Sashe 34
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ha......haisammmm" Da wani irin sanyi kalmar ta fita a bakinta,sanyin daya sauka cikin kunnuwansa ya sake raunana qarfinsa gaba daya,sai ya zabu sulalewa shi da ita duka suka zube a qasa. Saidai har yanzu fuskarsa tana saman kafadarta,rungumar yakejin kadai yake da ikon yi mata. Bazai taba yin komai da zai zama tilas ko tursasawa ba......kaman ma bai shiryawa wannan abun kai tsaye ba,amma wannan yanayin daya kunnu a dukka ilahirin jikinsa ya mantar dashi komai.
Shuru ne ya gifta a tsakaninsu,wani irin shuru daya wuce da komai daya faru,shurun daya sake samar masa da wata kyakkyawar nutsuwa da ya jima bai samu irinta ba.
A hankali ya zameta daga jikinsa ya miqe yana jin kamar kansa ya masa nauyi sosai,hakanan qafafunsa sunyi wani irin laushi,kasala yakeji irin wadda bai taba jin irinta ba,so samu yayi koda iya alwala ya koma saman gadon ya kwanta ko yanayinsa zai daidaita.
"Ki shirya kafin nayi wanka" Kawai ya fada yana nufar bathroom da wani irin taku da bata taba gani a tattare dashi ba.
Da qyar itama takai kanta daki,kunya nauyi da wani irin yanayi da takeji a jikinta suka mamayeta. Zuciyarta ta buga sosai sanda ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta. Ashe a haka ta fita?. Ba Brazzier?.....ba dankwali bare mayafi?. Sai yanzu ta gane......sai yanzu ta gane silar komai. Ta manta a haka ta fita......saita miqa yatsanta saman lips dinta tana zagayawa a hankali. Komai yana dawo mata......yadda yayi matan.......yadda ya shigar da bakinta gaba daya cikin nasa kamar zai cinyeshi.......yadda yayi mata wani irin riqo kamar zata karye.......wani yanayi daya shiga daya dimautata........yanayinsa na qarshe da bata fahimci komai a kansa ba
"Innalillahi" Ta fada tana jin wata kunya da tunda tazo duniya bata taba jin irinta ba. Ta maida dubanta ga qirjinta,suna nan a tsaye kaman masu gasar nuna kansu,kowanne kana iya ganinsa a muhallinsa daban.
"Na shiga uku" Ta sake fada tana waro ido,a haka shima ya gansu?,a haka ya matseta cikin jikinsa?,sai idanunta suka fara tara ruwan hawaye. Tana jin kamar ba zata iya sake hada idanu dashi ba har abada. A ranta takeji shima d'an duniya ne.......haka yake amma sultane yake yabonsa?,haka yake amma ya sani yake sauke idanunsa baya kallon kowa?,ashe haka halinsa yake?.
Tunda take ba wani d'a namiji daya taba riqe koda yatsarta ne ballantana hannunta saishi,a yanzun sai takejin kamar wani babban zunubi ta aikata. Ruwa ta sakarwa kanta sosai tana sauke ajiyar zuciya,sai data jiqe jalaf sannan ta saka soso da shower gel dinta ta soma wanke jikinta duk inda taxo saita tambayi kanta ya taba nan?,qila yaji nan gurin.....nanma ya taba?,sai da falaak ta fado mata a rai sannan ta qara hanzarin qarasa wankan nata.
Ya jima sosai ruwa yana dukan jikinsa kafin ya soma wankan ibada. Ajiyar zuciya kawai yake saukewa a jejjere kamar yaron da yasha kuka ya qoshi.
Ko bayan daya fito tsaye yayi gaban mirror yana duban kansa da kansa.
"Alhamdulillah" Ya furta yana motsa labbansa gami da cusa yatsunsa cikin sumarsa. Sake maimaita hamdalarsa yayi. Yana godewa Allah da komai yazo masa in halal way.......yana godewa Allah daya kasance bai taba irin wannan cudayyar da wata mace ba tunda yake a rayuwarsa sai yanxu.... Koma meye halal dinsa ce......ko auren meye dai halal dinsa ce.....mallakinsa ce. Sake duban kansa yake komai yana dawo masa cikin kansa,lallai Allah shine sarki buwayi gagara misali. Lallai Allah ya gama da dan adam. Haka abun yake?,shine abinda yake juyawa cikin kansa kawai,iya haka kawai?,sharar fage?,ya maimaita cikin kansa,sai murmushin da bai shiryawa ba ya subuce masa.
Ya godewa Allah daya sanya sirri tsakanin ma'aurata,yayi imanin inda abune da kowa yake gani yau kawai.....a iya haka saisu khadeem sunyi yaga yaga da namansa.
"Maleek fa?" Sai wani murmushin ya subuce masa a hankali. A dazun da ya kirashi yana tsakiyar bacci ne,kuma yadda maleek ke magana ya dago aika aikar da yayi. Haushi ya bashi sosai,kuma har yakai mata wayar a wuya yake da maleek din,da burin sai ya masa kaca kaca......amma zuwa yanzun sai yakejin me zaiwa maleek?,mai zaice masa?. Wani yanayi ne daya tabbatar ba wanda ya isa ya cika baki yace zai iya mallakar kansa. A iya haka bai mallaki kansa ba.....baisan ya zata kasance ba idan yakai matakin maleek.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 32*
Kaiwa nan gurin a tunaninsa ya tilasta masa kai tafin hannunsa saman sumarsa ya shafeta a hankali wani murmushin yana sake qwace masa,daya duba lokaci kuma sai yayi gaggawar watsar da tunanin ya jawo lotion dinsa ya fara shafawa. Yanajin wani sakayau cikin zuciyarsa da ruhinsa har ma da gangar jikinsa.
Moroccan jallabiyya ya saka fara qal da aka yiwa adon golden zare. Zaka rantse da Allah wani ado na musamman yayi saboda yadda rigar ta zauna masa ajiki ta haskashi ta masa wani irin kyau. Da sassanyan qamshin nan nasa ya zura wasu fararen flip flops sannan ya maida wayarsa aljihu ya fito a nutse.
Yana rufe qofan dakin tana fitowa daga cikin dakin itama. Kaman hadin baki ko ra'ayinsu ne yazo daya?. Farar abaya ce a jikinta,ta nade kanta tsaf da mayafin abayan daya kasance yalwatacce ne. Kasancewar abayar fara bai rage koda digo daya na kyan data mata ba,duk da bame duhun kala bace. Fuskarta tayi wani fayau da haske,kaman an sauya mode nata ko wani abu dake tattare da ita tsakanin mintunan da suka rabu kadai.
Idanunsa zube akan fuskarta,duka hannayensa suna cikin aljihun jallabiyyan jikinsa,saidai ko sau daya taqi yarda ta kalli ko sashen da yake ma bareshi kanshi. Zuciyarta har yanzu bugawa takeyi,wani tsoronsa takeji yana shigarta,wani kallo na daban take masa yanzu.
"Shima ashe haka yake?" Abinda kawai take nanatawa kenan a ranta,don haka ta zabi fara yin gaba duk da tana jin dukkanin idanunsa akan jikinta.
Gefan mayafinta taji an riqe,an kuma jawota baya kadan,ta tsaya cak qirjinta yana ci gaba da bugawa,saidai taqi yarda ta waiwaya.
"Ki jirani" Ya fada da wani soft tone sannan ya taka zuwa gaban fridge ya ciro gorar ruwa mara sanyi ya cika cup ya shanye. Baisan me yasa da kallonta kawai sai yaji maqoshinsa yana bushewa ba,numfashinsa kuma yana nauyi kadan kadan ba.
"Muje" Ya fada yana tsaye daga bayanta kamar wanda aka bawa aikin kula da duk wani motsinta dama fitar numfashinta.
Batasan sau nawa yake canza side daga hagunta zuwa damanta ba. Yana hagunta sai ta tsinceshi a damanta,kamar wanda yakejin kariyar da yake bata tayi kadan.
Haka kawai yakejin kamar kowa ma kallonta yakeyi,kamar kowa idanunsa yana kanta. Baisan me ya sanya wannan kishin ya qaru a qirjinsa ba,kawai tsaiwarsa a bangare guda yana jin bata gamsar dashi ba.
Kamar kowanne lokaci,yanayin na dabanne...... Kusan ko ina ba wani baqon abu bane masoya ne riqe da hannun juna suka kai kawo. Shuru ya ratsa tsakaninsu,shurun daya musu jagora,ya sanya zukatansu tunani mabanbanta. Wani nauyi takeji sosai duk sanda zasu daga taku su sauke tare,wani iri takeji duk sanda taga ya juya ya kalleta sannna ya kauda kai. KUNYA......a yau tasan ainihin zahirin ma'anarta......haka kunya take da nauyi?,duk yadda kallonsa ya zame mata kusan dabi'a a yau dai ba zata iya hada idanu dashi ba. To amma shi daga mode dinsa kansa tsaye yake takunsa kamar komai bai faru ba.
Idan ta tuna yadda ya ganta tana jin kamar ta nutse a qasa......tana jin me yasa ta fito?. Idan yadda ya sakata a jikinta ya dawo mata sai taji wani qaramin spark yana tashi cikin jiki da kwanyarta. A tsorace take,mugun tsoron da ba komai take ganewa ba,amma a sanda ya sanyata tsakiyar wannan qirjin.....faffadan kafadar da ta dade da sanin qarfinta......ta kuma dade da zame mata garkuwa game da abubuwa da dama sai da aka sanar da ita shigarta cikin wani sabuwar GARKUWA da bata taba shiga ba a rayuwarta.
Swissotel suka isa,sai a sannan ta tuna da iffah. Ta kirata bayan nan har sau biyu sun gaisa,amma basu sake haduwa ba. Batasan me ya faru ba,itadai taji ya cusa zaratan dogayen yatsun nan nasa cikin siraran yatsunta ya kuma hade tafin hannunsu guri daya.
"Welcome sir" Abinda ta dinga ji kenan daga bakin ma'aikatan hotel din,tun daga reception har suka kai qofar dakin data shima daya daga cikin manyan suits ne irin nasu,saboda tsarin gurin da komai na dabanne.
"Welcome sir" Kalman ya sake maimaituwa a kanta. Wani tsananin mamakin yana sake ninketa. Wato tayi kuskure......tayi kuma underestimating matsayinsa kenan?.....tunda tunaninta ma ya tsaya ne kawai a raffles makkah palace kadai yake da wannan girmamawar?,abun har swissotel ma?.....abun har askar na bakin haram.....WAYE SHI WANNAN MUTUMIN? Ta sake tambayar kanta daidai sanda taji tsoronsa yana sake shigarta,saita yanke zame hannunta cikin nasa tana daga idanunta tare da masa duban rashin yarda.
Sake matse hannun nata yayi,sannan ya daga idanunsa a hankali ya zube mata,qwayar idanunsu suka gauraya guri daya.
"Waye kai" Ta motsa labbanta zuciyarta na bugawa ta jefa masa tambayar. Ido kawai ya zuba mata kamar baya fahimtar yaren da take magana dashi,sai kuma wannan murmushin da yake narkar da kowacce jijiya dake riqe da zuciyarta ya subuce masa,sannan ya kauda kansa a hankali daidai sanda maleek ke bude qofan dakin.
Dole ta janye dubanta ta maida kan maleek din,sai taga yaqi kallonta,idonsa akan haisam.
"Fito" Haisam ya furta a nutse yana watsawa maleek idanunsa. Yayi kuma maganar ne ba tare da yabar maleek yace komai ba
"Am....amma tana ciki....."
"Muna iya komawa ni da ita?" Ya fada yana nuna akhnan da yatsarsa.