← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 176

Sashe 15

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun jiya ba tare da sanin kowa ba,daga shi sai abeer ya sanya aka maqala na'urar tsaro a kowacce kusurwa ta gurin da za'a gabatar da taron. Yayi ne da nufin samar da cikakken tsaro.....yayi ne don ya tabbatar da cewa yau din gidan ya zamana cikin tsaro. Musamman yau din data kasance sultane ya zabeta,ya zabeta a matsayin ranar da haisam da kansa zai gabatar da ahmad cikin iyalinsa.

"Bansan ko akwai wani shirin ba,bansan ko akwai wani tsarin ba,amma inaso kayimin alfarmar gabatar da ahmad cikin iyalinsa a karo na biyu.....a daren ranar lahadi,inaso a gaban kowa,kowa ya shaida dawowarsa......koda kuwa ka boyemin,jikina yana bani batar Ahmad tana da sila......tana kuma da dalili ba haka siddan ta faru ba.....na kasa nutsuwa muhammad,idan na kwanta fuskar ahmad yana qanqani nake hangowa". Sosai wani abu ya narke a zuciyar haisam din,yasan wannan ciwon a murya da idanun Nanay dinsa.....wannan dalilin ya sanya yakejin lokaci kamar yayi tsaho.....lokacin da zai bata albishir din safeenarta tabar wani reshe.....reshen da gata a gabanta ya kawo mata.

Haka kawai yaji yana ra'ayin monitoring gurin da kansa,amma kaman bazai iya ba saboda gajiyar dake nuqurqusarsa kwanakin. Daga ahmad har Muhammad basason yayi nisa dasu,sukan kashe Lokaci sosai tare dashi,wannan ya sanya saboda ya fara shiga tsakaninsu sosai,suke wani mugun bash in respect tamkar babban wa da kowannensu ya rasa bai samu ba.

Ya zauna gaban masarrafin cameras din,ya kuma bude kowacce shiyya,amma sai ya samu kansa da kashe kowacce camera ya miqawa abeer dake kebance a daki shi dasu beeno,ya zabi fuskar camera qwaya daya......fuskar camera da ta nan ya hangi takowarta tana isowa gurin zaman da aka tanadar musu.

Lafiyayyar atamfa ce a jikinta me wani irin kwantaccen launi mara hayaniya ko saurin jan ra'ayi,saidai kuma yadda ta kwanta a fatarta shine abu na farko da zai fara fusgar hankalinka fiye da kima.

Wani irin sassanyan kyau da karon farko idanunsa suka fara sauka akai......wani sassanyan yanayi......basaraken jikin nan saye cikin atamfar hausawa.....atamfar data zama daya daga cikin suturun da yayi research akai na yankin africa da yaji yana burgeshi sama da komai.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Atamfar dai aka warware,aka dorata daga saman daurin dankwalin kanta wanda aka matse da clip don kada ta sauka,mayafin kuma ya watsu a gadon bayanta da sample din shigar suturar ALKYABBA.

Idanunta.....labbanta.....dama fatarta dukka sunyi wani fresh......blue eyes dinnan sunyi fayau,don ba wani makeup saman kyakkyawar fuskarta sai anihin zallar madarar kyan da duk motsawar da zatayi yake magana akan kansa da madaukakin sauti.

Idanunsa ya lumshe a hankali yana jin wasu abubuwa suna spark cikin kansa,yaja boyayyen numfashi ya aje yana sake ware idanunsa daidai sanda take dab da abun zamanta. Idan har ya gani daidai kamar wadannan siraran labban sun furta

"Bismillah" Ne,sai yaji wani dadi yana sauka har qasan ransa da zuciyarsa. Siraran zara zaran fararen yatsunta da wani lalle me azabar ja ya yiwa ado me fusgar hankali ta sanya tana tattara lullubin saman kanta zuwa gaban rigarta da dinkin ya rufe komai ruf,saidai hakan bai hana bayyanar tudun qirjinta ba daya zauna dasss kaman zanashi akayi ba halitta ce cikin qirjinta ba.

Wani abu me qarfi yaji ya sauka masa.

"Me yasa ba hijab ba?" Ya yana motsa labbansa da qarfi,omar da yadanfi kusa dashi ya waiwayo da hanzari.

"Captain.......magana kakeyi?". Wadannan tsumammun idanun nasa ya daga a nutse ya zubewa omar su,kallon da ya sa ya omar janye dubansa daga kansa,bai kuma sake tankashi ba ya koma cikin hirarsu dasu naseeb.

Sake janye idon nasa yayi,yana sane ya yiwa omar irin wannan kallon,ya fuskanci tun dazun akwai wani magana ne cikin bakinsa.....ko a dazun bai shirya doguwar magana ba bare yanzun da yakejin komai yana sauka daga ainihin saitinsa daga kwanyarsa.

"Halal.....halal ce" Zuciyarsa ta fada masa a sanda yayi zooming fuskarta dab da dab. Daga nan inda yake yana iya hangen wani abu me nauyi cikin idanunta.....kamar kawai qarancin walwala saman fuskarta ta,kamar akwai abinda ke damunta can qasan ranta,hasalima wayarta na tsakanin yatsunta tana jujjuyata tana wasa da ita kawai,bata iya daga kai ta kalli mutane yadda ya kamata.

Haka kawai yaji sha'awar yayi magana da ita......a kwanakin nan aduk sanda zai tunata yana tunata ne da TAUSAYI. Ya yadda cikakkiyar marainiya ce ita gaba da baya ba tare da ita tasan marainiyar bace a karan kanta.

_smile.....its a sunnah_ abinda ya rubuta kenan ya kuma aike mata ya saqon karta kwana,sannan ya maida wayar gefansa ya ajiye yana maida kallonsa ga allon system din.

Akan idonsa saqon ya shiga. Yayi qara kadan,tayi kaman ta share,sai kuma yaga ta bude.

Reaction nata ya nuna sosai......wani irin reaction daya nuna zallar mamakinta a fili. Wadannan blue eyes din tadan bude kadan kafin ta maidasu daidai,ta sake dago wayar daidai fuskarta da alama tanason tantance number waye?.

Murmushi kawai ya subuce masa ba tare daya shirya hakan ba,yanayin sai yaji ya masa dadi. Tsokana......a tsakaninsa kawai dasu maleek irin haka take faruwa.....yau ne karon farko da tsokana ta hadashi da wani jinsi daban ba nasa ba. Wayar ya sake dauka,ya sake rubutawa a gajarce.

_smile mana please_ a wannan karon murmushinsa me sauti ne,saboda yadda yaga gaba daya ta diririce tana waige waige tana kuma sake kallon fuskar wayar tata,kafin ta tabo birra dake gefanta ta qaraso ta kuma rusuna ita kuma ta shiga nuna mata wayar birra tana kalla tana saurare.

Ya fahimci me takeson sanyata tayi sanda ta damqa mata wayar,ta koma ta zauna,saidai duk da wayar tabar hannunta yaga alamar bata nutsu ba,tanata rarraba blue eyes dinta kawai tsakanin jama'a,sai ya sake sauke murmushi yana jawo wayar ya danna Stwiched off ya kasheta gaba daya.

Sai a sannan yaji yadda parlor din ya dauki shuru,ya aro nutsuwa ya azawa fuskarsa kafin ya daga idanunsa ya bisu da kallo daya bayan daya.

Kowa kawai idanunsa yana kanshi,daga sanda yayi wannan murmushin me sauti sai ya dauki hankulansu,yadda yaci gaba da murmushi kadan kadan kuma ya qarasa kashesu gaba daya.

Yana da kirki sakewa da abokansa......amma ba kasafai zakaga yayi murmushi a jere har sau biyu haka ba.

"Lafiyanku?" Ya maze yana jefa musu tambayar

"Kai zamu tambaya captain,ko yau ka fito daga daki a daren farkonka iyakar murmushin da zaka yita yi kenan" Amjad dan kai tsaye ya fadi yana miqewa ya dauki wayarsa,don ya tabbatar tunda ya fadi wannan maganar akwai case ci gaba da zamansa a gurin.

Wani nauyi yaji ya kamashi,saidai bai bari sun fahimta ba ya bisu da tsaki,ya maida hankalinsa ga system din,yana jin kamar bayaso amma haka ya kasheta yana fadin.

"Yana daga cikin kyawun musuluncin mutum,yabar abinda babu ruwansa".

*_KOMAI NISAN DARE_*

*_KOMAI NISAN JIFA_*

*_KOMAI GIRMAN GONA........_*

*AGADEZ PALACE*

*sultane muhammad hammud meeting room*

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 14*

Saman kujerun da aka tanada cikin kebantaccen dakin ganawar na musamman. Dauke yake da Wazeer,babban alqali na jaha,wali,galadima,shugaban limamai,da shugaban malamai. Ta daya bangaren kuma tsoho ne me ran qarfe wato kakan safeena wanda shine kan zuri'ar diory hammani family a yanzu gaba daya wato mamman hamza,da 'ya'yan 'yan uwansa da a yanzu suke taka matsayin iyayensu ne a wajen mamman hamza din.

Daga bangaren sultane kuwa,yakumbo ce,sai qannanesa guda biyu da suke zaune a diffa da zinder,sai nannie sai kuma morsa safiyya da mammina dake zaune gaba kadan da morsa din cikin jin izza tare da mamakin dalilin wannan hadin da wannan kiran da sultane din yayi musu.

Kusan duk wani gaishe gaishe an kammalashi,sarkin malamai ya gabatar da addu'o'i sosai,sai shuru daya biyo baya kowa yana tattara hankalinsa ga sultane.

"Alhamdulillah......Alhamdulillah......alqawarin Allah baya tashi.....alqawarin Allah baya sauya ba,haka rabon bawa baya wuceshi,ban taba zaton wannan rana zata zo,ban taba tunanin zata riskeni ba......amma cikin hukuncin Allah bayan shekaru masu yawa da fidda rai sai gashi rabona ya dawo zuwa gareni...........muhammad,ku qaraso kaida ahmad" Sultane yayi maganan yana kallon wani guri.

Labulen dake wajen ya yaye kadan,ahmad ya fara yowa gaba,haisam na biye dashi,dukkaninsu cikin nutsuwa da kamalar data qara musu kwarjini. Shigar dake jikin almaz a yau din ta sake saka wani irin kwarjini a fuskarsa da kamala cikin halittarsa......irin wannan kwarjinin da duk wani ahalin sarauta ke dashi,a yau kamar an sauya fuskar almaz din,kamar yaune ranar farko da aka masa wanka da ruwan kwarjini irin na ainihin jini da 'yan gidan sarautar AGADEZ,kwarjinin haisam kuma sai ya sake haskashi da wani irin yanayi da ya sanya kowa zuba masa idanu.

Kamar an dauko babbar mota an jibga mata tsakiyar kanta.....kamar wadda jirgin sama ya daki tsakiyar qirjinta.....kamar wadda akayi dauka aka wujijjiga aka jefo daga saman wani dutse ko tsauni me tsananin tsaho haka taji yanayinta ya koma.

Batasan ta miqe tsaye ba har sai da suka hada idanu da haisam. Wani irin miqewa ta tsananin razana da firgici........amma kuma saita maye gurbin hakan da nuna alamun farinciki da tsananin mamaki.

"Almaz......ahmad" Tayi hanzarin gyara sunan tana soma takawa tana nufarsa.

Cak ya tsaya yana dubanta......abubuwa da yawa suna dawo masa saman kansa. Banda haisam yace kada yayi komai.....kada ya sake ya aikata komai wanda yake ba daidai ba,ba shakka ba abinda zai hanashi kwasheta da mari sannan ya kwasheta ya watsar guri guda.

Kanta tsaye ta rungumeshi tana sakin qirqirarren kukan da a zahiri yake cike da tsoro da kuma fargaba. Tsoron tonuwar asirinta......tsoron kada wani abu daban ya biyo baya......tsoron faruwar wani mummunan abu na yayewar sirrinta.
Chapter 15 · 0% Book details