← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 162 OF 176

Sashe 162

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Malamina.." Ta kirashi da sunan da take kiransa a wasu lokutan.

"Sleep babe" Ya fada muryarsa can qasa.

"Na sani.....amma banji kace komai ba"

"Sai da safe" Ya fada da yanayin daya tabbatar mata bacci yakeso tayi. Bata musu dashi,bata iyawa sam,sai bata sake cewa komai ba,ta maida idanunta ta kulle,har bacci yayi awon gaba da ita.

Sanda yaji tai relax sosai ya tabbatar masa bacci ne,sai ya zare jikinsa a hankali ya dauki wayarsa yana sauka zuwa parlor din qasa.

Dr farrah ya fara contacting,yasan yanzu haka tana asibitinta,ma'abociyar night duty ce,yasan zai wahala ace tayi bacci a sannan.

Sun jima sosai suna tattaunawa da ita,tayi connecting kiran da sauran teams din. A qarshe suka yanke shawarar ajiye kwanaki goma a gaba don cirewa akhnan jariran,don dukkaninsu girma da nauyin cikin yana basu mamaki,suna zuba ido suga wanne irin manyan babies haka zata haifa?. Dalilin da ya sake jan hankalinsu kenan ma wajen cire yaran,kada garin bata dama ya zame mata matsala.

Washegari kallonta kawai yake,yana jin kamar ya mata wani kuskure ko ba daidai ba. Itakam shirye shiryenta kawai takeyi. Yana jinsu sanda rumaisa tazo gurinta wadda surukuta takeyi yanzu kawai da akhnan din,duk da girma suke bawa juna sosai,saboda kowacce tana matsayin mata ga yayan daya.

★★★

*_AGADEZ & ETHIOPIA_*

Wani gagarumin shirin bikin aure ne ke motsawa tsakanin qasashen guda biyu. Bikin auren da tuntuni sati biyu kafin zuwan lokacin hotuna da short short videos na kayan auren kowacce ya karade social media. Harma wadanda ba 'yan qasashen ba suna tambayar yaushe ne bikin?,'yan wacce qasa ce da sauran su.

A yadda aka tsara....za'a faro bikin daga agadez dinne. Za'a dauro auren shehnaz da aisa,sai a daukosu a taho dasu jimma,sannan a nan a daura auren rumaisa da Anani,su karbi su shehnaz.....a basu su rumaisa da Anaani kuma.

Saukar safe prince sheikh muhammad haisam aba jifar da gimbiyarsa khadeeja sultane muhammad hammud sukayi a private jet dinsu cikin filin sauka da tashin jiragen sama dake agadez. Kai tsaye kuma motocin alfarma,cikin royal convoy dinnan nasa masu daukan hankali suka daukesu daga airport din zuwa personal home dinshi.

Narke masa idanu akhnan tayi,rabonta da agadez tunda aka kammala case din mammina. Ta qagauta taga babyn falaak,ta qagauta taga sultane....ahmad....morsa safiyya da yanzun take kallonta kamar mamminta,da wasu kamannin mammin nata da sai yanzu take ganinsu tattare da morsa din.

"Na dauka masarauta zamu wuce" Ta fada tana dubansa,don tun kafin motar ta fita daga airport ma,zuciyarta tana can. Amma lokacin da ta lura convoy din ya kama hanyar personal residence din haisam...sai taji ta kasa shuru.

Bai ma dago daga tablet din hannunsa ba ya amsa kai tsaye a taqaice

"A'a." Sai ta hade gira.

"A'a?" Ta maimaita. Sai a sannan ya dago idanunsa gare ta.

"Kin yi tafiyar sa'o'i da yawa."

"Haisam..."ta kirashi a narke.

"Akhnan." Shima ya kirata kama yadda suka saba idan akwai sabanin ra'ayi.

Sai ya gyara zamansa ya katse ta cikin nutsuwa.

"Wannan ba maganarki bane."

Ta san muryar nan,muryar da ke nufin ya riga ya yanke hukunci,sai ta jingina da kujerar motar tana hura hanci.

"Ni ban gaji ba." Wani dan murmushi ya bayyana a fuskarsa.

"Good." Ya fada kawai. Ta dan gyara zamanta.

"Ashe zamu iya zuwa kenan."

"No." Ya sake amsawa a taqaice. Halinnan ya motsa,na masu tsohon cikin da kusan haushin kowa sukeji. Ta watsa masa wani kallo me kama da harara a fakaice,shi kuwa ya ci gaba da kallon tablet dinsa kamar babu abin da ya faru.

Kaman zata saki kuka taji,batason wannan salon nasa.....wani irin salo ne da idan ya yanke abu duk tsaurin idanunka baka iya masa musu. Yana da wani irin kwarjini da badai ka kalli tsabar idonsa ka gaya masa wani abu ko ka musa masa ba.💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 149*

Bayan sun isa gida haisam ya tilasta mata cin abinci da hutawa,har sai da ta yi bacci na awa uku.

Tana ta farkawa kuwa toilet kawai ta shiga ta wanke fuskarta,ta bulla wani daki ta dauki ruww,bata ma kammala shanyewa ba ta soma lalubensa.

Ta same shi a office din nan nasa na cikin gida.

Da cikakkiyar sallama ta shiga,ya daga kansa daga wata takarda ya amsa mata yana qare mata kallo. Yadda cikin ke rinjayarta kullum bashi tausayi takeyi,amma ita din kafiyarta da irin jarumtarta na sake burgeshi wani lokaci.

Zama tayi saman sofa,har sai daya miqe da zummar kamata amma taka qarasa zama.

"Haisam." Ya dago kai.

"Mm?"

"Na huta."

Ya kalleta na wasu seconds bayan ya koma ya zauna. Sai ya rufe file din da yake dubawa.

"Good."

"Yanzu zamu iya zuwa." Ta fadi tana marairaice masa. Ya san ba zata daina ba,ba zata daina roqonsa ba.
Sai ya girgiza kai.

"One hour."
Idanunta suka soma tara qwalla.

"Da gaske?"

"One hour."
Ya maimaita.

"Ita zaki ki dawo." Ta gyada kai da sauri. Ta fahimci idan ba haka tace masa ba,tsaf zaice ba zata ko ina ba sai gobe. Ita kanta ta san ba zata yi biyayya a yau ba.

Sosai masarauta ta cika da farin cikin ganinta. Komai ya koma daidai cikin wani irin yanayi da kowa bai taba zaton faruwarsa ba. Wani irin mulki ne qarqashim jagorancin ahmad,wanda yake cike da hikima irin ta sultane da zamananci irin na ahmad din,da kuma shawarwari daga haisam. Mulkin sai ya zama wani iri,kuma na musamman,har yaso yafi na sultane dadi.

Me jego falaak na manne da ita. Morsa afiyya ta qi sakinta,kallon akhnan din kawai takeyi tana godewa Allah daya sanya komai yayi farko yana da qarshe.

Sultane kuwa ya kasa boye murnarsa shima da zuwan shalelensa. Don ma kunya ta hanata sakewa dashi.

Yarinyar falaak tubarkalla,qatuwa fara tas kamar ba daga cikin falaak ta fito ba saboda girma. Ta dade a hannunta ta hanawa kowa ita,har tanajin kamar ta bude idanu taga nata yaran. Sai a sannan taji itama mace takeson haifa,don ita sam basu tsaya tambayar wanne gender bane,haisam din yace kowanne Allah ya bashi yana so,yana maraba dasu.

Kaf ta manta dukka sharuddan daya sanya mata na zama ta huta da taqaita zirga zirga,bayan ya amince ya qara mata wasu awannin biyun akan awa dayar farko.

Sai data kusa zagaya rabin masarautar,inda duk ta dade bata shiga ba. Ta shiga wani sashe,ta fita wani.

Ta je wajen dawakai,dawakanta da tayi kewa,duk da haisam ya siya mata wasu daga qasashe daban daban,amma akwai sabo da kewa me yawa tsakaninta da wadannan. Ta je wajen lambuna,sun jima a ciki ita falaak suna tuna abubuwa da yawa da suka faru a gurin,ciki harda zuwan samarin dake neman aurenta,da ganinta da haisam a guraren na farko.

A jikinsa yake jin bata zauna ba yadda yace mata. Da yamma yana cikin meeting da shugabannin tsaro na gidan,daya daga cikin jami'an tsaronsa ya qaraso.

"Your Highness."
Haisam ya dago kai.

"Yes?"

"Sun bada tabbacin bata zauna ta huta ba" Sai ya ajiye biron hannunsa.

"How long?"

"Tunda kuka iso" A hankali Haisam ya lumshe idanunsa. Kwana goma kacal suka rage. Kwana goma zata kwanta a fedeta,amma ta kasa bawa jikinta wannan nutsuwar tun yanzu?.

Sallah ta koma yi sashen haisam dake cikin gidan,tana tura bedroom din yana tsaye ya kammala alwala shima zai wuce masallaci.

Tun kallon farko ta gane yana fushi. Irin fushin shiru din nan nasa.

"Me kuma nayi?"
Ta tambaya da salon kama kai irin na wanda yasan yayi laifi.

Ya juya a hankali.
"Kin huta?" Ta dan yi murmushi tanason boye laifinta.

"Eh."

"Really?" Yadda ya fadi kalmar ya sa murmushinta ya dan ragu.

"Haisam..." Ta kirashi ganin yana neman qureta da wannan narkakkun idanun nasa masu tsananin kwarjini.

"Kin zagaye masarauta yau son ranki." Shuru kawai tayi,cikin ranta tana gayawa kanta ashe an kai masa rahoto?. Wanne irin damuwa haka yayi da lamuranta?.

Ta dan kau da kai.
"Ba wani abu bane me yawa fa."

"Kina da tsohon ciki." Muryarsa ta yi qasa da wami nauyi a cikinta.

"Kuma kin yi tafiya me yawan da bai kamata kiyi ba right?" Ta yi shiru,shi kuma ya sake zuba mata idanun nan nasa masu girma da haske.

A hankali ya qaraso kusa da ita.

"Ba zaki kwana a nan ba." Ta daga kai da sauri,ta dauka zai barta ne ganin har ya sake qara wasu awannin. Ta saki jiki zaman gidan ya mata dadi sosai.

"Please" Ta fada tana tara hawaye.

"Zamu tafi gida tare"

"Haisam!"ta kirashi

"No."Ya katse ta.

"Bana son gardama akan wannan."Ta kasa yarda.

"Falaak fa....."

"Zata ganki gobe."

"Sultane...."

"Zaki zo gobe." Dukkaninsu sukayi shuru sannan ya qara da wani irin sanyin murya mai cike da damuwa

"Amma yau gida zaki tafi,shine kwanciyar hankalina da nutsuwata." Akhnan ta lura da wani abu a idanunsa. Ba iko bane. Ba tilastawa ba,kaman tsoro ne.
Irin tsoron da yake boyewa tun watanni da cikin ta ya fara wani irin girma. Tsoron wani abu ya same ta ko jaririn. Batasan me yasa sam baida jarumta akan komai daya shafeta ba. Rago ne shi sosai ta wannan bangaren ba kadan ba. Sai kawai ta sauke numfashi. Ta san cewa a wannan karon....ba zata ci wannan musun ba.

Motar ta bar masarautar cikin shiru. Irin shirunan mai nauyi da ke nufin akwai wanda yake fushi.

Akhnan ta zauna gefen window tana kallon hasken Agadez da suke wucewa.

Tun fitowarsu daga masarautar bata sake cewa komai ba. Bata kalli Haisam ba. Bata tambaye shi komai ba.
Shi kuma ya barta,saboda ya san wannan shirun nata.

Har yanzu ba abinda ya sauya sultane,har yanzu goyon bayan haisam yakeyi akan komai. Kaman baiyi kewarta ba kanshi tsaye yace mata tabi mijinta.

"Akhnan." Ya kirata bayan ya tabbatar bazai jure shirunta ba. Bata amsa ba,sai kawai ta ci gaba da kallon waje.

Wani dan murmushi marar qarfi ya bayyana a fuskarsa.

"Habibti." Ya sake kiranta dai bai gaji ba.

Har yanzu babu amsa,sai ya mayar da kallonsa gabansa.

"Good,at least now I know you're angry." A wannan karon ta juya ta kalle shi.

"Ka sani kenan."

"Mm." Kasa cewa komai tayi saboda qwallar data sake cika mata ido,sai ta sake mayar da kanta gefe. Shirun motar ya sake komawa kamar da.
Chapter 162 · 0% Book details