← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 176

Sashe 64

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya lumshe idonsa yana tuna yanayin data sanyashi,ya sake murmusawa a hankali kaman wanda ya samu tabin qwaqwalwa. Tunda yazo duniya bai tana jin yanayi irin wannan ba,ko shi yasa maleek yace sun dade a matsayin buhunhuna kuma bahuna?,akwai abinda maleek yaji kenan sama da abinda yaji a nasa jikin?. Iya tambayar kawai ta saukar masa da wani tashin tsigar jiki,kwanyarsa da zuciyarsa suka fara masa hasashen can inda maleek yaje,sai yaji kawai ya kasa zama shi kadai,ya jawo pillow din dake cikin motar ya sakashi a qirjinsa yana jin yadda mararsa take qullewa sosai.

Bai iya sake bude idanunsa ba sai sanda motocinsa suka sauka cikin masarautar aba jifar. Kowa ya tsaya suna jiran motar da yake ciki ta bude kanta da kanta. A nutse ya ajiye pillow din,ya zura qafafunsa qasa a hankali,kyakkyawan takalminsa qirar qasar italy ya fara fitowa,sannan gangar jikinsa yana sabe da 'yar saman suit dinsa.

Jikinsa a mace yake gaba daya,yayi wani laushi sosai,amma hakan bai boye kwarjininsa ba ko kadan.

Kaman kullum,duk inda ya taka hadimai ne da bayi suke zubewa suna gaidashi da girmamawa. Sashen nanay ya nufa,don qa'idarsa ne kome dare idan ya fita ya dawo sai yaje ya ganta,ballantana yanzun daya dauki kwanaki biyar ba tare daya sanyata a idanunsa ba.

Ciki lafiyayyen parlor din dake da girma da yalwa,cikin wani yanayi na kayan qawa da suke nuna zallar isa qasaita da qarfin ikon da masarautar oromo ke dashi.

Iyalin khadeeja yunnus jallata ne zaune a ciki,cikin wani yanayi na walwala qauna da fahimtar juna. Balqees,khansaaa,rumaisa,Aaanani,sai auta noorah wadda ke zaune gefe daban da camera dinta a hannu da alama wasu hotuna take dubawa.

Kaya ne fal a gabansu suna shiryasu cikin wasu irin abubuwa masu kama da akwati,suna yi suna hira cikin harshe da yaren oromo. Sallamarsa ta sanyasu tsagaita hirar tasu,cikin girmamawa da qaunar juna a tsakaninsu ya qara so suna masa sannu da zuwa.

A girmame ya gaida balqees da hasnaaa,sannan sauran suka gaidashi,noorah na maqale da hannunsa tana qoqarin nuna masa hotunan data dauka.

Hannu yasa da murmushi ya karbi camera din yana kallon hotunan,hotunane na wasu kyawawan tsuntsaye da shi kansa sai daya tsaya yana kallonsu. Hannu yasa yayi zooming hoton da kyau,harda aku.....dawisun da yasan bata dashi a baya cikin tsuntsayenta,ga wasu tattabaru da suka burgeshi sosai.

"Yaushe akayi wannan auta?" Ya tambayeta da murmushi kan fuskarsa yana waiwayawa gefansa inda take tsaye.

Murmushi itama ta saki daya qara bayyanar da kyan yarinyar,taji dadi sosai yadda obbo dinta idanunsa suka nuna burgewar da kayan sukayi masa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 58*

"Wancan satin da baka nan obbo"

"Ma sha Allah,Allahumma bareek,daga ina kika siyosu?"

"Nigeria" Ta fada qasa qasa,yadda tayi maganan kuma ya bawa kowa dariya a parlor din. Ya fidda manyan idanunsa waje.

"Nigeria kuma?" Kai ta jinjina tana dariya.

"Eh obbo,a HALY JASHERU VENTURES(07046665338)obbo......harda kaji tana siyarwa fa,masu kyau sosai obbo,zaka iyayin ado dasu......" Kai yake jinjinawa,yana mamakin qaunarta da tsuntsaye sosai,gari ya gari har Nigeria?.

"Taya kuka hadu noorah?" Balqees dake zaune riqe da habarta ta fada tana duban noorah din da mamaki.

Siririyar dariyar data bayyana quruciyarta tayi tana sake riqe hannun haisam.

"Tana zuwa nan qasar sarin pure mayukan zaitun,hulba,habbatussauda da man kwakwa dama sauran ire irensu". Kai ya jinjina sosai yana murmushi. Mutum ne shi da yakeso yaga dan adam me dogaro da kansa,zuciyarsa bata mutu ba sam,kuma duk cikin 'yan uwansa,tarin dukiya da mulki da suke ciki ba wanda baya juya business dinsa hatta da Aareef da yake bin noorah

"Ma sha Allah.....zan qara jari da alama a siya tattabaru,nima a kawomin dawisu da aku guda daya" Wani tsalle tayi tana d'aneshi,farinciki yana cikata,

"Na gode obbo na gode" Ta fada da harshen oromo farinciki yana cikata.

Tabe baki Aanani tayi,itakam haushi takeji idan noorah ta zauna tana bayanin riba da ake samu akan tsuntsayen.

"Kome yake cikin siyan wadannan dabbobin oho". Da sauri hasnaa ta juyo yana duban Aanani.

"Sirri ne....noorah ta fiku wayo,bansan ya akayi tasan abinda ake samu cikin kasuwancinsu ba.....riba ce ba qarama ba,ina kyautata zaton nan gaba kadan cikin mata na gidannan itace me arziqinmu" Maganan kusan ya saka kowa dariya,duk da suna lura da kusan hakanne abinda hasnaaa ta fada.

Tsautsayi shine abinda ya fito da ita daga daki. Zaman dakin a kwanakin ya fiye mata komai,ya fiye mata fitowa ta zauna a cikinsu,daga sanda ta fahimci tarin walwalar da suke ciki saboda auren captain sheikh,daga sannan ta sanyawa ranta nisantarsu dama zama a cikinsu. Ba yadda za'a zauna a tashi ba tare da sunyi wata magana data danganci matarsa da aurensa ba. Ba yadda za'a zauna lafiya ba tare da an tabo batun aurensa ba,saita zabi ta yita kwanciya cikin daki da sunan jikinta ne har yanzu baiyi qwari ba.

Ruwa take nema Don haka dole ta fito nan din,don freezer dinsu an fiddasu duka za'a sanya sabo,kuma basu qaraso ba har yanzu.

A hankali take takowa,sosai duk wanda ya kalleta zaiga ramar da tayi. Tana jin kamar iska tana yawo da ita cikin sararin samaniya ne kawai. Muryarsa taji sanda yake fadin.

"Nanay fa?". Kalma daya ce tak amma tasirinta a zuciyarta me girma da fadi ne. Sautinsa da muryarsa wani abu ne da har yanzu tasha kwatantata data sauran maza amma ba wanda ya dace tasa tayi daidai da tata a mizani.

Kaman ta juya ta koma saboda tsananin bugawar da zuciyarta takeyi amma saita kasa. Tayi kewarsa sosai,tana kuma buqatar ganin wannan kyakkyawan kamilalliyar fuskar dake da wani irin kamewa da nutsuwa.

Da sallama ta shiga,idanunta kuma a kansa. Sun amsa duka,amma shi kyawawan labbansa ne kawai taga sunyi motsi. Waigowa yayo shima kaman sauran mutanen cikin parlor din,sai da numfashinta ya kusa qwacewa na wucin gadi.

Wani kyau.....zallar kyau taga yayi mata duk da ya cire suit din saman sai T-shirt din cikin. Bata sani ba.....ko don ganinsa cikin qananun kaya wani baqon abune a tare dashi shi yasa?.

Idanunta ta lumshe zuciyarta na tsananin bugawa a qirjinta.

"Sannu saamee.....kin fito?" Balqees ta tambaya tana kallon idanunta. Kai ta daga a hankali ta motsa labbanta tana amsawa da

"Eh" Sannan ta daga idanunta tana zubewa akan fuskarsa. Ba ita yake kalla ba,still hankalisa yana kan camera din noorah yana ci gaba da kallon tsuntsayen da yaji sun burgeshi sosai. Lafiyayyu dasu da irin salon kiwon daya tabbatar sun samu kulawa.

"Barka da dare,ina yini" Ta fada da yaren oromo. Kansa ya daga yadan kalleta.

"Lafiya lau malama.....ya jikin naki?"

"Alhmdlh da sauqi" Ta bashi amsa wani abu yayi mata tsaye. General kulawa ce normal yadda ya saba. Yadda ya saba yiwa su noorah Aanani da rumaisa,harma sai taga kaman yafi nuna musu kulawa akan yadda yake nuna matan.

"Allah yasa kaffara" Ya fada yana miqawa noorah camera dinta.

"Nanay ta kwanta ko?" Kai noorah ta daga masa.

"Tun dazun,tace tanaso gobe ta tashi da wuri...."

"Nanay ta rasa sukuni fa,kaman gobe ba zatazo ba,tace surukarta kawai takeson gani......anya kwanan nan ba zaka rasa matsayinka gurin nanay ba?" Murmushi ya saki kadan yana jin jikinsa har yanzu ba qwari,murarsa kaman tanason yin gana,still mararsa a daure take har yanzun kaman tanason masa ciwon data saba lokaci lokaci.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Banajin akwai me iya qwace wannan".

"Saini" Muryar hussam ta cika parlor din sanda yake shigowa hannunsa dauke da mangwaro da aka yanka.

Harara ya juya ya watsa masa,hakan ya sanya hussam shiga taitayinsa,yadan koma da baya yayo sallama sannan ya shigo,kai tsaye kuma ya wuce kusa da Aanani zai zauna.

"Tashi" Haisam yace dashi kai tsaye. Shi da Aanani dukkansu ba haquri,abokin rigimarta ne sosai,kaman ba rumaisa bace sakuwarsa Aanani ce. Yayi narai narai da idanu yana sauya gurin zama,saidai ko sakewa haisam bai bari yayi ba yace masa.

"Ina report na ma'aikatan kamfanin can na dubai?". Idanu ya narke,bai taba ganin mutumin da baya gajiya da sabga ba irin haisam din.

"Obbo.....an kammala komai,kawai na d'aga qafa ne a gama biki sannan"

"Ni nace maka?" Ya fadi kansa tsaye idanunnan nasa na cikin na hussam.

"Kayi haquri......hukuma ta bamu sha biyar ga sabon wata zamu iya bude kamfanin mu"

"Alhamdulillah" Ya fada a hankali ya miqa hannu yana karbar wayar hussam din da yake miqa masa.

Hotuna ne na dukka sassan kamfanin,kamfanin da haka kawai ya shiga ransa saboda yawan abokan hulda na kasuwanci da suke dasu a qasar Dubai din. Haka kawai yaji a ransa wannan karon hussam yayi abun arziqin da bai taba yin irinsa ba,ya daga kai ya dubi hussam din dake bada labarin shima ya hada tasa walimar.

"Inde da shashashanci a ciki ka tabbatar ba za'a yita ba"

"Aah obbo....walima fa,ba party bane wannan na rantse" Idanunsa kawai ya maida kan wayar,sai baice komai ba yaci gaba da kallon hotunan. Yana ji a ransa ya kamata kawai yasa hussam ya fidda mata yayi masa aure,kaman hankalinsa sai yafi haka nutsuwa. Duk da ba wani shashashanci yake ba....jinin aba jifar dukka Allah ya shirya masa,kawai rawar kansa wani lokaci ke sanyawa basa shiri da haisam. Yana da tara abokai kala kala,hakan kuma baiwa haisam din ba,don yana iya kawo matsalar tarbiyya.

Da qyar takai kanta kitchen din tana ci gaba da sauraren maganganu da hirarrakinsu. Gaba daya sai yanzu take jin kanta lallai ita bare ce,lallai ita din wata dabance da babu wanda ya damu da ita.

"Zanje nima.....tabbas zanje" Ta fadawa kanta tana qoqarin hadiye abinda yake taso mata.

A yanzun ta shirya fuskantar matar haisam.....ta shirya tsaiwa taga wacece ita?,ta kuma shirya karbar haisam din koda dadi ko bata dadi ba.......zata gwada mata itace bare.....zata gwada mata itace ta shigo rayuwarsu.....itace ta fado muhallin daba nata ba.
Chapter 64 · 0% Book details