← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 176

Sashe 142

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Momma.....kin dade yau,suna kusa da titinnan fa?". Abun hannunta ta dauka tana sakawa. Abun hannun da kullum zata sakashi yana tuna mata da khadeeja ne da safeena. Ta sare zuwa yanzu da dukkan buri da fatan haduwarsu a gaba....saidai bata sani ba ko sai a rayuwa ta gaba?.

"Bansan me ya sakani wannan nauyin ba falaak......yau fargaba naketa fama da ita."

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 128*
__________________________
https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee*
___________________________

"Hmmm.....kin saka zancan ahmad dai a ranki....kin nunawa sultane kaman yadda yace kinfison d'anki a kanshi" Ta fada tana dariya. Dariyar itama momma tayi tana takawa zuwa hanyar waje falaak ta bita.

Bawai bataso ahmad yaci gaba da sarautar agadez bane kaman yadda sultane suka yanke da haisam......aah gani take kaman yayi quruciya da yawa.....a qalla a barshi ya cika shekara ko talatinne zuwa da biyar. Amma a qarshe ita kanta taga ba wani zabin sama da wannan,don haka sai kawai ta bisu da addu'a.

Daidai sanda take fitowa akhnan ta shigo cikin rakiyar hadimanta. Tayi kyau cikin wani tsadajjiyar atamfa exclusive wine colour da ratsin peach me haske. Wadda wuyanta da hannuwanta duka aka yiwa wani sirfani. Dan siriri ne na alfarma daga mafi tsadar zare. Tea boubou ce data zama kaman oversized a jikinta. Amma ko daga iya yadda dankwalin ya zauna mata a kanta.....sai tayi wani sirrintaccen kyau me jan hankali.

A saman kanta kuma saman daurin kanta na ture kaga tsiya ta dora mayafinta,saita fita a matar aure da wani irin aura me jan hankali.

Kaman yadda ta saba yanzu.....kanta tsaye ta isa jikin morsa safiyya ta rungumeta......itama saita rungumeta sosai tana jin wani farinciki yana mamayarta,kafin kuma ta zame a hankali tana gaidata,ta amsa mata tana riqo hannayenta,sannan ta riqeta suka fara takawa waje,daidai sanda hayaniya kadan ta qaru cikin gidan da motsin manyan qofofin gidan guards da securities.

Sanda motocin suka tsaya cak a muhallin tsaiwar motoci na gidan....gurin ya cika da securities da guards na Ethiopia dana agadez gaba daya.....siririyar busar sarauta na tashi cikin wani yanayi da ba hayaniya a ciki....haka kawai sai morsa safiyya ta samu kanta da qarin faduwar gaba.

Idanunta akan motocin sanda mutanen ciki suka fara fitowa,taga haisam ya fito,ya kuma zagaya side din motar daya fita a ciki zai bude,tabbacin mmamarsa ce a gurin,daidai sanda armelle ta qaraso tana mata magana akan kammala shirya dakin cin abincin,sai ta dauke idanunta tana maidawa ga armelle.

"Sannunku da qoqari.....hakan yayi,kowa yana iya tafiya tunda an kammala k....." Ta qarasa maganan tana maida idanunta inda haisam ya fita dazu. Saidai kuma ta gaza qarasawa,saboda abinda idanunta ke gane mata.

Wata razanniyar almara da Zuciyarta ba zata taba yarda da ita ba,don ta tabbatar idanunta ne suka yaudareta. Wata almara da taso tafi komai daga mata Hankali.

Khadeejanta take gani,tana magana da wannan nutsuwar tata tunta quruciya,da wasu shekaru na girma,idanunta akan haisam..

Idanu ta zuba sosai,saidai fa suna sake matsowa tana sake ganin khadeeja dinta muraran a gabanta.

"Itace.....Allah ita ce" Ta fada a fili ba tare data sani ba.....dukka ilahirin jikinta yana rawa,abinda ya sanya akhnan kama hannunta a nutse tana son bata nutsuwa,daidai sanda nanay ke janye idanunta daga haisam,wanda da alama wani bayani yake mata suka sauka akan morsa safiyya.

Cak ta tsaya tana kallonta. Ta sani yaronta baya qarya....haisam a tsahon shekarun data rauneshi,tun daga quruciya zuwa girma ba zatace ga sanda ta kamashi da laifin qarya ba,amma kuma sai yanzu take sake tabbatar da maganarsa a zahiri.

"Sadiyeee" Nanay ta faurta da murya me rawa.

"Itace.....ta kirani da sunan da iya su biyu kadai suke kirana dashi" Ta fada a fili. Idanun morsa safiyya ne ya cika da hawaye,ta soma takawa da sassarfa tana fadin.

"…Khadduu?” sunan saka nanay itama kasa jiran qarasowar morsa safiyya,saita soma takawa da nata hanzarin don ta cimmata.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

A tsakiya suka hade ita da ita,suka yiwa junansu wata wawar runguma da saur kadan su zube qasa,saida hadimai suka lullubesu daga idanun mutane akhnan da falaak harma da haisam suka tsaya a gefansu.

"Khadduu.....khadduu" Shine kawai abinda morsa safiyya ke maimaitawa tana jin kamar cikin mafarkanta take.

"Sadiyeeee.....'yar uwata" Nanay ta furta da qyar saboda kalan kukan dake neman shaqeta. Sake rungume juna sukayi sosai,kamar masu tsoron idan suka saki juna d'aya zai bace ya sake barin dan uwansa. Suka raunana zuciyar kowa dake gurin,musamman sultane dake gefe tsaye shida motii da motarsu sai yanzu ta ida qarasowa. Falaak ta fara qwalla,saiga akhnan tana hawaye har suna fita a idanunta. Tana hango wannan tatacciyar soyayyar ta 'yan uwantaka har ina?. Inda ace mamminta tana nan yaya zai wannann kyakkyawar haduwar zata kasance?.

Idanunta suka fada kan haisam,sai a sannan ta lura bai damu da kowa ba....ba wanda yake kalla a gurin sai ita,ita kadaice idanunsa suke kansa.

Ido daya ya kanne mata yana hade yatsunsa biyu,ya mata maga da ido da yatsun ba tare da yace komai ba.

"Kinyi kyau sosai.....karki kuka....zaki bata wannan fuskar".

" Wannan mutumin" Ta fada cikin ranta tana gayyato jarumta. Batasan a wanne layi zata sakashi ba....a komai ya qware,komai kuma ya iya,ya isar mata da saqon soyayya cikin salo,ba tare da kowa dake zagaye dasu ya fahimta ba.

Saida sultane da motii sukayi magana aka samu daidaituwar yanayin,suka fara takawa ciki hannuwansu cikin na juna,idanunsu cike da mamaki da qaunar junansu.

"Kin tsufa.....girma yazo"nanay tace da morsa safiyya cikin murmushin da zai gaya maka akwai abinda ta tuna zamanin suna tare ta fadi haka.

"Ke kuma har yanxu kina kuka idan kika tsorata" Dukkansu suka yi dariya cikin hawaye.

Kasa jurewa morsa safiyya tayi,ta waiwaya tana duban haisam.

"Kai ka dawomin da ita?ya akayi baka manta labarin khadduu dina ba saida ka dawomin da ita?" Tace da haisam dake musu gadi daga bayansu. Dariya kadan nanay ta sake cikin nishadi,duk da hawaye ne fal idanunta.

"Danki ne fa......dankine da baki sani ba" Cak morsa safiyya ta dakata da tafiyar,ta juya gaba daya tana kallon haisam

"La'ilaha illalllahu......muhammad?" Kasa qarasa magana tayi,har saida muryar sultane ta bayyana.

"Idan safiyya ta gagara ci gaba da tafiya....to a nemo abun daukarta mana" Maganan ya bawa kusan kowa dariya a gurin. Anaani rumaisa noorah da khansaa gaba dayansu suna jinsu cikin wata sabuwar duniya,gasu a baquwar qasar da basu taba zuwanta ba.

Wani irin zama ne akayishi cikin qawataccen parlor din na alfarma. Parlor ne da kusan sai manya manyan baqin sultane ko baqin da suka shafi cikin gidan ake saukarsu a ciki.

Zama ne me tsayawa a zukata.....cike da farinciki da walwala. Dariya da murmushi na gasken gaske ba fake ba,wani irin nutsuwa me cike da sukuni da kuma walwala. Karbar baqin zuwa yanzu ya wuce hawaye da runguma kawai......ya kuma wuce zaman tattauna abubuwan da suka faru da sake bude tarihi tsakanin nanay da morsa safiyya,ya zarce ga zaman cin abinci na bai d'aya.

Ba zancan surukuta a gurin nauyi ko jin kunya,motii nanay morsa safiyya da sultane sunaji a jikinsu dukkaninsu nasu ne.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 129*

Saidai duk a wannan zaman....a wannan yanayin idanun akhnan lokaci lokaci yana fadawa kan dan matashin saurayin da batasan waye ba,wanda a qalla zaiyi sa'an hairaan ya girme mata sosai ko ba'a fada ba.....amma tana ganin kamannin mamminta a tattare dashi..

"Da jinjirin safeena daya bata fa" Maganan da yaja hankalin morsa safiyya,hannuwanta na rawa take riqe da Muhammad. Zaman cin abincin da bai yuwu ba,sai koke koke ya koma sabo.

Akhnan jin Zuciyarta takeyi tana sake nisa da tsanar mammina sanda motii ya gama cikakken bayani shima muhammad ya dora da nasa,kafin motii ya sake karba.
Chapter 142 · 0% Book details