← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 176

Sashe 129

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma me yasa?,me ya sauyata?,me ya birkitata ta zama cikakkiyar maqiyiya kuma abokiyar gabar sultane iyalinsa dama masarautar agadez gaba daya?" Ta yiwa falaak tambayar wadda ke kwance a gabanta saboda jirin daya kusa kayar da ita

Da idanu kawai take kallon Akhnan,tana jin zuciyarta tana bushewa. Sai yau idanun Akhnan suka fara budewa tarwai kenan take kallon ainihin siffa da kamannin matar?,abinda yake yawo kenan cikin kan falaak wadda kanta ke kwance saman cinyar hairaan dake share hawaye tun dazun ta kasa ma magana.

A fusace ta miqe,ta gaji,tana buqatar yiwa mammina wadannan tambayoyin kai tsaye. Tana buqatar ganinta ido da ido,taji meye manufarta......meye matsayarta?,meye dalilinta na hargitsawa da dagula duk wani abu me kyau da sultane ya bari. Tarihi....Kyakkyawan mulki da kyakkyawar mu'amala.

Basu dakatar da ita ba.....hakanan kan hanya ba wanda ya dakatar da ita. Har haisam dake takowa zuwa bangarensu don bai shigo ba tun sanda zaman ya tashi,shima baga ganshi ba,idanunta ya riga ya rufe. Shima bai tsaidata ba,duk da baisan inda ta nufa ba,sai da yaga tana dosar shiyyar private chamber d'in Mammina.

Da idanu yakewa guard din dake hanya umarni,haka suka dinga matsa mata salin alin ba tare da cikas ko kallonta ba. Guard's din da mammina din ke ganin ta gama mallakarsu da dukka ayyukansu.

Qofar ta bud'e da qarfi. Mammina dake zaune cikin nutsuwa da annashuwa da wani golden cup a hannunta ta daga idanunta tana kallon Akhnan din,ba tare data motsa ba.....saidai can qasan ranta tana tambayar kanta abinda ya kawo yarinyar. Ba ita take tsammanin gani ba.....haisam taketa lissafin sanda zai tattaki ya sameta don nemawa mutanensa sassauci.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 117*
__________________________
✨ AMINTACCEN GURIN SIYAN THRIFT ABAYAS ✨
Ingantattun Thrift Abayas masu kyau da tsari akan farashi mai sauƙi da araha.
Muna kawo sababbin kaya akai-akai tare da rangwame na musamman.
🤍 Dukka sai a MK ABAYA BOUTIQUE 🤍
Duniyar Thrift Abayas masu kyau, masu tsari, da salo iri-iri domin kowane lokaci da kowane irin event.
Abayas masu inganci, masu salo, masu araha, kuma na zamani ga mata masu son ƙawata kamanninsu cikin kamala da kamun kai.
Karki bari a ba ki labari... Leƙo ki ga yadda MK ABAYA BOUTIQUE kullum ke cike da kyawawan Thrift Abayas akan farashi mai kama da kyauta.
'YAN SARI, 'YAN REPOSTING, DA MASU SIYA DON AMFANIN KANSU... DUKA INA MUKU MARABA! 🤝🤍
📱 WhatsApp: 07064399623
📞 Call: 08036027448
🔗 Join our Wholesalers Group:
https://chat.whatsapp.com/JBg80RmA47v7GoqvWdgLJT?s=cl&p=a&mlu=3
_________________________

“Me yasa?!” ta jefawa mammina tambayar tana kallon qwayar idanunta da wani irin zuzzurfan kallo da bata taba ganin irinsa cikin idanun Akhnan din ba.

“MEYASA kike mana haka?!” sai mammina ta d'ago idanunta a hankali.

“Ki rage murya.” ta fada cikin nuna isa da taqama.

“morsa safiyya fa?,me ta miki?" hawaye suka gangaro mata.

“Ahmad fa?,shima me ya miki?" Ta fadi tana samun tabbacin akwai dalilinta na shirya musu haka.

Takawa ta sakeyi,ta qarasa kusa da ita tana jin zuciyarta tana tsatstsagewar,fushi da kokwanto suna rinjayarta.

“Ke ce kika raineni…” sai muryarta ta fara karyewa.

“Ke ce kika bani kulawa…”

“Me ya sauya yanzu?!”

Shuruuuuuu......mammina ta zuba mata ido na wasu seconds. Sannan ta saki dariya.
Not warm laughter. Wata baqar dariya da tayi qaramar amsa kuwwa cikin dakin,wata dariya data kusa fasa zuciya da kwanyar Akhnan.

Akhnan din ta tsaya cak,saboda bata tab'a jin dariya haka daga gareta ba.

“Sauyawa?” ta jefawa Akhnan tambayar,tana mata wani qasqantaccen kallo still dariyarta kuma bata tsaya ba.

“Akhnan…” ta kira sunanta,sai ta ajiye cup d'in hannunta a hankali.

“Kin rayu cikin qarya ne shekaru da yawa.” ta fada idanunta kai tsaye cikin nata tana zurfafa kallonta a kanta.

“…Me?” Akhnan ta fada tana jin tunaninta yana girgiza.

Miqewa mammina tayi a hankali,ta qaraso kusa da ita.
Idanunta cike da wani irin tsohon qunci......kwadayin d'aukar fansa da tsumammen rashin imani.

“Kin tab'a tambayar kanki…” sai tayi qasa da muryarta.

“…me yasa na d'auke ki bayan mutuwar uwarki?”. Da Akhnan zata iya tabbas data girgiza mata kai alamun aah.....amma saita zabi ci gaba da kallonta kawai.

"Banyi saboda Allah ba.....saboda ni ban iya abu bati siddan ba....ban kuma iya abu na jira Allah ya biyani ba,nafi ganewa duka d'auka,nayi a take.....na samu sakamakon alfanun a take" Sai ta dakata tana sauke numfashi.

“sannan banyi ba saboda wani INA SONKI BA.....ban taba sonki ba Akhnan,koda na qasa da second daya!" Akhnan ta ji wani abu ya tsaya mata a qirji da wani irin nauyi kaman tana shirin faduwa,har sai data dafe wani table.

“…Mammina?” ta kira sunanta muryarta na fita da qyar tana rawa kaman mejin sanyi.

Sai Mammina ta matso kusa sosai.

“Na raineki ne…” ta fada idanunta suna sake qanqancewa da wani irin duhu.

“…saboda in tunasar da ita ta taba qwace a duniya......saboda a sanda take kwance a kabarinta ta tuna akwai wadda ta taba qwacewa abu duniya.....na raineki ne don na dauki fansa.....na aura miki dan uwanki almaz.....ahmad a yanzu bayan na saceshi da quruciyarsa.......na raineki ne don ko sanda tana ramin kabarinta kada ta huta......ko sanda tana ramin kabarinta ta d'an d'ani baqincikin da bazata iya tarewa 'ya'yanta ba......shi yasa na raineki da qiyayayar safiyya,don kada ta zama silar tsiranki” ta dakata tana maida numfashi. Wadannan maganganun data dade da binnesu tana binta da murmushin fake qauna,tana jin a yau ta shirya furzar mata dasu kafin takai rayuwarta mahallaka. Kamar zararriya haka akhnan ta zaro ido,tana jin kamar kowacce gaba dake jikinta ba'a jikin nata take ba. Tana jin kamar hauka ta fara kwanyarta ta samu damuwa shi yasa take rattabo mata wadannan bayanan.

“Uwarki.” ta fada da d'aci sosai a muryarta da bai boyu ba

“itace mace ta farko da wasu 'ya'ya maza har biyu suka sota kafin ni......ajani.....sannan kuma sultane.....ita kadai ta kafamin wannan tarihin da har na mutu bazai goge ba!."

Wani irin sanyi ya ratsa Akhnan. Qafafuwanta suka kasa motsi tana fatan wani ya tasheta a wannan mafarkin.

"Guraben da nake muradin mallaka......ita ta qwacesu ta mallakesu.” ta fada da muryar dake nuna tsohon ciwo.....tsohon miki ya tashi.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

“ta bashi 'ya'ya......ba d'aya ba.....ba biyu ba kafin na bashi koda rabin mutum....ke koda b'ari ne......sannan safiyya tazo ta sake laftamin wani ciwon ta hanyar bashi falaak?.” Akhnan ta soma girgiza kai,wasu iri hawaye da basu da misali.....hawayen da baka isa kayi controlling d'insu ba suka soma mata ambaliya.

“A'ah…” ta fada tana girgiza kai,tana jin kanta bazai d'auki wannan abun ba,kamar zaiyi tsawa.

"Eh!" Mammina ta fada da qarfi ta yadda zai isa kunnuwanta da kyau. Burinta ta qara hargitsewa ta yadda hakan zai sanadin haukacewarta gaba daya

“NA TSANETA!.” Sai ta sunkuyar da kanta kusa da Akhnan.

“lokacin data mutu…”

“ban so mata mutuwa ba a sannan......naso ta qare rayuwarta tana raye amma tana kallon yadda rayuwar d'iyarta take d'ai d'aicewa....bansan ma ya akayi rayuwarki ta tsaya a haka ba!....bansan waye ya tsaya miki ba!….” ta fada da qaraji kaman zata yage maqogoronta.

"Allah" Amsar da zaiso bata kenan.....amma ya zabi yaci gaba da tsaiwa behind the curtains and doors indai batayi yunqurin taba mata lafiya ba.

Akhnan ta ja baya da sauri kamar an mareta numfashinta ya rikice,kalaman sun mata nauyi da yawa.

“me kike cewa?....kinsan me kike cewa?."

Mammina kai tsaye da kallon nan tsirararsa ta zuba mata idanu .

"Ke ba 'yata bace!.....har abada!"

"Ke alama ce kawai ta tozarcin safeena a gareni!"

Akhnan ta soma girgiza kai cikin kuka. Gaba daya tana jin an dawo da quruciyarta yanzu tana rushewa daya bayan daya. Kowacce runguma?,kowacce nuna qauna?,kowacce kulawa?,kowanne murmushi?,kowacce soyayya fake ce?!.....jabu ce?!.....ba gaskiya bace?!.

“kinyimin qarya.....”

“ta shekaru da dama...…”

"Qwarai.....kuma na tsallake ba" Ta fada da iszgili a muryarta.
Sai ta juya baya a hankali

"Soyayya ba ita ke tafi da masarauta ba........power ce!" Ta fada tana watsa mata wani kallo.

"Kina zaton soyayyar malamin can zata kubutar dake.....kina tsammanin d'an gidan ibraheem zai zame miki garkuwa?" Ta tambaya wata dariya na bayyana saman fuskarta.

"Kina ganin kin tsallake duk shirina a kanki?,.....ba zaki tsira ba Akhnan.....baki da gata a yanzu....baki da wanda ya tsaya miki.....sai yadda naga daman juya akalar rayuwarki".

Hannayensa ya dunqule,yana qoqarin hana kansa afkawa chamber din,da qyar ya dawo da control dinsa.

Akhnan tayi wata irin tsaiwa a wurin kamar wadda aka cirewa numfashi,wani irin ringing
Kunnuwanta sukeyi kamar masu shirin kurumcewa. Zuciyarta na bugawa kamar wadda ke shirin kamuwa da ciwon zuciya.

“Kin san me yafi bani dariya?” ta tambayeta ba tare da ta juyo ba

“Yadda kika dinga kallona da idon soyayya shekaru.” kalaman suka fita da sautin qaramar dariya a muryar mammina din.

*_wai wai wai.😭😂.....lallai.....mara kunya yaji dadinsa. Ya Allah ka rabamu da makantar zuci.....kasa mufi qarfin zukatanmu_*

*_muje zuwa dai....saimun warware zaren duka in sha Allah_*😭😭

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*
Chapter 129 · 0% Book details