Sashe 164
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A cikin waiting parlor din dukkaninsu suka dakata,don haka ba wanda akhnan tasan da zuwansa. Basason su kasance tare da ita tunda wuri haka,saboda karsu kaya mata zuciya,shi yasa ta dauka daga ita sai haisam dinne kawai a gurin.
kowa na qoqarin boye damuwarsa. Daga bangaren kujerun dama nanay ce,zayne riqe da tasbaha. Labbanta na motsi da addu'ar da bata saketa ba tun daga ranar da haisam ya gaya mata Cs din akhnan. Morsa Safiyya na zaune kusa da ita,Idanunta na kan qofar da akhnan zata fito. Ta kasa tantance wanne matsayi take kai,gaba daya ma sai taji kaman addu'ar na shirin qwace mata. Sultane yaso ta zauna gida saboda falaak,amma ita kanta falaak din sai da akayi da gaske sannan ta zauna din.
Daga daya bangaren sultane dinne,zaune yake cikin nutsuwa,amma duk wanda ya san shi zai gane cewa yau zuciyarsa ba cikin nutsuwar da yake nunawa take ba.
Hussam na kusa dashi shi da Aareef,sau noorah dake zaune gefan morsa safiyya.
A nutse akhnan da haisam suka fito daga dakin,magana yake gaya mata qasa qasa wadda ba wanda yasan me yake gaya mata sai ita dashi.
Cikin doguwar farar rigar asibitin take takowa,hannunta cikin na haisam din.
Mamaki ya saukar mata ganin dukkaninsu a zaune a gurin,ba tare da sanin isowar kowa a cikinsu ba. Ta bude ido da baki dukka tana takowa,sai dukkaninsu suka hutar da ita ta hanyar tasowa suka risketa. Gaidasu taketa qoqarin yi,amma sukam ba wannan bane a gabansu. Yadda cikin ya qara qasa yadda take takawa da qyar kowa ke tausayawa. Addu'a ce kawai ke tashi a gurin,ta wani tana shiga cikin na wani,haisam na tsaye daga baya yana amsawa daya bayan daya.
A lokacin ne kuma nurse ta iso da wheelchair.
"Madam, we're ready."
Ta janyo wheelchair din kusa da akhnan din.
Kallonta akhnan din tayi,sai kuma ta kalli wheelchair din.
Ta girgiza kai a hankali.
"No." Ta fada a sanyaye. Murmushi nurse din tayi,tana zaton ba ta ji ba ne.
"It's okay. We'll take you comfortably." Ta fada cikin girmamawa.
Kai akhnan ta sake girgizawa.
"Ba zan hau ba." Ta maimaita mata wannan karon da yaren oromo yadda zata fi fahimta.
Mamaki ya kama nurse din,ta dan rusuna sannan tace
"But......"
"I can walk." Ta dakatar da ita ta hanyar qarasa mata bayanin.
A nutse ta janye dubanta,sai idanunta suka koma kan haisam.
"Ina son muyi tafiyar tare." Ta furta a sanyaye idanunta cikin nasa.
Wata irin nutsuwa ta ratsa fuskar haisam,kamar ya fahimci abin da take nufi. Ba maganar tafiya ba ce kawai.
A'a.....tafiya ce ta qarshe da zasuyi kafin su zama iyaye ita dashi.
Ya matse hannunta a hankali yana sake nutsa idanunsa cikin nata.
"Are you sure?" Ta gyada kai.
"Very sure." Ta amasa masa tana qoqarin maye gurbin tsoronta da murmushin.
Sai ya dan sunkuyar da kansa da yanayi na girmamawa tamkar yana magana da motii.
"Then we'll walk." Ta bata tabbaci tare da wani confidence na daban.
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 151*
A nutse nanay ta share hawayen da suka cika idanunta. Wata irin qauna take gani wadda take kafa kanta da kanta,take kuma kafa tarihi,koda ba'a gaya maka ba idan ka gani kasan cewa sun manta da kowa,sun manta da komai sai kawunansu.
"Allah Ya tsare ku." Nanay ta fada a fili. A hankali akhnan ta qarasa gare ta,ta saka hannuwanta suka ta rungume nanay din,rungumar da batayi yadda taso ba saboda cikin gabanta.
Rungumar da ta sa Nanay ta qara riqeta,kamar ba ta son sakinta.kamar rumaisa ko Aaani ne zasu shiga dakin tiyatar. A yadda takeji a yanzun,batajin idan su dinne ma zataji hakan.
"Ki dawo min lafiya diyata." Nanay ta fada cikin rawar murya
"In sha Allah." Ta amsawa nanay da jarumta sosai a muryarta.
Sai ta matsa wajen morsa Safiyya,morsa safiyyan da ta riga ta fara kuka tuni. Ta kasa jurewa,idan har wani ke rubuta qaddarar wani,zatacw bata taba hango akhnan din zata iya daukar ciki me girma irin wannan dake jikinta ba a yanzu.
"Sannu da qoqari biftu....sannu da ibada." Akhnan ta yi dariya kadan cikin jin nauyi.
"Ni kuma bana son kina kuka." Qoqarin shanye kukan tayi ta janye jikinta kadan tana son bawa kanta qwarin gwiwa.
"Ki dawo da kishiyoyina ko masu gidana lafiya qalau"
"Ana gudun kishiya kuma kina nemanta momma" Akhnan tadan tsokaneta kadan.
"Eh,to wadannan su kam ya zanyi dasu?." Ta fada tana qarasa goge fuskarta.
Duk suka yi dariya.
Ko da cikin damuwa ne,amma hakan ya sake rage musu tension.
Daga nan ta juya zuwa ga Sultane,na dan lokaci suka tsaya suna kallon juna ita dashi. Wannan qaunar ta daban dake tsakaninsu kana iya ganinta cikin idanunsu.
Sultane ya daga hannunsa ya dora shi saman kanta.
"Allah ya sanya albarka a abinda zaki samu biftu.....Ki dawo mana da farin ciki in sha Allah"
Qwalla taji ta taru a idanunta,aai ta gyada kai kawai.
Ba ta yarda ta yi magana ba,saboda ta san idan ta yi hawaye ne zasu zubo. Kuma ta yiwa haisam alqawari ba zatayi kuka a gabansu ba. Koda zatayi kukan,zata yishi ne a jikinsa.....a kafadarsa.....a gabansa shi kadai.
Juyawa tayi tana maida hannunta cikin na haisam. Ba wheelchair. Ba gaggawa. Kawai su biyu. Miji da mata.
Masu tafiya zuwa lokacin da zai canza rayuwarsu har abada.
Corridor din yayi tsawo,amma babu wanda ya yi magana na wasu daqiqu tsakanin ita ko shi.
Ita ta fara matsawa sosai kusa da shi.
"Haisam."
"Na'am." Ya amsa mata yana qoqarin kore damuwa.
"Kar ka firgita idan na firgita." Ta fada a sanyaye. Sai ya yi murmushi kadan,wancan murmushin da ita kadai take iya fitowa da shi saman fuskarsa.
"Too late." Ya furta ba tare daya kalli fuskarta ba. Murmushi me sauti kadan tayi.
"Kana tsoro ne?"
"A lot." A yau ya bata amsa kai tsaye ba wani kwana kwana.
Ta dago kai ta kalle shi tana jin amsar tasa har cikin zuciyarta. Mutumin da yayi hannun riga da tsoro......amma a yau yana bata tabbacin tsoro kai tsaye daga bakinsa.
"Ni kuma bana tsoro." Ta furta kai tsaye.
"I know." Ya amsa a wannan karon yana maido dubansa kan fuskarta.
"Why?" Ta tambaya taba rungume hannunsa sosai,sai ya tsaya na dan lokaci daga tafiyar da sukeyi ya kalleta da kallon da ya saba yi mata tun farkon soyayyarsu.
"Because you're stronger than all of us." A wannan karon,hawaye suka cika idanunta. Kafin ta samu damar amsawa
suka isa qofar theatre din.
Ta dauka zai tsaya ne kaman yadda kowa keyi daga waje,amma sai taga suna shiga tare dashi. Wani irin sanyi da farinciki ya mamayeta. Bata fahimci yana gurin za'ayi aikin ba sai da taga sun bashi medical gown yana sakawa.
Ta lumshe ido tana kallonsa sanda yake daure rigar a jikinsa. Ta masa kyau.....sosai,wani irin kyau daya haska har cikin qwayar idanunsa.
Hannunsa cikin nata suka mata anesthesia suka kwantar da ita,sai suka ajiye masa kujera kusa da kanta ya zauna idanunsa cikin nata. Shi da ita dukka suna jin maganganun likitocin da zasu mata aiki wadanda dukansu mata ne,sai anesthesiologist namiji da wani guda daya daban da bazaizo kusa da ita ba.
Ko sau daya bai bari idanunta sun huta daga kallonsa ba.....tana jin sanda aka soma yaga fatar cikinta cikin nutsuwa da takatsantsan. Ta daga idanunta tana kallonsa sosai.
"You look pale."
"I don't." Ya fada da murmushinsa dinnan me taushi yana juya kansa kadan.
"You do." Ta maimaita masa tana son yin dariya.
"Focus on yourself." Ya fada yana dan lakuce mata hanci da yatsansa. Murmushi ta sauke
"Allah you are scared."
"I'm not......giifii mana" Ya fada yana dan yamutsa fuska yadda take masa idan ya dameta da tsokana.
Likitar ta yi dariya,don duk maganan da suke tana jinsu. Komai nashi asali burgeta yakeyi,a yanzun da taga mu'amalarsa ta zahiri da matarsa sai abun yake sake burgeta qwarai. Ta girme masa nesa ba kusa ba,amma tana yabawa halayensa sosai.
"Your husband is definitely scared." Itama ta sanya musu baki.
A karo na farko akhnan ta ga ya kasa musantawa.
"Can everyone stop discussing me?" Ya fada yana basarwa sosai,abinda ya bawa kowa na dakin dariya,dariyar kuma ta cika dakin.....ta rage mata tsoro.
"Hold my hand tighter" Akhnan ta fada da muryar rada. Idanunsa cikin nata ya sauke mata wani murmushi me laushi,ya kuma sake matse hannun nata cikin nasa. Abinda ya lura,yadda yake qoqarin bata aminci.....itama dake kwance cikin irin wannan yanayin qoqarin bashi nutsuwa takeyi.
Lokaci ya ci gaba da tafiya a hankali,yana debo mata memories din rayuwarsu ta baya. Wani tayi murmushin kunya wani ta musanta kadan ba hayaniya ko motsi me qarfi. Doctors suna aikinsu,komai na tafiya yadda aka tsara.
"Remember madeena?" Ta dan yi mamaki.
"Yanzu?" Saboda bata dauka labaransa zasuyi tsaho haka ba,kwata kwata ya hana tunaninta komawa kan Cs din da ake mata a yanzu haka,yanata daukarta yana cillata wasu duniyoyi.
"Yes." Ya amsa mata,sai ta yi dariya a hankali.
"Me yasa?" Ta sake tambayarsa,ya dan yi shiru kafin ya ce
"Saboda a lokacin ne na fara gane....." Sai ya dakata kaman yana ja mata rai,ya saba mata irin haka idan yana bata labari,sai suyita rigima.
"Gane me?" Ta tambaya da zumudi
Idanunsa suka sauka a kanta da wani laushi.
"That I was already in trouble." Ta hade gira.
"Wane irin trouble?" Sai ya dan matsa yatsunsa dake cikin nata.
"The kind where a man stops thinking about himself."
Akhnan ta ji wani irin abu ya taba zuciyarta. Inde zai magana da ita irin haka,sai ya sake matsa zuciyarta da soyayyarsa.
Ko yanzu.....a irin wannan lokacin......har yanzu yana qoqarin rage mata tsoro,bai barta da firgici ko damuwa ba.
Sai kuma wani motsi ya sauya yanayin dakin.
Likitocinne suka fara magana da juna cikin farinciki a muryarsu.
Akhnan ta juya kanta kadan,bata fahimci komai ba tukuna. Saidai a take qaramin sauti ya cika dakin. Rauni sosai a muryar dake son nuna jarumta da qwazo......sabon sauti ne.....mma ya isa ya sauya komai.
Hawaye taji sun cika idanunta kafin ma ta sani. Ta sake juya kai zuwa ga haisam.
Fuskarsa ta sauya gaba daya,kamar mutumin da aka cire masa duniya aka ba shi wata sabuwa.