← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 176

Sashe 125

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gate up" Ya furta a nutse sanda ya iso gabanta. Idanunta ta lumshe tare da budesu gaba daya. Fushi ya kamata tayi dashi,haushinsa ya kamata taji......yaji ya kamata ta masa......amma ta kasa. Duk sanda zai kalleta da wadannan idanun.....duk sanda zai tsaya a gabanta duk sai taji kwarjininsa ya mamayeta. Tana jin yana kakkarya zuciyarta da kallonsa kawai ba tare da yakai ga yin magana ba.....hakanan ta samu kanta da d'ora hannunta cikin nasa sanda ya miqa mata tattausan tafin hannunsa.

Bata ankara ba ta jita lullube cikin faffadan qirjin nan nasa.....wannan faffadan qirjin daya zame mata wata mafaka ta samun nutsuwa da duk duniya bata jin akwai wani guri da zata samu shigen wannan nutsuwar. Wannan faddadan qirjin dake cike da tausayi rahama da kuma jin qai. Wannan faffadan qirjin dake cike da hikima yake lullube da jarumar zuciyar da kullum idanunta ke kalla da wani irin alfahari.

Ajiyar zuciya taji ya sauke har sau uku,kaman akwai wani abu a boye dake damunsa. Ya lumshe idanunsa yana jin yadda wannan dumin nata dake bashi comfort yake ratsa gabbansa a hankali yana tayar masa da wannan feeling din da yakai wani saqo ya binneshi da zummar adanashi zuwa wani lokaci.

Sai daya tabbatar ya aike ma da zuciyarta nutsuwar da zata isheta na awannin,sannan ya janyeta yana motsa wadannan labban nasa da take matuqar so.

"Get dressed" Ya fada yana rarraba kallonsa tsakanin blue eyes dinta da suka rame kadan.

"Ina zamu?" Ta tambaya tana motsa tiny lips dinta daya gaza jurewa,sai daya matsa da bakinsa yakai musu sumbata kadan.

"Zaki gani" Ya fada yana riqe tsintsiyar hannunta softly.

Kai tsaye ya bulla da ita bedroom din da suka zabi kwana a ciki tun ranar da suka sauka a agadez din. Yace dai ta shirya,amma ja tayi ta tsaya,tana kallonsa ya bude bangaren daya adana mata kyawawan hijaban da aka dinkasu da wani irin dinki me aji da tsadajjen yadikan da ko sunansu bata sani ba. Ya ciro wani dark coffee ya wareshi,ya sanyata mata,sai ya juyata zuwa fuskar madubi yana daure mata igiyar hijabin,fuskarta da tasa dukka suka bayyana,ya zube mata qwayar idanunsa yana kallon fuskartata yana jin wani abu me qarfi a kanta yana ratsashi,tun daga fatarsa har zuwa jini da b'argonsa.

Ya ci gaba da daure igiyar hijabin a hankali kamar wani abu mai daraja da yake tsoron ya b'aci. Itama sai ta kasa d'auke idanunta daga reflection d'insu cikin mirror d'in.

Yadda yake tsaye a bayanta… yadda dogayen yatsunsa suke gyara hijabin nata da nutsuwa......komai nasa yana saka zuciyarta bugawa da wani irin nauyi.

Daya kammala bai matsa baya,sai yaci gaba da tsaiwa kusa da ita.....ba kusa kawai ba.....wata irin kusa da har jikinsa yana gogar nata,idanunsa cikin nata ta cikin mirror din.

"You look dangerous.” Ta d'an had'e gira saboda yadda ya fad'i kalmar cikin low voice d'in nan nasa wadda ta tilasta tsigar jikinta zubawa. Kamar dai zuciyar da gangar jikin sunason mantawa da yanayin da take ciki,kamar dai suna gaya mata MUNA KEWARSA.

"Dangerous?" Ta fada da wata murya kamar meyin rad'a. Sai ya d'an sunkuyar da kansa kusa da kunnennata.

"Mm" Ya fada yana sauke wani irin nannauyan numfashi. Ya sake maida idanunsa kan fuskarta ta cikin madubin ba tare daya d'aga kansa ba.

"Beautiful enough to make a sane man forget himself.” wani abu me sanyi taji yana bin dukka sassan jikinta,sai ta kauda idanunta daga mirror d'in saboda kallon nasa ya fara kassara mata qafafu.

"Kana yawan fad'in abubuwan da suke rikita mutum.” wani lallausan murmushi ya saki,qaramin murmushin dake nuna zallar miskilancin dake b'oye a bayan izzarsa.

"And you keep doing things that make me say them.” ya fada yana narke mata da wannan sakalcin nasa daya kwana biyu bai gwada mata ba.

Lips dinta ta hade dukka ta tura cikin bakinta don tana qoqarin hana kanta yin dariya. Sai ya d'aga hannu ya gyara d'an gashin daya kwanta kusa da goshinta yana maidashi sosai cikin hijabin. Yatsunsa suka d'an shafi fatarta lightly. Idanunsa ya lumshe saboda wani saqo da hakan ya aike gabbansa suna gaya masa kamar kusancin ya masa yawa.

"Haisammm" Ta kirashi da wannan sunan.....ta kirashi da wannan yanayin da yake qishirwar ji a tattare da ita

"Me yasa kake kallona haka?" Ta tambaya don da gaske yana narkar mata da zuciya ne kawai,a yanayin da takejin duka irin wannan abubuwan dole tayi nisa dasu,don har yanzu tana jin rashin sultane a tattare da ita. Sai ya bud'e idanunsa slowly ya sake had'a su da nata a mirror din da wani irin intensity.💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 113*
_________________________
*_SHUWA INCENSE AND MORE_*

😊
*_kai daga jin sunan basai an gaya maka ba_*

*_kai daga jin sunan basai ka tambaya ko tsaya tunanin maganar me ake ba_*

*_MAGANA CE TA GIDAN QAMSHI_*

*BAFA GAMA GARIN QAMSHIN DA KIKA SABA JI BA HAJJAJU*

*KINA QONA TURARE YANA QAURI*

*KINA SAKA KHUMRA TANA BIN SHANUN SARKI*

*WANNAN DIN TURARE NE DAKE DAWWAMA A DAKI DA JIKI.....DA SALON QAMSHIN DAKE MANTAR DA ZUCIYA DUK WANI B'ACIN RAI*

*TASTED AND TRUSTED👌👌👌100% HAJJAJU*

*NA DABANNE A CIKIN NA DABAN*🙌🏽🙌🏽

*idan akazo kan SHUWA INCENSE an tashi magana*

*idan ma kinsan baki shirya jan magana ba a duniyar qamshi to kisha zamanki hajajju*

*_zaku iya magana da ita kai tsaye ta wannan number wayar_*
+234 704 229 3387
__________________________

"Because every time I look at you…” sai ya sake sassauta muryarsa sosai tana yin can qasa.

"..…I feel like Allah spent extra time creating you.” da qyar ta iya qwatar numfashinta ta kuma saukeshi a hankali saboda yadda ya sanya zuciyarta na bugawa da wani irin qarfi.

Juyowa yayi da ita a tausashe da wani irin sanyi tana fuskantarsa sosai har suna musayar numfashi. Kallon da yake mata yanzu sanyayar mata da kowacce gaba yakeyi da wani tarin sonshi da qaunarsa.

"Sannan.....wannan hijab din....." Ya furta hana mutsuka yatsunsa saman kafadarta da wani irin softness kaman yadda tantance sulb'in yadin.

"...…is already testing my patience.” wata irin kunya ce ta taso ta lullubeta,ta kuma fahimci sarai abinda yake nufi.....amma sai takejin zai mata nauyi. A irin wannan lokaci?,a masarautar?.

" Haisaammm" Ta kirashi da wannan sound din da wannan yanayin. Sai kawai ya langabar mata da kansa kamar wani innocent man.

"What?" Ya fada a narke yana sauke mata murmushi. Boye fuskarta tayi cikin qirjinsa tana jin wani sanyi da sassauci yana saukar mata. Ba shakka MIJI NA GARI duniya ne.....a kowanne rashi da mace zatayi....kowanne irin maraici da zata fuskanta,muddin akwai miji na gari....komai zata fuskanceshi da wani irin sauqi da sassauci.

"Muje kiga abinda na kawo" Ya fada yana janyeta daga jikinsa yana saka mata takalmanta.

Hannunsa cikin nata.....ba tare da damuwa da mutanen da suke wucewa ba dama me kallonsu. Cike da wannan kulawar da tattalin suke takawa. Yana mata hira kadan kadan da ta sake dauke hankalinta,sai gasu a babbar bargar dawakai na gidan.

A nan dawakanta suke.....da dukkan wasu dokuna da sultane keji dasu. Dokuna masu tsadar gaske da wasunsu ma kyauta ce ake bashi daga sarakai na qasashe daban daban.

Zuciyarta taso ta karye,amma daya dafa kafadarta ya juyo da ita tana fuskantarsa idanunta cikin nasa sai wani abu ya sassauta daga zuciyarta.

"Kin shirya?" Ya tambaya da kulawa. Kai ta gyada masa a nutse duk da yadda zuciyarta ke bugawa kadan kadan,saboda gurin ya tuna mata abubuwa masu yawan gaske game da sultane. Tun daga quruciyarta zuwa girmanta da rabuwarta da gidan dalilin aure.

Hannu ya sanya da kansa ya bude mata,saboda cikin gidan sam baya yawo da guards dinsa. Musamman idan har tare yake da ita,tana mamakin yadda yake kaffa kaffa da ita.

Suna sanya qafa wata kyakkyawar Arabian mare ta fito(macen doki ingarma na musamman,irin wanda su kansu masu dawakin sunsan na dabanne).

Idanu akhnan ta waro waje wani numfashin mamaki yana qwace mata.

"Ma sha Allah....tabarakallah" Ta fada da sautin daya sanyashi waiwayawa ya kalleta. Abubuwa da yawa.....dabi'u da yawa nata sun fara sauyawa zuwa na koyarwar musulunci sosai. A baya zata ce wow ko wani abu makamancin haka....amma a yanzun kalaman bakinta sun sauya ba tare data sani ba.

Zame hannunta tayi daga nasa tana isa gaban dokin da wani irin d'oki. A hankali tayi d'age saboda tsahon dokin,ta dora hannunta saman wuyanta tana shafawa a hankali. Kamar tasan waye a gabanta sai itama dokin ta sunkuyar da kanta.

Hannunsa nade a qirjinsa yana monitoring irin walwala da farincikin daya gani cikin idanunta,wadanda suka bace bat daga randa rasuwar sultane ga shiga kunnenta. Iya wannan kawai ya isheshi nasa farincikin shima. Waiwayowa tayi tana kallonsa.

"Ina ka samu irin wannan dokin?" Ta fada da murmushi,saidai bayan maganan ta fito sai taji tambayar ta mata banbarakwai bayan kwanyarta ta dawo mata da hoton WANENE HAISAM din.

Da tarin sauqin kan nan nasa sai ya saki murmushi,ya sauke hannuwansa yana takowa cikin nutsuwa inda take tsaye.

Hannunsa ya d'ora saman dokin yana tayata shafashi a nutse

"You still remember that race?” ya fada yana saka idanunsa a nata.

"No" Ta fada a hankali tana dubansa itama da blue eyes dinta dake wani shining ta siririn hasken almurun. Taku uku ya qara,ya kama hannunta suna matsawa daga gefan dokin kadan,ya sanya hannuwansa dukka yana riqe da qugunta suna musayar numfashi a tsakaninsu.

"Kin manta?.....You chased me for months after that.”

Numfashinta ta riqe a hankali,hippodrome yana dawo mata fes a kanta kamar yanzun komai yake faruwa.

Wannan qwararren mahayin daya fara sanya mata tsorom tsere na farko a duniya....boyayyar fuskar nan.....wadannan idanun da su kadai suka bayyana kansu.....sai faduwarta ta farko rashin nasarar farko cikin rayuwarta.

"Kaine?" Ta fada da wani irin excitement a fuskarta tana waro idanunta gaba daya waje.

"You were the rider at Hippodrome?” ta sake maimaitawa da alamun dake nuna ta dade tana zargi dama.

Qasa yayi da kansa kadan,murmushi yana qwace masa.

"The one who stole your trophy.” ya fada da wannam ginshirar tasa. Idanu ta zuba masa cikin tuhuma
Chapter 125 · 0% Book details