← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 176

Sashe 73

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da kanta a qasa yake,amma hakan bai hanata fahimtar tarin banbancin da bangaren da yake dashi ba da dukkan sauran sassa na gidan. Tun daga yanayin tsari da tsarin shiga na security da hadimai dake kai kawo a sassan,yanayin sanyinsa da wani irin lallausan qamshi da iskar sashen gaba daya take bayarwa tamkar an halicci wata qaramae aljanna ce cikin gidan.

Daidai da qasan sashen da takalmanta ke takawa tamkar gaya mata suke

"Barka da zuwa wani sashe na musamman" Komai na sashen cikin wata nutsuwa yake,daidai da iska da shuke shuken da suke cikin sassan sai take ganin tamkar su kansu nutsuwa ta ratsasu,kamaar akwai wata tarbiyya ta daban tattare dasu.

Tun kafin sukai doorstep din ta fahimci akwai wani babban baqo cikin parlor din,akwai wani me girma dake zaune a ciki,saboda yawan adadin dogarai dake zagaye da kowanne taku na sassan nasa.

Tana daga gefan nanay sanda suke sallama cikin parlor din. Su biyu ne rak a ciki,wanda kafin ka qaraso zaka dauka tarin mutane ne a ciki,amma haiba da kwarjinin mutane biyun dake dakin a idanun Akhnan sai taji kaman a cike dakin yake.

Haisam.....wanda a kansa idanunta suka fara sauka. Wani irin sauka a hankali tamkar fadowar ganye daga jikin reshen bishiya zuwa qasa. Cikin ba zata nashi idanun suka nutse cikin nata.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 66*

Sanye yake da short sleeve leaf green t.shirt,sai dogon trouser nude color daya dan ciza kadan. Wannan sassalkan gashin nasa yana warwatse saman kansa da wani irin yanayi da zai tabbatar maka baiyi tajeshi ya kuma kwantar dashi yadda ya saba ba.

Manyan idanun nan nasa sun rusuna kadan da wani irin yanayi daya canza launinsu,rusunawar da sukayi ta qara musu wani irin kyau,ta kuma sake kusantar da eyelashes dinsa na qasa dana sama da suke da tsaho sosai kaman zasu hade. Kallo ne na sakanni,saidai ya tafi da wani irin yanayi da saqo da batasan ya fita a idanunta ba. Wani irin kyau.....kwantaccen kyan nan me sanyi da wani irin sassanyar nutsuwa take hanga a tattare da fuskar nan ma'abociyar haiba.

Fuskar data kwashe darare tana kawo mata farmaki cikin mafarkinta, fuskar data kwashe kwanaki tana juyi saman tattausan gadonta tana gilmawa ta cikin duhun dakinta....fuskar da sannu a hankali kewarta ta fara illatata ba tare da ta farga ba. Wani sassanyan aniyar zuciya ta qwace mata,taimakonta daya ta sauka ne a hankali daga zuciyarta zuwa hunhunta ta fidda siririyar iskar ta hancinta.

Idan har taga daidai.....wani abu taga ya hadiya a hankali,ya kuma motsa bakinsa kadan kaman zaiyi magana,sai kuma taga ya zare idanunsa daga kanta.

Kan motii ya maida dubansa,wanda yake zaune dab dashi saman wani ottoman lallausan offwhite. Kallo daya tak yayi mata wani abu ya tsarga masa,tun daga tsakiyar kansa zuwa tafin qafarsa yaji kaman yana neman loosing control nasa,baya buqatar hakan kuma,a yanzun da yake gaban motii da kuma nanay.

Baisan abun zai zame masa jarrabawa ba sai daya gaza samun ganinta na wadannan kwanaki. A duk inda zai sanya hannunsa sai yaji bai ajesu daidai ba. Kaf pillows dinsa na saman gado ba wanda baisha matsa ba.....amma still baya samun sassaucikoda na daqiqa daya. Ya sauya pillows ya sake qara wasu amma still ba wani taimako da yake samu. Baisan daga inda matsalar take ba.....

Hirar su ta shekaran jiya yake tunawa. Shi da maleek da suke turkey yanzu haka shida falaaq din,sai naseeb. Hirar ta ranar iya su uku ne,don naseeb yace iya hirar masu iyali ce kawai,saidai shi dimma daga qarshe shuru ya musu tsakanin naseeb da maleek suketa shaqiyancinsu.

Ya sani,wani abun idan maleek ya fada dashi yake,maganan maleek ta qarshe ta sanyashi yanke kiran ba tare da yace musu komai ba,sukayita qoqari sake kiransa amma yaqi basu wannan damar.

A daren idanunsa ya maida ya lumshe yana jin yadda ciwon ke sake masa qarfi. Baisan dalili ba,amma har bayason dare yayi cikin kwanakin nan. Tun yana irga kwana daya biyu uku har zuwa sati guda.

Yayita zuwa gurin nanay dukka satin,zuwan dashi karan kansa baisan dalilin yinsa ba. Yakan jima zaune yana jiran nanay,yakan jima zaune suna hira dashi.

A satin ya dauka zaiga koda gilmawarta,a satin ya dauka ko sau daya zasu hadu gurin cin abinci a gurin nanay amma ba koda alamunta,sai saamee dake neman kusanci dashi.

Basai an gaya masa ba.....a matsayinsa da matakin karatunsa.....tabbas akwai wani gagarumim sauyi dake neman zuciyarsa idanu rufe,saidai ya gaza samun qwaqwarar hujja ko shaida da zai gasgata hakan.

A yanzun da idanunsa suka sauka a kanta.....a yanzun da take takowa zuwa cikin parlor din.....idanunsa basa kanta.....amma cikin jininsa da jikinsa yakejin takunta....cikin jininsa da jikinsa yakejin wannan kusancin. Yana jin kamar wani abu daya rasa ne yake takowa zuwa gareshi,yana jin kamar wani sashe na jikinsa da aka cire aka wurgar ne yake dawowa zuwa anihin jikinsa.

Nauyi da kunyar mootii takeji,wani irin nauyi da ko sultane batajin nauyinsa haka. Ta wani sashen sai take ganin wasu kamaceceniyar yanayi da dabi'u a tsakaninsu.

Cikin girmamawa ta isa gabansa,ta zube a hankali tana gaidashi da harshen oromo data fara kama kalmomi da yawa na kurkusa,kaman gaisuwa da sauransu.

Da murmushin nan me cike da dattako da kulawa ya amsa mata

"Anya khadeejatu?.....har yanzu baku gama bidi'o'in naku ba?" Mootii ya fadi sanda Akhnan ke isa gaban gadon haisam din,sai kuma ta samu Nanay ta ja mata kujerar dake dab dashi din.

Wani abu guda daya data lura dashi,komai na nanay ya ta'allaqa ne akan yadda zata bawa haisam kulawa.....kamar yadda tata kulawar kuma a yanzun dukka ta tattareta a kanta.

A kunyace ta zauna,saidai abinda ya bata relief janyewar nanay a nutse ta koma kusa da mootii daya koma kujerar can kusa da qofa yana riqe da wasu takardu a hannunsa,wannan ya haifar da tazara a tsakaninsu,don parlor ne me girma qwarai.

Idanunta ta daga zuwa kan fusarsa,saidai gaba daya kalaman bakinta sun maqale saboda samun lumsassun idanunsa da tayi a kanta. A hankali ta maida bakinta ta rufe,ya riga ya saukar mata da wannan dafin.....ya riga ya luguiguita zuciyarta da wadannan narkakkun idanun nasa da suka sake narkewa.

"Kwananki nawa da sanin bani da lafiya?" Ya furta softly saidai tana jin wani abu can cikin sautinsa.

Samun kanta tayi dayin qasa da kanta,tana jin wani kimarsa tana tabata sosai. A yanzun wani kallo na daban take masa.....ba don dukiyarsa ko.matsayinsa ba.....aah,sai don yadda ta samu ahalinsa da sanin ma'anar GIRMA da MUTUNTAWA.

"Kwana uku" Ta furta a hankali da siraran labbansa da yaji kaman ya miqa yatsunsa a shafesu a hankali.

Kai ya jinjina a hankali,yana jin yadda gaba daya jijiyoyin jikinsa suke narkewa. Qamshinta.......shigarta da yanayinta gaba daya. Kwana sha hudun yake sake maimaitawa cikin kansa. A kwanakin ya dinga jin wani abune yana masa yawo a kai,a kwanakin ya tuna duk wani memories nashi da ita tas.....ba abinda ya manta tun daga zamansu a agadez zuwa ganinsa da ita na qarshe. A kwanakin ya dinga jin wani abu yana yawo da zuciyarsa cikin wani irin yanayi.

Duk debe kewa da library da litattafansa ke masa a wannan lokacin su gaza dauke masa komai.

"Kwana uku?" Ya maimaita a hankali kaman wanda kwanakin sukayiwa zuciyarsa nauyi.

Fuskarta ta narke a hankali,tana jin kamar bata kyauta ba......tana jin kamar abun bai dace ba.

"Bahaushe yace gaida me gaidaka ko?" Can wani sashe na zuciyarta ya tunasar da ita. Ta tuna yadda yake kula da ita duk sanda wani ciwo ko rauni ya sameta.....a saudiyya....a festival d'l'Aîr. Baiyi bacci ba...
Bai samu sukuni ba sai data samu......amma ita yanzu?.....sau daya tak ta kasa gwada masa halaccinta?.

".....ko sau daya...." Ya sake fadi a hankali da wani irin coolness idanunsa cikin nata.....yana jin wani abu me qarfi yana fusgarsa.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

".....baki nemeni ba?" Ya qarashe da sigar tambayar data sanyata lumshe ido tana jan wani numfashi. Shigar kalmar data gauraya da sautinsa cikin kunnenta.....wani irin lallausan sauti da takejin kamar ba muryarsa ba....kamar ya manta waye da waye a gurin.

"An hanani....."

"Na sani....." Ya tari numfashinta ba tare daya bari ta qarasa ba.

"Nanay ko?" Ya sake fadi da wani nauyi cikin muryarsa. Sai ya maida bayansa ya jingina sosai da fuskar kujerar.

"Me yasa rashin zuwana ya masa ciwo?" Ta tambayi kanta da kanta cikin jikinta har yanzu da idanunsa a kanta. Da zai taimaketa....da zaiyuwu daya debe wadannan tsimammun idanun nasa daga kanta,rikitata yake.....sosai yake sanyata jin tana rikicewa.

"Ko sau daya....ko da tambaya?...koda saqo?.....koda daga bakin qofa ne?" Ya sake fadi da wani lallausan sauti me cike da tuhuma.

Kaman zata shide taji,don sai taji muryar tasa tayi wani mugun kusa dashi,kuma koda data motsa saita fahimci ya rage distance din dake tsakaninsu ne.

"Don Allah......kayi haquri" Ta fada a rarrabe tana jin wani kunya da nauyin kusancin daya samar a tsakaninsu. Kamar idanunsa baya tuna masa nanay da motii dake gurin?.

"Ba komai" Ya fada a hankali yana sake relaxing sosai cikin kujerar karo na biyu,sannan ya maida idanunsa ya lumshe.

Har cikin zuciyarta takejin bata kyauta ba.....amma da wanne harshe.....da wannw yanayi zata cewa nanay GANINSA NAKESON YI?. Da wanne idanu zata cewa nanay KEWARSA NAKE?.

Tayi imanin baisan abinda takeji cikin zuciyarta ba.....inda ya sani bazai tuhumeta da komai ba.

"Da nine.....da sai a kiramin bappi ko?".

" Kayi haquri naceeeee" Ta furta da sauri a wani mugun narke da wata irin shagwaba da bata yita da kowacce manufa ba....illa manufar yabar zancan haka.

Yanayin ya sanyashi cije lips dinsa na qasa a hankali yana lumshe idanunsa. A hankali bakinsa ya furta!
Chapter 73 · 0% Book details