← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 176

Sashe 41

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Salman alfarisy......wani babban sahabin annabi ne S A W,asalinsa mutumin farisa ne wato iran a yanzu,Ya yi tafiya mai tsawo yana neman gaskiya (addinin musulunci)
Ya yi bincike daga addinai daban-daban har ya kai ga Musulunci. Gonar dabino ta salman alfaris,wani tarihi ya nuna annabi ya shuka dabino 300 ne a gurin dukka saboda sakawa salman alfarisi fansar kansa da ubangidansa yayi,akan saiya shuka dabino 300 kowanne ya fito ya bada 'ya'ya anci,yayi hakanne don baiyi niyyar 'yantashi ba,saboda kowanne dabino a qa'ida yana daukan shekara bakwai ko takwas kafin ya bada 'ya'yan da za'aci zuwa goma. Da yakaiwa annabi S AW kukansa,suka hadu shi da sahabbai kowanne da irin dabino,annabi S A W ya dinga karba yana dasawa,sai daya dasa 300 cif,suka kama cikin qaramin lokaci suka kuma bada 'ya'ya kaman yadda ubangidan ya buqata.....da haka salman alfaris ya samu 'yancinsa cikin gajeran lokaci. Amma wasu bangare na tarihi sunce ba haka bane.....amma koma dai yaya ne.....dabino abune me daraja a gurin annabi S A W,zamu so dabino,zamuci gaba da ci,muna fatan samun ladan koyi da sunnah na fiyayyen halitta S A W" Suka qarasa masa salati tare.

Kai take juyawa a hankali,tana jin dadin tarihin sosai. Wata dabi'a data fara shigarta,har ta siya litattafai da dama na tarihin sahabbai tsakanin makka da madeena,tana son kuma ta samu dama ta karancesu gaba daya da kanta.

A hankali yaci gaba da bata tarihin salman alfarisy,jarumtarsa....hikimarsa gwagwarmayarsa da yaqunan da akayi dashi.

Shuru kawai tayi,kanta saman cinyarta,wani irin shuru me cike da nutsuwa,muryarsa kawai take tashi da wani irin laushi da sanyi.

Yana fadin komai da cikakken details.....kwanan wata da shekarar da komai ya faru. Sunayen sahabban da suke gurin da sauran abubuwan da suka wakana bayan da kafin sannan tamkar yana gurin a lokacin.

Sanda ya fara lissafa mata falalar da madeena ke dashi sai da taji tsigar jikinta tana tashi. Da gaske sunan umara da hajj kuwa take zuwa.....da gaske batasan komai akan guraren ba. Zuciyarta tayi wani irin laushi,hawaye sosai suka cika mata idanunta,qaunar gurin tana sake kamata da gaske,inama tun zuwan da take tasan duk da wadannan falalar da sauran gurare masu daraja haka.

(Ya Allah,dukkan musulmin dake da burin zuwa gurin nan don isar wanda ke kwance a gurin muhammad S A W Allah ya qaddara zuwansa......masu niyya da son komawa Allah ya cika mana burikanmu gaba daya,Allah kasa miyita zuwa,ka qaddara shahadarmu acan son hasken fuskar masoyinka muhammad S A W🙏🏽🙏🏽).

Batasan sun isa gurin ba,sai da taji motar na magana da yanayin isowarsu gurin,ya kashe motar a hankali,ya waiwaya yana dubanta. Zare seatbelt dinsa yayi,ya ya bude motar ya sauka ya zagaya ya bude mata.

Ta jima fuskarta a kife tana qoqarin daidaita hawayenta,yana tsaye harde da hannuwansa kawai yana kallonta,baice mata komai ba har sai data debi adadin mintunan da sukayi mata sannan ta gyara hijab dinta,ta daga kanta idanunsu suka hadu guri daya,saita dauke dubanta a kanshi da sauri.

Wani kyau blue eyes dinta yayi masa,wani kyau daya sanya tsigar jikinsa wani irin zubawa harsai daya dunqule hannunsa,yadan cije lips dinsa na qasa kadan,yayi taku biyu baya yana bata daman fitowa.

Tun daga farkon gurin tasan gurine bana wasa ba,gurine cike da wata ni'ima da qananun qoramu,wanda iyasu kadai sun isa sanyaya ran mutum.

A hankali zuciyarta ta dinga haske tana washewa,ta dinga taka gurin tana ganun nau'in dabinai kala daban daban,wanda tunda take bata taba ganin kalar wani ba. Kowanne kuma da sunansa da launinsa. Dandano ne ta kasa sawa a bakinta,sai taji kaman zai kalleta,zai kalle mata baki yaga yadda take tauna.

Tsaiwa kawai tayi tana kallon yadda ake loda dabino cikin boot na motar,idanunta sunyi laushi kaman yadda takejin jikinta gaba daya yayi laushi. Kanta ke mata ciwo tana jin kuma yadda zazzabin jikinta yake sake daduwa,amma kuma ba zata iya gaya masa ba.

A hankali ta sake curewa guri daya tana jin sanyin Ac din motar kamar yana son mata yawa,duk da tasani bai saka sanyin da zai dameta har haka ba.

Idanunsa akan kyawawan titunan madeena,amma haka kawai hankalinsa yake jin yana kanta. Shurun yayi yawa,ba irin shirun dazu bane wannan. Ya juya a hankali ya zuba mata idanunsa kadan sannan ya janyesu,hannunsa ya miqa kan Ac din motar ya kasheta gaba daya. Zaman da tayi yafi masa kama dana wanda yakejin sanyi.

"Kina lafiya?" Ya fada sanda ta taka a hankali zata shige dakinta. Kadan ta waiwaya ta kalleshi,sai ta daga masa kai a nutse ta tura qofar tana wucewa. Minti kusan daya yana tsaye kafin ya janye idanunsa yana duba lokaci. Already sunyi sallar isha'i a can,yau kam jikinsa hutu yake buqata,don ya samu energy na shiga Ethiopia jibi.

Ya sake ninkawa kansa nisantar masaukinsu ne saboda ita. Tun daga wancan ranar da abun ya faru.....tun daga wancan lokacin sai abun ya zame masa kamar wani jarrabi. Zai wahala ya kwnata barci bai ganshi cikin wani irin yanayi ba ita dashi. Zai wahala yayi bacci biyar guda hudu bai farka cikin buqatar wankan tsarki ba. Ya tabbatar ci gaba da mu'amalarsa kusa da ita sosai.....zuciya ce bata da qashi,komai zai iya wakana,amma a yau yadda ya gaji sosai,yana saka rai zai kwanta ne yayi bacci me dadi da bazata zame masa barazana cikin mafarkinsa ba.

_hmmmm.....anya kuwa?,yau daikam Allah yasa a tsaya iya mafarkin ma_

Ruwa me dumi sosai ya cika bathtub dashi,ya zare kayansa cikin kasala da gajiya ya shige ciki yayi luf abinsa yana jin yadda dumin ruwan ke ratsa qasusuwansa. Kusan mintuna talatin da biyar ya bata sannan ya wanke jikinsa ya fito. Sosai sumar kansa ya kwanta saboda ruwan data nada,hakanan duk wata gargasa dake a jikinsa qirjinsa da hannuwansa,ya daura towel sannan ya dauki qaramin yana rage damshin dake saman kansa.

Kaman jira ake ya fito kira ya shigo wayarsa,koda ya duba sai yaga omar ne.

"Ya salam" Ya fada yana murmushi,omar ne ya sani,bazai kirashi haka siddan ba sai ya matsanta masa,tabbas sai ya takura masa hankalisa zai kwanta. Baya raba dayan biyun kuma sai da suka gama magana da maleek sannan ya kirashi.

"Ya akayi?" Yace da omar yana daga wayar. Wata dariya omar ya saki. Baqon abune a gurin haisam din ya daga wayarka bai fara maka da sallama ba.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Captain.....kome zaka fada ka fada........amma tsokana dole ne".

" Halan kana da isashen lokaci ne ko?"

"Ko babu zan qirqirar maka".

"Alright.....bismillah" Ya fadi yana jan stool ya zauna kawai akai. Ya sani,kafin omar din ya gama iskancin tsokanarsa har jikinsa ma qila ya bushe,don haka bai damu da neman handrayer da zai busar da sumarsa ba,sai kawai yaja body cream da perfume lotion da suke sake sanya gargasarsa ajiye wani irin fitinannen qamshi ya soma shafawa yana jin omar yana duk kalar shaqiyancin da yaga dama.

Da qyar ta zare kayan jikinta ta maida gurbinsu da wata tattausar sleeping dress data tsaya iya gwiwa data zo ta tarar birra ta aje mata. Tun da yamman ta sallami birra din bayan birra ta gama komai da tasan zata iya nema a daren,don daman tasan zasu iya kaiwa dare.

Saman lallausan gadon da nannade wanda yasha shimfidar offwhite din comforter bedsheet da duvet dukka kala daya.

Sannu a hankali zazzabin dake jikinta ya fara yawa,ta soma jin zafin ita kanta a karan kanta wanda yake tafe da wani irin ciwon kai. A hankali takejin zafin zazzabin har cikin idanunta da labbanta,ta sake curewa guri guda tana fesar da iska me zafi daga bakinta.

"Bappi" Ta fadi a hankali lokacin da ta soma jin jikinta dukka yana mata nauyi,ta lumshe idanunta tana jin wani irin kadaici yana saukar mata.

A hankali ta soma jin yanayin nata yana sauyawa,daga zafin zazzabi zuwa wani irin sanyi me ratsa qasusuwa,sanyin da takejin kamar ba cikin comforter take ba,kamar wadda ke kwance a sararin da babu komai face rigar jikinta zallah

"Bappi" Ta sake fadi a hankali idanunta suna tara ruwan hawaye. Sosai ta qanqame pillow din tana cusa kanta a tsakiyarsu. Kewar sultane take.....amma sai takejin akwai wani abu daban data rasa.....akwai wani gurbi daban daba na sultane ba.....akwai wani abu daban da take kewa sama da kewar sultane.

Idanunta ta lumshe,hoton fuskarsa ya gilma mata,kafin ta iyayin komai kuma sai wata irin mahaukaciyar kewarsa ta lullube ruhi da zuciyarta gaba daya ba tare data bar mata gurbi komai qanqantarsa ba.

"Aah" Ta fada tana girgiza kanta duk da nauyin da yayi mata. Batason ta yarda ko ta aminta da abinda zuciyarta keson gaya mata. Ba haka bane.....tanajin wani kusanci ne kawai ya jawo haka wanda zayazo ya wuce.

Hankali kwance omar ke bashi dukka bayanai akan kamun mammina. Yayi relaxing sosai yana saurarensa,bayan ya gama ji din kuma ya gyara zamanshi da kyau.

"Sati daya.....sati daya nakeso su riqeta a gurinsu.....kafin satin na kammala da issue din company din,inaso komai ya gama fits lokaci daya".

"An gama......amma kamar a wayar uwargida za'a samu phone number nata?,ina buqata zan qarasa wancan binciken daka bani" Kai ya jinjina a hankali.

"Alright.....ka riqe wayar ina zuwa" A nutse ya miqe yana zare towel din jikinsa bayan ya saka boxers da moroccon jubah fara tas,jikinsa na fidda qamshin cream perfume dinsa me wani irin qamshi laushi da kwantar da zuciya ya soma takawa zuwa qofar fita ba tare daya saks bedroom slippers dinsa ba.

Numfashi ta sake ja sosai tana jin kamar yana neman yayi mata kadan,tana kuma sake cusa kanta cikin pillows din,abinda yake qara mata qarancin iskar da take shaqa.
Chapter 41 · 0% Book details