← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 176

Sashe 52

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To in sha Allah" Ya amsa masa a girmame. Wayar ya katse,sannan ya miqe a nutse ya wuce bathroom,ya tsarkake kansa ya hado da alwala ya dawo,ya tsane jikinsa sosai,wannan gargasar data lullube ko ina na jikinsa. Ya shirya kansa cikin silk Moroccan jubah,fara qal me adon golden din zare. Wani irin kyau yayi.....ajiyayyen kyau da zaka dauka wani ado yayi bawai jallabiyya bace a jikinsa. Ya sani nanay yanzu haka tana can tana jiransa,don haka ya zura flip-flops masu taushi farare ya dauki wayarsa ya soma fita a dakin,qamshinsa yana tsayawa a duk inda ya gifta tamkar bai wuce ba. Kan hanya ya kira ahmad,yana tafiya da nutsuwar nan dake sake nuna kwarjininsa.

"Ya yanayin sultane?.....ya komai yake tafiya a masarauta?" Haisam ya fadi yana bada hankalinsa ga ahmad.

"Jikinsa yana nan kamar yadda yake......ba wani ci gaba a yanayin farfadowarsa da kuma komawarsa dogon baccinsa". Kai haisam ya gyada a nutse.

"Ka nutsu ahmad da kyau......karka karkata damuwarka da sanya idanunka akan ciwon sultane kadai.....a yanzu tarkon da kake ciki yafi wanda sultane yake ciki......ba wanda ya isa ya yiwa sultane komai a yanxu.....kai din kaine abun hari......kaine abu mafi sauqin da za'a cimma,tabaka kawai yana nufin taba ran sultane ne gaba daya"

"Bani shawara....." Ahmad ya furta. A duk sanda zaiyi magana da haisam,duk yadda yakai ga sarewa,duk yadda yakai ga mutuwar jiki da rasa fata da buri......maganganun haisam kawai suna gina wannan da gini me qarko a zuciyarsa. Yana gina masa JARUMTA.......yana gina masa YAQINI har sama da yadda yake dashi a baya.

"Banason tasan komai......banason tasan rashin lafiyarsa.....duk wanda zai iya gaya mata inaso ka shaida masa abinda nace"

"Idan da bamu hadu dakai a rayuwa ba......da yanzun a wanne mataki.muke?" Ahmad ya fada a sanyaye da wani yanayi daya sanya wani irin tausayinsa shida Akhnan samun muhallin zama na sosai cikin zuciyarsa.

"Ba azzalumai bane ku,koda babu ni Allah bazai bari ku tozarta ba" Yayi furucin da wani yanayi daya sake sanyawa ahmad nutsuwa me tarin yawa a zuciyarsa.

~Dukkanin magungunan da tasha da allurai bata ji ko guda daya da yayi mata aiki ba. Bata kuma saka ran zaiyi mata aikin,saboda ba maganin daya kamata su bata kenan ba.

Ba wanda bai shigo ya mata sannu ba.......ba wanda bai nuna kulawarsa a kanta ba,amma sai takejin wannan kulawar da komai ma sunyi mata kadan. Abinda take gani saman fuskokinsu ke sake daga hankalinta. Kowaccensu daidai da noorah auta cikin walwalarsu suke,walwalat data tabbatar tana da nasaba da isowar matar captain obbo,ta sake tabbatar da hakan kuma sanda ta fito daukan ruwa mara sanyi babban parlour din,ta samesu dukkansu wasu saman sofas wasu zaune a qasa suna sake tattauna maganarta da gagarumar walimar da zasu shirya ranar data fito daga gidan koyon rayuwa da al'adun masarauta.

Da qyar ta maida kanta daki,bata kuma sake fitowa daukan ruwan ba sai a yanzu. A daddafe take takawa saboda matsanancin ciwon da kanta yake mata,gabanta ya yanke ya fadi sanda hancinta ya fara jiyo mata wannan qamshin.

Shi kadai yake da irin wannan qamshin a duk fadin duniya cikin mutanen data sani......cikin mutanen da take mu'amala dasu. Qamshinsa na dabanne,don haka wanzuwarsa a guri ma ta zama ta daban,kamar yadda koda ya iso guri komai nasa yake banbanta dana kowa. Zataso qafafunta su bata hadin kai tayi gaggawar barin gurin kafin ya iso,amma zuciyarta ta jefawa qafafunta umarnin da har ya iso gurin ta kasa tabuka komai.

Bai lura da ita ba,har sai daya kusa shiga dan walkway din da zai sake sadashi da sassan nanay mafi kusanci.

"Barka da dare" Ta fada a hankali tana fatan idanunsa yakai kanta tana rusunar da qwayar idanunta qasa.

"Yauwa......ya jikin?" Ya fada a tausashe yana dauke idonsa daya sauke a kanta zuwa gabansa.

"Alhamdulillah" Sai ya gyada kansa a nutse ya soma takawa zuwa gaba.

"Allah ya bada lafiya" Ya fadi a nutse yana sake yin nisa da inda take tsaye.

"Ameen" Ta amsa can qasa muryarta tana rawa,tana jin yadda yake qulewa,tana jin yadda yakeyin nisa da inda take tsaye. Duk takunsa saya ruwan hawaye yake saukar mata. Iya abinda zai iyayi kenan?. Me yasa kaman damuwa da lamarinta da kulawar da a baya yake d'an nuna mata sukayi qasa sosai?,me yasa suka ragu fiye da kafin tafiyarsa?.

Me yasa bazai karanci damuwarta ba kaman yadda ya saba karantar damuwar 'yan uwansa dama kowa daya damu dashi?,me yasa bazai kalli cikin idanunta ya karanto abinda ke danqare a kansa a zuciyarta ba?. Zuciyarta tayi wani irin rauni,ruwan gorar data dauko ya fara mata nauyi a hannu,ta riqeshi sosai cikin hannun nata,ta daga qafa zata fara takawa maganansa ya mata bazatar data saki ruwan a qasa.

"Ko akwai wani ciwon da kikeji?,idan akwai ki fadawa nanay,koda asibiti ne sai a sake da tests ko?" Ya fada da kulawa. Qasa tayi da kanta tana kasa hada idanu dashi,sannan ta daga kanta a hankai.

"Da sauqi.....ina samun sauqi" Kai ya jinjina yana sake komawa hanyar walkway din

"Ma sha Allah,haka akeso". Tana sake jin yana mata nisa....har zuwa sanda qamshin turarensa ne kawai ya rage a gurin banda wannan gangar jikin da wannan kyakkyawan ruhin da take mafarkin mallaka. Tsugunnawa tayi tana laluben ruwanta daya fadi,saboda hawayen da suka cika mata idanu sun hanata ganinsa,ta aza hannunta akai ta dauka ta miqe da sauri sauri tana wucewa ciki.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 48*

Kuka sosai ta fashe dashi tana qoqarin boye kukanta don kada Aanaani dake zaune tana amsa waya ta jita. Ta lura daidai da kallo ma ba kai tsaye yake kallonta ba. Haka yake kallonsa akan kowacce diya mace yana qoqarin kauda idanunsa a kanki.....amma me yasa sai a yanzun haka yafi zafafarta?. Ta tabbatar ba irin wannan kallon yakewa matarsa ba......bama irin wannan kallon ya mata ba har yaja ra'ayinsa a kanta ba. Me yasa bazai.kalleta da dukkanin idanunsa ba kamar yadda ya kalli matarsa?. Ta tabbatar tana da dukkan wata siffa hali da dabi'a da yakeso game da d'iya mace......ta tabbatar indai zai kalleta yau gobe zuwa jibi.....lallai wataran zata samu kyakkyawan gurbi da muhalli a ransa. Ta sanshi ta karanci dukkan wata dabi'a tasa,tasan abinda yakeso tun daga kan sutura yanayin turare abinci da yanayi(weather)na gari dana muhalli,tayi kuma amfani da dukkan wannan ta fara samar da magana me dan tsaho a tsakaninsu,koda kuwa akan karatu ne amma taci wannan galabar. Ba irin farkon zuwanta ba.....ba kamar a baya ba da daga nesa kurum take hangensa......me zai sanya ta tsaya a iya haka?.

"Wacece ita?" Ta samu kanta da tambayar kanta bayan dogon tunanin data gama. A kaf dabi'arsa ta gama gane baya wani ra'ayin mu'amala da mata,baya zurfafa kallo a kansu,wannan ya bata relief na cewa itace kawai zatayi nasarar shiga rayuwarsa. Ta yaya wannan din ta shiga rayuwarsa?,wacece ita?,dame ta fita?,dame take taqama?. Wadannan tambayoyin gaba daya suka kwadaita mata son gani da sanin WACECE AKHNAN.

Duk da tana fargaba,zuciyarta kuma tana gaya mata koma wacece zata samu nasarar mallakar sheikh muhammad din tako ina ta cika mace tabbas......to amma kuma tana fata duk cikar da tayi ita ta fita ta kowacce fuska.

Tsam nanay ta miqe sanda yake shigowa dakin,fuskarta shimfide da murmushin nan da yake sake nuna dattakonta da tarin nutsuwar da yaranta suka gada daga gareta.

Shima nasa idanun suna kanta,yana dubanta da wani kalan tarin qauna da soyayya da tausayi na jiran wasu mutane data dinga yi a rayuwarta na tsahon shekaru ba tare da tana da tabbaci akan komai daya shafesu ba. Ya lumshe idanunsa yana kama hannayenta,yana jin wani irin sassauci da sanyi a ransa a duk sanda ya tuna cewa shine zai zama silar yankewar wannan jiran.....shine zai kusantata da nesanta.....shine zai zame mata tsani na sake rayuwa da mutanen da sukafi soyuwa a ranta.

"Zauna nanay" Ya fada yana zaunar da ita saman lallausan tuntum dake zube kan kilishin dake dakin. Bata musa masa ba,ta zauna shima ya dawo gabanta ya zauna saman qafafunsa yana dubanta.

"Na dauka kin gaji da jira kin kwanta". Murmushi tayi ta girgiza kai.

"Nace zan jiraka muhammad,munyi kewarka sosai.....zanso ace a yanzun haka a irin wannan yanayin surukata tana gefena kamar yadda kake zaune a gabana.....amma al'ada tayi mana wannan shamakin" Ta fada tana murmushi. Yau kawai sai yaji kunyar nanay ta kamashi,yadan sauke kansa qasa. Wai shine da mace?,shine ya auri wata macen?.

"Yaya take Muhammad.....gayamin" Da mamaki kadan a fuskarsa ya daga kai yana duban nanay din. Idanunta basu qaryata abinda ya fita yanzu a bakinta ba. Da gaske take tanason ganinta,wacce irin qauna ce wannan?,tun kafin tasan wadda ya kawo mata a matsayin suruka?,tun kafin taga wacece?. Babban abun,a duk lokaci itin wannan da zai dawo daga tafiya ba wanda Nanay takeji ko ta gani saishi,amma a yau maimakon zallar kulawar nan a kansa shi kadai ta soma rabata da wata?. Tun a ranar farko?.

"Lafiya alhamdulillah nanay" Kai ta gyada a hankali.

"Nace da hasnaaa ta bani ita a dazun muyi magana saita manta.....fatana daya ta kasance me fikira kamar yadda mijinta yake,ta kammala karbar horo cikin qananun kwanaki don ta iso cikin ahali" Qasa yayi da kansa kadan yana murmushi,shi duka ba wannan ba.....izzarta Allah yasa ta barta tayi abinda ya dace,yana fatan izzarta ta barta ta ajiye komai na agadez ta shiga practicing al'adu da dabi'un fada da masarautar aba jifar.

"In sha Allah nanay" Ya fada yana zama sosai wannan karon.

Hira suka shiga yi a tsakaninsu,irin hirar yaushe gamo. Hirar da take kama da hirar masoyan da sukayi nesa da juna. Abubuwa masu yawa suka tattauna,basa ma ko kallon abincin da tasa aka shirya kala kala daga nau'ikan abinciccikan alfarma na al'adarsu da tasan yafiso.
Chapter 52 · 0% Book details