← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 176

Sashe 76

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Magajin sarauta a wata duniyar da kullum ta daga kai,....kullum ta daga kai taga irin girma da matsayin daya siya mata.....kullum ta daga kai taga tarin qauna da soyayyar daya siya mata ya jawosu zuwa cikin rayuwarta......kullum ta juya tunaninta tana duban yadda ya kawo wata mace cikin rayuwarta wadda ruhin mahaifiyarta ya koma ga ubangijinsa yana mararinsa......saita rasa ME YA DACE TA BASHI?....ME YA DACE TA SAKA MASA DASHI?.

"Ki soshi" Amsar da zuciyarta ke bata kenan aduk sanda ta xurfafa cikin irin wannan tunanin,amma saita juya kan nata a hankali,saita dinga ganin kamar ba a wannan muhallin bane kyautar zuciya.....ba'a daidai wannan lokacin ba.....ba'a wannan yanayin ba sam sam.

"Mun wuce ai,dani da motii" Amsar nanay ta shiga kunnuwanta a hankali suka bata wani sauti na faduwar gaba. Sai data qara yawan numfashin da take zuqa zuwa ga hunhunta tana jin wata siririyar fargaba. Zamanta na duk minti daya a nan gurin hatsari ne.....hatsari ne ga zuciyarta gaba daya. Komai da zata kalla nasa.....komai daya shafeshi idan ta kalla sai taji kamar zuciyarta kamar tana sake nutsewa a cikin wani sassanyan ruwa a hankali da wani irin nisan nutsewa.

"Giiftii" Nanay ta kirata da sautin da yaja hankalinta sosai.

"Na'am nanay".

" Na bashi aronki......ki zama kusa da inda yake,ki kula dashi,na kwana uku kawai". Ta fada a nutse amma kaman itama tanason fahimtar wani abu cikin kalamanta data fada din.

Wani nauyi taji kaman nanay ta aza mata. Sun tafi sun barta.....sun tafi sun barta a muhallin daba kowa,daga ita saishi. Sun tafi sun barta da wannan sheikh din....wannan malamin dai da yake mata tsananin kwarjini.....sun tafi sun barta da wannan mutumin da a kullum....daga ita sai zuciyarta tasan yadda take gudun fanfalaqi.....yaqi da fadi tashin qaryatawa dama boyewa gami da binne abinda ke cikin ranta da zuciyarta gaba daya.

Anya?,tana da qwarin gwiwar jure wannan kusancin?,anya tana da wannan jarumtar?,ta kula dashi?......zata iya?.

"Giiftii" Ta sake kiranta.

"Amma ba kulawa dashi kadai ba......" Ta fadi tana yanke maganar,ta bawa iska dama a tsakani sannan ta sake cewa.

"Ki kula da kanki ma...." Sake jin wani nauyi tayi yana sake daureta sosai. Kunya kuma tana samun kyakkyawan muhalli tana cakudewa da fargaba cikin ranta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Ki kula dashi da dukka nau'in kulawar data dace......irin kulawar da mace ke bawa mijinta. Karki bari yaga gazawarki duk qanqantarta.....saidai kowacce kulawa tana da iyaka" Ta tsagaita da magana kamar tanason ji ta bangaren akhnan din.

"Yana da hali me kyau,bawai don yana yarona bane......kuma idan bashi da lafiya,yana komamin kamar qanqanin yaro ne,wannan din dabi'arsa ce.....tun daga quruciya har zuwa yanzu daya girma bai sauya ba" Wannan kalmar ta nanay ta qarshe tana jin yadda ta furtata,da wani sassanyan murmushi a cikinta......wani kalan murmushi da koda akhnan bata ganshi ba tasan yana tuna mata da wani bangare ne na quruciyarsa,sai taji kaman Nanay taci gaba,kaman nanay tayita bata labari akan abinda ya shafi quruciyarsa.

"Giiftii" Ta sake kiran akhnan din a tausashe,kiran daya ratsa har zuciyar akhnan din. Sautin ya isa kunnuwanta da wata irin nutsuwa,tana sake ji kamar tana magana da mamminta ne.

"Ko tsakanin harshe da haqori ana sabawa......a kwanaki ukun nan,koda zakiga alamun yana fushi dake....." Saita sake dakatawa,sannan ta dora a hankali.

"Ba fushi bane.....kulawace da baya iya boyeta". Wani siririn murmushi ya kubcewa akhnan......murmushin da batasan yadda akayi ta samar dashi a saman fuskarta ba.

Maganan nanay ta yanzu.....kalmarta data fada a yanzu,hakan yana nufin......ba fushi yakeyi da ita ba dazu?....hakan yana nufin kulawa ce?. Kenan itama tana cikin jerin sahun mutane masu muhimmanci a gurinsa da zasu iya samun kulawa?.

"Idan namiji irinsa yayi shuru......kiji tsoron shurunsa....musamman a inda akayi rashin kyautawa......amma idan yayi magana,wata qofa ce ya bude miki" A hankali ta gyada kanta tamkar tana gaban nanay. A hankali duk wata kalma dake fita daga bakin Nanay ke burgeta......a nutse takejin kowacce kalma daga bakin nanay din tana samun wani kyakkyawan gurbi da matsugunni a ranta. Kamar tana buda mata wani babi ne.....kamar wani kundi me matuqar daraja da muhimmanci take buda mata.

"Yana da wata zuciya da take MAKAHON SO...qila shi yasa Allah ya damqa masa 'yar uwarsa a matsayin matarsa......a jininki da nashi kawai nakejin zaku fahimci juna koda baku magantu wa junanku ba....." Maganan tata ta sake kaiwa qarshe da wani irin taushi.

"Ki zauna dashi..."

"Ki kula dashi......Allah ya tsareku".

"To nanay.....na gode" Ta fadi da wani harshe data fara koyon ladabin magana dashi. Wani harshe da yake mata dadi matuqa....wani yanayi da ita kanta idan tayi magana da mutane dashi yake burgeta.

Idanunta ta lumshe sosai tana relaxing bayanta jikin makarin kujera. Taja iska sosai cikin hunhunta sannan ta fiddata a hankali. Tunaninta gaba daya yana komawa kan nanay ne. Tana jin ta aza mata wani nauyi me girma amma kuma sai takejin kamar dolenta ne.

Ta kula dashi.....ta kula dashi.....idan baida lafiya yana koma mata kamar qanqanin yaro ne.....ta yaya?,ta ina zata fara da wannan aikin me girma da nanay ta aza mata?.

"Zaki iya akhnan.....zaki iya......darajarki....martabarki da mutuncinki a idanun nanay....... Zaki iya akhnan......ki tuna,ya sadaukar......da sadaukar da yawa a kanki......ki tuna akhnan,ya baki kariya ya kula da ciwonki mabanbantan lokuta.....a lokutan da bakisan daraja da girman kulawar ba" Maganar data fara mata yawo kenan a kanta,ta bata wani qwarin gwiwa,ta kuma sanyata bude idanunta a hankali ta maida dubanta kan wayarta.

Number birra ta laluba,bugu daya kamar kullum birran ta daga.

"Kada ku damu da rashin dawowata birra....." Saita gaza qarasa mata tana jin kamar yayi nauyi ta gaya musu tana gurin sheikh haisam....

"Karki damu uwar gijiyata,nanay ta yimin bayani,yanzun haka ina kan hada miki kayayyakin da zaki iya buqata zuwa sassan"

"Na gode" Kawai tace da birran tana yanke kiran.

Iska ta furzar daga bakinta,qwaqwalwarta tana mata bita da tilawar wasu daga cikin qa'idojin masarautar data karanta.

Zata zama daga ita sai haisam cikin sashen kenan iya adadin kwanakin,baqi hadimai ko bayi sai idan su suka lamunce musu shigowa. Duk wani guri da yayi kusa da falukan dake kewaye da dakunan baccin sashen ba wanda yake da ikon zuwa sai bisa sahalewarsu. Zuciyarta tadan buga kadan,ta ware tafukan hannunta tana kalla kamar wadda take neman shawara daga gurin wani.

Koda ta kira shehnaz a yanzun tana jin ita da shehnaz din suna rayuwa ne a mabanbantan duniyoyi. Babu lallai ta fahimci komai daga cikin abinda zata gaya mata. Falaak ce....kuma tana jin nauyin magana data shafi haisam da ita. Ita din gaba take da ita,kamar yadda dukkaninsu haisam din yake gaba dasu.

Qarar wayartata shine ya sake dawo mata da tunaninta daga inda ya tafi,birra ce,ta daga kiran tana sakawa a kunnenta ba tare data ce komai ba.

"An kawo komai da komai ranki ya dade"

"Na gode birra" Ta fada a nutse. Bin wayar da kallo birran tayi,a yanzun data koyi godiya abun mamaki yake baiwa birran,mamakin me yake sauya dabi'arta ne sannu a hankali a hankali?.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 69*

Kayan jikinta ta kalla,suna da dan nauyi kadan,bata iya zama da kaya masu nauyi harta wuni dasu,me ya kamata tayi yanzu?,ta ina zata fara abinda ya dace?. Miqewa tayi tsam ta soma takawa zuwa hanyar fita ko zata samu kayan da birran tace an shigo dasu,saidai tana bude qofar ta tsinci suitcase dinta tsaye a qofar dakin. Ta danji mamaki kadan,don tasan ba lallai birra ta iso gurin,to waye ya iso da ita?.

Bata tsawaita tunaninta ba ta jawota zuwa dakin da kanta,wani abu da cikin rayuwarta ba zata iya tuna sau nawa kwata kwata ta taba yinsa ba.

Ta kwantar da ita tana budeta saqo ya fado cikin wayarta. Hannu ta sanya ta dauki wayar,ganin sunan nanay ya sanyata komawa ta zauna sosai tana kallon wayar.

A nutse take bin rubutun,wani irin tsararren menu ne nanay ta shirya mata. Yadda zata kula dashi step by step,kowanne minti zuwa awa daga safiya zuwa dare.

Koda ta gama karantawa murmushinne ya sake subuce mata

"Ya Allah,na gode daka ceceni" Ta motsa labbanta a hankali tana furtawa. Sosai taji dadi.....taji dadin menu din,kamar tasan abinda take saqawa kenan a ranta,yaya zatayi?.

Menu din ya zame mata kamar wani d'an jagora a sanda take cikin tsananin duhu.

Ajiye wayar tayi ta miqe tana sake bude jakar. Ga mamakinta atamfofi a ciki dinkakku,lafiyayyun super Holland vlisco masu asalin kyau da taushi,marasa nauyi wadanda zasu baka daman sakewa cikin dinkunansu.

Mamaki kadan ya kamata,yaushe yanayin tsarin jaka da suturarta ya sauya?. Duk da bata da masaniyar komai akan suturarta amma wannan sauyin yadan bata mamaki.

Hakanan ta cire doguwar riga a ciki,wadda aka mata wani budadden dinki daga qasa,ya bude sosai,ya kuma zauna das a qirjinta,ya fitar da dogon wuyanta da kafadunta dake tsaye kyam wadanda suka dace da qirar jikinta. Tsaiwa tayi tana kallon kanta sosai,Dinkin ya taimaka wajen fitar da shape din qugunta daya baje sosai tare da budewar da rigar tayi ta qasanta. Cikin ranta karo na farko da taji atmfa ta shiga ranta,ta kwanta mata a rai. Tayi qoqarin ta daura dankwali amma ta kasa,duka hannuwa suka gaji,sai kawai ta wurgar dashi a nan,ta matsa ta dauki wani mayafi data gani cikin kayan ta yafa saman sassalkar sumarta.

Takawa tayi a nutse tana fita daga dakin,sannu a hankali sai hankalinta ya rarrabu wajen neman qofar fita. Kamar wadda aka juyarwa da kai,kaman bada qafanta ta qaraso dakin ba,kaman bayan shigowarta an canza tsarin ginin gurin,saita kasa tantance qofar fita,dole ta dinga bi hanya bayan hanya tana dubawa.

Qofa ta qarshe taga tayi mata kama da qofar data shigo din a dazun,tadan lumshe idonta ta aza hannunta akan handle din tana addu'ar Allah yasa ta dace can dince.
Chapter 76 · 0% Book details