← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 176

Sashe 114

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Now.....explain your self" Murmushi ya sake subuce masa,sai ya miqe ya zauna sosai yana dubansu daya bayan daya.

"I'm not explaining anything".

"Wallahi zakayi kuwa" Mutallab ya fada yana nunashi da yatsa.

"Yes.....ya kamata....don ka fola da yawa billahi.....not just smiling fa.....BRO WAS STARRING" Ya fada yana kaurara muryarsa da buda hannuwansa kaman me shirin kama wani abun.

Wani irin dariya maleek yakeyi sosai,har yana sunkuyawa. Shi ya sani.....yana da falaak a gefansa,ya sani muddin akhnan din jinin falaak ce.....dole haisam ya zauce.....dole ya zauce babu ko makawa.

"He has entered the dangerous stage fa....."

"......the my wife stage" Omar ya qarasa yana sake qoqarin kwaikwayon muryar haisam din again.

"Women are unnecessary emotional responsibilities.” omar ya sake fada da yanayin muryar haisam din.

Ya gama fahimta,kawai sun hadashi a nan ne saboda suyi masa titsiye. Ba wannan yanzu yafi buqata ba. Hutu....hutawa yakeso yayi.....so yake yaji duminta,so yake ya jita a gefansa. A yau yadda jininsa ya tsinke dinnan sosai,ya sani zaisha wahalan bacci....zaisha wahala kafin ya iya dauke mata ido a yau. A kwana biyar din daya qyaleta shi kadai yasan yadda yake surviving.

Miqewa yayi abinsa yana riqe da rigarsa.

"I hate all of you" Ya fada a kasalance yana soma takawa.

"No....you loved one person" Sai suka sake saka dariya.

Khadeem ya nutsu zuwa serious.

"But seriously....." Ya tsaya kaman yana nazari.

"......I’ve never seen you this relaxed around anyone.”. Shuru dakin ya dauka,don dukkaninsu kaman tambayar tana ciki kawunansu ne.

A karon farko,da fidda dukkanin gaskiyarsa.....bawai kare kai ba,ya jingina da bangon da yake daura dashi,idanunsa sun zama soft sosai,ya motsa labbansa da nutsuwar nan tasa.

"She makes noise in my head disappear.” sake shuru dakin yayi.
Saboda ko su sun san wannan magana tana da nauyi coming from him.

“You people are witnessing the downfall of a proud man.” maleek ya fada yana satar kallon haisam yana boye dariyarsa.

"Maleeekkkkk"

"Sorry babban yaya.....tuba nake" Maleek ya fada da sauri yana surrender.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Matse qwalla omar ya hau yi,duk da na wasa ne amma yayi calling attention kowa.

"Our emotionally unavailable Sheikh has fallen.......khadeem muna da meeting.....dole mu nemi aure" Dariya ta kaure gaba daya a dakin,haisam ya kaiwa omar cafka saiya zille.....sai kawai ya bude qofar yana fita yana bar musu dakin.

*A K H N A N*

Rudewa......mamaki......da shiga shock sosai su shehnaz sun yishi. Yadda suke juya zancan tun daga fitowarsu bayan kammala komai da sallamar tarin investors din dakeson magana da ita tace sai tayi shawara da mijinta duk tana jinsu.

Itadai abu daya ta sani,da gaske komai ya tashi daga mafarki zuwa gaske. Shin akwai wani sauran abu yanzu daya rage daga haisam wanda bata sanshi ba?.

Wanne irin mutum ne shi me abun mamaki?. Me yasa ya zabi ya boye mata komai?. Me ta bashi a duniya.....me ta mallaka masa data cancanci wannan kyautar?....wannan girmamawar?,.....wannan kambamawar?.

"DAME ZAN SAKA MASA?" Tambayar data rasa amsarta kenan,saidai a hankali maganganun aisa suka zame mata kamar wani tsani.

"Akhnan......baki da masoyi a yanzu sama da sheikh haisam.....ba don ya mallaka miki dukiya ba,saboda soyayyarki a idanunsa daban take da wadda aka saba gani. Baki da wani abu da zaki bashi akhnan a yanxu.....saidai ki soshi.....kici gaba da sonshi......ki riqeshi ki bashi kulawa. Ki kiyaye mutuncinsa....ki faranta masa.....ki sallama masa kanki.....ki miqa masa komai naki. Kin tsinci LU'U LU'U a cikin juji......kina dab da yasar dashi sultane ya cafe miki shi. Kin kalleshi kina mamakin alfanun da wannan abun me datti zaiwa sultane.....ashe shi ya fuskanci lu'u lu'u ne. Sai yanzu daya wanke mikishi tas.....sannan kimarsa ta sake fita" Ta yarda da maganganunsu d'ari bisa d'ari......amma a yanzun abinda ke damunta shine. Ta yaya zata aminta da haisam ta gamsar dashi d'ari bisa d'ari take sonsa. Ta yaya zai fahimci don Allah take sonsa badon dukiya ba?. Ba don abinda ya mallaka mata ba?,ba don shi din a yanzu wani bane?.

Wannan ne ya dameta,bata jima a sassan baqi na residence din ba tabarsu dasu Aanani ta wuce suit dinsu din tace kanta ciwo yake mata.

Wanka tayi wai ko zataji sassauci cikin ranta. Ranar farinciki ce a garesu da dukkan me qaunarsu amma wani karyewar zuciya takeju da wani irin weakness. Haka kawai taji kuka takeson yi,saita koma a hankali ta zauna bakin sofa bed ta soma rera kukan.

Tana tuna komai data masa a baya.....maganganunta.....raininta da izgilinta. Ta yaya zai gamsu da ita cewar da gaske take?,ta yaya zai fahimci komai ya fara kafuwa a zuciyarta tun kafin tasan komai game dashi.

A hankali ya bude suit din nasu da sallama a labbansa kamar yadda ya saba. Duk inda zai shiga,koda ba mutum to zaiyi sallama. Kai tsaye yake takawa yana wucewa cikin dakin yana sake jin shauqin isa gareta kamar ana fusgarsa.

Sanda ya buda qofar.....idanunsa suka sauka a kanta sai yaji wani abu ya tsaya masa cak

"Kuka?" Ya fada a hankali,saidai kuma sautin ya isa kunnuwanta. Share fuskarta ta fara yi da sauri,bataso ya gani,batason wani abu da zai b'ata wannan mode din nasa,batason wani abu da zai ware wannan farincikin da take gani shimfide saman fuskarsa.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 103*
_________________________
https://chat.whatsapp.com/BkfPzSEDhnsIwyCD8LNGkm?s=cl&p=a&mlu=0

*IDAN KINSAN BA ORDER DIN KAYA ZAKI DINGA SAKAWA BA*

*IDAN KINSAN BA BUSINESS KIKE DA NIYYAN YI NA KAWO KAYA DAGA CHINA BA KARKI SHIGA*

*_DON ALLAH KARKI BATAWA KANKI LOKACI_*

*_Assalamu alaikum my loyal people_*

*_Barkanmu da wannan lokaci,kuma barkanmu da warhaka_*

*_akwai da dama cikin mata wadanda suke sha'awar yin order kaya daga CHINA zuwa NIGERIA,NIJER,CAMERON,CHAD da GHANA_*

*_Amma rashin samun amintaccen company....ko hannun wanda zasu dinga siyan kaya ta hannunsu cikin aminci ya hanasu_*

*_To a yau addu'ar da yawa daga cikinku ta amsu,don nayo muku tsarabar kamfanin da zakuyi siyayya ta hannunsu su kuma dora muku kayanku har qasarku cikin aminci ba tare da fargaba ko d'ar d'ar ba_*

*_kunsan komai nawa TASTED AND TRUSTED ne,to wannan kamfanin idan akwai abinda yafi TASTED AND TRUSTED ma shine_*

*_Baki da fargaba kota sisin kwabo,ni SAFIYYA HUGUMA na tabbatar da hakan_*

*_Zaki iya kasancewa dasu group nasu,inda a nan zaki hadu da agent dinsu da CEO nasu gaba daya ta wannan link din,zaki samu bayanansu da komai da ya shafi mu'amala dasu_*

*INA ME BAKU TABBACIN AMINCI DA INGANCI DA SAUQIN MU'AMALA DASU DA IZININ ALLAH,BAN TALLATA MUKU SU BA SAI DANA GWADA*

*Allah ya dafa mana,yasa mana albarka a nemanmu,ya albarkaci halal dinmu ameen summa amee*
__________________________

"Nothing" Ta fada da wannan jaririyar muryar tata me taushi.

Qofar ya rufe a hankali sannan ya tako cikin nutsuwar nan tasa. Tun kafin ya qaraso,dukkanin kulawarsa da idanunsa suna kanta.

A nutse ya qaraso gabanta,ya kuma tsugunna saman qafafunsa yana riqo hannayenta.

"Me ya saki kuka?" Ya tambaya a tausashe yana bata dukkan kulawarsa da hankalinsa. Da sauri ta girgiza kai,amma hawayen da suka sake zubowa sai suka qaryatata.

Miqewa yayi a tausashe,ya bata hannuwansa dukka ya dagata daga kan sofa din ya maye gurbinta,sannan ita din kuma ya azata saman cinyarsa. Dararewa kadan tayi saboda guntun towel ne kawai daure a jikinta,amma saita lura hankalinsa ma baya gurin. Hannunsa ya miqa ya tattare mata gashinta zuwa gefen kafadarta daya.

"Hey" Ya fadi ganin yadda take qoqarin hanashi kallon qwayar idanunta.

"Talk to me" Ya sake fada da wani irin laushi a muryarsa dake fita can qasa.

Papers din kamfanin dake ajiye saman dressing table din dake gabansu ta kalla,sannan ta dawo da dubanta kansa.

"Me na taba yi maka a rayuwa?" Ta tambayeshi kanta tsaye,blue eyes dinnan nata cike fal da hawaye.

Girarsa yadan hade kadan yana duban fuskarta,amma hakan bai hanata ci gaba da magana ba,don tanajin kamar taso kanta da yawa.

"Wanne irin alkhairi na taba yi maka.......da zan cancanci wannan girman?".

Shuru haisam yayi,kallon da yake mata yanzu ya sauya gaba daya. Wani irin zuzzurfan kallo me cike da taushi .

" Na taba rainaka fa...." Ta fada da rauni sosai a muryarta hawayenta suna sauka saman kuncinta

"......na taba fahimtarka ba daidai ba...." Ta fadi tana sauke idanunta qasa kunyarsa tana cikata.

"Amma kuma kai...." Ta sake fada tana motsa labbanta a hankali.

".....ka bani kuma kana sake bani abubuwan da ban isa nayi mafarkinsu bama".

Idanunsa ya lumshe a hankali sannan ya budesu kamar maganganunta sun taba wani guri me zurfi a zuciyarsa.

Hannunsa dukka ya sanya yana zagayeta ta gefan cikinta,idanunsa sun sake laushi sosai,qamshin jikinta daya cakude da qamshin shower gel dinta har yanzu suna tashi da wani irin sassanyan yanayi dake assasa wani feelings me matuqar qarfi a dukkanin jikinsa.

"Look at me" Ya fada da wani irin laushi. Idanunta ta daga masu jiqe da hawaye,hawayen da suka jiqa dogayen eye lashes dinta suka sanyasu sukayi wara wara tare da nuna ainihin tsahonsu.

Babban yatsantsa ya sanya yana dauke mata hawayen softly,yana yi yana sake qarewa kyakkyawar fatarta kallo me wani irin sulbi sheqi da daukan hankali.

"“You think too little of yourself ko?" Ya fada yana dage mata dukka girarsa. Girar data burgeta ainun yadda take a cike da baqin gashi,gata dab da ita kuma a yau tana kallon yadda Allah ya qera masa ita da kwantaccen gashin da suka kusa hadewa da juna.

"Ba sadaka na baki ba...." Ya fada a nutse

"......i just honored my wife" Cak numfashinta ya dakata na wucin gadi. Kalmar MY WIFE din tana sauka saman zuciyarta da wani irin nauyi da kuma kima me yawan gaske.

"A cikin wadannan....." Ya sake fada da wata nutsuwa cikin kalamansa da maganarsa.....ya fada din kuma yana maida idanunsa kan takardun dake gefan.
Chapter 114 · 0% Book details