← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 176

Sashe 72

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 65*

"Giiftii" Sunan ya maimaitu cikin kan saamee tare da muryoyin da suka maimaita sunan a tare.

Tasan kuwa abinda ta fadi yanzu hakan nanay din?. Sunan giiftii?,ta yaya zata dauki suna me daraja irin wannan ta bawa macen da bata fito daga asalin qabila da yarensu ba?. Ta yaya zata bari haka ta faru?.

Qasa Akhnan tayi da kanta,tana jin wani nauyi hawaye suna taruwa a idanunta. Me yasa ya zabi daukota ya kawota cikin wannan tarin girmamawar?,bayan ba wani babban abu da tayi masa data cancanci haka?. Meyasa ya tsallake kowacce mace sai ita?,meyasa ita ya zaba?. Wannan kalar halittan bai cancanci SO ba kuwa?.....me zaki sadaukar masa da zaiyi daidai da karamcin daya shimfidawa rayuwarki?" Tuhumar da zuciyarta keyi mata kenan. Wani irin girmansa taji yana hauhawa cikin ranta. Wannan sunan shekaran jiya cikin bincikenta akan qabilar ta gano girma da matsayin sunan.....ta gano irin masu girman matsayin da suke ake bawa shi.....yaushe ta cancanci haka?,wacce irin qauna ce haka tsakanin nanay da mamminta?.

"Jininmu da darajarmu giiftii.........ki riqemin muhammad kawai irin riqon da uwa zata yiwa d'anta" Nanay din ta fada da rauni sosai cikin idanunta. Nauyi maganan itama tayi mata,sai nanay ta zare idonta tana maidawa wani sashen,kamar yadda al'adar hadimansu yake,sunsan komai a sanda ya dace su yishi basai iyayen gidansu sun buqata ba.......wata hadima jakadiya ta matso dauke da wani lullubabben faranti.

Idanun saamee fes a kan farantin,har zuwa sanda Nanay ta bakadeshi,take tayi ido biyu da mayafin nanay din.

Wani mayafi ne me tsananin daraja a idanun nanay din.....mayafi mafi girman tarihi tsada da qauna a gurinta. Irinsa uku ne da ita,wanda duk tsadarsa bata yafashi,ta ajiyeshi kawai a gurin ajiya na musamman cikin kulawa.

Tsakanin hasnaa da balqees data aurar,ba wanda baiso ta bashi shi ya tafi dashi gidansa ba amma ta qiya,sai gashi a yanzun.....a gaban idanunta taga ya daukeshi,ta wareshi,ta kuma lullubawa Akhnan shi.

"An rufeki da darajarmu......kina qarqashin kariyarmu" Jakadiyar ta furta cikin girmamawa,wanda tana daya daya cikin mutanen da sukasan darajar mayafin a tattare da nanay din.

Idanunta saamee ta janye tana kullesu saboda ruwan hawayen da taji suna neman yi mata ba zata sanda su rumaisa ke dariya qasa qasa cike da farinciki.

"Shikenan wallahi,an samu me qwace matsayin captain obbo.......Allah giiftii ta zartashi yanzun dai a zuciyar nanay"

Giiftii " Ta sake maimaita sunan a ranta.

Bawai suna kawai nanay ta bata ba......wata irin daraja ce,ta dagata sama da sauran dukka matan Ethiopia gaba daya.....darajar da sai da akayi shelar dimbin mutane kafin a mallaka mata ita. Ba suna kawai Nanay ta bata ba,matsayi ne da har abada bazai tabe zame mata ba.

Kadan kadan mutane suka fara raguwa,sai mata mafi kusanci na qwarai ga nanay da motii. Sauya hall akayi,wannan hall din yasha banban da wancan,wannan din an yishi ne cikin yanayin da zai bada daman cin abinci ga kowa a sake.

Ba jimawa aka shigo da wani babban tray,wanda kallo daya saamee tayi masa wani murmushi ya subuce mata. Farinciki ne fal fuskarta da wani boyayyen murmushi,kamar ba ita bace a mintunan dazu take fakar idanu tana tsane hawayen fusarta da gefan lallausan mayafinta ba..

Kai tsaye aka wuce da farantin gaban Akhnan din. Ta daga idanu a nutse tana kallon yadda aka jera qananun cups masu qaramin faranti daga qasansa dauke da wannan coffee din na asalin noman qasar oromo.....wannan coffee din da zuwa yanzu batajin akwai wani coffee daya kaishi dadin d'an d'ano saman harshenta. A jere suke da wani irin tsari da zai burge me kallo.....to amma ita.....batasan me zatayi dashi ba.

"Gabatarwa......zaki gabatar da irin taki girmamawar zuwa ga baqinmu masu girma.....manya masu matsayi a gurin nanay dama masarautarmu....muna buqatar ganin taki qwarewar" Saamee ta furta a hankali tana sakin murmushi.

Daga inda nanay take tana jin dadi ne,a nata zaton bayani saamee din ke mata wanda zata fahimta,don haka cikin murmushi take kallo Akhnan din.

Wani abune ya motsa a zuciyar Akhnan din,a nutse ta waiwaya sashen da saamee din ke zaune tana zube mata blue eyes dinnan nata masu daukan hankali.

Tun bata shaidata......har ta fara shaidata. Yarinyar da akwanakin da tayi tare da nanay ita kadai ke matsanta shigowa gurinsu da tarin hidima da maganganu na kulawa akan haisam.

"Nanay captain sheikh bai shigo ba......nanay abincin captain sheikh......nanay coffee din captain sheikh......nanay captain sheik yayi baqi....me za'a kai musu......nanay ruwan zafi.....bazaisha girkin hadimai ba" Sannu a hankali sai abun ya fara mata wani irin. Bata da wata magana ta daban saita captain sheikh,duk wani da'irar maganarta a nan take qarewa,bata sauya suna ballantana wanda kulawarta take kai.

Ta dauka ba zataji komai ba......ta dauka ba zataji wani sauyi daga zuciyarta ba.....to amma a hankali sai ta samu kanta da fara jin wani abu yana matse zuciyarta a duk sanda ta shigo ta ambaci sunansa.

Bata tana d'aga kai ta kalleta ba sai a shekaran jiya.....shekaran jiya da tazo tana fadin..

"Kamar Captain baya da lafiya nanay........naga Dr Aawel ya fito daga sassansa"

"Zan bincika" Nanay ta fadi kaman yadda ta saba amsawa saamee da duk maganan da tazo da ita inde akan haisam dinne a taqaice,bata kuma bari aci gaba da yinta.

Abu na farko daya dasa zargi a ranta,sanda ta daga kan don ganin wacece wannan da maganarta kullum iri daya ce?,kuma akan mutum daya?,sai ta samu idanuwan yarinyar suma suna kanta,saidai kuma wani kallo take mata da yake nuna a sace take kallonta.

Suna hada idanu Akhnan din ta dauke kai tana maida idanunta kan bowl din da nanay ta kawo mata me cike da wata irin dahuwar wani nama da batasan naman meye ba. Tana jinta sanda take takawa tana fita,haka kawai taji wani abu ya mata tsaye a wuya.

Me yasa batasan komai akansa ba sai wata?. Me yasa take satar kallonta irin haka?. Duka duka saamee din kimarta da zatinta a kallon data mata da kuma nata idanun bata wuce irin nasu birra ko bara'atu ba. Bata da wannan haibar sam irin wanda takan hanga tattare dangane dasu rumaisa,hatta da noorah ma,duk da ta gabatar mata da kanta a matsayin qanwar sheikh haisam kamar sauran......amma a yau data daga kai ta kalleta sosai daban take ganinta a cikinsu.

"Zo" Nanay ta kirata da tattausan murmushi da kuma yanayi na qarfafa gwiwa. Tsam ta miqe,tana takawa a nutse tana nufar nanay. Miqewa tsaye tayi,tana duban farantin da jakadiyar ta biyo Akhnan dashi.

"Ki shayar da baqinmu da hannunki" A hankali Akhnan ta gyada kai,saidai can qasan zuciyarta wani abu daban yana harba mata.

Ba shayar da baqinsu bane manufar,abinda tafi fuskanta shine......anason auna karamcinta ne. Idanun Nanay data kalla sun nuna mata komai.....taga kuma yarda da ita da yarda da halinta dari bisa dari cikin idanun Nanay,don haka ta soma takawa a hankali.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Da idanu saamee tabi takunta,ba yau ne ta fara ganin takun tafiyarta ba......amma kuma duk sanda zata kalli takun sai ya kwance mata wani abu cikin kanta. Tana takawa ne majestically......da wani irin yanayi da burgewa a takun yake tasirantuwa cikin kanta,amma kuma wannan halittar ta KISHI take wancakalar da wannam daga idanunta.

"Jin kai ne kawai da girman kai" Shine abinda take bawa duk wani motsi na Akhnan din da takunta. Tana sane,tana kuma lissafe a kwana goma sha hudun data dauka tana shiga dakin da maganar haisam akan harshenta bata taba daga idanunta ta kalleta ko sau daya ba......hakan kuma bawai yana nuna kara ko alkunya ba,ko kuma batajin abinda take magana a kai a dukka kwanakin,aah......tana lura da ita. Wani irin izza gareta.....tarin dagawa da girman kai data lura bada kowa take doguwar magana ba.

Sai a dazun da taje da batun baida lafiyan. Ba rashin lafiyar ya sanya ta kalleta ba.....qilan yadda take maganan ne kamar zata saki kuka.

Wani abu tayi.....wani abu da bata taba yinsa ba kaf tsahon rayuwarta illa ga mutum daya wato SULTANE.

Kujera kujera ta dinga bi cikin nuna girmamawa ta miqawa dattawan cup din bayan ta tabbatar kowanne ta cikashi.

"Allah yayi miki albarka" Suka dinga furtawa ga duk wanda ta miqawa. Wani irin dadi ta dinga ji tun kafin ta gama,can qasan ranta takejin wani irin farinciki. Har cikin jikinta takejin addu'ar tana ratsata

"Haka bakin babba yake akan yaro?" Ta dinga fadi can qasan zuciyarta. Tunda take ita ake miqowa.....tunda take ita akewa hidima,yau sai gashi tayi qanqanuwar hidimar da aka tara mata tulin albarkar da batasan yawanta ba.

Sanda take komawa mazauninta sai hankalinta ya lula can wata duniyar. Sanda tana da shekaru goma a duniya......sabda morsa safiyya ke tattara mabuqata dattawa a duk ranar juma'a. A jerasu tasa a daukota ta dinga binsu da sadakar kudi da abinci kamar haka suna sanya mata albarka.

Abun yana mata dadi a sannan,haka kawai ba tare da itama tasan dalili ba,amma daga randa mammina ta fahimta saita soma sukar abun,a hankali sai abun ya fara fice mata daga rai,ta bijire ta kuma daina zuwa din,hakanan morsa safiyya ta haqura ta sanya hairaan taci gaba har zuwa sanda aka aurar da ita.

Cikin wata Royal buggy suke tafiya a nutse cikin hanyoyin masarautar. Wata qaramar mota da ta sake sanyawa Akhnan sallama irin ikon masarautar. Tana da tsananin kyau da daukan hankali,a bude take da wani irin yanayi dake nuna iko da isa.

"Zamu qarasa mu duba muhammad" Nanay tace da Akhnan dake zaune a gefanta. Batace komai ba,ta danyi qasa kawai da kanta,haka kawai taji zuciyarta tana tsalle,tana motsawa a nutse da wani yanayi data jima bata jishi ba.

Cikin qasaitaccen parlor din nasa da yake da wasu irin views har guda uku,wannan ya bashi wani irin tsari haske me kyau da kuma hangen qawatattun tsirrai data lura kamar a nan aka haliccesu. Wasu irin furanni da flowers masu kalolin dake daukan hankali,furannin da kana iya jiyo mabanbantan qamshinsu daga cikin parlor din.
Chapter 72 · 0% Book details