Sashe 128
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A can gefe kuwa haisam ne,yana zaune shiru. Cikin wannan tarin nutsuwar tasa,haiba cikar kamala,yana kallon komai cikin idanun da basa bari a gane me ke zuciyarsa. Baiso zuwa zaman ba.....amma takanas morsa safiyya ta sameshi da roqon alfarmar ya shiga zaman.
"Kai kadai muke kalla yanzu a matsayin wakilin sultane da muka yarda dashi" Ta fada muryarta tana rawa. Magananta da yanayinta yaso karya masa zuciya. Yanajin kamar ya bayyana mata nanay ko zata samu sassauci daga radadin da takeji.
"Zanje.....zanje in sha Allah" Ya amsa mata.
D'aya daga cikin dattawan majalisa ya gyara zamansa kafin yayi magana ta farko tun bayan zamansa a gurin.
“Kamar yadda dokokin masarauta suka tanada…” ya fada yana bud'e wasu takardu
“…akwai kadarorin da baza’a tab'a ba har sai an tabbatar da sabon tsarin mulki.” bata ko d'aga qafa ba mammina ta d'ago kai da sauri. Mamaki take......dama akwai wanda ya rage da zai qalubalanci abinda ta tsara tana so?. Duk da komai yana hannunta,abinda yayi saura baida yawa.....Shima tana da interest a kansa gaba daya. Don har yanzu wannan ZUCIYAR DUKIYAR AJANI din da take kyautata zaton na hannun sultane iya bincike bata ganta ba.
*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*
*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*
*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*
08187255862
*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*
*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*
*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*
08187255862
*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*
*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261
*SHAIDAR BIYA*
08187255862
*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*
*QASAITA👑*
*HUGUMANKU CE*✍🏽
💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 116*
_________________________
*_Mg's ORGANIC SOAP_*
*_Shin kin gaji da banke banken sabulu wa fatarki?_*
*_Kullum ba ci gaba?_*
*_Kullum jiya iyau sai sake lalacewa ma da takeyi?_*
*_matso maza ga maganin matsalanki da izinin Allah_*
*MG'S ORGANIC SOAPS*
*_kamfanin da ya shirya tsaf don samar miki da sabulun da zai sanya fatarki KYAU ta goge tayi haske ME AJI bana bleaching ko me bata fata ba_*
*_KALAN 'YAN ABUJA.....kalar hutu hajjaju,asalin kalar fatarki ta anihin_*
*_Masu matsalan SKIN irinsu PIMPLES,SPOT,ACNE,SUNBURN in sha Allah kukanku ya qare....matsalarku ta qare_*
*AKWAI PACKAGE DA SUKE HADAWA GAME BUQATA*
*yammata.....zaurawa....amare.....da iyayen gida masu capacity wanda ya hada da*
Soap
Facewash
Face cream/body cream
Scrub
Serum
Cleanser
Glow oil
Toner *duka cikin package din*
*_INA MASU FAMA DA NANKARWA(STRETCH MARK)MG'S ORGANIC SOAP bata barku a baya ba_*
*Ku nememu kai tsaye a wannan number don GYARA DA MAGANCE MATSALOLIN FATARKU*
0806 299 1549
*MG'S ORGANIC SOAPS*
*_takenmu (MAIDA TSOHUWA YARINYA....A SABUNTA YARINYA ZUWA SABUWAR HALITTA)_*
_________________________
“Sabon tsarin mulki?” ta tambaya da gadara cikin muryarta.
“Mijina ya riga daya rasu......”
“.....Dukiyarsa mallakin gidan sarauta ce.” Safiyya ta amsa cikin nutsuwa jarumta da rashin tsoro.
“Kuma gidan sarautar yana da magada." Ta qarasa maganan tana sauke idanunta akan mammina.
Wurin ya d'an kaure da maganganu qasa qasa. Wasu suka fara kallon juna.
Mammina ta d'an matse lips d'inta,tana jin wannan qasqancin da takeji cikin jininta a duk sanda safiyya ta qalubalanceta,a magana ko a aiki ko a ra'ayi,tun sultane yana raye.
“Magaji yana prison.”
“Ko ba haka ba?” mammina ta fada tana sanya idanunta cikin na safiyya da nufin bar mata wani ciwo.
Da sauri cikin fushi akhnan ta d'aga kanta tana duban idanun mammina.
“Ke kika shirya masa!” ta samu kanta da fad'a ba tare da wata shakka ba.
Hayaniya ta tashi cikin hall d'in,cikin mamakin qarfin halin akhnan din,wasu amsarta itace daidai da ra'yinsu tuntuni,amma basu da 'yancin bayyanawa.
Juyawa mammina tayi kanta a hankali zuwa ga akhnan
“Ki kula da harshenki Akhnan.” ta fada cikin sanyin murya mai razanarwa
“Rashin ubanki bai kamata ya koya miki rashin hankali ba.” Kafin Akhnan ta sake magana,qofar hall d'in ta bud'e da sauri.
D'aya daga cikin jami'an da aka zube cikin gidan tun rasuwar sultane wanda ba wanda yasan amfanin me suke ya shigo. Sai wani jami’in ya shigo da numfashi sama-sama kamar wanda yaci gudu.
A hannunsa akwai wasu takardu masu hatimin masarautar agadez.
“An samu wasu sabbin hujjoji.”
Wurin ya yi tsit nan take maganansa na amsa kuwwa cikin hall din.
Idanu haisan ya aza a kanta yana tattara dukka attention dinsa a kannata,mammina ta d'an jingina bayanta jikin kujera.
"Calm....too calm" Ya fada can qasan ransa.
Jami’in ya qarasa gaban majalisar ya bud'e takardun.
“Wasiku ne…” muryarsa cike da nauyi ya dora
“…da suka shafi wani shiri na tayar da tawaye.”Jami’in ya ci gaba da karantawa.
Lissafowa ya fara yi,sunayen guards,lokutan ganawa da kuma sirrin shirin fasa prison d'in da Ahmad yake kulle. Komai a tsare daki daki. Sai ya karanta layi na ƙarshe.
“zuzzurfan bincike ya bayyana cewa dukkan umarnin sun fito ne daga MORSA SAFIYYA". Maganar tazo da wata irin razani.....wani irin gigitaccen yanayi da hankali bai taba kawoshi ba. Wurin ya hargitse da surutai.
Wasu suka mikewa tsaye cikin mamaki.
“QARYA NE!” falaak ta fada da wani razanannen sauti. Bata gane komai akhnan,kawai hannunta ta miqa gurin da jami'in dake daura da ita yake tsaye ta fizgi takardun daga hannunsa.
Da sauri ta fara dubawa,zuciyarta na bugawa. Tunaninta taji kaman zai juye lokaci guda,saboda hujjojin sun yi kama da gaske sosai.
“No…” ta fada da harshen faransanci a razane. Cikin rawar murya ta sake cewa
“Wannan ba gaskiya bane…”
Mammina ta miqe tsaye a hankali,wani kwantaccen murmushi da ba kowa zai iya ganeshi ba kwance qasan Fuskarta
“Hajiya Safiyya…” ta fada cikin izgili da cikin cikakken iko
“Bisa dokar masarauta…”
“…ana zarginki da had'a baki wajen tayar da tawaye akan karbar karagar mulki"
"Ina jami'an tsaro?" Ta fada da muryar gaggawa. Kaman a shirye suke daman,umarnin kawai suke jira,nan take suka shigo cikin hall d'in. Makamai d'aure a jikinsu,kamar wadanda sukayi shirin shiga fagen yaqi.
Da sassarfa akhnan ta miqe tana matsawa gaban morsa safiyya. Wani irin tashin hankali.....burin bata kariya da bata taba jinsa ba na har abada ya taso mata.
“Babu wanda zai taba ta!” ta fada tana fidda manyan blue eyes dinta waje.
Dakatawa sukayi,kaman sunji umarni daga gareta ne,saidai ba haka ba. Har yanzu ita din d'iyar sultane ce,wani abu bai sauya wannan matsayin nata ba,kuma ita din matar sheikh haisam ce,babu wanda zaiyi kuskuren kaudata koda giyar wake yasha.
Mammina ta lura da hakan,sai idanunta suka qanqance. Wai me yasa har yanzu da sauran wannan mutucin nasu a idanun mutane?,harda mutanenta ma ballantana nasu mutanen?.
“Wannan rainin hankalin ne ya lalata wannan gida!” ta fada tana duban kowa dake gurin.
"Tana ganin ta isa ta sauya doka kota hana zartar da ita?." Ta fada da sigar tambaya me cike da zafi.
A hankali,kuma cike da tarin nutsuwar nan morsa safiyya ta miqe tsaye. Cikin alhini. Cikin mutunci. Kamar ba ita aka karantowa wadannan munanan zarge zargen ba,ta gyara mayafinta cikin nutsuwa,sai ta kalli Mammina kai tsaye.
“Ina miki jaje.....Kin kasa cin galabata yana raye.”
“Shi yasa kika jira mutuwarsa......wannan itace CIKAKKIYAR FADUWARKI....WANNAN KE NUNA KIN KASA KIN GAZA....ina sake jajanta miki akan gazawarki" ta qara fada wani murmushi yana fita daga saman labbanta.
Wannan murmushin dai.....wannan murmushin data tsana a fuskar safiyya. Wai sai yaushe?,sai yaushe zata samu nasarar dakushe wannan murmushin?. ta d'an matse hab'arta tana jin murmushin safiyya kamar zubar garwashin wuta saman fuskarta.
“Ku tafi da ita.....doka ta hau kanta” matsawa sukayi,saidai kowa ya kasa saka mata qarfe ko tabata.
"Muna iya tafiya" D'aya daga cikinsu ya fada muryarsa da nauyi sosai.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
Kuka falaak ta rushe dashi,yayin da Akhnan jikinta ya dauki rawa da wani matsanancin fushi. Gaba daya hall d'in ya rikice da wani yanayi me taba zuciya.
Duban akhnan morsa safiyya tayi,sannan ta kama hannunta a tausashe tana murzawa da wani yanayi daya taimaka wajen tattara nutsuwarta na dan lokaci.
“Ba kowanne yaqi ake cinshi da ihu ba.” cikin nutsuwa ta d'ora
“Wani lokacin gaskiya tana jira ne kawai......tana jiran lokaci ta bayyana kanta tayi yado da yabanyar da kowa zai ganta". Saita zame hannunta daga cikin na akhnan din ta fara takawa cikin nutsuwarta.
Dab da haisam ta dakata,ta tsaya ta kalleshi still da murmushi.
"Ga amanar 'ya'ya na nan.....ina da tabbaci da yaqini a kanka,na yarda dakai d'ari bisa d'ari,ba zaka taba cin amanar sultane ba.....ba zaka gaza daga riqon amanarsa ba.....ba kuma zaka kasa ba har abada" Ba tare data sake kallonsa kota sake cewa komai ba,taci gaba da takawa tana fita,jami'an tsaro a gabanta wasu a bayanta.
Kallo daya kawai.
Amma kallon ya isa ya saka wasu daga cikin dattawan majalisar jin tsoro. Saboda har yanzu Haisam bai motsa ba. Bai hana komai ba. Kuma wannan shiru nasa… shi ne mafi tayar da hankali a cikin duka masarautar. Baga mammina kawai ba.....ga kowa da kowa,kowan din da ajin da yake sanyashi.
"Sun hada kai ne da mammina"
"Shima tsoro yake"
"Bazai iya da ita ba" Da sauran maganganu masu kama da wannan.
*BAYAN SHUDEWAR WASU AWANNI*
Daren Agadez ya yi nauyi da tashin hankali mara misaltuwa a zukata da rayukan al'ummar masarautar dama na wajen masarautar.
Tun bayan tafiya da morsa safiyya sam akhnan ta kasa samun nutsuwa. Tayi kuka irin kukan daya ninka wanda tayi randa ta tako agadez ta tarar ba sultane babu dalilinsa.
Komai yana mata yawo a kai,kama Ahmad,canjawar masarautar da wani mummunan yanayi mara dadin ji ko saurara.
MAMMINA......yadda komai ya sauya cikin d'an lokaci. Yadda komai ya fara ta hannunta?. Komai ya soma ta sanadinta?. Komai ita ta shukashi?,ita ta farar dashi?.
Ta kasa yarda d'ari bisa d'ari akan haka kawai komai ke tafiya haka,saboda a duk rayuwarta,ko da Mammina tana da tsauri… ta tab'a d'aukarta a matsayin uwa......da idanu irin na uwa take kallonta.
Ita ta raineta tun shekarun quruciya har ta girma ta zama mutum......ita ta koya mata abubuwa masu tarin yawa. Ita ta rungumeta lokacin da tana qarama,lokacin da batasan komai ba,batasan kowa ba,lokacin da batasan hagunta ba batasan damanta ba.
Ko da akwai nisa a tsakaninsu wannan nisan baya hana mammina sanyata ta jita kamar tana a gabanta.