Sashe 130
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*BOOK 03///PAGE 118*
__________________________
✨ AMINTACCEN GURIN SIYAN THRIFT ABAYAS ✨
Ingantattun Thrift Abayas masu kyau da tsari akan farashi mai sauƙi da araha.
Muna kawo sababbin kaya akai-akai tare da rangwame na musamman.
🤍 Dukka sai a MK ABAYA BOUTIQUE 🤍
Duniyar Thrift Abayas masu kyau, masu tsari, da salo iri-iri domin kowane lokaci da kowane irin event.
Abayas masu inganci, masu salo, masu araha, kuma na zamani ga mata masu son ƙawata kamanninsu cikin kamala da kamun kai.
Karki bari a ba ki labari... Leƙo ki ga yadda MK ABAYA BOUTIQUE kullum ke cike da kyawawan Thrift Abayas akan farashi mai kama da kyauta.
'YAN SARI, 'YAN REPOSTING, DA MASU SIYA DON AMFANIN KANSU... DUKA INA MUKU MARABA! 🤝🤍
📱 WhatsApp: 07064399623
📞 Call: 08036027448
🔗 Join our Wholesalers Group:
https://chat.whatsapp.com/JBg80RmA47v7GoqvWdgLJT?s=cl&p=a&mlu=3
___________________________
Girgiza kai akhnan tayi,wasu irin zafafan hawaye suna wanke mata fuska
“Don Allah kiyi shiru…” ta fada cikin karyewa. Ji take kaman zatayi hauka.....kaman kwanyarta tana damulewa a duk kalma daya da zata fito daga bakin mammina.
"Abinda yake sake bani dariya shine......yadda kika dinga gudu zuwa jikina a duk sanda wani ya b'ata miki rai ko ya miki ba daidai ba....." Cak kalaman mammina suka tsaya cikin iska.....komai na quruciyarta yana dawo mata ana mata kamar wadda aka kunnawa faifan rayuwarta. Daga kai tayi ta sake kallonta.....tamkar ba itace wannan matar data tab'a rainonta ba?. Tamkar ba itace wannan matar data kira UWA ba.
"Ashe baki taba sona ba?" Ta fada tana zubawa mamminan idanu,tsantsar karaya suna nunawa cikin idanun nan nata da ruwan hawaye yake kwarara.
Murmushi tayi,irin murmushinnan me sanyi wanda yafi mari ciwo
"Na gaya miki ai....amma inajin kina buqatar maimaici ne.....so ko?.....kinsan me ake kira soyayya a fada?"
"Rauni" Ta qarasa maganarta.
"Amma kina rungumeni....kina cemin d'iyata" Akhnan ta furta cikin fitar hayyaci tare da jin komai yana zame mata kamar mafarki ko wasan kwaikwayo.
Juyowa tayi tana kallonta sosai,Idanunta babu taushi ko kad'an
“Ko kina tunanin rungumar da nake miki na gaskiya ne?” sai ta saki wata dariya me ciwo
“Duk lokacin da na kalleki…”
“…ina ganin fuskar uwarki." Riqe qirjinta akhnan tayi,numfashinta na sarqewa.
"Ki tsaya.....don Allah ki tsaya" Ta fada tana fatan ta tsaya din,tana fatan kuma ya zama mafarkinne. Saidai ko alaman ta tsaya ba tare data amayar ta tsiyayar da dukka magangun bakinta batayi ba.
"Uwarki ta samu abinda nakeso......wato sultane...."
"Tsahon shekarunnan yana bauta mata saboda sanyi da taushin halinta.....tsahon kuma shekarun da suka biyo bayan mutuwarta din ya gagara mantawa da ita duk da tarin kyautatawata a gareta,safiyya taxo ta sake lullube wannan gurbin da nake harin samu....."
"Na tsani yadda yake kallonta....." Ta fada muryarta na cracking.
"Na tsani yadda ya kasa mantata" Ta sake fada wannan zallar wutar qiyayyar na nunawa qarara cikin idanunta. Sake takowa tayi gabanta.
"Da Gaske na girmar dake.....saidai ki tuna,kowanne halin kirki nawa qwara d'aya.....yaqine ga mataccen jikin safeena".
Wani irin baya akhnan taja,tana jin yadda quruciyarta ke rugurgujewa a gabanta. Mammina ta gyara mata gashi sau ba adadi.....ta rungumeta sanda tana kuka.....ta tsaya mata a gurare masu tarin yawa.....mafi girma ta kirata da D'IYATA.....duka wannan FAKE NE?!.....qarya ce?.
"Ya zama dole a kanki ki godemin.....don na barki da ranki ba kaman yadda na salwantar da wasu ba.....na barki kin rayu cikin daular mulkin mahaifinki......ba kaman yadda na hana 'yan uwanki zama cikin tasu daular ba.....ahmad d'an sultane da safeena......da kuma d'an AJANI jinjirin da bashi da suna" Sai ta fara takawa da wani irin taku dake nuna zallar rashin imani a tare da ita
"Ke wace irin macace?" Akhnan ta fada a tsawace tana jin yadda take sake tarwatsewa a gaban mammina. Murmushi ta sake mata tana duban fuskarta.
"Mace me son nasara......abinda ya hanani cinyeku tunda wuri.....shine sultane.....yanzu kuma babu shi.....ba wanda ya isa ya dakatar dani daga dukkan shiri na....."
"Daga yau.....kada ki sake kallona a matsayi uwa!" Ta fada tana takawa zuwa qofar da zata fiddata a gurin.
"Saboda nima ban taba kallonki a matsayin d'iya ba......sannan....." Sai ta dakata.
".....ki shirya.....kece plan dina na qarshe.....ba kuma wanda ya isa ya kareki" Tana kaiwa nan ta bude qofar ta shige tana maidata ta kulle.
Yana jin takunta......yana jin takun wucewarta......amma baima kalleta ba,saboda dukka hankalinsa yana kan kowanne fitar numfashin akhnan da komawarsa. Qirjinsa na masa wani irin ciwo,yana jin kamar bazai dauka ba.....kaman iya abinda zai iya dauka kenan. Akhnan red line dinsa......wanda tabbas idan mammina ta sake ta qetarashi,komai zai sake muni sama da munin da yake dashi a yanzu.
Kasa motsi akhnan tayi,kamar jikinta ya manta yadda ake numfashi. Kamar qafafuwanta sun daina daukar nauyi.
“Mijina ya kasance nata kafin na zama komai…”
“Murmushin da nake miki yaqi ne…”
“Na rainaki ne saboda kina tuna min ita…” Kalaman suna ta maimaituwa cikin kanta. Idanunta suka soma rawa. Kwanyarta ta kasa karbar abinda taji,sai numfashinta ya fara qoqarin rikicewa.
"Aah.....aah....aah" Haka ta fada a jajjere tana dora hannunta akan bakinta wai ko zata iya hana kanta zubda hawaye. Gaba daya qirjinta taji yana mata ciwo,kamar an tsaga an ciro wata tsoka daga muhallinta.
Sai ta juya da sauri ta fito daga chamber d'in. Cikin takunta na tangal-tangal,kamar wadda tasha wani abun maye ta bugu. Hawayenta kawai sauka suke ba qaqqautawa. Cikin tsoro hadiman suke matsawa suna sauke idanunsu qasa daga kallon matar sheikh muhammad haisam din. A yanayinta kawai basu tab'a ganin rauni a tattare da ita ba irin na yau.
Ta kai qarshen corridor din da qyar,sai qafafuwanta suka kasa daukarta. Ta dafe bango da qarfi. Numfashinta na rawa.
A lokacin ne yake sake takowa zuwa gareta,cikin sassarfa da karsashi da tarin kuzarin nan nasa wanda a yau yakejin kamar ya zarta kullum,kamar jinin da zuciyarsa ke bugawa zuwa ga gangar jikinsa na yau ba irin na ko yaushe bane.
Qamshin nan nasa shi ya gaya mata shine ya iso gabanta. Ta d'ago idanunta tana dubanshi......suna hada idanu sai wani sabon kuka mai ciwo ya kubce mata.
“Haisam…” ta fada da wannan sautin da yakeso,saidai a yau wannan muryar ba irin wadda yake da muradin ji bace.
Bata iya jira ya risketa a inda take tsaye ba,ta soma takawa zuwa gare shi da sauri. Kamar mutum mai neman mafaka.
Kafin ta isa din qafafuwanta suka sake tangal-tangal da ita.
Tareta haisam yayi da sauri. Ya mata kyakkyawan riqo kafin ta kai ga fad'uwa. Da qarfi ta kama rigarsa ta riqe sosai cikin hannunta,yanayi riqon daya zame masa ma'auni na girman zafi da rad'ad'in da takeji a zuciyarta.
"Tayimin qarya......tasa na qare girmana tana yaudarata". Kallon fuskarta haisam yayi.....kumburarrun idanunta....rikicewar numfashinta kawai sai suke neman d'auke tasa nutsuwar. Ya sake matse haqoransa yana qara tilastawa kansa controlling abinda yakeji din.
"Me tace miki?" Ya tambaya cikin sanyin murya kaman baiji komai ba. Jikinsa ta shige sosai......dukka jikinta yana rawa. Daya bayan daya ta gaya masa.....sak yadda mammina ta fada baiji ta mañta ko ta rage abu ko qwara daya ba.
“Ashe duk shekarun nan…” ta fada ko ina a jikinta yana rawa.
“…ni ba d'iya bace a wajenta…” .
Hannunsa ya dago,ya riqe bayan kanta a tausashe. Ya jawota jikinsa sosai kamar yana qoqarin tattara dukkan b'angarorin zuciyarta da suka tarwatse.
“Ki kalle ni.” ya furta da wata sirrintacciyar murya me taushi. Sai ta d'ago idanunta cikin hawaye kamar yadda ya buqata.
“Abinda mugun mutum ya kasa bayarwa…” ya furta yana share mata hawaye
“…ba yana nufin baki cancanci shi bane.” wasu sabbin hawayen ne suka sake bin kuncinta bayan wadanda ya share mata.
Kamar wuta haka yake jin d'igarsu har cikin tsakiyar zuciyarsa.
"Kinjini?" Ya fada yana tattaro fuskarta a tsakiyar tafukan hannayensa.
"Rashin soyayyarta......" Ya fada da muryar rad'a.
"Ba laifinki bane" Sake riqe hannayensa tayi sosai tana girgiza kai hawayen sun kasa controlling kansu suma.
"Na yarda da ita.....na qaunaceta" Wani kallo me taushi ya bayyana a idanunsa.
"And that says more about your heart…”
"Than hers........" Ya qarasa fadi yana jin yadda numfashinta ke a rikice kamar zuciyarta ta kasa d'aukar nauyin gaskiyar da taji.
Da wani irin taushi ya mata muhalli me kyau a qirjinsa,ya kuma lullubeta da dogayen hannayensa,ya mata rumfa ruf ta yadda ta bace gaba daya a faffadan qirjinsa. Yana jinta,tana son sakeyin magana,sai ya lumshe idanunsa yana furta.
"Shshshsh..... Ki bari numfashinki ya daidaita tukunna"
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Qara mannewa tayi cikin jikinsa,tana sauke wani irin kuka me nauyin gaske. Hannunsa saman kanta yana shafawa a hankali har zuwa gadon bayanta. Idanunsa suna runtse,yana jin yadda bugun zuciyarsa ke sake motsawa da wani irin nauyin gaske.
"Bansan me yasa yakemin zafi ba......ya kamata na tsaneta yanzu" Ta fada muryarta na sarqewa da kukan.
"Ki tsaneta......ki tsaneta gwargwadon yadda zaki iya.......is allowed" Ya furta da wani taushi a muryarsa,idanunsa har yanzu a kulle. Ya fahimci ciwon da take ciki,mutum mafi kusa da ita tun tana yarinya...... ashe duk shekaru yana rayuwa da qarya......me yafi wannan ciwo?.
"Zakiji ciwo giiftii.....zakiji ciwo sosai....."
"......Mutum mai zuciya mai tsabta idan aka cuce shi…”
"...…ciwon yakan zurfafa.” Ta girgiza kai tana kuka a hankali.
“Na kira ta uwa…”
Sai ya share hawayen gefen fuskarta da babban yatsansa yana dubanta a nutse.
“Kuma kin yi hakan da zuciya d'aya ba.” ya sake karkatar da kansa yana kallonta cikin idanunta
“Kar ki ji kunyar hakan.” sai ta sauke idanunta qasa.
“Amma ni wawiya ce…” tayi maganan muryarta tana rawa.
Yatsunsa ya sanya,ya dago habarta a nutse yana jin kalmar data gayawa kanta da kanta ta masa ciwo.
“Kada ki sake fad'ar haka.” yadan kausasa muryarsa.
“Kin ji ni?” Ta kalleshi cikin rawar ido irin na wanda ke qoqarin dakatar da hawaye.
“Mai yaudara ne yake da laifi.” ya fada yana cusa tafin hannunsa cikin nata.
“Ba wanda ya bada gaskiyarsa ba.” hawaye ya sake gangaro mata ta dukkanin idanunta biyun. Sai ya jawota jikinsa yana matseta sosai da wani irin dumi da taushi daya mamaye ilahirin jikinta.
Ya bari ta yi kukanta.
Bai hanata ba. Saboda ya san: 👉 wasu ciwukan hawaye kad'ains suke iya rage su.
Na wasu seconds corridor d'in ya yi shiru. Sai sautin kukanta kad'ai,da bugun zuciyar Haisam da yake ji har kunnuwansa.
Ya bata tazara da ratar mintuna kafin ya motsa a hankali,ya d'an sunkuya kusa da kunnenta.