← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 176

Sashe 11

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Goge" Yace da abdii yana cilla masa wayar. Yadda ya cilla wayar banda abdii din ya nuna zafin naman cafeta ba abinda zai hanata faduwa ta fashe a qasa.

"Amma......" Abdii ya bude baki zai magana,yanason gaya masa hoton tarihine,kuma ba kowa bane ya fito a ciki,yanason ya ganar dashi ba komai a cikin irin wanna hoton,amma kallo daya.....kallo daya daga haisam din ya kulle bakin abdii.

"Tashin hankali" Omar ya fada qasa qasa yanayi sosa sumar kansa. Irin wannan kallon na haisam dukkaninsu sun sanshi. Kallo ne dake daureka da dukka wata jijiya ta jikinka,ya hanaka musu ko motsi har sai kayi abinda yace maka.

"Obbo na goge"

"Ka gogeshi daga trash ma" Ya fadi yana isa bakin fridge ya fidda ruwa mara sanyi ya soma zubawa a glass cup.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 10*

Kallon kallo aka fara yi tsakaninsi,banda naseeb daya fuske. Har cikin zuciyarsa baiga laifin haisam ba.....ballantana haisam din da tun da can sunsan halinsa. Sarai ba wanda ban sanshi ba akan kishi,diya mace kadai wadda bai hada alaqar komai da ita ba kishinta yake ballantana wannan da igiyar aure ta gilma tsakaninsu koda ba soyayya?. Mutumin da kishinsa ya hanashi yayi soyayya da kowacce mace?. Saboda bazai so ba kuma sannna ya sakarwa wani?. Shi a karan kansa kallon haisam yake da yake fadin auren Akhnan tsani ne kawai zai zame masa.......amma ya sani,wani aure ne da Allah kadai yasan yaushe zai qare.......ga alamu nan kuma shi da kansa yana barwa kansa da kansa ba tare ma da yasan me yake aikatawa ba.

"Da alama hoton dai yana da muhimmanci sosai". Khadeem ya fadi wanda idan bai tsokani haisam ba tun da can dama shi baya jin dadi.

Ya jishi sarai,ya kuma fahimci inda ya dosa,amma sai yayi banza dashi,bai bashi amsa ba har sai da yayi bismillah ya dansha ruwan ya ajiye cup din.

"Ba kowane ya kamata ya riqe wasu abubuwa ba"

"Bafa hoton bane.....itace" Omar yayi gulmar da amjad da yafi kusa dashi,amjad din da mamakin haisam duka ya kasheshi ya kasa magana.

Sam omar ya manta dabi'arsa......wani irin kaifin ji gareshi,bai kuma san haisam din yaji ba sai sanda ya bashi amsa sanda yake dab da fita.

"Ban saba raba abinda na mallaka ba da kowa......komai da yake mallakata zai zauna a iyakokina har sai sanda ya daina amsa wannan sunan".

Yana jinsu.....yana jin kakacinsu da komai nasu,ya tabbatar idan da yana zaune a cikinsu sai sun kusa cinyeshi,tsiya kam ya barsu a yanzu suyi son ransu.

Murmushi kadan ya subuce masa,murmushin dashi kansa baisan daga ina ya taso ba.......kawai ya tuna yadda ya nuna ne. Shi kansa bazaice ga abinda ya jashi ba,bazaice ga abinda ya sanyashi yayi wani reaction din ba,abu daya kawai ya sani,bai samu salama har sai daya samu tabbacin abdii ya goge,duk da baida zargi ko haufi akan abdii din.

"Me kenan?,kishi?....." Yaji tambayar ta subuce masa. Kansa ya girgiza a hankali yana dogare gwiwar hannunsa jikin murfin motor din.

"Ba kishi bane wannan.....dom ba irin wanna feeling din na saba ji ba....."

"Eh qarfin wannan ya d'ara na kishin da kake zaton kana dashi?.....saboda wannan din zahiri ne ba gaibu ba". Kai ya sake kadawa a hankali,ya aza dukkan qarfinsa yana ture tunanin gefe,don yana ganin maganan wani qofa daban da babu ita takeson bude masa,sai ya fidda wayarsa ya turawa omar gajeran saqo.

_Zan shiga gurin sultane_ ya aike masa yana maida dubansa kan titunan da suke wucewa.

_Ka sanar dani idan akwai buqatarmu a kusa,zan zama cikin shiri kusa da wayata_

Amsa ta shigo masa da gaggawa daga omar. Murmushi ya saki dan siriri,wanda har ya sanya har kyawawan labbansa suka bude kadan.

Masoyin gaskiya ba qarya bane,ubangiji yana iya hada zukata suso junansu da tsaftatacciyar soyayya da aminci. Kaman dai......su bakwai din tamkar uwarsu daya ubansu daya,ba wanda keson ganin kuka ko damuwar daya,hakanan dukka team dinsa da yayi aiki dasu,da wani abu ya sameshi har abada suna zabar su ya samesu.

Idonsa ya lumshe sannan ya bude,baisan yadda sultane zai karbi maganar ba..... Zai iya jurewa?......ko kuma bazai iya dauka ba?. Ya fidda numfashi a hankali yana tuna maganganunsa dazu da almaz.

"Ka bari muje tare,na bayyanawa duniya na santa,nasan adadin fuskokin da take dasu......ta batamin hotona a fuskokin al'umma.........ta yaya sultane hankalinsa zai fara daukan ni d'ansa ne bayan na amsa sunan surukinsa na kwanaki uku?".

Ya sani,abune me matuqar nauyin gaske,amma a yadda Ahmad din ya sauya a yanzu,ba kowa bane zai gane farat daya shine wancan almaz din ba,uwa uba sai Allah yayi wani abu cikin hikimarsa,ya hana sultane da duk wani me ruwa da tsaki ganawa da almaz a wancan lokacin,so da yawa basusan fuskarsa ba.....idan kuwa har mammina ta zama na farko da zata bankada maganar......zaiso haka,don zata burmawa kanta wuqa kakkaifa idan har hakan ta kasance.

_Tofa......sheikh haisam........ko sultane zai yarda dakai?,ko sultane zai gasgataka?_

Tun daga bakin babban gate din daya mallaki manyan katangun masarautar ya sanya salaana ya saukeshi. Cikin nutsuwa da kamala ya dinga takawa zuwa cikin gidan,yana kuma gaisawa da dukkan hadimai,tun daga masu tsaron qofofi har zuwa masu kai kawo don tabbatar da komai na tafiya lafiya cikin masarautar dama wadanda uzurorinsu ne suka fito dasu.

Komai yana nan akan tsari doka da qa'idar daya bayar. Hakanan kowa yana bakin aikinsa daidai da yadda ya dace. Ya sani komai zai tafi daidai din,dom fiye da rabin masu tsaron dukka sun fito ne daga qarqashinsa da kuma horonsa.

Daga iyakar da yasan labarin shigowarsa masarautar zai iya kai mata......daga nan ya danna wani device don bawa mutanensa umarnin dauke hankula da masu kula da doguwar hanyar nan dake shimfide da interlocking,doguwar hanyar data zama kebantacciya da ba kowa ke da ikon binta ba,doguwar hanyar kuma da zata iya sadaka da sasannin sultane akhnan morsa mammina dama sashen baqi na musamman makusanta.

A nutse ya bude qofar ya maidata kamar yadda take,ya kuma soma takawa a nutse yana kutsawa ciki.

*A K H N A N*

Bayan dukka tarin hayaniya da shiga cikin jama'a data jima batayi irinsa ba a yau.......ta zare jikinta daga cikinsu tun bayan sallar isha'i awa daya da rabi data wuce,ta kuma zabi dawowa dakinta da nufin tayi sallan magariba ta kwanta ko bacci zai dauketa.(haramunne bacci bayan sallar magariba,manzan Allah yace duk wanda yayishi bayan ya farka duk abinda ya sameshi ya zargi kansa).

Alwala tayi kawai sannan ta rage kayan jikinta da taimakon birra kamar kullum. Ta tayar da sallah sannan ta idar bayan ta cewa birra bata buqatar kowa da komai.

Da gaske take data fadi hakan,har yanzu wani nauyi takeji cikin zuciyarta,nauyin da batasan na meye ba......saidai bayan wucewar kowacce awa tana duban agogo.....kuma lissafin KWANA HUDU ZUWA YAU bai tsinke daga kanta ba,duk da qoqarin manta hakan da takeyi.

Zaune tayi saman abun sallar bayan ta kammala sallar. Zuciyarta ta nace da tambayar

"Kwanakin sun qaru" Idonta ta lumshe,tanason sanin ainihin damuwarta akan zancan.

"Ba wanda ke maganar qaruwar kwanakin........ko sultane baiyi wani magana ba akai......"

"Me yake damunki ne akhnan?.....me yasa kika damu da qarin kwanakinsa?.....me yasa kika damu da rashin jin motsinsa......da rashin jin komai ma daya shafeshi?" Zuciyarta ta jefa mata tuhumar data tilastata bude dukkanin idanunta tana kallon guri daya. Guri dayan da take ganin kamar a kallonsa kadai zata samu amsar tuhumar da takewa kanta da kanta.

"Qila saboda shima ya nuna damuwa a kanta a sanda buqatar hakan ta taso......qila saboda yayi mata wani gagarumin taimako na kubutar da rayuwarta.....qila....qila qila din da yawa,saidai abu daya daya sanya komai dauke mata dif shine......qila tana jin wani kadaici.....wannan kular......wannan kulawar wadda ke mata kamanni da takura da tsanani a wasu lokutan duka babu su. Taji wannan sosai yau a jikinta,a taron walimar.....ta dinga jin cewa inda yana kusa.....inda yana tare dasu a sannan,qila lullubinta......rigarta data dinga zamewa dukka idanu da hankulansa suna kai. A yanzu fa?duk da kulawar birra.....duk da tarin hadimai amma sai takejin kaman ta rasa wannan bangaren.

A hankali saita kifa kanta saman cinyarta,sai takejin kamar wani abu ta rasa me girma. Amma duk da hakan zuciyarta taqi amanna dari bisa dari,zuciyarta hujjoji kawai take bata mabanbanta. Hujjar an mata aure a sanda bata shirya ba.....hujjar aure da mijin da bata shiryawa ba.....hujjar zata bar qasarta......kamfaninta......sultane dinta dama komai nata.

A yau da kanta ta hadawa kanta ruwan wanka,saidai rashin sabo dayin hakan ruwan yayi zafi da yawa harsai data fita ta qara tara na sanyi,shi kuma ya kusa salamcewa,a haka tayi wankan,ta fito kuma ta shirya cikin farar gown cotton me yankakken hannu,rigar da saboda rashin kaurinta kana iya hangen shatar bra dinta idan ka sanya idanu sosai.

Iskar dake ratsowa ta tsakanin labulen dakin ya tabbatar mata hadarin dake ta hada kansa dazun a yanzu ya kammala wannan aikin. Ta shaqi iskar can cikin hunhunta da zummar fesarwa,saidai cak ta tsaya da iskar cikin hancinta saboda gauraya datayi mata da wannan qamshin.

Wannan qamshin dai daya zame mata jarrabi.....wannan qamshin dai dake sama mata wata dukkan nutsuwa ya kuma birkita mata tunani a wadansu lokuta....wannan qamshin.......wannan qamshin,saita saki iskar da sauri,ta sake shaqar wata da hanzari da nufin tantancewa.....shin da gaske qamshin takeji ko kuma gizo ne hancinta yake mata?.

Sake bude idanunta tayi tana sakin iskar a karo na biyu. Qamshin dai da gaske takeji,hancinta bai mata qarya ba a dukka karo ukun,to amma bataga koda alamar gilmawar kowa ba ballantana tayi tsammanin shine.
Chapter 11 · 0% Book details