Sashe 16
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idanu kawai morsa safiyya ta zuba musu shida mammina din,zuciyarta na wani irin tsalle a qirjinta,wani yanayi takeji da yake sake bata tabbacin lallai shi din jinin safeena ne. Sai ta miqe tsaye cak,tana jin qafafunta suna rawa ta qarasa gabansa. Ta yarda da sheikh haisam har fiye da yadda ta yarda da kanta,tunda ta gansu tare ta tabbatar akwai wani abu,to amma tanason ta bawa zuciyarta tabbacin da babu shakka ko kokwanto a kansa.
A hankali yayi taku biyu yaja baya yana raba jikinsa dana mammina.......sannan kuma ya juya kansa gefansa yana duban morsa safiyya dake tsaye tana kallonsa da idanunta da suka cika taf da qwalla.
Haka kawai yake ganin wasu abubuwa tattare da ita,haka kurum duk dabai shaida wace ba yakejin wani strong connection daga idanunta zuwa nasa. Wani nutsuwa da kuma wani kalar aminci yana baibayeshi.
Taku uku ta qara,ta iso gabansa,ta miqa masa hannunta,saiya bi hannun nata da kallo
"Hannunka" Ta fada tana sakin murmushin dake cakude da qwalla. Bai musa ba ya miqa mata hannun nasa,ta riqe cikin nata ta soma janye hannun rigar dake jikinsa.
Hannunsa ta soma jujjuya tana neman abinda takeson gani. Ta sake juya hannun zuwa saya b'angaren,take idanunta suka gano mata abinda takeson gani din.
Wata runguma me qarfin gaske takai masa tana sauke wani nutsatsen kuka me taba zuciya,sai kawai ya samu kansa da riqeta sosai cikin jikinsa. Wani abu yaji yana motsawa har qasan zuciyarsa.....wani irin motsawar zuciya da zaije bai taba jin emotion irin wannan ba. Karyewar zuciya ya dinga ji kamar shima ya saki kukan,saidai tuni ya horu ya kuma karantu akan dabi'un basarake......ya kuma haddace kusan dukkan al'adu da dabi'ar masarauta.
"D'ana ne......ahmad ne.....ebba na.....ebba masoyi" Sunan yaji ya harba cikin kansa.....sai yaji wata wuta ta kawo cikin kansa,ya daga idanunsa yana saukewa a kanta still duk da tana jikinsa. Kamar yana tuna sunan.....kamar yasan sunan a wani mafarki daya taba yi.....kamar yasan sunan a wata rayuwa daya taba yi a baya.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
"Ki zauna safiyya,kiyi haquri" Nannie itama da idanunta suka cika da hawaye ta fada bayan ta miqe tana kaman morsa safiyya ganin yadda kukanta yake qara yawa ainunn,har dukka jikinta yana amsawa.
Wani irin sanyi takeji suna bin dukka gabbanta.....wani irin yanayi da ba zata tantance wanne bane. Dan uwanta ahmad dai?,ahmad da aketa fadi wanda batayi wayon da zata ganeshi ba a sanda ya bace?. Amma wannan fuskar kamar tana mata kama da wata fuskar.......duk da ta rasa ganowa inda ta taba ganinta,koma a inane tasan bataga fuskar da yawa bane da babu abinda zai hanata tunawa.
A hankali ya qaraso gaban sultane,sultane din dake zaune saman doguwar kujera shi da akhnan da falaak da suke zaune dama da hagunsa.
Sulalewa yayi saman gwiwarsa cikin tsananin girmamawa yana soma gaidashi da yaren Tuareg,abinda ya saka tsananin farinciki a zuciyar sultane,don bai taba tunani ko kawowa zaiji yaren ba.
Daga gaban sultane sai ya isa gaban manyan da suke nan gaba daya ya fara gaidasu,suna girmamashi yana girmamasu,yanayin daya sanya taruwar qwalla cikin idanunsa.
Ashe wannan shine tushensa?,ashe wannan shine asalinsa?,ashe wannan ne dalilin da yasa kullum kuma kowacce rana yakeji a ransa rayuwarsa ba tasa bace?,ashe shi yasa yaqi gamsuwa rayuwar da yake gudanarwa itace rayuwarsa?.
Komawa yayi ya gaida yakumbo nannie da morsa data iya amsawa da qyar saboda kuka,sanda ya iso kan mammina ji yayi zazzafan mari ya kamata ya sauke mata ba gaisuwa ba,amma koda tuna da kalaman haisam sai ya basarwa yana gaidata da wani irin yanayi daya sanya gabanta tsananta faduwa.
Irin kallon da take gani a idanunsa suna tabbatar mata da gaske almaz dinne,irin kallon da take gani tattare dashi yana gaya mata cikin hayyacinsa yake......cikin kuma hankalinsa yake. Ba wani abu daga tunaninsa daya bace.....ba wani abu daga tunaninsa daya sauya ko ya samu naqasu.
"Almaz ne" Ya fada yana kallon tsakiyar idanunta bayan ya miqe da sautin da ba wanda yaji daga shi sai ita.
Wani abu taji ya daki qirjinta......abun daya taho da tsananin qarfinsa ya kuma dunqule mata a qirjin ya sanyata jin jiri tana daga zaunen,sai gashi ta gagara zama tana neman sulalewa.
Nannie ce ta tarota tana salati,wani irin numfashi mamminan ke fiddawa gumi kuma yana yanko mata saboda yadda take kokawa da numfashin nata,da alama iskar gurin bata isarta.
"Akwai taimakon da za'a bata?" Sultane ya fadi yana duban haisam adan rude,kai haisam ya gyada,sannan a nutse yace.
"Daki kawai za'a kaita.....sannan a kunna mata wadatacciyar iska a bata guri ita kadai". Da sauri sultane yasa aka kira tafisu da sauran manyan hadimanta suka dauketa bayan sultane ya taka har zuwa bakin dakin taron.
"Yanzu zamu kammala zaman,idan akwai wani rashin ci gaba a yanayinta a kira likita kafin mu fito" Ya fadi sannan ya juyo yana dawowa ciki.
Dukkanin takardun gwaje gwajen qwayar halitta nashi dana ahmad DNA test ya gabatar musu,bawai kuma don kowa bai yarda ba,aah saboda sake samun tabbaci da nutsuwar zuciya.
Duk wanda yake zaune a gurin girmama lamarin ubangiji yakeyi,sunata juya abun tare da taya sultane murna.
Saidai ba wanda yasan ta yadda ahmad ya bayyana.....ko ta yaya aka ganshi,duk da kowa akwai wadannan tambayoyin a ransa,amma rashin bayyanarwa ya sanya ba wanda ya nemi ba'asin jin hakan.
Wazeer,babban alqali na jaha,wali,galadima,shugaban limamai,da shugaban malamai dama ahalin diory hammani sunka wuce bisa rakiyar sultane gami da sake yiwa junansu barka da arziqin dawowar ahmad din cikin ahalinsa,sai dakin ya kasance daga sultane falaak da akhnan,sai morsa safiyya da nannie. Sai haisam dake zaune cikin kujera. Ya motsa zai fita tun sanda tsohon mamman hamza zai tafi amma sultane yace ya zauna. Akwai maganganu da yawa daya gani tattare da tsohon,wanda basu taba haduwa shi dashi ba sai a ranar.
"Gobe hammud inason ganinka,kai da abokin takarata daya kayar dani" Ya fada yana duban haisam. Koda wasan kaka da jika yasha banban a ayaren Oromo da yaren Tuareg amma ya fahimci tsokanarsa yake,sai yayi murmushi sultane yana fadin.
"Zanzo da kaina....zamu riskeka gida in sha Allah".
Ko a yanzun yana zaune cikin kujera,waya ce a hannunsa yana sake tattara wasu bayanai. Idanunsa basa kan kowa amma cikin jikinsa yakejin Kamar akwai wasu idanu a kansa. Zaifi so sultane ya sallameshi don gurin ya sake zama na ahali sosai wato yasu yasu.
Tsakanin ahmad da haisam batasan sau nawa ta raba idanunta a kansu ba. A duk sanda ta kalli ahmad din,sai ta dinga ji wani yanayi yana shigarta. Kaifi da qarfin jini.....wani yanayi na yau itama tana da yaya?,tana da wani jigo namiji dan uwa?.
Idan ta kalli haisam sai taga bataga komai ba,bata hangi komai ba sai wani basarwa da shariya daga gareshi. Tunda ya shigo ba zata iya tuna ko sau daya da taga ya daga kai ya kalleta ba. Har gwara falaak data gaidashi taga yayi kamar ya kalli sashen da take yana amsa mata da wannan kamewar tasa.
Ta sake zare dubanta daga kansa a hankali
"Meye alaqarsa da bayyanar ahmad?......mene alaqarsa da nemoshi?" Ta tambayi kanta kokwanton data kasa warwarewa kanta shi. Daga idanunta ta sakeyi tana saukewa akan ahmad dake tsugunne gabansu ita da falaak.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 15*
"Ni sunana ahmad,kefa kefa?" Ya fada yana dubansu dukka su biyun.
Murmushi ya kubcewa falaak sosai da yafi kama da qaramar dariya.
"Yaya ahmad.......ni sunana falaak.....ita kuma khadeeja,akhnan ko biftu,daa itace babba,amma yanzu tunda ka dawo kaine babban" Saida sukayi murmushi dukkansu harda ahmad din. Ya maida dubansa akan akhnan,har yanzu batayi magana ba. Da gaske dai haka dabi'arta take.....haka yanayinta yake,ba wani abu bane daban da a baya ya dauka. Ya hadiye wani yawu mai tauri da quna......ya dinga maimaita furta.
"Alhamdulillah" Da tuni qanwarsa yake aure?,da tuni zuwa yanzu alaqa da mu'amala tsakaninsu tayi nisa?. Da mummunan nufin wancan shaidaniyar ya cika da yanzu me kenan?.
Hannunsa ya miqa musu dukka sun biyun son suyi musabaha,sai falaak ta dora nata akai,amma akhnan saita noqe.
"Ehemmm......ko har yanzu ban shiga cikin ahali ba?" Ya tambayi akhnan yana dubanta. A hankali ta sauke idanunta akan hannun nasa,wani abu ya narka zuciyarta sosai tashin farko.
Yatsun sultane take gane a nasa hannun,tsahonsu da yanayin zubinsu,hatta da girman babban yatsansa na sultane ne,sai ta miqa masa nata hannun a hankali dukka ya hadesu guri guda nashi dana falaak da akhnan din.
"Duk da zaku tafi a sanda ni nazo,ina fatan zan zame muku kamar sultane ko?,babban yaya naji kuna cewa shine madadin uba" Wani sanyi taji yana ratsa zuciyarta a hankali.
A baya inda yana nan?,inda yana rayuwar ta qila shine zai dinga bata shawara?,shine zata dinga kaiwa kokenta?,shine zai duba daidai daba daidai ba qilan sama da yadda sultane yayi?.
Idanunsa basa kansu,amna kunnuwansa suna gurin,musamman sanda ya isa gabansu......musamman sanda ta sanya hannunta cikin nasa sai yaji wani abu ya masa tsaye a wuya. Halal ce......ba haramun ba,dan uwnata ne na jini,uwa daya uba daya,to amma haka kawai wani wutar kishi ta d'isa saman ransa.
"Na tsaidaka muhammad.......bari na barka haka sai gobe?" Sultane ya fadi wani girma yana fita daga idanunsa zuwa ga haisam. Wata irin qaunar haisam din yakeji sama da yadda yakejin ta yaransa,bai sani ba ko a nan gaba zai qaunaci ahmad kamar irin haka ko sama da haka?.
Miqewa yayi fuskarsa adan sake,yana bawa sultane hannu sannan ya juya a nutse ya fara takawa don ficewa daga gurin.