← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 176

Sashe 149

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haisam yana kallonta fiye da wajen,yana monitoring na reaction dinta sosai. Burinsa gurin ya burgeta kaman yadda yake burge kowa,burinsa gurin yayi mata,duk kuwa da cewa ya riga yaga alamun hakan a fuskarta.

Akhnan ta fito daga motar a hankali tana kallon wajen kamar mafarki.....kamar almara,komai a wajen tana dubansa daya bayan daya. Bata taba ganin guri irin wannan ba. An qirqiri komai cikin duwatsu da sahara?. Wanne irin guri ne wannan?.

“Haisam…”

“Hmm?”

“Mutane suna rayuwa a nan gaske?” Ya dan sunkuyar da kansa kusa da kunnenta.

“Only a few can afford to.” ta yarda da maganansa dari bisa dari sanda suke shiga ciki,staff dinsu suna nan nan dasu cikin kulawa. Tsarinsu da yadda suke tafiyar da baqi kawai ya isa ya gaya maka lallai sun saba karbar manyan baqi,kuma manyan mutane a kowanne sashe na duniya.

Ta tsaya cak tana kallon suit dinsu bayan an shigar musu da luggage dinsu,an kuma samar da sauran duka abinda haisam yace a kawo din,banda coffee da sukace yanzu zasu kawo,oromian coffee dinnan nasa.

Duka suite din kamar private palace ne,kaman kowanne guri da zaiyi masauki a duniya.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

floor to ceiling glass walls,private heated pool,outdoor fire lounge,desert-view,bathtub,giant king bed mai white linen,soft hidden lights,private spa section,dressing room da ya fi wasu apartments girma,duk sai daya ja hannunta a hankali da wani irin kulawa don ya tabbatar komai yayi mata yadda takeso.

Amma abin da ya fi girgiza Akhnan…...shirun wajen. Kamar duniya ta tsaya musu cak,ba wanda kuma ya rage a cikin ta,daga ita saishi.

Ta juya a hankali tana kallon Haisam.

“Ka taba kawo wata mace nan?” ta masa tambayar tana jinjina yadda yasan kowanne guri daya dace da ma'aurata....ba'a iya qasarsa kawai ba....a qasashen duniya daban daban.

Idonsa ya tsaya a kanta na wasu seconds. Kishi.....ya fada qasan ransa,dariya yakeso yayi,amma yasan idan yayin zai jawa kansa jagwal,shi da yake buqatar dare mafi tarihi a amangiri din.....ba iya wannan daren ba.....ya shirya musu yadda zasu lalace sosai shi da ita a gurin,sai kawai ya fuske

“No.”

“Da gaske?” ta sake tambaya. Ya lumshe idanunsa,sai a yanzu ya yarda da kalar rigimar mata.

“Ban kawo kowa cikin duniyata haka ba.” ya fada yana cire agogonsa yana ajiye wa a hankali.

Idanunta ta zuba masa tana jin tarin qaunarsa a ranta. Royal billionaire aura dinsa ya kara fitowa,calm,untouchable,dangerously composed.

Ya taka zuwa glass wall din yana kallon desert sunset,yana sake girmama iko da buwayar ubangiji,yadda launin sama ke sauyawa a duka lokaci irin wannan.

Sai ya juyo gare ta.

“But you…”Ya tsaya kadan.

“You belong here.” idanunta ta lumshe a hankali,tana jin yadda yake sake shigar da ita wata sabuwar duniyar da batasan da ita ba,wani sabon lainin soyayyarsa dake taso mata kaman zai hallakata.

"Ko a map.....babu gurin nan.....ko map ya kasa tattara gurin nan a cikinsa......haka nakeso na mallaki nutsuwarki.....zuciyarki da dukka lokacinki a wannan sabuwar duniyar" Ya furta da sautinsa me zurfi....wannan husky voice din da idan yana mata magana takeji kamar ya tabbata yana hira da ita har abada.

Knocking din da akayi ya katse musu komai,wannan shurun....da kallon da yakewa cute face dinta yana jin duniyarsa duka ta tattaru a wajen.

Ta bude idanunta tana sake saukewa a kansa sanda yake dawowa ciki,hannunsa dauke da tray me azabar kyau,wani irin Royal tray da aka shirya asalin oromian coffee dinsa da baya rabo dashi a ko ina.

"Kai" Ta fada da sauri tana dora hannunta saman hancinta sansa tururin coffee din ya isketa har inda take sanda ya ajiye tray din ya soma zubawa don ya fara dumama cikinsa.

"What?" Ya dago kai yana tambayarta da lumsassun idanunsa.

"Wanne irin coffee ne wannan?"

"Me ya faru?" Ya tambayeta yana duban mug din daya cika da coffee din da tun kafin yakai gasha yawunsa ya fara tsinkewa saboda yadda ya dahu sosai.

Kanta ta girgiza tana kallon mug din da yake shirin kaiwa bakinsa.

"Wannan kamar ba coffee dinka bane" Kadan yayi sipping,sannna ya saukeshi idanunsa cikin nata.

"Shine.....ba abinda ya rabasu dana jimma" Taku biyu ta matsa baya tana yamutse fuskarta.

"Dadi kakeji?....dadi yake maka?" Yadan tsaya da mamakin ganin kamar hankalinta yadan tashi,sai kuma ya dage mata girarsa duka biyun alamun yes. Kai ta girgiza ta juya,ganin tana neman hanyar fita ya kirata a tausashe.

"Hey.....giiftii" Ta waiwayo a hankali tana jin iskar dakin kamar ya sauya mata. Da girarsa da idanunsa ya tambayeta,saita tura baki gaba.

"Ni tunda ka shigo dashi naji iskar dakin ta canza". Idanunsa ya zaro waje,yana mamaki don shikam baiji komai ba. Yayi shuru irin na wanda ke nazari.

"Okay" Kawai yace da ita,sai ya fara tattare tray din kawai,ya dauka yana zuwa ya wuceta a tausashe yana fadin.

"Stay in your room,coffee ne yazo ya sameki,shine zai fita ya baki guri" Ya fadi da kulawa sosai cikin muryarsa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 136*
___________________________
*_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________

Idanunta ta lumshe duka sanda ya kammala fita daga dakin da coffee din.

"What a simple man" Ta fada a hankali muryarta qasan maqoshinta. Batasan me yasa yake da sauqin kai har haka ba,da fari idan ka kalleshi.....zaka dauka zaiyi taurin kai.....zaiyi wuyar sha'ani.....kuma bazaiyi dadin mu'amala ba. Amma kuma sai ka mu'amalanceshi......sai kasha tarin mamaki.

Mu'amalarsa da ita ya sanyata ta sake komawa bitar tarihin ma'aiki da mu'amalarsa da iyalansa,sai a nan ta fahimci tsantsar aiki da ilimi ne yake aikinshi a gurin.

Komai yana qoqari wajen ganin ya kwantanta yadda annabi ya koyar. Taushinsa.....rahamarsa da tausayawa iyali. Yadda yakan tsokani matansa a gurare......tayasu hidima dama yi musu hidimar gaba daya. Sai taji yana sake burgeta,sai taji yana sake shiga ranta,sai taji a duniya tafi kowacce diya mace dacewa da abokin rayuwa na gari.

Taji wani tausayinsa kadan ya taba zuciyar ta,sarki ne shi a gaban duniya......wani abun girmamawa da cika umarninsa.....amma a gida.....a gabanta,yana maida kansa kamar bawa saboda taji dadi.

Ta taka zuwa babban glass door din dake corner din dakin tana tsayawa. Batasan me yahau kanta ba,amma dai ita taji qamshin coffee din ya mata strong da yawa.

Ta sauke idanunta zuwa ga hasken waje dake shigowa,wanda ke nuna yadda rana ke bankwana da duniya. Gurin ya mata ya mata ya mata,har batasan yadda zata misalta ba. Yasan ko ina.....ko ina me kyau.....kowanne guri da zai bawa mace mamaki ya tsaya a zuciyarta. Ta dora hannunta saman glass din tana sakin murmushi tana kallon Huge glass walls. Soft lights. Warm neutral colors masu daukan hankali dake gurin. Ta tuna sanda suke shigowa private villa din nasu. A cikin duwatsu take,a cikin duwatsu aka ginata.

A nutse ya tura qofar dakin yana shigowa bayan ya kammala shanye coffee dinsa. Yayi tsaye daga bakin qofar yana qare mata kallo. Duk sanda zai kalleta.....wata tauraruwa yake gani,ba khadeeja ba.....ba akhnan ba....ba biftu ba.....ba giiftii dinsa ba.

Ya sauke hannuwansa yana takowa cike da nutsuwa. Batasan ya shigo ba,sai duminsa taji a bayanta,ya jawota yana rungumeta ta baya,ya dora habarsa akan kafadarta yana tayata kallon villas din dake gine cikin duwatsun amangiri din ta glass din.

"This place doesn’t look real…” ta furta a hankali kamar me rada. Sauke idanunsa yayi yana kallon yatsunta daya shimfidesu cikin tafin hannunsa. Ba gurin ke masa kyau ba. Itace take masa,ita take haska gurin cikin idanunsa. Baya mantawa,zuwansu na qarshe da 'yan shidansa.......baiji wannan nishadin ba....baiji burgewar gurin a idanunsa kamar yanzu ba.

"It's....."

"......But you look better.” ya fada yana sumbatar dogon wuyanta da wani irin laushi. Tsigar jikinta taji ta zuba,tadan motsa kadan tana murmushin kunya

"You flirt too much these days.” sai ya manneta a jikinsa da kyau kamar zai narke a jikin nata su zama abu guda.

"I’m making up for lost time......ke dince....." Sai ya kasa qarasawa,idanunsa suna lumshewa gami da bude kansu. Yana tuna darare masu yawa data dinga fiddashi daga saitinsa.

".....bansan me zance ba" Ya fada jikinsa na wani irin laushi. Ya karantar da ita karatuttuka masu nauyi a madeena,ta kuma dauka da kyau. Yadda take sarrafashi abun yana kwance masa kai,har sama da yadda ya dauka zata iya..... Harda sabbin darasissikan da bashi ya bata ba. Ta bude hannunta da kyau,ta karbeshi da kalan rayuwar da yakeso,ta sakar masa ragamar kanta da kanta,tana kuma tayashi sarrafa komai yadda zai qayatar dashi.

Da yace mata baya buqatar komai daga gurinta sai SOYAYYA QAUNA KULAWA DA LOKACINTA. Ta dauki dukkan wannan abun daya fada da muhimmanci. Yace mata bayason ra wahalar da kanta gurin neman hanyar da zata mallakeshi......saboda a mallakensa yake indai a kanta ne. Ya gama mallakuwa already,tun ranar farko daya aza idanunsa a kanta. Tayi dariya ranan sosai.

"Amma.....fada mukeyi fa haisamm......bakaso mu hadu ko a hanya.....baka kallona.....ka dauka banyi noticing bane?" Ya lumshe idanunsa kana ya budesu yana murmushi.

"Na sani.....bazan kuma manta ba......ina kishin mazan daketa zuwa ganinki da sunan aure ne........ina tsoron mu dinga haduwa kina kallon cikin idanuna,saboda banaso ki gane komai a lokacin. Ina tsoron naci gaba da ji da ganin mazan dake zuwa gurinki,kada naje nayi loosing control dina saboda kishi......" Sai ya dakata.

".....akhnan" Ya kirata da yanayin daya tilasta mata maida hankali kansa.
Chapter 149 · 0% Book details