naseeb har mun yi lissafi a hanya."Ya nuna Haisam.

"Shi yana shirin twins." Sai ya nuna bassinets din.
Chapter 166 · 0% Book details