← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 176

Sashe 54

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Me yasa duk yadda na dade da sultane da kowa da kowa dake cikin masarauta bana jin girman kewarsu haka a raina?. Me yasa banquntata da yawa ba daga rashinsu a kusa dani?,saishi?.....WAYE SHI?,meye na musamman a tattare dashi da kewarsa ta dara ta kowa nauyi cikin zuciyarta?.

D'isar qwallar kawai taji saman cinyarta,sai wani irin mamaki ya kasheta.

"Qwalla akhnan?,qwalla saboda kewar D'A NAMIJI?" Ta jima jikinta a sanyaye tana jin zafin abun. Me yasa ta sake masa haka da yawa?,me yasa ta bari suka saba da ganin juna da jin motsin juna?,wanne irin sakarci tayi haka?. Hannu tasa ta dauke qwallar tana gayawa kanta,har yanzu itace dai akhnan muhammad hammud.....bai kamata ta bari wani abu ya karyata ba,amma dai daga qarshe sautinsa.....qira'arsa.....karatun qur'aninsa ta kunna da qaramin sauti can qasa,shine abinda ya sama mata nutsuwar data samu yin bacci a wannan daren.

★★Duk zirga zirgar daya yini cikinta tsakanin gidan prime minister da gidan governor na jimma a yinin ranar data zama ta qarshe tun daga safiya zuwa yanzun da sararin samaniyar jimma ke bada wata lallausar iskar hadari hakan bai ture tunaninta ko sau daya daga ransa ba.

Baisan meye me qarfi da girma haka dake maqale da ita a zuciyarsa ba. Kwanaki ne da suka zame masa cikamakin kwanika masu muhimmanci wajen cika alqawari kan aikinsa. Yayi handling muhammad jinjiri ga ahalin ajani a sirrance bisa sharadin ba zasu bayyana dawowarsa cikin ahalin ba har sai ya kammala nasa aikin......ya rufe file na case din mutuwar ajani,ya miqawa gwamnatin qasar Ethiopia tamim babba tamim qarami da dukka qasurgumayen masu laifin da ake ci dasu cikin haramtaccen gidan villa street da ya salwantar dashi. Abu guda daya ya nema su daga masa qafa suyi masa alfarma shine,gurfanar da zaituna cikin asalin qasarta tushenta,wanda ya buqaci su bashi wasu watanni don komai yazo daidai da yadda ya tsara.

A yanzun aikin da ya yiwa qasar ba wata alfarma da tafi qarfin ayi masa ita.......bama wannan lokacin ba.....tun a bayan,yana da wani irin girma kima da martabar da gaba yake da alfarma kowacce iri ce,ballantana a yanzun. Ya sake samun wani girman na musamman,darajarsa ta sake ninkuwa,hakanan ya sake shiga cikin abubuwa masu tsada da darajar da qasar Ethiopia din ta mallaka.

Ya dauka ya kammala aikin a kwana biyun kawai,saidai ahalin ajani sun dora masa nauyin daya hada da moti na zuwa kebantaccen gurin da moti dinne kawai ya sanshi inda sauran kaso me girma na dukiyar ajani take.

Tafiyar tazo masa da wahala sosai,bai sani ba gajiya jikinsa ya fara yi ko kuwa?. Shi kansa ya sani,a wannan karon yayi aikin daya kamata ya daukarwa kansa da kansa hutu,ya bawa gangar jikinsa dama ta huta sosai. Kwanansu uku a gurin suka kammala komai,aka fidda dukiyar data bawa moti lambar yabo daya iya dauke wannan sirri na tsahon shekarun da amininsa ya buqata. Yawan adadin dukiyar daya gigita kowa,saidai moti ya shaida musu,akwai reshe daya daya rage da ajani ya fadawa wani cikin aminansu.

Sun zabi killace muhammad a tare dasu,ya saba dasu zuwa sanda haisam zai bada umarnin sadashi da dangin mahaifan safeena kakanninsa kenan.

A wannan yammacin da motocin alfarmar da suke zama tambarin prince sheikh muhammad haisam suke tafiya cikin wata irin nutsuwa saman kwaltar......idanunsa can qasa qasa cike da tarin gajiya......idanun da suke zube saman kwalta yana ganin yadda yanayin ya fara juyewa irin yanayin da yakeso......irin yanayin da tsirrai ke wani irin kyau,yanayin da tsirran ke fidda sabbin ganye masu daukan hankali,su kwantar da duk wata qura da ka iya damun dan adam da walwalarsa.

Lafiyayyen agogon fatar da yayi luf saman kyakkyawar fatarsa dake lullube da nu'imtacciyar gargasa ya kalla. Yamma tayi sosai.....amma zuciyarsa yaji tana karkata wani guri na daban a maimakon gida.

Wani guri ya dan danna daga seat din gabansa

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Mu wuce palace training home" Ya furta da wani nutsuwa da jan aji,jan aji da ginshirar data dadu saboda gajiya da kasalar da yakeji. Daga ta cikin abinda ya danna din aka dawo masa da amsa cikin girmamawa,da alama ya tura saqo ne zuwa ga driver din motar.

Maida idanunsa yayi kan kwaltar yana kallonta,kafin a hankali murmushi ya subuce masa,wani tattausan murmushi daya qarawa fuskarsa ajiyayyen kyau.

Ya sani.....kuma jikinsa yana bashi,zaije ya tarar da wani yanayi tabbas saman fuskarta. Abinda ita kanta bata sani ba.....abinda ya jima shi kuma da kara tarsa da kuma lura dashi shine. Ita din wata iri macace me son kulawa.....macace meson a damu da ita,wanda hakan qila ya samo asali ne daga fake love da fake caring na mammina. Wadda ta kadaita a dukkan komai,ta tattara kulawarta da damuwarta a kanta a zahiri ba tare data hadata komai da kowa ba. Ta tashi da wannan yanayin,ta saba dashi,shi yasa komai yake zuwa mata a baqo a duk sanda aka dauke kai daga lamarinta.

Da gaske yayi busy din da dukka wayoyinsa ma basa hannunsa,ya ajiyesu a killataccen guri. Amma behind hakan akwai wani TARKO da yakeso ya d'ana,akwai wani ANALYSIS da yakeso yayi.

Daga ranar da hannuwansa suka kai gangar jikinta,daga ranar da hannuwansa sukakai muhalli da guraben da bai taba zaton zasu je ba.....daga ranar ya tabbatar MUTUWA ce kadai zata iya sanyawa ya zare igiyoyin aurenshi daga kanta,koda mutuwar ma baya tunanin ta isa ta sanyashi yayi hakan. Daga ranar daya qetare iyakar da bai taba qetarewa wata mace ba sai a kanta,....daga ranar daya shiga wani yanayi da babu wata diya mace data taba ganinsa a cikin sa,koda kuwa nanay dinsa......daga wannan ranar ya dasawa kansa MALLAKA......ita din mallakinsa ce.....koda da kallo na idanu zaiyi bakin qoqarin hana kowacce halitta isa gareta ta hanyarsa.

Yana da kishi......yana da kishi sosai ya sani,wannan kishin bazai taba bari ya barwa wani ita ba. Koda baiji mafi girman soyayya a ransa ba.....amma ya raba wani sirri nasa da ita,ta ganshi cikin wani yanayi na fitar hayyaci,shi kuma bazai taba bawa wani d'a namiji hannuwansa sukai kan inda nashi hannun suka kai ba.

Idanunsa ya lumshe yana jin tunaninsa kawai na qarshe kaman an dora masa wuta saman zuciyarsa,sai kawai ya miqa hannu yana sassauta necktie din dake daure a wuyansa cikin lafiyayyar luxury suit din jikinsa da kalarta ta fidda anihin ma'anar kalmar KYAU a tattare dashi,ya maida idanunsa ga hanya sanda suka fada titin da zai sadasu kai tsaye da qofar killataccen gidan.

~Da wannan miskilar fuskartata take zaune birra na qarasa daure mata dogon gashinta a tsakiyar kanta. Fuskarta tayi wani fayau,wani irin ajiyayyen kyau na samun ninkin kulawa da wani sirrantattun abubuwa da batasan amfaninsu ba da suka ratsata. Da farko batasha saboda bai mata kama da abun al'adarta ba,amma daga qarshe zenabu ta zauna ta amintar da ita tasha cikin hikima. Kuma koda tasha din ya mata dadi a baki,ya mata kama da wani abunsha da sukanyi na al'adar buzaye,tun daga ranar bata sake musun sha ba.

A girmame aka nemi izinin shigowa sannan aka turo qofar,bata damu ta waiwaya ba,ta zubawa kanta idanu ta ciki madubi tana kallon yadda shigar kayan sukuwar dokin suka mata kyau.

Qoqarin kokawa takeyi da tunaninta da dukkanin iyakacin qarfinta......qoqarin koyawa kanta rayuwa takeyi dashi ko ya nemeta ko bai nemeta ba,shi yasa yau da yammar nan ta buqaci a shirya mata doki zata hau cikin gidan tayi sukuwa a faffadan filin wasannin ball dake cikin gidan.

Alitash ce,daya daga cikin hadimanta na cikin gidan,wanda sosai takejin dadin zama dasu kamar yadda suke dasu birra. Wasu irin bayi ne data rasa wanne irin horo aka musu haka na iya faranta ran ubangidansu da duk abinda yakeso a sanda ya dace?.

Ko a yau da tace tanason hawan dokin,ta dauka a yadda tsare tsarensu yake zasu hana,amma sai gashi tana cikin bathroom tana wanka suka shaida mata an gama shirya komai.

Zenabu ce kawai taso tadan mata gyara kan shigar da tayi. Wando ne skinny daya kama jikinta sosai,ya fidda kowanne lungu da saqo da tudu na jikinta,kamar yadda fingilalliyar rigar itama ta fidda dukiyar fulaninta kamar ka saka hannu ka cirosu,suka kuma fidda plate tummy dinta kamar bata taba sanya masa abinci ba tunda Allah ya halicceshi,saidai kuma daga baya ta sanya aka yiwa gurin tsarin da daga ita sai hadiman data zaba su shiga harta gama hawan nata,basu kuma sake cewa komai ba.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 50*

"Allah ya qara daukaka darajarki.....an kammala" Ta fada da girmamawa. Tadan juya ta kalli alitash,sai kawai suka burgeta.

"Na gode......"

"Amhara tace ko zaki fara cin wani abu?" Alitash ta fada da kulawa. Kai ta gyada a hankali,ba shakka zata iya bawa hadimai da bayin agadez maki casa'in ta cikashewa wadannan zuwa dari bisa dari. Ta fahimci zataje din,saita miqe suna mara mata baya zuwa parlor din da tafi zama cin abinci.

Falon yana cikin falukanta da tafiso a 'yan kwanakinta cikin gidan. Komai ya kasance da tsarin gargajiyar dake nuna al'adar oromia. Wasu abubuwan nasu suna burgeta,amma yadda ba wanda yace mata komai,ba wanda ya taba mata bayani,itama bata damu ta daga kanta ta tambaya ba.

Kafin ta qaraso sun saita mata takalman da zata sanya ta cire wadanda ta fito dasu a qafarta kamar yadda suka saba,ta zare wadancan ta saka wadanda suka batan,ta fara takawa a nutse tana nufar traditional royal dining table din.

Ta san abinda tafi buqata a yammacin,abinci mara nauyi,koda ta makara bataci abincin rana ba,don haka bata takurata da tambayarta me zataci ba,ta soma serving dinta.
Chapter 54 · 0% Book details