Sashe 77
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yadda ta soma tura qofar cikin nutsuwa haka yake daga kanshi cikin nutsuwa yana sauke nakakkun idanunsa dinnan a kanta gaba dayanta.
Zaune yake kan wata irin sofa da zata bashi daman hutawa dama miqewa qafafuwansa sosai. Yana jingine da wani tattausan massage pillow a gadon bayansa yana amsa wayar da tsabar nutsuwa irin tasa bakajin abinda yake fadi,sai wadannan labban nasa masu sulbi dake motsawa a nutse.
A hankali ya soma tafiyar da idanunsa yana sauke mata wani irin kallo,tun daga saman kanta da mayafin data yafa ya zame zuwa rabin kanta saboda haduwa da yayi da sassalkan gashin kanta,har zuwa zara zaran yatsun qafarta da suke nutse cikin tattausan carpet din dake malale a parlor din.
Wannan kallon yaji bai masa ba......sam bai masa ba,bai isheshi ba bai gamsu ba,sai ya sake maida idanun nasa daga qafarsa yana aikensu zuwa ga jikinta a karo na biyu. Tsaiwa ta farko ya dakata daidai qugunta dake juyawa a hankali sakamakon takowa da takeyi zuwa ciki,sannan qwayar idanun nasa suka sake tsaida birki akan cikakkun qirjinta da suka cika rigar jikinta.
"Hutun sati biyu suka bayar.....sunce kayi haquri ka karba a haka,akwai sauran qananun case......" Maganan da omar yake fadi masa kenan ta cikin wayar da yaji ta fara nisa da kunnuwansa ainun,saboda zare wayar da yayi daga kunnen nasa ya ajiyeta kawai a gefansa ba tare daya damu da kasheta ba.
"Subhanallazi khaaliqunaa" Ya fada can qasan maqoshinsa adam apples dinsa yana kai kawo tsakanin maqogoransa daga farko zuwa qarshe.
A hankali taji kaman qafafunta suna lanqwashewa......wannan nauyin dake cike da narkakkun qwayar idanunsa yana sauka a kowacce gaba ta jikinta. Wani irin kallo da ta jishi a yau har cikin jininta.....wani irin kallo da takejin kamar sai ya huda fatarta sannna ya huda tsokarta,ya kuma huda qashinta sannan yakai ga bargonta bayan ya tsinke kowacce jijiya ta jikinta. Wani zuzzurfan kallo da bai taba yi mata irinsa ba.....wani irin kallo da a yau karon farko ta jishi sama da kowanne kallo daya taba yi mata a rayuwarsa.
Sallama takeso tayi masa amma ta kasa......duk yadda taso motsa labbanta tayi sallamar amma abun ya gagareta,saidai ga tarin mamakinta sai taga ya motsa labbansa yana lumshe wadannan narkakkun idanun nasa yana furta.
"Wa'alaikumussalam warahmatullah" Abinda yadan qara mata rudani akan wanda take ciki. Itace ta samu nasarar yin sallamar ba tare data lura ba?,ko kuma shine kunnuwansa sukaji masa haka?.
Ta qarfafi kanta da dukkan iyawarta,ta samu takai kanta saman daya daga cikin sofas din dake daura da tasa ta zauna. Qasa tayi da kanta kada,har yanzu tana jin nauyin idanunsa dake kowanne sashe na jikinta.
"Sannu......ya jikin?" Ta fada da hausa saboda bataso ya amsa mata da French ya qarasa kassara mata zuciya a daidai wannan yanayin da take qoqarin daidaita kanta da qoqarinta.
"Alhamdulillah" Ya fada kaman wanda yake tsoron kada aji sautinsa,yana maida jikinsa ya jinginar ga massage pillow din still idanunsa a kanta,baiyi kuskuren janyewa ko sau daya ba.
"Akwai magunguna inji nanay a cikin gurincan......amma kafin sannan me zakasha?.....coffee ko black tea?" Ta fadi tana daga blue eyes dinta da wani irin sanyi tana zubesu a fuskarsa.
Ji yayi a sannan kamar yana nutsewa cikin ruwan qanqara......wani irin abu me sanyi yana ratsashi daga cikin idanunta kai tsaye zuwa cikin nasa idanun dama gangar jikinsa gaba daya.
"What a beautiful eyes" Ya furta can qasan maqoshinsa,labbansa kadai suna motsawa a hankali ba tare da sautin ya fita ba.
Duk wata laka ta jikinsa ta gama zare masa ita,bayajin bakinsa zai iya cewa komai da ita,sai kawai ya daga mata kai a hankali.
Wannan kallon nasa kasheta kawai yakeyi......wadannan idanun nasa,har yanzu bata tsinci wani abu dake kassarata ba.....wani abu dake mata illa kaf rayuwarta ba irin yadda idanunshi yake da tasiri a kanta ba.
Ta motsa tana miqewa a hankali,still ya sakejin bazai iya raba idanunshi da kallonta ba. Binta yayi da kallo da dukka idanuwanshi......irin kallon nan nakai tsaye yana kallon yadda take dagawa da sauke Qafafunta a hankali,yana kallon yadda qugunta ke juyawa kamar da gayya takeyin hakan dashi.....yana kallon yadda iska ke kada mayafinta hade da gashinta daya fito ta qasan mayafin.
Har ga Allah kallon ya mata nauyi.....har ga Allah takejin yadda idanunsa ke keta kowanne tsaro na jikinta,da wannan qarfin halin da wannan qarfin gwiwar tabi direction din dake nuna mata inda kitchen din gidan yake takai kanta kitchen din da qyar.
Daidai lokacin da take cikin kitchen din,take binsa da kallo kusurwa kusurwa. Karo na farko a rayuwarta data samu daman taka cikin kitchen din,bama kitchen din ba,karon farko data kusanci cikin aninihin ginin nasa kenan. Tana ji a ranta zata riqe amanar haisam kamar yadda nanay ta buqata.....zata riqe amana kamar yadda tace a gabanta.....amma hakan ba yana nufin zata kasa ko zataqiyin yaqin da zata samu nata gurbin da muhallin a zuciyarsa ba. Hakan kuma ba yana nufin zata kasa yaqarta ta hanyoyin da tasan zata tsira da nata kusancin da soyayyar ba.
Tsaiwa tayi a hankali tana jingina da qofar kitchen din,tana jin adadin bugun zuciyarta,saita maida idanunta ta lumshe tana qoqarin saita bugun zuciyartata.
A baya ta dauka ita din jaruma ce,a baya idan akace mata iri ko shigen haka zai faru da ita game da wani d'a namiji.....ya sakata fargaba.....ya ninka bugun zuciyarta to zata qaryata hakan......amma cikin lokaci qanqani ya zama namiji na farko daya fara birkita lissafin qwaqwalwarta dana rayuwarta gaba daya.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Me yake kallo?.....me yake kallo haka tattare dani?" Ta yiwa kanta da kanta tambayar murmushi yana qwace mata tana kuma bude idanunta a hankali.
Cikin idanun samee nata idanun suka sauka,saamee din da tayi tsaye tana qarewa akhnan din kallo wani kibiyar kishi yana hudata
"Haka take da kyau?,haka take dama?" Ta maimaitawa kanta tambayar har taji kaman zata zauce cikin qasa da minti uku. Wannan shine karo na farko data ganta kusa da kusa haka,ba shigar nan me nauyi me ado da take tunanin ita ke qara kwarzantata da qara mata kyau,ashe shigar ba abinda take mata sai sake boye kyanta.
Haka kawai taji yarinyar batayi mata ba. Halittarta ce bata qaunar SHISHSHIGI sam,idan zata soka zata soka kawai.....idan baka mata ba baka mata ba. Batason a dinga shiga al'amuranta tun asalinta,wannan ya sanya tashin farko aka samu wani irin clashing me girman gaske tsakaninta da saamee.
"Barka da warhaka" Saamee din ta fadi,saidai tana cire kusan fiye da rabin irin girman daya kamata a al'adance ta bata cikin gaisuwar.
Minti kusan guda cikakke,minti gudan da saamee ta cire tsammani ta fidda rai akhnan din zata amsa mata,bayan minti gudan sannan muryarta ta motsa da
"Barka" Ta fadi tana takawa da wannan tafiyartata da saamee ta tsana. Wannan tafiyar da take sawa saamee din taji ita qasqantacciya ce.....wannan tafiyar da saamee ke jinta kamar cikin tsakiyar ranta.
"Me kike da buqata?" Ta furta tana d'an duban akhnan din da taga tana wucewa kai tsaye zuwa kitchen island din dake tsaftace ba komai a samanshi.
Bata amsawa saamee din ba,don hankalinta ma bawai yana kanta bane kwata kwata. Tunaninta da hankalinta yanzun ya tafi ne akan recipe na black tea da nanay ta aika mata cikin menu dinnan. Kayan hadin da komai daya kamata ta saka. Zata iya?,zai shawu?,a karon farko ita akhnan zata dafa wani abu a duniya?.
Yadda bata amsa mata ba,haka saamee bata sake cewa komai ba,bata kuma fita daga kitchen din ba. Taja baya ta tsaya tana qarewa akhnan kallo qasa qasa.
Yau wataqila ta zama ranar farinciki ta farko a gurinta. Ranar da akhnan din zata gaza dafa abinda ya shigo da ita kitchen din,wanda koma meye ta tabbatar haisam dinne zaiyi amfani dashi. Ta fahimci hakanne saboda kusan salo da pattern don nanay kenan. Sarrafa komai da motii zaici ko yasha da hannunta muddin tana da lafiya.
Ta sani.....ba abu bane boyayye,akhnan din ta fito daga gidan sarautar da ita daya ce suka mallaka......ta kasance SHALELE ba'a masarauta kadai ba......har a dukka qasar agadez gaba daya. Tana qarqashin kulawa da tarin hadimai....to mene zata iya?,me zata iyayi saidai komai ayi mata.
Daga wucewarta yaji parlor din ya masa shuru.....daga wucewarta sai yaji kamar ta wuce da komai....komai kamar ya tsaya kaman yadda wayarsa da omar ta katse ba tare daya sani ba.
Baiyi wani tunani na biyu ba kawai ya miqe a hankali,ya zura tattausan slipper din daya dace da yanayin shigarsa ya soma takawa a hankali kanshi tsaye yana nufar kitchen din.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 70*
Ta gama duba duka kayan hadin,ta kumayi qoqari sosai wajen fidda komai ta ajjiye saman mulmulallen bar counter dake kitchen din,wadda aka zagayeta da wasu irin kyawawan kujeru masu tsaho.
Sake komawa tayi tana duba bangaren electric din dake ajiye guri guri cikin tsari a kitchen din,duk wani nau'ikan kayan wuta kala kala,a nutse ta zabi coffee maker dan madaidaici daya,ta dawo dashi saman bar counter din ta ajiye.
Kayan hadin tea din take dubawa da daya da daya tana zubawa,kai zakace batasan da tsaiwar saamee cikin kitchen din ba. Koda motsinta bazai nuna maka tasan da tsaiwarta ba ballantana aikinta.
A nutse ya tura qofar kitchen din da sallama a bakinsa cikin sautin nan nasa. Husky voice dinsa me wani irin zurfi da sautin amo me tsayawa a rai da zuciya.
Idanunshi a kanta yana mata wani duba me dauke da mamaki,ta masa wani irin kyau da tsaiwarta a kitchen din,sai ya ganta wata mace ta daban.