← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 176

Sashe 133

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ku koma ku gaya mata wani abu." Yayi maganan calmly kamar ba shine zuciyarsa ke zabalbala ba. Ba wanda ya iya koda motsa yatsarsa,sai ya sake magana. A hankali. Amma kowace kalma nada wani irin kaifi dake iya fede zuciya saala saala.

“Ahmad…” ya irga da nutsuwa sosai.

“Safiyya…”

“…na ƙyale ta.” Akhnan ta tsaya cak,saboda yadda muryarsa ta canza.

“Na ƙyale ta tana wasa da iko…” ya fada yana tsuke idanunsa sosai launinsu yana sake jirkita zuwa yanayin da suke komawa idan yana cikin tsananin fushi da b'acin rai.

“Saboda tana tona kanta da hannunta.” gaba daya suka qarasa daskarewa a gurin da jin irin saqon da yake aikewa mammina.

Sai ya d'an juya kadan. Ya kamo hannun Akhnan gaba d'aya cikin nasa. Riqon hannun da su kansu saida suka bi hannuwan nasu da kallo.....wani abu cikin kansu da zukatansu yana gaya musu SAQO NE DAGA ZUCIYAR WANI ZAKIN MAZA.

“But this woman?” Ya furta yana dubansu,duba irin na kai tsayen nan wanda babu sassauci a cikinsa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

“MATATA CE!!!.”
Wani irin shiru me ban tsoro ya sake ratsawa.

“And if Mammina has forgotten…” ya fada da wani nutsuwa me karya qashi da zuciya.

“…ku tuna mata.”
Sai ya matsa gaba kad'an.

“Akhnan…”ya kira sunan Lower voice,amma cike da wnai respect cikin kiran sunan kawai.

“…ita ce layin da babu wanda yake tsallakawa!!!.”

Kamr jininsu ya tsaga ya ajiye wannan saqon haka sukaji. Jami’in da yake shine shugaba sai yarasa yadda zai hd'iye yawunsa.

Har a jijiyoyin jikinsa yakejin wannan ba gargadi bane kawai.......RANTSUWA CE!!!......ALQAWARI NE.

Hannunsa ya sanya,ya karb'i takardar daga hannun jami'in finally. Ya kalla na second biyu. Sannan ya zame yatsunsa daga na akhnan,ya yayyagata gida biyu.

Akhnan ta zaro ido. Gaba daya Guards d'in kowa ya shiga wani irin shock.

Saboda babu wanda ya tab'a karya umarnin Mammina haka a bude a bayyana a gaban jama'a.

Saki takardun yayi suka zube k'asa iska tana sake d'ai d'aitasu a gurin da wani yanayi na rashin daraja da tozarci.

“Ku fita.” ya fada calmly. A karon farko babu wanda ya motsa saboda tsoro. Sai ya d'an d'aga gira kad'an.

“Ko sai na manta cewa ku kuna aiki ne kawai?”

Sunkuyar da kai sukayi da sauri,suka kuma soma retreating da sauri. Amma saidai kafin jami’in ya fita,haisam ya sake kiransa.

“Tsaya.”
Mutumin ya tsaya a take kamar yadda ya buqata,sai haisam ya zuba masa ido da wani irin sanyi mai kashe jiki a idanunsa.

“ka fada mata wannan da kyau.” ya furta a hankali

“Na yi shiru saboda na yarda.”

“Kar ta tab'a kuskuren tunanin na kasa tsayarda ita.” dukka gurin ya dauki shuru

“Saboda ranar da zata sa ni shiga tsakaninta da Akhnan…” ya damqe haqoransa har hakan yana nuna alama ta saman kumatunsa,ya kuma dunqule hannunsa yana son boye azalzalar da zuciyarsa ke masa.

“…ita ce ranar da zata fahimci ban tab'a shiga yaqi da ita ba tun farko.” taku uku yayi ya basu baya ba tare da sake umartarsu su fita ko su zauna ba.

Kamar masu turereniya suka soma fita,kamar suna son barin wajen kafin wani abu ya faru.

Tsaiwa kawai akhnan din tayi tana kallonsa. Tsahon saninta dashi.....tsahon sanda ta fara ganin fuskarsa idan ka cire randa tamim yaso tafka wannan gangancin bata taba ganin fuskarsa a haka ba.

Wani irin sautin bugu zuciyarta take bayarwa.

"Ya salaaammm......ya ilaheeee" Ta fada cikin zuciyarta. Zaki ta nema.......sai kuma ta samu sama da abinda yafi zakin. Jarumta.....qarfin zuciya da zallar kwarjini me yagalgala zuciya.

A hankali ya juya gareta,nan take yanayin idanunsa ya canza,ya sake komawa wannan haisam din......SOFT HAISAM da take gani kowacce rana.....ba wanda ya gama magana yanzu haka a gabanta ba. Sai ya d'ago hannu ya shafi gefen fuskarta cikin kulawa.

“No one will touch you.” ya fada da dukkan zarrarsa.

“Na miki alqawari.” ya sake tabbatar mata.

A yinin ranar gaba daya,wani yanayi daban take gani tattare da haisam din.

Wani abu ya sauya a cikinsa......
Ba a fuska ba. Ba a kalamansa ba.Amma a idanunsa… akwai wani irin yanke hukunci da ya fara bayyana.

Kamar zuciyarsa ta gaji da jiran lokaci. A daren ranar.......akhnan ta soma lura da kowanne canzawar motsi na haisam. Kad'anne.....wata irin kakkaifar alaqar zuci data qullu tsakaninsu ba tare da dukkaninsu sun ankara ba ya sanya take gane komai nashi a yanzun.

Yawanci idan dare yayi yakan kasance kusa da ita. Ko yana karanta wani abu. Ko yana karatu a library dinsa. Ko kuma kawai yana zaune yana kallonta idan ta kasa bacci.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 121*
___________________________
*_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
__________________________

Amma a yau yawan fitarsa ya qaru. Wayarsa tayi ringing da yawa sama da yadda ya saba ji. Yana amsa wayarsa cikin low voice. Yana fita balcony. Ko ya shiga private study.

Dogayen calls,muryarsa low da wani irin controlled a cikinta. Ko kusa.....ko alama bata d'auka zata tsaya koda a gefan wannan matsayin da take ganin ya azata ba. Bata taba zata ko tunanin matsayinta yakai har yau haura haka ba sai a yau din. Saboda ita.....saboda ita kawai ya rasa dukka nutsuwarsa?.

Cikin dare sau biyu tana farkawa ba tare da ta ganshi kusa da ita ba kaman yadda ya saba.

Ta miqe a hankali tana sauka daga gadon,ta shiga toilet tayi fitsari. Shi yasa takejin wani emptiness a cikin baccin nata,ashe rashinsa ne a kusa da ita?. Mamaki ya sanyata sakin murmushi duk da jagulewar da har yanzu zuciyarta take ciki game da lamarin mammina.

Tana fitowa daga toilet din sai ta hango haske a kunne ta corridor.

Ta taka a hankali ta tsaya bakin qofar. Idanu ta zuba sosai,qofar bata kammala rufuwa ba,akwai siririn space da yayi ragowa,wanda ta nan ne hasken ya samu daman fitowa. Ta nan din ta hangeshi,idanunta ya sauka a kansa a hankali.

Haisam zaune cikin dim light. Files da takardu sun cika table din dake gabansa.

Wayarsa a kunnensa. Wani old map a buɗe gabansa. Qasa qasa takejin muryarsa,wannan muryar da yau tun dazu amonta ya canza da wani launi na daban.

“No.” ya fada da low and cold voice

“I said before sunset” sai yayi shuru yana sauraron dayan b'angaren. Ya motsa a hankali yana daga wata takarda yana kallonta.

“Everything must be ready.”

“No mistakes.”

Idanunta ta lumshe tana kuma budesu lokaci daya dukka a kansa. Duk wannan yaqin da akeyi hakan bai hana soyayyarsa ginuwa cikin ranta ba. A yau yadda yayi matan sai ta sake jin tafi kowacce mace sa'ar samun miji da ba irinsa. Sai ta jita tana komawa sarauniyar matan duka duniya....bawai sarauniyar agadez kawai ba.

Bata tab'a ganinsa cikin irin wannan tension din ba.

Komai na iya taku da tsaro yabi jikinsa.....don haka a jikin nasa yaji kamar motsinta.

Baya taja kadan,sai kuma taga qofar ta bude. Haisam ya fito. Sanye da black qatar thobe da bai rufe maballan gabanta ba,wannan ya sanya lallausar gargasar dake qirjinsa a kwance ta fito.

Hannunsa ya sanya a hankali yana shafa gurin maballan,shima ya manta.....ya mañta a bude suke tun dazu,sau yasa hannunsa daya da yatsunsa yana qoqarin ballewa. Kunya ta kamata,ta dauke idanunta gefe. Hala yaga tana kalle masa qirji shi yasa ya ankara da bai balle ba yake ballewar. Idanunsa suka sake sauka a kanta instantly. Na second biyu,tsigar jikinsa na tashi a hankali saboda yadda farar night gown din ta mata kyau ta kuma karbeta duk da kaurinta,gashin gaban goshinta ya fito sosai ya kwanta,ya sake fidda kyanta.

“Me yasa baki kwanta ba?” yayi tambayar calmly.

Akhnan ta kalleshi cikin shakku.

“Kai fa?” ta fada softly

“Tun ɗazu baka huta ba.” Sai ya d'an yi shiru. Kallon da yake mata yanzu,cike yake da tunani

“Akwai abubuwan da ya kamata su motsa kafin lokaci ya kure.” ya fada da tattausan sautin nan nasa.

“Wane irin abubuwa?” ta tambaya cikin rashin fahimta tana matse girarta. Ta masa kyau....wani irin mugun kyau,sai ya kasa riqe kansa ya matsa kusa da ita a hankali.

Hannu ya daga yana gyara mata gashinta daya biyo ta cikin dankwalinta me santsi ya kwanta gefan kunnenta,sannan ya sake gyara mata zaman dankwalin.
Gentle habit nasa data lura dashi kenan,yana killace komanta.

“Things that should’ve been done earlier.” idanunsa take kalla,wadannan idanun masu taushi da tsananin haske,amma a yanzun idanun sunyi nauyi,kamar bai yi bacci ba kwata kwata,cakude da wani boyayyen sirri.

“Haisammm…” ta kirashi da sound da yanayin nan da yakeso a muryarta.

“Me ke faruwa?”
Sai ya zuba mata ido na wasu seconds. Wani irin kallo mai zurfi. Kamar yana jin ciwon ganin ta cikin wannan halin yake sake kallonta sosai.

“Trust me a little longer.” bata gane ba....sam bata fahimci me yake nufi ba,wannan amsar tasa,ta qara mata rud'ani.

Ta sani......haisam baya roqon trust,yawanci kawai yake daukar mataki ne. Sai ta zabi ta matso kusa da shi.

“Yana da alaqa da Mammina?” ta tambaya kai tsaye. Ya matse haqoransa guri guda.

“It has to do with ending this." Sai ya kamo hannunta ya sanya cikin nasa. Yanason wannan kyakkyawan lallausan tafin hannun.

“Ki koma ki kwanta" Ya fada yana murza mata bayan hannunta a hankali.

“And no matter what happens tomorrow…”
Chapter 133 · 0% Book details