← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 176

Sashe 143

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan zuciyar dukiyar ajani din.....ta muhammad ce....yamin wasiyyar ya barwa duk abinda safeena zata haifa,saboda yasan bai zarce kason daya zama haramun ka kyautar ba...kuma kaman yasan zai zamana baida kaso a dukiyarsa......muhammad yaqi karba.....yace na riqa masa.....ko na bawa obbo dinsa,shi kam yanzu neman ilimi zai tafi,kuma in sha Allah sati me zuwa zai wuce madeena can zaiyi dukkanin karatunsa,haisam ya gama masa komai lokacin tafiya kawai ya rage ".

Data daga idanunta tana kallon haisam.....ba miji kawai ya gani ba. UBA ta gani.....wata KADARA ta gani me tsananin tsada da daraja. Wani LU'U LU'U da mallakarsa sai me tsananin sa'a. Ta sake maimaitawa kanta tambayar.

"Wanne abun arziqi na taba yiwa Allah a duniya ya mallakamin wannan LU'U LU'UN?" tayi tambayar a hankali qasan ranta tana kallon shehnaz da tayi joining dinsu.

Bata manta ba......a safiyar yau ya mata abinda ta kasa riqe kukanta. Ta samu labari dama daga birra.....kaf kayan da mammina ta dinga saidawa tana gwanjonsu ya maidosu. Secretly ya sanya mutanensa suka dinga shiga suna siyan kayan da farashin da yafi kowanne tsada da daraja. Komai ya maidashi a muhallinsa,kamar ba'a taba ba. Kwatsam sai ga takardar kamfaninta a hannunsa.

Sahel couture.....kamfanin da mammina ta d'ai d'aita shi da mummunar sata......tare da hadin bakin ma'aikatan bogin data zuba a kowanne reshe na kamfanin,sannan kuma ta aza alhakin hakan akan aisa qarara. Ba kunyar nannie ba komai......taso ta mata tozarci,saidai bayan haisam ya maidata kamfanin bisa murde hukuncin mammina,ya dora aisa a wasu hanyoyi da dabarun da sai da suka gano daga inda komai ya fara. Ya barta taci gaba da rusa kamfanin har zuwa sanda tayi gwanjonsa. Ya ninka kudin ya kuma siya ta hannun jabeer ba tare da tasan waye ba.

Saidai kuma.....a yanzun da takardun saheel couture yake dawowa hannunta da sunan mallakinta a karo na biyu.....ba sahel couture take gani ba. Wani gingimemen kamfani take gani,wanda yake da qarfin jarin da zai iya gogayya da sauran kamfanunuwan qasar waje. Sun mallaki komai nasu na qashin kansu,ba buqatar zuba hannun jari daga kowa.

Sahel couture din daya zama wani na duniya gaba daya....ya fara qoqarin gina reshe a dubai,kusa da kamfanin turaren daya mallaka mata. Kamfanin turaren da har yanzu ta gasgata yarda ya zama nata. Saboda duk sanda suka zauna ita dashi......yanaso ya qarasa handling komai na kamfanin.....ya buda mata komai a matsayinta na CEO....mamallakiyar kamfanin sai ta kasa qarasa zaman dashi.

Kudaden da take gani yana lissafi kawai akai suna gigitata tare da gaya mata anya reality ake magana?.

Bai wani yarda ta masa godiya ko daya ba.....hasalima ya b'uge da tsokanarta ne. Tayi kuka sosai tana tuna ranakun baya data rainashi.

A yanxun kuma da yake dawo mata da danginta daya bayan d'aya. Yake dawo mata da ahalinta.... Ruhinta farincikinta dukka tattare da ita saita rasa dame ya dace ta saka masa?.

"Ya dawo mata da morsa safiyya.....jajirtacciyar uwar dataso rasawa.....ahmad.....ga muhammad da kwata kwata duniyarta batasan dashi ba sai yanzu. Ya qara kusanto mata da nanay....amintacciyar mahaifiyarta.....ya sake qara mata yawan 'yan uwa ta hanyar hada nasabarta dasu Anaani.....rumaisa.....noorah.....Aareef.....hussam.....balqees da khansaaa duka.

Idan ta juya ta kalli Ahmad......ta kalli muhammad..... Sai taji wani abu me laushi da nauyi saman zuciyarta.

Ashe dai itama tana da gata?,ashe 'yar gata ce itama sama da qasa,yayyen nan maza da take ganin wasu dasu.....ashe dai itama tana dasu?.

Wata qauna lokaci guda irin ta 'yan uwantaka ta soma tasiri tsakaninsu,amma duk da haka sai taga kamar falaak ma ta fita murna da d'oki. Don ita din,bata da saurin sabo,uwa uba wannan dabi'ar miskilancin har yanxu bata barta ba.

Daga baya mazan motii sultane ahmad muhammad hussam Aareef da haisam suka wuce sukabar iya matan. Su dai su akhnan suna zaune suna kallon ikon Allah. Lokaci lokaci sai nanay ko morsa su kalli juna,su saki murmushi,kosu riqe hannun juna. Sun manta dasu dake gurinma kwata kwata.

Sabuwar 'yan uwantaka....tsohuwar soyayya,dangantar zuci ta fara motsawa. Hirarsu suke suna tuna baya,suna tuna daa....amma kuma idan suka tuna da safeena ako wanne gurbi saisun tsaya sun zubda hawaye.

Anaani da noorah da kuma hasnaa sun wuce sashe na musamman dake manne dana nanay na baqi na musamman,amma rumaisa ta wuce kitchen inda 'yan aikin morsa safiyya ke qoqarin sake dora wani abun,duka cikin nuna girmamawa da karramawa ga baqin nasu.

Yadda suke tuna safeena da yawan kukan da taga sunayi ya sake karya mata zuciya. Sai kawai ta miqe. Bata gaji da ganinsu haka a tare ba.......tana jin kamar mamminta itace ta ukunsu,tana tare dasu a sannan,don haka saita yanke bin rumaisa kitchen.

Wani abu daya data lura dashi.....mulkinsu ko sarauta da yawan dukiya da iyayensu dasu kansu suka mallaka bata sanya sun rasa kansu cikin masu jin izza ko girman kai ba. Tana mamaki zamanta a Ethiopia yadda zata samu rumaisa a kitchen,duk da tarin hadimai dake qarqashinta wadanda aka ajiyesu kawai donsu hidimta mata.

Ko yanzu data shiga,ta sameta ita da me aikin morsa safiyya guda daya......wadda asalinta 'yar oromo ce. Tana hada wani abinci rumaisa na gefanta tana kalla suna hira.

Yadda taga rumaisa ta zage tana tayata hadawa,kawai saita samu kanta da sha'awar zama kamar haka. Falaak ta iya komai.....itama dai kamar su rumaisa din,ita aka baro a baya. Morsa safiyya ta taba fadi,duk daba da ita take ba,amma a sannan ta riqe abun,hartana jin zafinta tana ganin da ita take. Fada takewa falaak a wani yammaci datayi kuskuren hada mata wani abincin gargajiya na abzinawa.

"Macen da bata iya girki ba ta rako mata duniya ne. Koda mahaifinta waye......samun hanya ko qofar zuciyar d'a namiji.....tana ga cikinsa,wato abincinsa."

Burinta a yanzun daya ne tak!....ta zama cikakkiyar macen da zata hidimtawa mijinta ba....ba wadda bayi zasuyi hidima da ita sannan suyi da mijinta ba. Sai ta samu kanta dayin tattaki tana harhada plates din da aka gama amfani dasu.

Daga me aikin har rumaisa sunso hanata amma taqi. Suka dinga juyawa time to time suna kallonta,har me aikin ta gama tabar musu kitchen din,saiga Aanani tana santin agadez,harta sauya kayanta zuwa na lounge wear,masu kyan gaske da taushi irin wanda safiyya huguma ke kawosu,saqar qasar china da kaloli masu kyan gaske. 08187255862.

A sannan akhnan din ta nade hannun rigarta,dankwalinta ya zame tana son koyon yadda ake kwaba wani abincin fulawa. Rumaisa tana ta dariya,saidai kuma tana mamakin yadda lokaci daya ta canza.

"Wallahi ni kam ba ruwana.....idan obbo yazo ya tarar kin manta dashi".

"She already did" Wannan muryar tasa me taushi da nauyi ta bayyana.

Cikin shakkarsa suka waiwayo,kowacce tana kallonsa tana qoqarin kama kanta,yayin dashi kuma dukka idanunsa suke kan akhnan.

Muryar ta isa ga kowanne sashe na jikinta,sanda ta waiwayo kuma mamaki ya cikata. Yana sanye da All black pyjama da suka fidda sirrin kyansa. Wato a yau ya amsa cikakken sunan d'an morsa safiyya,shi yasa kanshi tsaye yake takowa har kitchen dinta?. Ba kunya.......ba nauyi?.....ba iso?.

"Allah ya fara kishi.....bari na gudu" Rumaisa ta fada can qasa tana radawa akhnan,saita tsame hannunta daga kwabin,ta isa famfon sink kafin ya qaraso ta wanke hannayenta ta lalubi qofa.

"Tsayani mana yaa rumaisa" Anaani ta fada itama da wannam tsoron nasa da rashin son wargin da suka sanshi da shi tana bin bayan rumaisa din salin alin.💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 130*

Wani irin emotion ne,dake fusgar zuciya da gangar jiki zuwa ga 'yar uwarta......zuwa ga d'aya b'arin nata.....zuwa ga abinda zuciyar da gangar jikin sukeso. Tana ta kwab'a fulawar.....taqi kuma juyowa gareshi,saidai dukkanin gangar jikinta... Dukkanin wani bugu na zuciyarta.... Duk wani sashe dake gangar jikinta jiran isowarsa yakeyi.

Shima kamar ita.... Idanunsa duka yana kanta,yana takawa da wani nannuyan yanayi na kewa,kamar ya shekara bai ganta ba. Saidai shi din yana qoqarin karantarta ne,tun daga tsaiwarta,ya zubawa bayanta idanu sosai. Idonsa ya lumshe yana fidda wani siririn numfashi. Boubou ce a jikinta,gashin nan nata me tsaho da santsi yasauka har kusa da mazaunanta,mazaunan da duk da cewa cikin sakakkiyar sutura suke......amma hakan bai hana bayyanarsu da bayyanar shape dinsu ba da tudunsu. Ya hadiye yawu a hankali yana jin wani irin mahaukacin kishinta. A tausashe ya isa bayanta yana karantar yadda ta qagu ya iso garetan,amma wannan izzar tata tana hanata nunawa. Baiga laifinta ba.....bazai kuma rabata da izzarta ba,don izzar na daya daga cikin abinda ya dauki hankalinsa da ita,yake kuma kan daukar hankalin nasa.(koda kun dade da miji.....ki zama me kamun kai da izza,bawai izza na girman kai wajen kyautata masa da biyayya ba.....aah....izza na kamun kai da nutsuwa,ba baragada......ki zauna kin b'andashe cinya da jiki,waike an zama d'aya,kai a wargatse ba kintsi,da wata bulalliyar rigarki wai ta zaman gida ce,tafi dadin sawa bata da nauyi. Ki zauna da daurin qirji koda datti wai ai wanka zaki shiga yanxu. Kai a tsaitsaye sai kice wai kitso kiketaso kije kin kasa.......please ki zama me aji,harshi kansa mijin yasan ke me aji ce,bawai yammatansu na waje ne kadai zasu zama hakan ba. Sometimes ma fa daidai da kiranki idan yayi kina iya ja masa aji,phone call,kina gani kidan basar ko sai ta kusa tsinkewa da sauransu,normally maza irin wannan attitude din yana jan hankalinsu sosai. Ba always available ba. Ya fita kullum kina hanyar kiransa,baisan ya kiraki ba. Wataran ki kama kanki,ki barshi ya kiraki da kansa mana,ire iren wadannan suna da alfanu sosai,amma hakan kada ya hanaki yi masa biyayya kyautata masa da faranta masa.......amma ki koyi jan class koda time to time ne).

Cikin faffadan qirjinsa ya adanata yana mannewa da bayanta,ya sanya hannuwansa yana lanqwaso hannuwanta sake cikin flour din ba tare daya damu zata bata masa jiki ba,ya aza kansa saman kafadarta yana sauke mata wani irin numfashi me nauyi.

"Haisammm manaaa" Ta fada a shagwabe tana qoqarin zame hannunta don kada ta b'atashi. Sai ya sake mata hannun,amma kuma ya musu kyakkyawan masauki saman qirjinta yana musu kyakkyawan riqon daya sanya jikinta duka ya hau rawa.

"I’m jealous of anyone who makes you forget I exist.” ya fada da wani yanayi cikin muryarsa yana lumshe idonsa,har yanzu kansa yana kafadarta.

"Come" Ya fada da wani irin energy yana sakinta,sannna yasa dukka hannuwansa biyu ya juyo da kafadunta tana facing nasa,sai kuma ya sake boyeta cikin jikinsa yana mata kyakkyawar runguma.

"Mmnnn"
Chapter 143 · 0% Book details