← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 176

Sashe 44

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eh". Ruwa ya dinga zuba mata tana wanke fuskarta da bakinta. Yabi hannuwanta da kallo yadda suke kakkarwa,ta kammala ya jawo qaramin towel ya damqa mata. Ta dauka iyaka kenan,sai taga ya riqe tsintsiyar hannunta,bai kuma saketa ba sai daya tabbatar ta kwanta sosai ya maida duvet din ya rufeta.

Idanunta a lumshe numfashinta yana sauka a hankali,tana jin qarar ruwa a toilet din,tana jin alamun wanke sink din dama duk gurin data bata da qaramin brush.

Slippers din ya zare daga bakin toilet din,ya tako a nutse har zuwa bakin gadon. Tana jin tsaiwarsa amma ta kasa bude idanunta saboda sanyin dake nuqurqusarta.

*_Assalamu alaikum warahmatullah_*

*_Akwai pyjamas/home wear/lounge wear tsala tsala masu dadin zaman gida da bacci_*

*_Sabbi kar a mutunce cikin jakarsu,a affordable price_*

*NA IYAYE DA YARANSU*

*_kina kasuwancinsu?,Maza zoki gwada wadannan dana kawosu......quality dinsu ya girmi farashin_*

*_ki siga ki siyawa yara.....masu dadin sawa a zafinnan.....ga taushi ga ba nauyi_*

*_maza tuntubi huguma ta nan don ki ganewa idanunki_*

08187255862

Idanunsa ya zube fes a kanta,sai ya lura da yadda haqoranta suke haduwa guri daya amma tana qoqarin hana hakan faruwa. Aman da tayi relief ne yasan zata samu.....amma baisan me yasa har yanzu sanyin da takeji yaqi raguwa ba,da alama jininta yana da qarfi sosai. Har qasan ransa yaji bazai iya tafiya ya barta a haka ba,sai ya juya a nutse ya fara bude windows na dakin tunda ba fanka ko Ac,dole su baqaci fresh air komai qanqantarta.

Ta cikin rufaffun idanunta take iya ganin duhun daya mamaye dakin. Ta cikin rufaffun idanunta take iya jin motsin haurowarsa gadon,hakanan ta cikin rufaffun idanunta takejin sanda ya janye duvet din,saidai abinda ya bata mamaki lokacin da taji ya hauro daya side din ta samanta,ya kuma fara laluben zip na sleepwear din jikinta.

Duk wata tsiga ta jikinsa saida ta zuba saboda wrong position daya dora hannunsa. Maimakon ya kama zip sai hannuwansa suka tafi wani guri na daban. Kamar an jona masa wutar lantarki a jikinsa haka yaji wani irin shock daya harba tare da harbawar jinin da zuciyarsa take aikewa a kowanne second zuwa sassan jikinsa.

Abun yazo mata a bazata....wannan ya sanya numfashinta ya dauke na wucin gadi ta kuma kaiwa hannunsa cafka ta riqe sosai zuciyarta na dokawa da matsanancin qarfi.

"Ka......kkkaaaaa" Sai kuma ta kasa fada,ta kasa hada haruffan saboda bugun da zuciyarta keyi din ya hana daidaituwar kalaman saman harshenta har sukai ga fita.

Yasan me takeson fadi,sai kawai ya sauqaqe mata,ya saukar da kanshi daidai kafadarta,da wani irin sauti da yayi ma kunnuwanta laushi da yawa,sautin da yafi kama da rad'a yace.

"I'm.....I'm sorry.....“That wasn’t my intention.” ya fada yana dakatawa kamar wanda ke zaben kalmomin da zaiyi magana dasu

"......yi directing dina zuwa zip..........sanyin da kikeji yayi yawa" Ya fada yana jin kalaman kamar zasu qwace daga bakinsa,don abinda yakeji a yanzun cikin jikinsa kamar zai wuce ne da numfashinsa.

Duk magananshi da harshen France yana sake sawa komai yana qwace mata ne....muddin zai bude wannan husky voice nashi ya yara mata french to yana sanyata tajita kaman ZERO,yana sanyata tana jin kaman bata iya komai a yaren ba....kaman bata iya pronouncing na yaren yadda ya dace ba....ballantana yanzu. Muryar dayake mata magana dashi wata murya ce ta daban,wata murya ce ba kalar wadda ta saba ji daga gareshi ba.

"Nooo..." Ta fadi tana dan jan kalmar da dan tsaho. Akwai kafiya cikin muryarta,shi kuma ba wannan yake buqata ba a yanzu. Koda wanne lokaci zata iya loosing yanayinta inde bai samar mata da abinda zai bata dumi sosai ba.....ba kuma abinda zai wannan aikin nan da nan sai skin to skin.

A hasashensa cikin duhun ya sake kai hannunsa jikinta,cikin sa'a ya dora hannunsa akai,saidai akwai alamun nata hannun yana gurin. Ture hannun gefe yayi,ta buda baki da niyyan magana tana son maida hannunta gurin,saidai hannun nata a ainihin fatarta ya sauka don tuni yakai zip din qasa.

A nutse ya soma sabule mata rigar daga kafadarta zuwa daya kafadar,dukkanin labbanta rawa suke,magana takeson tayi amma bata da wannan energy din.

Wani irin yanayi ne me wahalar fassara a gareshi.....bashi kadai ba,ga duk wani kamammen namiji daya adana samartakarsa hakance zata kasance dashi. Dukka hannuwansa rawa suke lokacin da yayi mata kyakkyawan masauki cikin faffadan qirjinsa,ya maida hannuwansa dukka biyun ya mata kyakkyawar runguma. Fatarsa ta manne da tata,yalwataccen gargasar nan me santsi dake lullube da qirjinsa ta sauka gefan kuncinta......fuskarta ta nutse tana samun kyakkyawan masauki cikin qirjinsa. Karo na farko a rayuwarta da wani d'a namiji ya kusanceta irin haka.....kamar yadda ya zama karo na farko da wata diya mace ta kusanci gangar jikinsa har haka......sannan yaji kaman kusancin yanason kutsawa tare da danna kai ya zarce iya skin nasa kawai. Kamar akwai wani abu dake qoqarin bonding nasu da wani irin zafi da sauri me kama da walqiya.

Sake boyeta yayi sosai cikin qirjinsa yana jinsa a hankali yana fita daga ainihin wannan duniyar zuwa wata duniyar ta daban,hancinsa yana zuqo mata daddadan qamshin da lallausar sumarta da fuskarsa ta shige ciki tayi mayafi da ita. numfashin da yake zuqa a yanzu cikin hancinsa yana jin cewa ba ainihin numfashinsa da yake shaqa bane a kowacce rana. Bugun da zuciyarsa takeyi a yanzu yana jin ba ainihin wannan zuciyar bace a qirjinsa a yanzu.....duniyar da yake ciki.....mintunan dama awannin dukkaninsu ba irin sauran awannin da yayi a shekarun rayuwarsa gaba daya bane.

*_Assalamu alaikum warahmatullah_*

*_Akwai pyjamas/home wear/lounge wear tsala tsala masu dadin zaman gida da bacci_*

*_Sabbi kar a mutunce cikin jakarsu,a affordable price_*

*NA IYAYE DA YARANSU*

*_kina kasuwancinsu?,Maza zoki gwada wadannan dana kawosu......quality dinsu ya girmi farashin_*

*_ki siga ki siyawa yara.....masu dadin sawa a zafinnan.....ga taushi ga ba nauyi_*

*_maza tuntubi huguma ta nan don ki ganewa idanunki_*

08187255862

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽

💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 41*

Cikin qasa da second biyar taji gaba daya an zare mata sha'awar yunqurin qwatar kanta da takeyi.....cikin qasa da second biyar ta soma jin wani irin mani'imcin dumi yana ratsata.....cikin qasa da second biyar ta soma jin wata irin nutsuwa me aminci tana mamaye gangar jikinta da ruhinta gaba daya.

Numfashi taja me nauyin gaske,wanda ya zuqo mata anihin qamshinsa na gasken gaske dake tashi da laushi a gargasar dake qirjinsa wadda tafi kowanne luxury pillow data taba using saboda bacci santsi laushi da wani irin calmness.

"Oud Wood,Baccarat Rouge,Amouage Interlude,Midnight Oud,Royal Ember,His Scent" dukka cikin turarukan ta gaza gano wanne ne ainihin turarensa?,wanne irin qamshi ne wannan me azabtar da zuciya?.

Qamshinnan nasa… mai ɗumi da laushi…
yana manne da shi a dukka wani yanayi na rayuwarsa,dare ko rana,kamar wani bangare na jikinsa,wani abu ne da ba a iya mantawa da shi ko bayan ya tafi.

"Zan zauce......please,kaman ina loosing control dina" Ta motsa labbanta tana fada a hankali,saidai ta barwa zuciyarta da fatar bakinta sirrin abinda takeson fada din. Tana jin kamar ta furta,amma wani abu yana danne mata kalmominta. Ta lumshe idanunta tana jin wani yanayi yana fusgarta.

"Me nakeji?,ya Allah" Ta fada tana lumshe idanunta,wani irin feeling da bata taba jinsa ba yana taso mata,saidai bata kalleshi da idanun ma'anarsa ba,sai wani abu na daban.

Idan yace ya rasa hayyacinsa da ita riqon daya mata kawai na wasu mintuna bazai qaryata ba. Abu daya ya iya ganewa,saukar numfashinta a hankali,da gumin da yake goshinta wanda ya fara ratsa fatar qirjinsa,sai damshin da yaji daga gadon bayanta inda tafukan hannayensa ke kwance a gurin saboda tsaro....gudun qetare iyaka,tabbacin zazzabin da yayi mata mummunan kamu ya sauka kenan.

Yayi shuru yana jin yadda jikinta ya sake gaba daya.....yana jin yadda iskar numfashinta ke fita da wani irin nutsuwa. Koda ba'a gaya masa ba ya sani bacci ne ya dauketa,irin baccin nan dake cike da nutsuwa me yawan gaske.

Tunda ta fara gumi dole ya rage duvet din da suke ciki,ya yayeshi gefe yana kallon window da yake ganin fatsi fatsin ruwa,daya saurara sosai sai ya fahimci ruwan sama ne yake sauka,wannan ya sanya wani sabon zafin tasowa. Yabi siririn hasken dake shigowa dakin ta tsakanin labulen dakin,wanda ya sauka direct a kafadunta.

Ya sauke idanunsa a hankali,mamaki kadan yana kamashi,duk da cikin duhu ne amma hakan bai hanashi ganin glowing skin nata ba.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Ya furta yana jin wannan abun daya danne yana taso masa yana kuma nema yafi qarfinsa fiye da dazu.

Cikin ransa yakejin inde bai tashi ba.....inde bai canza makwanci ba komai yana iya faruwa. Ya fara rasa control dinsa......ya fara jinsa sama sama......ya fara jin kamar numfashinsa yana neman qwace masa.

Ya yunqura sosai zai miqe,daidai sanda akayi wata tsawa data sakata farkawa daga baccin daya mata wani irin dadi. Ba tare data shirya ba ta damqeshi da kyau tana sake qanqame hannuwansa a muhallin da yakejin hadarinsu a tattare dashi yafi hadarin bindiga me bullet.

Tun ba yau ba....tun a wancan ranar ya gama karantar tana tsoron tsawa,amma a yanzun kalan riqon data masa bazai harfar musu da d'a me ido ba. So yake ta sakeshi,ta gyara kwanciyarta,ya kunna Ac,ya dawo ya kwanta koda daman sofa bed ne ko saman Normal sofa,don tunda aka fara ruwa yasan shima bazai barta ba,ba zata iya kwana ita daya ba

"Sakeni" Ya samu ya furta da qyar,don bayajin zai iya mata dogon jawabin ba tafiya zaiyi ba.

"Tsoro nakeji don Allah" Ta fada muryarta na rawa,hankalinta yana kan window din,saboda walqiyar da ake sakeyi ta tabbatar wata tsawar a gaba na nan zuwa,ba kuma tare data lura da muhallin da taketa riqe masa hannu ba.

"Ki sakeni mana" Ya sake fadi wannan karon yana dan kausasa muryarsa kadan saboda ya fara loosing control dinsa.
Chapter 44 · 0% Book details