← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 176

Sashe 110

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani soft smile ne ya bayyana saman labbansa,not mocking.....fond.....very fond.

"My princess....." Ya kirata da wannan sautin dake kasheta.

"“I barely look away from you.”. Idanunta ta lumshe saboda yadda muryarsa tayi taushi da yawa.

Yadda ta lumshe idanun sai ya hade eyelashes dinta na sama dana qasa,saita sake masa wani irin kyau me daukan hankali. Gaza jurewa yayi,yakai hannunsa ya shafi gefan fuskarta.

"There’s nothing outside more interesting than my wife.” ya motsa labbansa a nutse yana hada kalmomin. Ya rasa da wanne sabulu take amfani,baisan da wanne abu take kula da fatarta har haka ba......amma yanasan ran wataran zai gani.....zai kuma tambaya.

Da dukkan wata kalma daga bakinsa sai da zuciyarta ta buga.....wannan karon ba saboda kishi ba.....aah.....saboda shi. Saboda shi dai....wannan malamin.....saboda shi....wannan yariman.....saboda shi....wannan boyayyen identity din da take xuba idanu taga ranar da zai gaya mata komai da bakinsa.

"Kaine mutumin hippodrome?" Tambayar ta subuce mata sanda yake maida cufflinks dinsa.

A bazata maganar tazo masa,amma sai ya daga kansa da murmushi yana dakatawa daga sanya cufflinks din. Da wannan dangerous smile din nasa yake takowa inda take zaune,hannayensa zube a aljihun wandonsa da ya yiwa tucking. Ya lura wannan tambayar na daya daga cikin manyan tambayoyin dake damunta.

Sunkuyawa yayi daidai fuskarta,ya bata lite kiss kaman yadda ya saba,sannan a nutse yace.

"Nayi alqawari.....zan baki amsarki.....not now,idan na dawo". Ta gamsu da maganansa,kuma yadda ya amsa matan sai ya qara zumudinta nason jin amsar tasa.

"Da shehnaz da aisa.....zasu iso dubai yau in sha Allah,nan da hour biyu.......zasuje bikin bude wancan kamfanin dana gaya maka,dukkanmu fan na brand dinne" Tayi maganan qwayar idanunta bata kallon nasa. Murmushin gefen baki yayi,a nutse ya dakata daga takawar da yakeyi.

"Ma sha Allah....dubai na musu barka da zuwa" Yadda yayi maganan kamar dubai mallakinsa ce ta sanya ta daga kanta tana dubansa,sai ya basar yana jawo briefcase dinsa.

"Zanje tarbosu......don Allah.....zasu sauka a five falm Jumeirah". Shuru ya danyi sanda yake bude briefcase din nasa. Ta lumshe idanu tana dan jin fargaba. Idan ya hanata zuwa tarbarsu.....kenan hakan yana nufin yawon da zasu d'an fita susha iska ma bazai bari ba.

"Karsu sauka a Jumeirah......zan saka a bude musu dayan suite din dake cikin residence din nan su sauka a ciki" Jerarrun fararen haqoranta ne suka fito,wadanda suka qara mata wani irin kyau. Tsaiwa yayi cak yana kallonta gami da jin komai yana tsaya masa da murmushinta kawai.

"Na gode.....na gode sosai" Idanunsa ya lumshe yana budewa,sai kawai ya bude mata dukka tafukan hannayensa.

Batayi tunani na biyu ba,ta miqe a hankali,tana takawa kamar me tausayin qasa,yanayin takunta da yake sanyawa wani lokaci yake kishinta idan tana tafiya a waje....saboda yana ganin kamar kowa idanunsa yana kanta.

A nutse ta fada faffadan qirjinsa tana sauke ajiyar zuciya......shi kuma ya maida hannuwansa ya kulleta a ciki yana matseta a tausashe.

Ko sau dubu jikinsu zai hadu.....sau dubu idan zai sake rungumeta yana jin kamar yau ne.....yanzun ne runguma ta farko a rayuwarsa da zaiyi mata.

"......sannan" Ta fada a hankali tana fargabar gaya masa,amma husky voice dinsa data cika mata kunne ta bata qwarin gwiwa.

"Fadi kawai.....aminci ne tsakaninki da mijinki......ba tsoro ba"

"Zamu fita......sunason small outing.....na kwana biyu ko uku" Shuru ya ratsa tsakaninsu,sai bugun zuciyar junansu dake ratsa kunnuwansu. Na wasu mintuna,ya zane jikinsa a hankali,sai itama taja baya tana sauke idanunta a kansa.

"Shikenan.....bazai bari ba,dama aisa ta fada i wasn't like i was before,ina da aure yanzun" Ta fada a hankali idanunta yana son tara hawaye ganin baice komai ba yana komawa cikin daki.

Jikinta a sanyaye ta koma saman sofa tana zama,tuna zurfafa tunaninta.

"Take the security team" Taji soft voice dinsa a gefanta yana furtawa a hankali sanda yake zama a sofa din dake dab da tata yana maida socks din qafarsa.

Idanunta da suka cicciko da qwalla ta daga tana dubansa,sai shima ya nutsa nasa qwayar idanun sosai cikin tata sanda yake maida safar cikin lallausar qafarsa.

"Da gaske?" Ta fada da wani irin ban mamaki. Murmushi ya sakar mata ne laushi wanda ya narka wani abu me sanyi cikin zuciyarta.

"Did you expect me to say no?” ya tambayeta yana dage mata girarsa gaba daya bayan ya kammala maida socks din yana soke yatsunsa duka cikin na juna.

Kunya ta kamata na yadda ta yanke hukunci haka kai tsaye,sai ta danyi qasa da kanta. Ya saki siririn murmushi yana janye idonsa daga kanta. Wallet dinsa dake gefe ya dauko ya bude.

Wani black card ya ciro,da wani car key,sai wani katin na daban ya dorasu saman table din dake tsakaninsu.

"Use this" Ya fadi a taqaice,maganan data sanyata daga kai tana duban inda ya ajiye kayan.

Sanda ta saka hannu ta dauka sai taji komai yana mata sanyi. Keys ne na motoci kusan kala biyar,black card wanda base an gaya mata darajarsa da kuma a hannun waye ake samunsa ba.....sai wannan card din data gaza gane ne meye.

"Haisam" Ta fada a sanyaye.

"Oh my god" Ya furta softly. Baisan meye a muryarta haka ba,da idan ta kirashi komai yake kwancewa daga cikin kansa ba. In zata maimaita sunanshi sau dubu yanaso,bazai gaji daji ba,har baya fatan wataran ta sauya sunansa da wani sunan na daban.

"Wannan fa?" Ta fada tana dan jin nauyin tambayar,amma kallo daya ya masa ya amsa mata kaman bai fahimci nauyin abinda takeji ba.

"It gives you access....." Yadan dakata.

"........to restaurants.....lounges.....shopping floors" Sake tsayawa yayi kadan.

"........dama duk inda kikeson zuwa" Sake bude wallet din nasa yayi,sai ya ciro wani slim metallic card yana sake ajiye mata.

".....And this one is for restricted places.”

"Restricted?" Ta fada can qasan zuciyarta lamarin yana fara girmamar kanta.

"Yeah.....So they stop asking questions the second they see you.” kasa magana tayi,har sanda ya sake takowa gabanta,ya kama hannunta yayi kissing deeply.

" Ki kulamin da kanki.....sannan 2days yayi yawa kina fita.....if possible zan sadaukar musu da kwana biyu.....kwana dayan nawa ne.....zamu huta saboda next day kinaso kije kiga grand opening right?" Kamar wadda kanta ya karye haka ta gyada masa kai a hankali. Ya lumshe idanunsa yana sake budesu dukka a kanta,yanason ta tashi ta rungumeshi so samu,ta bashi deep kiss,amna bayaso ya cika matsa mata,don haka yayi waving mata hannayensa yana fita da baya da baya har ya kammala fita gaba daya.

Da taimakon ambaton Allah yanayinta ya daidaita. Ta zauna kawai tana juya duka cards din daya bata. Batasan wanne kalar tunani zata sakeyi kuma a kansa ba,kawai maganan jiya ne da zuciyarta ta gaya mata. Ta samawa kanta salama,ta kalli komai kawai.....ta jira sanda ya shirya fito mata a mutum.

Aiki suke da agogo ko aiki da lura ko zallar sanin makamar aiki ne bata sani ba. Amma abinda yafi bata mamaki sanda security alert ya gaya mata security team din suna jiranta don rakata airport dauko su shehnaz.

Haka kawai ta samu kanta kalar shigar data lura idanunsa sunfiso,shigar da zata rufe komai nata banda zagayen fuskarta da tafin hannunta.

Yalwatacciyar abayar da asalin matan sarakuna a qasar dubai ke amfani da ita,sakakkiya sosai wadda ba abinda zata nuna nata.

Daga bakin residence dinsu ta fara cin karo da security uku. Abun mamakin dukka mata ne,su suka karbi jakarta suka riqe mata suna gaidata cikin girmamawa,sannan suka shiga private elevator din suna sauka qasa.💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 99*

Mota hudu ne,kowanne akwai security a ciki. Qwaya daya ce kawai maza amma duka sauran mata ne a ciki.

Tafiyar mintuna kadan suka isa dubai International Airport,kuma suka samu tuni jirginsu shehnaz ya sauka,don duk duka batafi jiran minti sha biyar tayi ba taji ana kiran sunanta.

Ko bata waiwaya ba tasan shehnaz ce,wani tattausan murmushi ya subuce mata sanda take juyawa.

Sanda idanunsa suka hadu itama saita gaza jiran qarasowarsu,ta fara takawa don isa garesu,da sauri daya daga cikin security din tayi mata magana

"Easy ma'am.....please allow us to secure the area first". Tsaiwa tayi tana sake tattara nutsuwarta,kaman yadda shehnaz ta dakata cak tana bude idanunta cikin mamaki.

" Ba zaki qarasa gurinta ba sai an tabbatar da ingancinki" Aisa ta radawa shehnaz tana qyalqyalewa shehnaz din da dariya.

Clearing hanyar suke mata da gaske,cikin wani strict professionalism.....kamar tana qarqashin important protection da dukkaninsu idanuwansu suka gani.

"Ku daina kallona haka mana" Akhnan ta fada sanda suke takawa qarqashin kulawar security zuwa inda motocinsu suke suna damqe da hannun juna dukka su ukun

"Wallahi sai yanzu nakejin kamar kina wata different duniya da tamu" Maganan ya saka akhnan sakin dariya kadan,mai hali baya fasa halinsa,ba abinda xai sauya shehnaz dai da gaske.

Ko a cikin motar bakinsu dukka yaqi mutuwa,kada ma shehnaz taji labari. Ba abinda ta rage daga abinda idanunta suke gane mata.

"Wacce empire din ya kaiki ne akhnan?" Shehnaz ta fada tana kama bakinta idanunta cikin na akhnan.

"Shehnaz manaaaa" Ta fadi da irin salon yadda take magana idan shehnaz din ta dameta a baya da dogon surutunta.

Murmushi aisa tayi,sannan tace.

"Na baki shawara?....ki qyaleta kawai,duk abinda yake cikinta saita fada,gwara ki rabu da ita"

Cikin girmamawa da sanin aikinsu daya daga cikin security din data fuskanci itace shugaba take tambayarta,zasu ci gaba da tsaiwa suna jiranta ne?,kamar ance zata sake fita,ta amsa musu kafin ta juya suna shigewa ciki,kunnuwanta suna cika da maganganun shehnaz.

"Tun a elevator.....ba button na floors.....sai access card kawai.....private royal suit guda.....ni da aisa kawai?....biftu....wannan ba hotel bane.....Masarauta ce" Ta qarasa fada tana fadawa saman lallausan gadon dake da girma da fadi bayan da akhnan ta nunawa aisa nata dakin daban. Dauke idonta akhnan tayi daga kan shehnaz tana maidawa kan aisa

"Don Allah har yanxu jamaal baice komai ba?......na gaji da wannan bakin inaso a kullemin shi" Batasan magananta ta bada wata ma'ana ta daban ba,sai da taji sun sake mata shewa su biyun. Hannuwanta ta daga musu.

"Don Allah,kada ku fassarani".

Hutawa sukayi sosai,cikin mintina aka wadatasu da dukkan abinda suke da buqata. Ba shehnaz kawai ba,aisa da kanta daga qarshe kasa shuru tayi itama.

Awa daya kawai dukkaninsu suka shirya suka fito,suka samu security team din suna jiransu kamar yadda suka umarta.
Chapter 110 · 0% Book details