← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 176

Sashe 71

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa kawai qoqarin mallakar kansa yakeyi,musamman ahmad daya samu wani irin training daga gurin haisam na dan zaman da sukayi tare. Kallon dake cikin idanun ahmad din sun mata nauyi,saidai ko daya taqi yarda ta bari yaga haka cikin idanuwanta.

Ya motsa zuwa gaba kadan,cikin wata kakkaifar murya yace.

"Bansan me kikeyi a nan a daidai wannan lokacin ba" Idanu ta sake zuba masa,sannan ta saki wani shu'umin murmushi tana gyara tsaiwarta.

"Yaro man kaza......" Ta furta da wani yanayi,sannan ta mamaye maganar tata da fadin.

"A daidai wannan lokacin,yanayin lafiyarsa yana iya sauyawa.....kai bakaga kamata gurin zuwa dubashi akai akai ba?". Idanunsa ya qanqance sosai a kanta.

" Anyi masa komai daya kamata....baya buqatar wata qarin kulawa ta daban tunda ba lokacin tashinsa bane.....bayan duka wannan kin sani......doka ce an hana kowa shigowa gurinsa irin haka"

"Kowa?....kowa?" Ta maimaita sau biyu tana kallon ahmad din. Can qasan ranta tana jin wani b'acin rai yana ratsata. Wai sai yaushe komai zai saitu?,yaushe lalacewarta yakai haka?.

Yaron data raineshi da hannayenta,yaron data bashi rayuwa irin wadda takeso,yaron daya zama tamkar bawa a gareta yau shike da iko da fada a ji cikin rayuwarta data masarauta gaba daya?.

Ba shakka da tasan zai zama haka.....zai mulketa koda na rana d'aya ne tabbas data kasheshi bata bari taga zuwan wannan ranar ba.

"Ni ba kowa bace.....bana cikin sahun jam'in KOWA da doka zata hau kansa" Tayi maganan a hanzarce tana takowa don wuceshi. Alwai wani abu dangane da yaron,akwai wani abu da bata so da yake qyalli cikin idanunsa,kamar shige shigen abinda yake fita daga idanun sheikh haisam.

Da kallo ya bita,yadda ta fita din baiyi masa ba,a gaggauce da yanayin da yake gaya masa lallai akwai wani abu da take birnewa,sai kawai ya ciro wayarsa,yayi kira dukkanin qofofin da zata fice,ya bada umarni tsare masa ita har sai ya tabbatar da komai na sultane lafiya yake.

Wayar ya ajiye,sannan ya fara takawa a hanzarce yana wucewa dakin sultane din. Ya daga labulen yana shiga bakinsa dauke da sallama,duk da ya sani babu me amsa masa.

Ba kowa kaman yadda ya zata,yaci gaba da takawa zuwa inda yake. Yana nan kwance kaman yadda ya barshi,ba wani abu daya canza daga fuskarsa ko yanayin kwanciyarsa. Yakai hancinsa zuwa bakinsa da hancinsa ya tabbatar da bugawar zuciyarsa yadda take.

Wayarsa ya ciro kai tsaye,ya kuma kira haisam,daidai sanda yake tsane kansa da towel bayan ya fito daga wanka da ruwa me dumin gaske saboda yadda mararsa har yanzu taqi sassauta masa.

Shuru yayi yana sauraren dukkanin bayanan ahmad,har sai da ahmad din ya kammala.

Ka bincika dakin,komai da komai,qasan shimfidarsa,gefe da gefan gadon,kada ka sanya hannunka,kayi amfani da hand glove,bayan labulaye,cikin pillow dinsa,toilets da bathroom" Abinda yace dashi kenan.

"Ka maida kiran video call,ka ajiye ta inda zan iya ganin motsinka"

"Yes sir" Ahmad ya amsa masa da girmamawa. Miqewa haisam din yayi,yana gyara daurin bathrobe din jikinsa sosai,sannan ya koma ya zauna yana amsa video call din da Ahmad yayi requesting masa.

Ya sani,ba yadda za'ayi tayi shiga da fitar banza. Duk sanda ka ganta akan abun hari to lallai ba shakka akwai wani saqo da zata bayar ko ta aiko a bayar din.

A nutse yake monitoring motsin ahamd,yana bincike ko ina idanunsa suna biye dashi har ya kammala,saidai ba wani abu da aka samu.

"Ka kuncemin Ac dincan" Haisam ya fada a nutse yana duban ahmad.

"Kafin ka kunce,ka samu bargo ko wani abu me laushi ka shimfida daga qasan,incase ko meye karmuyi losing nasa"

"Tom" Ahmad ya fadi,kujera da duk abinda za'a nema haisam ya lissafo masa,Ahmad din ya cire babbar rigar jikinsa yabar 'yar ciki,ya taka kujerar yana bin abinda haisam yace masa step bai st

Cikin mintuna biyar ya kwanceta.

"Ka ajiye screw driver din,kasa hannunka duka biyun ka tallafe fuskar" Yace masa.

Hakan yayi,ya kuma sauke fuskar Ac din a hankali,sai ga wasu qananun kwalabe mitsi mitsi an huhhuda tsakiyarsu kusan guda biyar.

Gaban camera din ahamd yazo ya jera masa su yana huci,zuciyarsa tana wani irin tafasa gumi yana tsatsafo masa a goshinsa.

"Me muke jira da matar nan obbo?" Ya fada a ladabce,saidai hakan bai hana bayyanuwar fushinsa ba.

Wani murmushi ya saki,siririn malalacin murmushi sannan ya maida idanunsa ga ahmad.

"Sultane ahmad......sultane kadai muke jira" Ya amsa masa idanunsa cikin na ahmad din.

*_A B A J I F A R P A L A C E_*

Babban dakin taro ne me cike da wani irin alatu na alfarma.......lafiyayyun kujeru farare da table table masu daukan hankali da nuna alfarma. Chandelier masu na asalin dutsen crystal masu tsananin tsada,masu tsaho ne sosai sun mamaye roofing dakin taron da wani irin yanayi da zai sake nuna maka zallar alfarma da IKO dake tattare da gurin gaba daya.

Rana ce data kasance ta farko cikin tsarin karbar baquwar dake aure da jinin aba jifar. Saidai al'adar ta kasance ta daban data dauki hankulan duk wani me iko da duk wanda ke rayuwa cikin masarautar.

Sati biyu......sati biyu tayi hannun nanay suna wani irin karatu wanda daga ita sai nanay din. Sati biyu nanay tayi tana bata kulawa da kanta,sati gudan da koda su Anaani nanay bata bari sun ganta ba sai da qyar,ballantana haisam da saidai wani lokaci taji muryarsa kawai.

Wani irin shaquwa.....qauna da fahimtar juna masu tarin yawa ne suka gilma tsakanin nanay da Akhnan din. Da gaske,har cikin jininta takejin nanay din kamar safeena......kamar mahaifiyar data rasa din.

Ko nanay bata fito kai tsaye ta gaya mata ba,ita din ta fahimci wata gagarumar soyayya da nanay kewa haisam.

Jiya ta fara b'aro mata wani karatu data dinga jin kamar zata nutse.

"Dokoki da qa'idar daya kamata kowacce mace ta kiyaye......mu'amalar auratayyarta da miji......yadda zaki kai kanki ga mijinki,yadda zaki karbeshi a duk sanda ya kawo kansa gareki......yadda zaki karanci yana cikin buqatarki........da yadda zaki bashi kulawa" Duka sanda nanay ta jero kasa hada idanu tayi da ita. Sarai nanay taga hakan a tattare da ita,amma tayi kunnen uwar shegu kaman bata fahimci Akhnan najin nauyi ba. Abu daya kawai dakewa nanay dadi shine......wata irin kwanya data fahimci Akhnan nata ita.....saurin ganewa da dauke komai,har wani lokaci murmushi yakan kubce mata,can qasan ranta kuma takance.

"Bansan wadanne irin yara zaku haifa ba keda Muhammad......kamar sai daya gwada ya samu mace me shige basirarsa?".

Cikin wata shiga ta alfarma ta fararen tufafi Akhnan din ke zaune,fararen tufafin da fararen duwatsun dake jiki suka qara musu wani irin kwarjini da daukan hankali.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

A iya kwanakin al'amuran sun sake sanyayar mata da jiki. Tana ganin wata sabuwar duniya.....sabuwar rayuwa.....sabuwar daular masarautar da kamar za'a ciyar da kai da lu'u lu'u. Karo na farko data fara sanin cewa SAMAN KOWANNE MULKI AKWAI WANI.....SAMAN KOWANNE IKO AKWAI WANI......SAMAN KOWACCE IYAWA AKWAI WATA.......SAMAN KOWACCE ALFARMA AKWAI WATA.

A iya suturun da aka ware mata kawai ta sani sunkai adadin abinda ta mallaka a rayuwarta......tabbas inda narka kudinsu za'ayi ba abinda zai hana sukai adadin dukiyar da take taqamar ta mallaka. Kullum idan ta kwanta zuciyarta na cika da mamakin ME YAJE YI AGADEZ?.....me yasa ya qasqantar da kanshi?,me yasa ya zabi wofantar da dukkan wannan gatan nasa da yake dashi?,ya zabi rayuwa qarqashin alfarma?,bayan alfarmar shi take bi da kanta?.

A kwanakin idan tace zuciyarta daidai take tayi qarya. Ta samu dukkan kulawa da walwala,wani irin jiqaqqen gata.....amma aduk sa'ilin da dare zaiyi sai wata irin kewa ta taso ta danneta. Sai wata irin kewa ta rugo ta lullubeta......wata irin kewa da sannu a hankali ta fara sallamawa ta fara tashi daga SABO ta fara juyewa zuwa wani abu na daban......wannna abun da har yau bata yarda da kalmar SOYAYYA bace.

Dukkanin wasu qawaye.....matan sarakuna......dama matan dake da iko da fada aji cikin masarautar aba jifar ne tattare a dakin. Murmushin dake fita daga fuskar mama oromo kawai zai gaya maka rana ce ta musamman.

Daga daya bangaren tana zaune ne cikin rukunin kujerun da iyali kuma jinin nanay da abba jifar ke da ikon zama. Saamee ce,da dukkanin idanunta da motsinta yake kan Akhnan,ba'a iya yau kawai ba......a dukka kwanaki goma sha hudun bata yarda koda kwana daya ya kufce mata ba tare data kusanta kanta da ita ba,ta kuma bar mata shaida da tabon da zata gane ITACE SAAMEE ba.

A kwanaki sha hudun,tayi dukka qoqarinta na neman kusanta kanta da dukka hidimar data shafi sheikh muhammad haisam din,a sanda al'ada ta nesantashi da Akhnan din. Kwanakin sun mata dadi,sun kuma maido abinda take kalla da sunan kulawa tsakaninta da haisam din.

Saidai a yau dukka farincikinta yana neman rushewa,muddin wannan taron ya gudana yadda al'ada tace.....to Akhnan ta taka mataki na farko mafi girma da qarfin da zai tabbatar da sunanta cikin na haisam dama na masarautar.....zata koma amsa sunan KHADEEJA MUHAMMAD HAISAM JIFAR maimakon KHADEEJA MUHAMMAD HAMMUD.

Amsa wannan sunan kuwa shi yake nufin nan da kowanne lokaci zata tare a gidan da zata zamto sarauniya mafi girman iko,gidan da jaridu suketa maganarshi,ya shiga bakin 'yan media da al'ummar gari saboda baqon tsarin ginin da aka masa da tarihi bai taba zuwa da wani wanda ya mallaki irinsa cikin Ethiopia da kewayenta ba.

"Takwarata ce......wadda ta fito daga tsatson mutum mafi soyuwa a gareni.......saidai daga yau tabar amsa sunan Akhnan......." Muryar nanay tayi amsa kuwwa cikin dakin taron daya dauki wani irin shuru kamar babu me rai a cikinsa.

"Tun daga yau.....tun daga yanzu ba baquwa bace......" Ta sake fadi a nutse,sautinta yana ratsa shurun. Sai ta miqe sannu a hankali da wannan haibar nutsuwar da tarin kamala.

Gaban Akhnan ta qarasa,ta miqa hannunta ta riqe hannun Akhnan din sosai cikin nata,sannan tadan dagashi sama kadan

"Za'a kiraki......." Ta sake dakatawa tana numfasawa da wani irin zaquwa tarin qauna da soyayya

"GIIFTII(giiftii a yaren oromo yana nufin mace me daraja ,macen data fito daga gidan sarauta iko ko matsayi,ko macen da ake girmamawa sosai)"

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862
Chapter 71 · 0% Book details