← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 176

Sashe 18

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Biftu" Taji muryar aisa da tayi wani irin mugun sanyi ta kira sunanta.

"Aisa?" Ta maimaita sunanta itama tana jin wani yanayi.

"Kiyi haquri biftu.....na kasa.....na gaza riqe wannan amanar,komai yafi qarfina biftu bazan iya ba,zan ajiye zan dawo agadez" Tayi maganan muryarta wani iri. Shuru akhnan tayi,zuciyarta na faffasa yadda taji sautin muryar aisa. Muryar aisa ba haka take ba.....ba haka yanayin aisa yake ba,bata da wannan raunin,tana da taurin zuciya da kafiya shigen nata,duk da cewa ita ta fita sauqin sarrafuwa da sassauci.

"Mene ne aisa?"

"Komai ma biftu,komai ma,amma kiyi haquri ki yafemin,zanzo zamu zauna,komai nawa yana gayamin KIN GAZA AISA.....komai nawa yana gayamin kaman naci amanarki ne,kamar ban kyauta ba,kamar zunubina bazai wanku ba,kamar na zama sanadi.....kamar nice sila" Dukka tayi maganan muryarta tana sake raunana sosai.

Maganganun sunwa akhnan nauyi da girma da yawa,tana qoqarin magana taji alamun aisa ta datse kiran,ta kalli screen din,saita soma yunqurin kiranta amma na'ura ta shaida mata wayar a kashe take gaba daya.

Bata natsu ba,ta miqe ta zauna ta fara kiran shehnaz. Kaman dama wayar na hannunta ne tana jiran kiran akhnan din ta daga.

"Shehi....Qu'est-ce qui se passe avec Aïsa?(me yake faruwa da aisa?" Ta tambayeta da french.

"Je ne sais pas.mmmmc'est étrange,je me demande pourquoi elle pleaurait(Ban sani ba nima,baqon abune wannan.....inata mamakin me yasata kuka)" Ta fada da alamun damuwa sosai cikin muryar shehnaz din.

Shuru akhnan tayi,tana sauraren bayanan shehnaz.

"Tun kwanakin can nake jin yanayinta kamar ba'a daidai ba,bata fadamin ba bata kuma nuna tanaso naji ba shi yasa ban matsa mata ba,amma koma meye gobe ko jibi tace zata taho,ko bata sameki ba ni zan jirata naji" Kai ta gyada a hankali

"Allah ya kaimu". Ta katse wayar sannan ta koma a hankali ta kwanta,saidai har zuwa sanda bacci ya dauketa aisa ce a ranta.

*M A M M I N A*

Bata taba jin tana so tayi kuka a rayuwarta ba irin yau........ta jima kuma bataji kuka yana neman hallaka numfashinta ba irin yau din.

Duk wani hadimi da hadima dake kusa kusa da dakunan baccinta ta sallamesu,ta kuma kulle kanta a daki tayi wani irin kuka harda ihu daidai da yadda take jin baqincikinta zai ragu.

Batasan adadin tsahon lokutan data dauka ba a haka ba,har sai data tabbatar ta samu sassaucin abinda takeji qasan ranta,sannan ta shiga bandaki tayi wanka da ruwan sanyi waiko zata samu sassaucin abinda takeji cikin jikinta.

Dawowa tayi dakin,tayi zaman dirshan,zaman 'yan bori tana qoqarin farfasa tunaninta daya bayan daya.

Ayau,ta samu dukkan tabbaci da yaqinin sheikh muhammad haisam yana cikin jerin sahun mutanen da suka shigo agadez don farmakarta

"Idan ba haka bane?,me ya hadashi da almaz?......kenan dama can almaz din yana hannunsa?,idan haka ne dukka al'ummar villa street suna hannunsa kenan". Wani irin zazzafan gumi taji ya karyo mata,haka kawai takejinta kamar ita kadai ce.....haka kawai takeji kamar ita kadai ta rage a wannan sansanin,......a wannan filin. Batasan me yake damun tafsu ba,cikin kwanaki gaba daya wani nesa takeyi da ita wanda ta bada uzuri da juyawar ciki da har yanzu ta kasa saurara mata. Da waye zatayi shawara?,waye zai hango wata mafitar da ba lallai ita din ta hangota ba?.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Tambayar da tayi mata tsaiwar mashi aka,bata kuma samo amsarta ba......sai wani courage daban da takeji daga wani sashe na zuciyarta.

"Karki yadda ki fadi.....karki yadda kaikai qasa......koda yanzu kina tunani motsinki zai iya zama barazana.......ki bashi lokaci,sanda zai tashi daga agadez zuwa qasarsa......wannan futar ki tabbatar ta zame masa fita ta qarshe daga qasar......daga yankin nan. Fitar da zata sama nisa na har abada tsakaninsa da agadez da kuma sultane.

"Ki daure......a qarasa komai dashi......ya fita yabar qasar,komai zaizo da sauqi" Wani murmushi ta saki,murmushin dake da alaqa da sassaucin data samu da 'yan qanqanuwar mafitar da zuciyarta ta bata.

Burinta a yanzu ba control bane......babban burinta a yanzu shine ta qarasa aikinta na ture kaza daga kan qwai ta kwashe qwan.....kauda sultane me gaba daya,ta kuma tumbuke bishiya daga tushenta,tayi rantsuwa........ta kuma lashi takobin tabbatar da wannan aikin,a kusa ko kuma a nesa.

Wayarta dake gefe ta dauki qara da tsuwwa,ta waiwaya ta zuba mata ido kamar ma ta manta da ita. Kamar ta shareta,kaman kada ta dauka,amma sai sunan dake harbawa saman screen din yaja hankalinta,ta miqa hannu ya daga ta saka a kunne.

Batace komai ba,amma maganan da ake mata daga wancan bangaren ya sanya wani shu'umin murmushi subuce mata.

"Ko a iya nan kun kammala aikinku......inaso kowacce hujja ta bata ta salwanta kamar komai bai taba faruwa ba.....burina akan sahel couture ya gama cika........aiki ya kammala.......ku jira sakamakonku........ina alfahari dakai" Takai qarshe tana cije labbanta da haqorinta irin na zallar muguntar nan,sannan ta zare wayar a kunnenta har yanzu murmushi yana sauka saman fuskarta.

"Kafin na tafi......ya kamata kowa ma ace anbar masa wani babban tabo.....babbar barakar da bazata taba gyaruwa ba" Ta fada a bayyane tana jin alamun nasara na tare da ita kena,tunda har a sanda take zaton faduwa babban labarin nasara yazo mata.

*_RANA BATA QARYA_*

Cikin wani irin tarin nutsuwa yake zaune gaban sultane,wanda ya kebe ne daga shi saishi,duk da cewa shi da maleek ya fara yin magana dasu.

Sanye yake cikin wata qayatacciyar jallabiyya da asalin kudinta ita da cloak thobe din jikinsa yake isa babban jari da tarin al'umma marasa qarfi. Wasu irin thobe da a idanu kawai idan ka kallesu kasan an nunawa kudi iyakarsa wajen mallakarsu.

"Na aura maka biftu ne......saboda fadin manzan Allah.......mu aurar da diyoyinmu ga maza irinka,idan ka sota zaka mutuntata ka mutunta ahalinta,idan ka qyamaceta kuma ba zaka wulaqantata ba........haisam,bazan boye maka ba,ba kuma don ban aminta dakai ba aah......ina sake jaddada maka ne kaji tsoron Allah akan khadeeja.....bazan boye maka ba,inason khadeeja sama da kowa cikin 'ya'yana.....amma hakan........" Sai zuciyar sultane dake kashingide saboda rashin qwarin jiki da yake fama dashi ta raunana. Ya yunqura ya miqe ya kuma zauna sosai,rabon da yaji alamun taruwar hawaye cikin idanunsa tun rasuwar mahaifiyarsa.

"Amma hakan bazai hana na aurar da ita ba,saboda hakan shine cikar kamalar mace.........ina sake baka amanarta......ba don ina kokwanto kan cikar kamalarka ba,a yanzun duk duniya,ba wani d'an adam dana aminta dashi sama dakai" Wani irin nauyi yakeji sultane yana sake aza masa.......wani irin sanyi dukka yake ji yana bin jikinsa. Yana jin kamar bazai iya ba.....kamar bazai kai labari ba. Ya sani,idan ana maganar amana wata abace me girman gaske......abace da idan ba ita tsallake siradi kansa baya yiwuwa a gurin bawa. Zata kasance abu mafi santsi a tafin hannun bawa ranar qiyama,ita zaa aza maka a hannunka ka tsallake wannan siririn zaren da ko kaurin gashi baikai ba.....siririn zaren dake tsakanin wutar jahannama,ka tsallaketa da ita,tana santsi kamar tarwada a hannunka. Duk sanda ta subuce ta fada to zaka bita ne ka daukota don ba zaka wuce ba sai da ita,idan kaci amana zaka yita sintirin daukota daga wuta Allah ya tsaremu,idan kuwa ka kiyayeta lafiya qalau shikenan zaka wuce,wucewar da babu wani bawa da yake da tabbas a kanta.
(Ya Allah,ka bamu ikon kiyaye amana....Allah ka tsallakar damu siradi lafiya).

"Muhammad" Sultane ya kira sunan haisam da yanayin daya sanyashi daga manyan idanunsa kadan ya kalleshi.

"Akwai wasu abubuwa a wancan ranar dana gani......akwai abubuwa da yawa dana saka musu ayar tambaya.....akwai abubuwa masu yawan gaske daya kamata ace na sani inaji a jikina hakanan......inason nasan gaskiya muhammad......inaji a jikina akwai wani boyayyen abu......shin zaka iya riqo da hannayena na sauka daga mulkina na damqawa ahmad?......zaka iya dafawa raunina ka fiddani daga cikin duhu zuwa haske?" Maganan ta zowa haisam a bazata,magana data sake tilastashi daga kansa a hankali yana duban sultane,yana masa wani kallo ne dake bayyana gaskiyar magana manufa da abinda yake fadi daga tsakiyar zuciyarsa ne

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 17*

*M O R S A S A F I Y Y A*

Zaune suka a gabanta dukka su biyun,sanye kowaccensu da abaya data banbamta gurin launi da design din ma gaba daya.

Falaaq na sanye da dark mint green,wadda aka saqata da ainihin satin material me kyau da tsada. Yayin da akhnan ke sanye da baqar abaya,Japanese nida da aka saqata daga asalin yadin silk me yauqi dake shaking yana sake qawata farar fatarta dama ainihin kalar baqi wul din da abayar ke dashi.

Zaune suke gaban morsa safiyya,a kebantaccen dakin kwananta da babu kowa a cikinsa,daga ita sai 'ya'yan nata guda biyu.

Dukkaninsu tafukan hannuwansu suna cikin nata,na tsahon wani lokaci suka dauka a hakan,duk wani magana da zata musu koda kalma daya bata bari ta fadeta suna nesa da ita ba,ta damqesu sosai cikin nata hannuwan,tana jin kamar ba zata iya zame hannun nasu daga cikin nata ba.

Wani emotion ne me nauyi tun daga idanunta zuwa zuciyarta,irin wannan yanayin da UWA data aurar da d'iyarta ne kawai ta sanshi a ranar da za'a karbe diyar daga hannunta zuwa gidan wani.

Sheshsheqar kukan falaak ita ta haifar da wani irin shuru a tsakaninsu,wani irin shuru dake dauke da nauyin da zuciya ce kadai tasan iya adadin mizaninsa.

Komai akhnan tana jinsa ne kamar almara,komai tana kallonsa ne kamar wani shirin film ko a littafi. Yau ita akhnan?,itace wani d'a namiji zai dauketa cancakat?,daga mahaifarta?,daga masarautarta?,daga cikin iyali da ahalin data taso a ciki?. Ba Niamey kawai zata bari ba.....ba agadez kawai zata bari ba.....aah,zatabar qasarta da nahiyarta ne gaba daya.

Karon farko da taji kukan falaak ya sanya wani rauni cikin zuciyarta,lokaci na farko da riqon da morsa safiyya ta yiwa hannuwanta take jinsu har cikin qasusuwanta da zuciyarta.
Chapter 18 · 0% Book details