← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 176

Sashe 59

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nanay" Ya kirata da girmamawa bayan sun kammala cin abincin da ita ta dinga zuba masa har sai daya qoshi.

"Sheikh muhammad" Ta fadi da murmushi. Yakanyi murmushi a duk sanda ta kirashi irin hakan,sai yaji sunan kaman yafi dadi a bakinta.

"A duniya.....wanne buri ne kike fatan cikarsa kafin ki koma ga mahaliccinki?". Tayi shuru tambayar tana ratsawa cikin kanta. Tana da wasu burika na daban......amma ta sani inde ta riga muhammad rasuwa to zai iya cika mata su,koda bata gani da idanuwanta ba,amma a yanzun burin da take dashi shine taga 'yan uwanta.

"Muhammad......burina bana jin me cika ne" Ta fada a raunane. Matsawa gabanta yayi sosai,ya kama hannuwanta ya riqe cikin nasa.

"Kija numfashi sosai nanay,ki fadi duk wani burinki,a gaban muhammad dinki kike" Murmushi ya subuce mata dake hade da ruwan hawayen da baikai ga zuba mata ba.

"Na sani.....wannan jan gwarzon namijin,zakin d'ana" Maganan ya sashi qaramar dariya,duk da ba yau ya fara jin ta fadi haka a kanshi ba,amma murmushinta kawai ya sanya wani farinciki a zuciyarsa.

"Burina naga safiyya da safeena,duk da nasan zai wahala rayuwa ta bamu wannan damar" Ta fadi cikin alamun karaya da yanke tsammani.

"Idan na sadaki da koda wani abune daya shafesu......wannan burin naki ya cika?" Samun kanta tayi da qanqame hannunsa sosai har yaji hakan cikin jikinsa,idanunta cikin nasa sosai.

"Koda abinda ya shafesu ka hadani dashi muhammad inaji a jikina zai zamana kamar ka hadani dasu ne kai tsaye......amma anya...."

"Kisa a ranki a nan kurkusa wannan burin naki zai cika" Har cikin tsakiyar kanta sai da taji wani abu,mamaki ya hanata cewa komai da wata irin shakka data cika zuciyarta.

Tafi kowa sani.....ba maqaryaci bane......idan ya fada koda da wasa ne sai ya cika. Wannan ya sanya yake kiyaye harshensa akan fadin abubuwa sosai don baya fadin abinda bazai aikata ba. To amma idan ta gamsu da abinda ya fada fa?. Ta ina zai nemo mutanen da ko burbushinsu ba wanda ya sake gani ko ya sake jin labari shekaru kusan talatin?. Amma kuma gaskiyarsa wata abace da ko yaushe take sake nuna zahirin waye shi.

_ki yarda kawai nanay.....mu lu'u lu'u followers muna tayaki murna da haifar jarumi kuma nagartacce,ya rabbi kasa mun haifi sanyin idaniyarmu muma_🙏🏽🙏🏽

★★★Kwananta daya tak ta soma karbar wasu darussa na sabuwar rayuwar data dinke tunaninta tsaf. Wasu irin al'adu na girmamawa,sutura,yanayin magana da yanayin kula da miji da bata taba ganin irinsu ba.

Komai da ake qoqrin azata akai da koya mata mamaki yake bata. Tanason karanta da fahimtar dukka dalilan yin hakan. SARAUTA ta tabbatar gidan wani sarautar ya shigo......gidan sarautar dake da wani irin tsare tsare da tarbiyyar da a tunaninta bata dauka wani gidan sarauta zai kasance irin haka ba. Abu daya da bata gane ba shine......waye shi a masarautar tasu?. A rannan yace mata shi BAWA ne......amma tako ina maganarsa ta gaza shiga zuciyarta da ranta tayi tasiri. Ba wata alama ta bauta a tattare dashi......horon da ake bata kuma baiyi kama da koyarwar da za'a zauna ana yiwa matar bawa ba.

Sabuwar rayuwa take shiga......wata irin sabuwar rayuwa da bata taba sanin da zamanta a duniya ba. Sai a sannan ta tuna da zancan aisa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

"Duk yadda kike ganin kinsan duniya da yawa,qasashe masu tarin yawa,kin cakuda da mutane qabila kala daban daban......amma akwai inda zaki shiga kiga kin koma kamar wadda batasan komai ba.....rayuwa gaba da gabanta ne.....kafi an fika,Allah ne kawai a sama" Tayi maganan ne tun farko farkon fara zuwan manemanta da sultane ke sahale musu ganinta. Ta raina daya daga cikinsu daya kasance d'an sarkin Cameroon,duk da tarin dukiyarsa da wayewarsa. A lokacin aisa taso ta aureshi......amma ta gaya mata ba'a halicci d'a namijin daya hada dukka qualities din da take buqata daga gurin namiji ba,auren wanda bai hada wadannan nargartar ba tabbas zai zama tozarci ne da qasqanci a tattare da ita,koma baya da rasa martabarta.

Wata irin kulawa ake bata.....wata irin girmamawa da tattalin da hatta su birra saida suka raina yadda suke kula da ita a agadez. Komai nata ya canza,daidai da fatarta tasan akwai wani abu daban dake faruwa a rayuwarta.

Qamshin jikinta ya zame mata qamshi na biyu dake debe mata kewa bayan qamshinsa.......qamshin turaruka na SHUWA INCENSE AND MORE( +234 704 229 3387) wani qamshi da yake sanyata dadewa cikin duvet duk safiya idan ta farka tana shaqar qamshin yana kai mata har cikin kwanyarta,yana kuma qoqarin kwashe mahaukaciyar kewarsa da takeji tana qoqarin hanata dukkan walwala. Ta dauka a kowacce rana zai shigo ya ganta......ta dauka kowacce rana zata zame masa ta ziyara,saidai abun mamaki babu shi ba dalilinsa. Ba kiransa a cikin kwana biyar din data dauka cikin gidan.

Amma a kowacce rana hasnaa da rumaisa da wasu mata da batasan su waye ba suna ziyartar gidan. Cikin kulawa take ta kowacce fuska,cikin kulawa da tattali take da wani irin gata daya sanya ta soma tambayar kanta,wacce irin rayuwa tayi a baya ne?,gata ne da kulawa ta samu?,ko kuma copy ne kawai na gatan ba original ba?.

Abun mamakin yadda kwanyarta ke kwashe komai......ita kanta me dora mata tsarin tana ganin mamaki qarara kwance saman fuskarta.

Bawai suna da wani qarfin ikon sauya mata rayuwa bane.....aah ta yarda tabi komai yadda aka tsara saboda tana buqatar fita daga gidan. Tana buqatar sanin WAYE SHI?,tana da buqatar ganin anihin rayuwarsa,hakan kuma dukka ba zata samu ba sai tayi qoqarin maida kanta yadda sukeso.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽
[5/25, 11:33 AM] +234 916 570 6016: .💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 54

Suna waya da shehnaz,aisa da morsa lokaci lokaci......amma har yanzu ta gaza samun sultane sai sau daya tak. Shima maganarsu dashi gajeriya ce......ya mata wata magana a qarshe data sanyata fashewa da kuka.

"Gida nakeso na dawo bappi......gida nakeso nazo na ganka" Murmushi ya sake mata.

"Nace miki ko bayan na mutu kike kuka ko biftu?" Ya fada da murmushi

"To ko mutuwa nayi indai haisam bai lamunce kizo ki ganni ba ban yarda kizo ba.....idan kika bishi hakanne zai samawa ruhina salama koda cikin kabarina......duk da ina lafiya cikin qoshin lafiya,muna kan wani aiki ne da yake janyemin lokaci,duk sanda kika nemeni baki sameni ba....karki saka a ranki wani abu ne mara kyau,cikin aminci nake da kiyayewar Allah".

Tayita kiran aisa sa shehnaz ko zataji wani abu,amma ba wata alama data nuna akwai damuwa ko matsala cikin masarautar,haka ahmad data kira shima abinda ta gani kenan,wannan ne ya sanya mata nutsuwa a ranta,ta maida hankali ta kammala wancan training din ta fito,tunda duk binciken da tasa a mata sunce basu gano komai a kansa ba,wannan karon ita zata nuna masa adadin nata ikon.

Batasan me yake faruwa ba,tasan dai kawai ta tsinci kanta tsundum da yawan duba wayarta. Duk bayan shudewar wasu mintuna saita duba screen din wayarta,daga haka saita fara zarcewa zuwa gurin kira.

Takan jima da wayar a kusa da ita,takan jima tana juya wayar a hannunta,batasan me take jira ba,batasan me take nema ba. Sannu a hankali sai wadannan hotunan data fuskanci da yawa an daukesu ba tare daya sani ba......a mabanbantan lokuta a kuma mabanbantan gurare suka zame mata qawaye.....suka zame mata abubuwan da duk rana ranar ba zata fito ta fadi ba bata buda ta kalla ba.

Daga qarshe ta sani.....ta bari zuciyarta tayi mummunan sabo da al'amuransa......sabon da batasan meye dalili ba.....sabon da batasan meye ya kawoshi ba......ta sani ta saba ta saba ta saba......amma duk da haka akwai abu daya dataqi yarda a karan kanta cewa SOYAYYA CE.

Yarda da cewa tana sonshi tana jin shine qarya ta qarshe da zata qara yarda zuciyarta ta qulla mata. Ta sani tadade da kashe duk wani gurbi na taso wani d'a namiji a zuciyarta. Ko meye takeji ta yarda ta sallama da cewa SABO NE SILA.

Tasha kallon number daya kira a wancan ranar......amma kuma ta dade da yiwa zuciyarta bore wadda ke shawartarta ta gwada kiransa. Yasan inda zai ganta......yasan number da zai kira ya sameta,bai nemeta ba......ta yaya dalilin sabo zata bari alfaharinta na diya mace yayi qasa?.

Tana tsoron sabo ya karya wannan alfarmar don haka a wani yammaci ta dannawa number delete,amma batasan me ya sanya wani abu ya tsaye mata a wuya ba bayan ta goge number.

Ranar farko da hawaye suka cika mata idanu ranar da kewarsa ta hanata bacci. Tayita juyi,tayi alwala tayi sallah duka wannan kewar data rasa wacce iri ce ta hanata sakat.

Me yasa duk yadda na dade da sultane da kowa da kowa dake cikin masarauta bana jin girman kewarsu haka a raina?. Me yasa banquntata da yawa ba daga rashinsu a kusa dani?,saishi?.....WAYE SHI?,meye na musamman a tattare dashi da kewarsa ta dara ta kowa nauyi cikin zuciyarta?.

D'isar qwallar kawai taji saman cinyarta,sai wani irin mamaki ya kasheta.

"Qwalla akhnan?,qwalla saboda kewar D'A NAMIJI?" Ta jima jikinta a sanyaye tana jin zafin abun. Me yasa ta sake masa haka da yawa?,me yasa ta bari suka saba da ganin juna da jin motsin juna?,wanne irin sakarci tayi haka?. Hannu tasa ta dauke qwallar tana gayawa kanta,har yanzu itace dai akhnan muhammad hammud.....bai kamata ta bari wani abu ya karyata ba,amma dai daga qarshe sautinsa.....qira'arsa.....karatun qur'aninsa ta kunna da qaramin sauti can qasa,shine abinda ya sama mata nutsuwar data samu yin bacci a wannan daren.

★★Duk zirga zirgar daya yini cikinta tsakanin gidan prime minister da gidan governor na jimma a yinin ranar data zama ta qarshe tun daga safiya zuwa yanzun da sararin samaniyar jimma ke bada wata lallausar iskar hadari hakan bai ture tunaninta ko sau daya daga ransa ba.
Chapter 59 · 0% Book details