← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 176

Sashe 101

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kece bakiso....kin manta?,amma yanzun kike nemansa?" Murmushi ta saki tana cusa kanta cikin pillow din da har yanzu bar mata qamshinsa.

★Farar cotton din riga ce a jikinta me zuwa hade da hijab saqar qasar Malaysia,wadda aka yita musamman saboda gudanar da ibadar sallah.

Kallon wayarta ta sakeyi a karo na biyu da saqonsa ya shigo mata,tsoro da mamaki cakude akan fuskarta,tuni ne dai yake sake mata.

"Minti goma sun shude.....mintuna biyar suka rage idan baki fito ba.....zan shigo har ciki,zan kuma daukeki ko a gaban waye" A jikinta takejin zai iya,a jikinta takejin zai aikata,saita sauke wayar a hankali zuciyarta tana wani bugawa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 90*
_______________________
https://chat.whatsapp.com/IZGMwJXP8Oa5qUc4sDSKZv?s=cl&p=a&mlu=3

*_YI JOINING DON SAMUN DAMAN KOYAR ABUBUWA KAMAN HAKA_*

Abaya
Stone laffaya
Glitter laffaya
Stone veils
Glitter veils
Bead work
Paint work

08036027448

*_Karki bari wannan sassauqar damar ta wuceki_*
____________________________

Qarfe shida ne na safe,meye ya faru da zaice lallai saita take dokar nanay ta fito da safen can bayan sassan nanay?. Ya bari kowa ya tashi,ido na ganin ido ya shigo ganta mana?. Kafin ta sauke wannan tunanin kiransa ya shigo kai tsaye.

"Gan.....ganinan" Ta fadi muryarta tana rawa kadan. Saita zame wayar daga kunnenta tana ajiyeta. Tsoro take kada ya shigo kaman yadda ya fada,ya taho dakin kansa tsaye,taje suyi kacibus da nanay,to tace mata me?,ta kare kanta da wacce hujja?.

Slippers masu tashi ta saka bayan ta daure igiyar hijabinta a bayan kanta,wanda hakan ya bawa tudun gashinta dake boye a hijab din nunawa.

Kamar wata barauniya haka take takawa,sannu a hankali tana bude parlours da dakunan zaman baqi tana bin direction din daya gaya mata.

Har ta gama shiga da fita zuwa hanyar da zata kaita bayan sassan ba wanda ta gamu dashi,sai a qofar qarshe rumaisa ta tura tana shigowa hannunta dauke da wani file.

Baya taja da sauri tana bawa akhnan hanya fuskarta da murmushin girmamawa tadan rusuna,duk da ta girme mata kadan.

"Barka da safiya matar captain".murmushi akhnan ta qirqiro,don har ga Allah adan rude take.

"Barka kade likitarmu.....mun tashi lpy?"

"Lafiya alhamdulillah,ya gajiya,ina fatan bamu gajiyar dake ba"

"Alhamdulillah likita"

"To ma sha Allah,bari na qarasa ciki,saikin dawo" Rumaisa ta fadi tana yin gaba. Da dan mamaki akhnan tadan bita da kallo,basu da damuwa kuma basu da matsala,sanya idanu ko bin qwaqwafi. Wata rayuwa suke simple,basu matsawa rayuwar kowa ba.

Inda watace,koda bada wata manufa ba saita tambayeta ina zata je?,amma ita tayi gaba abinta tana sabgar gabanta kawai.

Maida qofar tayi tana ficewa tare da qoqarin bin hanyar daidai.

Komai fari ne a jikinsa,tun daga kan jallabiyyar jikinsa har xuwa thobe din dake matsayin kamar after dress daya dora saman jallabiyyar. Hakanan takalmin qafarsa.....da amam din daya dora(rawani),wanda ya masa wani irin nad'i dake nuna zallar qwarewa wajen sarrafa daurin rawani saman kai.

Ya fita fes.......sak matashin yariman malamin nan da duniya keyi dashi. Ilimi.....kyau sarauta da dukiya gaba daya. Qamshinsa kawai ke kai kawo a gurin da wani tattausan yanayi daya saje da safiyar ranar,safiyar da ba wata wadatacciyar alamun samun rana a wunin gaba daya,saboda yadda hadari ke lullube da ko ina.

Idanunsa ya zube fes a kanta,idanun nasa suna lumshe kansu suna kuma budewa.

Farar fata cikin fararen kaya,wani mugun kyau tayi masa,tamkar sabon fure daya fita a ranar,aka samu arashi kuma wadataccen ruwan sama ya sauka a ranar.

Wani irin abu yakeji yana fusgarsa zuwa gareta......kyawawan blue eyes din nan nata da suke juyawa a hankali,da alama tanason hango inda yake tsaye.

_ki taimakeni karki fadi.....idan kika fadi har cikin zuciyata ciwon zai kasance......ki kalli gabanki_

Saqon daya shigo wayarta kenan,idanunta ta daga a hankali bayan ta gama karanta saqon tana miqar da kallonta zuwa gabanta.

Yana jingine da wata farar mota qwaya daya,kansa da idanunsa dukka suna kan wayarsa. Ta lumshe idonta tana hadiye wani abu a hankali.

"Ya hadu" Ta fada can qasan maqoshinta tana motsa labbanta a hankali. Karo na farko da idanunta ya taba sauka akan wani d'a namiji taji ya wuce da dukka numfashinta da nutsuwarta. HAISAM.....wani namiji da yasha wucewa da numfashinta.....tunaninta......nutsuwarta dama komai nata. HAISAM d'a namiji a duniya na farko daya taba mallakar tunaninta da zuciyarta,daga qarshe ma ya mallaki gangar jikinta gaba daya......itakam ta yaya zata iya rayuwa ba tare dashi ba?.

A iya jiya kadai ta fadawa kanta wannan maganar har batasan adadi ba. Rashinsa a kusa da ita kawai ya sanya baccinta ya zama wani iri......ina ga ranar da zata bude idanu ta tsinci babu shi?.

Wannan JAN AJIN nasa......da wannan basarwar tasa yabar kansa saman wayarsa Kamar ba shine ya hangota yayi directing nata zuwa inda yake tsaye ba.

Sai zuciyarta ta soma motsawa da wannan kalar kishin nasa. Kishinta a yau akan wayarsa yake,karo na farko data fara jin tana kishin wayarsa sosai kamar d'an adam.

Yasan ta taho....me yasa bazai bar kallon wayarsa ya kalleta ba?. Tambabayar data qaraso da ita gabansa kenan,saidai tabar tazarar taku kusan biyar tsakaninsu.

"Ina kwana?" Ta furta a hankali daya daga cikin lectures na nanay suna mata tasiri ciki tunaninta.

Dukka juriyarsa ce ta qare,ya cire kansa daga wayar ya zube mata narkakkun idanun nan,wadanda da qyar suka samu bacci a daren jiya saboda matsananciyar kewarta. Baije gareta ba,saboda yanaso ya yiwa kansa control......yanaso ya barta ta huta,yanaso ta dawo nutsuwarta ta rage tsoron daya yake gani nasa a idanunta.

Kamar wanda abinda ya kawoshi kenan kawai shine kallonta,ya tsareta da lumsassun idanunsa wanda idan kana dan nesa kadan dashi zaka dauka a rufe suke ruf,saboda yadda sukayi laushi sosai,sannan eyelashes dinsa suka sake taimakawa wajen yiwa idanun nasa rumfa.

Ji yayi kowacce kalma ta maqale a maqoshinsa,bazai iya amsa mata ba,sai kawai ya matsa daga jikin motar ya bude murfin ya juya ya mata alama da idanu na ta shiga.

Motar ta kalla sannan ta kalleshi da tambaya fal idanunta,idonsa ya lumshe mata yana girgiza mata kai alamun bayason tace komai,saita hadiyi wani yawu a hankali ta tattara qwarin gwiwarta tunaninta yanason canko mata abinda yake shirin yi

"Wannan fa kamar laifi ne" Ta fada blue eyes dinta suna tara qyallin hawayen tsoro.

Ya gani.....yaga komai dake idanunta. Ya karanci kamar sun hada baki ita da nanay ne sunason wahalar dashi,sai ya soma takawa majestically yana nufarta,bai kuma tsaya ba,sai daya cike duk wata tazara dake tsakaninsu. Qugunta ya riqe sosai ta cikin tattausan tafin hannunsa yana sake jawota gabansa sosai

Kansa yake qoqarin saukewa saitin wuyanta sanda yake bata amsa da wata kasalalliyar murya

"Noooo....." Ya fada yana sauke mata muryar da nauyi cikin kunnenta.

"It's called rescuing my wife" Ya fada yana daukarta cak yana rabata da qasa tamkar ya samu 'yar tsana.

Ta tsorata da hakan,saboda abinda bata zata bane,suata qanqameshi sosai tana riqe wuyansa. Blue eyes dinta a waje sosai,wannan sassanyan qamshin nasa yana tururuwar shige mata hanci.

"Shi bayajin kunya?,baya tsoro kowa ya gansu?,a haka?,a tsakiyar masarautar?".

"Nanay zata...." Ta fadi sanda ya bude motar yasa qafarsa yana qara bude murfin motar sosai ya kuma sakata cikin motar kamar qaramar yarinya,saidai yadda ya zube mata narkakkun idanun nan nasa ya sanya ta kasa qarasawa.

"She'll forgive us eventually....." Ya amsa mata da yaren French da a yau taji ya sake taushi cikin harshensa.

Sukunyawa yayi ya bata wani soft kiss,ta lumshe idanunta tana jin sanyin labbansa akan goshinta. Ta kasa bude idanun tayi shuru tana sauraren yadda zuciyarta ke bugawa cikin nutsuwa,har zuwa sanda ya rufe murfin motar,taji shuru nadan sakanni sannan ta jishi ya shigo gefanta.

"Mu tafi" Ya fada da muryar umarni cikin yaren oromo.

"Ina zai kaimu"? Ta tambayi kanta a nutse sanda take bude idanunta lokacin da taji wannan tattausan tafin hannun nasa cikin nata.

Ya sauke wani abu a kowanne sashe na jikinta,wani irin dumi da tafin hannunsa ke dashi.....wani irin laushi da tasha tambayar kanta.

"Dukka maza haka tafin hannunsu yake?,ko nashi ne haka?"

Kansa taji ya kwantar a hankali saman kafadarta,da wani irin yanayi na shagwaba da narkewa.

"Good morning my princess......." Ya fada yana matse tafin hannun nata a cikin nasa ba tare daya qarasa fadin abinda yaso ya fada din ba,yana jin wani yanayi yana mamayar jikinsa a hankali.

"......Good morning to the woman currently occupying most of my thoughts" Ya sake fada da wani irin taushi yana saka hannunsa ta baya ya zagaye qugunta.

"Morning" Ta fada tana jin yadda harshenta da muryarta suke sarqewa gaba daya. Wani irin kusanci yake bata......wani irin kusanci yake kawowa tsakaninsu da takejin ba zata jure ba. Batason ta sake wani abu da zata bada kanta irin wanda tayi daren shekaran jiya.

"Ina zamuje?banaso nayi nisa" Ta tambayeshi kai tsaye tana jin fargaba kadan.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Murmushi ya sake kawai,sai ya zame ya maida kansa saman cinyarta,ya kwanta rigingine yadda zai samu damar kallon kyakkyawar fuskarta data fito da wata irin kamala ta tsakiyar hijabin,wanda daga qeya acucin da tayi da tudun gashinta ya fito sosai.

Hannunsa ya miqa a hankali ya shafi gefan fuskarta data masa kyau sosai,kaman dazun idanunsa suna lumshewa sannan su bude da kansu. Wani irin murmushi.......classy murmushi da bata taba ganinsa saman fuskarsa bane yake fita akan fuskartasa a yanzu.

"Ina zamuje?" Ta sake maimaitawa tana qoqarin riqe hannunta da a yanzu ya sanya yatsarsa yana zagaya siraran labbanta.

"Wata duniya......" Sai ya dakata kamar me jiran wani abu.

"......inda daga ni saike"

"Hh.....hais" Saita gaza qarasawa ganin yadda ya zubawa labbanta idanu. Ta tuna....sunansa duk sanda zata furta kamar yana kunna wani emotions ne cikin kansa,saita yanke kiran sunan. Da wanne suna zata kirashi ne?,wanda bazai tayar da wata fitina ba?.

Murmushi ya kuma kasheta dashi,wannan soft dangerous smile din nasa kafin ya sake motsa labbansa.
Chapter 101 · 0% Book details