← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 176

Sashe 78

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba wannan akhnan din ba yake kalla ba.....ba wannan biftu din ba.....ba wannan khadeejan ba princess of agadez ba. Wata matar gida....responsible matar gida. Da iya tambayarsa kawai da tayi me zaisha din?,ta gama kwance masa tunani.....da iya tambayar data masa kadai a dazun ta goge masa tunani.....ballantana yanzu da yazo ya sameta a tsaye da nufin zata dafa abinda zata bashi da hannunta?.

"Ya salam....." Ya fada a hankali,mamaki yana sake kwance masa kai.

"Barka da warhaka obbo......fatan ka fito lafiya" Saamee ta fadi da wani iri narkakken ladabi yana lanqwashe kanta.

"Barka kade" Ya amsa mata idanunshi da zuciyarsa gaba daya suna kan akhnan dake auna adadin kayan hadin tana zubawa cikin mini coffee maker din.

"Ya jikin?,Allah ya qara lafiya me dorewa". Ta fada tana satar kallonsa.

" Ameen" Ya amsa mata,daidai sanda idanunta sukayi kyakkyawan gani. Hankalinsa da gangar jikinsa dukka akhnan suke nufa. Wani abu me nauyi ya danne mata zuciyarta. Bataji zata iya bar musu kitchen din,bata jin zata iya basu wannan space din,duk da adoka da qa'ida barin kitchen din ya zama wajibi a kanta.

Taji shigowarsa......sallamarsa da takowarsa.....amma bata daga idanu sam ta kalleshi ba,saita zabi ci gaba da abinda takeyi.

Wani bala'in burgeshi tayi.....wani bala'in tafiya tayi dashi. Wannan jan ajin.....wannan basarwar,wannan dauke kan data sake masa sanda yake jan daya daga cikin kujerun bar din ya zauna idanunsa zube a kanta.

Baice mata komai ba kaman yadda batace masa ba,sai wani irin kallo daya kafeta dashi tamkar an bashi gadinta da aikin lissafa duk wani motsi nata.

Taji idanunsa a kanta,amma still bata dago ba,kallonshi yakeso tayi....koda sau daya ne da wannan blue eyes din nasa,amma akwai alamu gilmawar wani irin izza a idanu da fuskarta da yake hange.

Ya fahimci da gaske ba zata kalleshi ba,sai ya miqa zara zaran yatunsa ya zare cokalin da take saka amount na hadin tea din yaci gaba da zubawa shima ba tare da yace komai ba. Hakan baisa ta kalleshi ba,taci gaba da tsaiwa kawai tana harde hannayenta a qirjinta.

Kawai takejin batason wanzuwar yarinyar a kitchen din. Haka kawai takejin zamanta a kitchen din bai mata ba. To amma ba zata bata kalmomin bakinta ba ko sau daya a kanta ba. Tunda tazo Ethiopia ko sau daya ba wani wanda takejin bai mata ba......amma akan saamee taji wannan,bawai tana da wani babban dalili bane,don bata da lokacin saka hankali da idanunta akan kowa sai akan abinda ya shafeta tun asalinta SHISHSHIGI shine kawai abinda bataso bata qauna.

"Saamee" Abinda ya fadi kenan idanunsa akan coffee maker din da yake duba adadin kayan daya zuba. Ba tare daya qara kowacce kalma ba saamee din ta soma takawa tana fita daga kitchen din. Zuciyarta kamar zata fashe.....fadin qirjinta tana jin ya yiwa zuciyarta kadan,wani abu ya dunqule mata ya fidda wani zazzafan hawaye daya sauka saman kuncinta.

Kunnata yayi ya saitata,sannan a hankali yaja kujerarsa baya yana zube idanunsa akan Akhnan. Still miskilar tasa ba abinda ya sauya,kamar tasan me yake buri?,sai kawai ya miqe a hankali yana aza hannunsa saman sassalkar sumarsa da duka yau take a hargitse yana sake hargitsata hade da wani yanayi da yaji yana yamutsa kwanyarsa gami da saukar masa da wani irin tashin tsigar jiki.

Ganinta yake son yayi in full details bada wannan mayafin ba.....so yake ya ganta gayarta,don haka ya soma takawa a tausashe,ya kuma mamayeta ba tare data ankara ba,saiji tayi ya debe.mayafin kanta gaba daya ya duqunquneshi cikin hannunsa. Sanda ta juyo yana dunqule mayafin ne,ya kuma zuba mata ido yana ganin yadda sumarta ke warwarewa daga dan qulletan da tayi da sirirn band.

"Ma sha Allah" Ya fada can qasan ranshi yana hadiye wani yawu. Yadda sumar ke sauka tana bajewa zaman bayanta har dab da mazaunanta ya sake harba wani abu me qarfi gaske zuwa ga sassan jikinsa. Ta zube masa blue eyes dinnan da yaga tsoro qarara a cikinsu. Taku daya yayi ya isa gareta,ya kuma.jawota cikin jikinsa,wannan karon bai jira komai ba ya mata wani kyakkyawar runguma data amsa sunanta cikin jikinsa.

Wannan karon.....bada gangar jiki kawai ya rungumeta ba,wannan karon da dukka zuciyarsa ta dinga ji kaman ya rungumeta,ya narke mata sosai cikin jikinta,ta motsa kadan amma sautinsa ya sauke mata komai.

"Jinyata nanay tace kiyi please,ba haka nanay takeyimin ba....idan bani da lafiya na kwanta akan cinyarta.....bata cewa na tashi......kada kici amanar da nanay ta baki mana" Ya fada yana sake shigewa cikin jikinta kamar dukka burin rayuwarsa dama maslahar rayuwar tasa ta ta'allaqa da dogon wuyanta ne.

Tana da saurin amincewa da maganar mutumin duk da ta bawa fili har ya shiga rayuwarta,don haka bata ji cewa maganansa ba haka bane,saita daina yunqurin zamewar,ta tsaya sosai kaman yadda yakeso,wannan ya bashi daman sake laqumeta cikin faffadan qirjinsa yana sansanar qamshinta sosai kamar zai zuqe duk wani qamshi da yayi saura a jikinta.

Cikin mintuna qalilan yaji ya fara birkicewa. Itama birkicewar ta fara yi,don ba qaramin dafi yake saukar mata ba daga zazzafan numfashin da yake saukewa wuyanta,sannan taji ya fara sauya akalar yana kawo hancinsa saman qirjinsa kaman yana son cusa kansa tsakanin halittun qirjin nasa.

Fuskarsa ya zare a hankali sanda coffee machine din ya kashe kansa da kansa bayan yakai inda ya kamata yakai. Ta dauka zai zare jikinsa ne.....amma ga mamakinta sai kawai taji ya dagata cak ya dorata saman kitchen island din.

Bar chair din ya jawo dab da ginin da take kai a zafafe sannan ya zauna akai,ya raba cinyoyinsa tsakanin nata,nata qafafun suka kasance tsakiyar nasa.

A yau yana jin duk wani qarya da yakewa kansa tana warwarewa.....kafiya da taurin kansa yaji gaba ana kwanceshi daya bayan daya.

Yasa hannunsa,ya kamo zara zaran yatsunta ya cusa tsakiyar nasa ya matsesu gam,saidai a tausashe yadda ba zataji zafi ba. Ya zuba musu idanu yana kallonsu kafin ya maida dubansa ga fuskarta sannan qirjinta dake wani irin bugawa.

"Bugawar da zuciyarki takeyi a kullum tana wuce kima" Ya furta softly yana lumshe idanunsa kamar wanda ya tashi daga baccin da bai isheshi ba.

Qoqarin daidaita numfashinta da bugun zuciyarta ta soma yi,saidai ya hanata wannan damar ,yama sake rikita mata lissafinta gaba daya sanda yace da ita.

"Sau nawa zuciyarki zata gaya miki sona kike kafin ki amince da abinda yake gaya mikin?" Saura kadan,saura qiris numfashinta ya qwace mata,saura kadan ta rasa fitar numfashinta na daqiqa ta samu ta riqeshi da qyar ta hanyar zaro idanunta waje......amma wadannan tsimammun idanun nasa.....wadannan idanun nasa masu cike fal da dafi da maganad'isu suka hanata masa qarya,illa furta kalmar.

"Ni?" Da tayi adan birkice.

Duk da abinda yakeji cikin jikinsa amma hakan bai hanashi sakin wani siririn murmurshi ba bayan ya lumshe idonsa ya kuma.budesu yana gyada kansa.

"Yes.....ko kin bani dama na fiddo gaskiyar hakan?". Wani sabon kallon daya watsa mata ya sanya ta fara jin kamar narkewa takeyi tana bin jikin island din,sai kawai ta yanke ture yatunsa a gigice tana fadin.

"Tea dinka ya zama ready"

"I know" Ya amsa mata kai tsaye yana sake hanata damar sauka daga kan island din kamar yadda tayi niyya da farko.

Yana sake mamayeta da hannuwansa.

Ta bayan mazaunanta ya zagaya da hannunsa,ya kuma soke yatsunsa cikin na juna,ya mata qawanyar da babu damar ta motsa,gwiwoyinta suna tokare da qirjinsa,sai kawai ya sanya kafadunsa ya raba tsakanin qafafunta ya shige ciki yana dora kansa saman tattausar cinyarta.

Gigicewa tayi gaba daya,ta dora duka hannunayenta saman kansa da niyyar ture kansa,saida dogayen yatsunta tuni suka samu daman nutsewa cikin tattausan gashinsa.

Wani irin abu yaji yana ratsashi,ya lumshe idanu yana sauke wata ajiya zuciya. Kaman susa take masa cikin kan kasa yaji,wani abu me dadi yana ratsa tsakiyar kansa nasa har cikin kwanyarsa.

"Karki janye......don Allah....." Ya fadi a hankali sanda take zare yatsunta ganin yadda ture kan nasa bai tsinana mata komai ba.

"Pleaaseeeeee" Ya sake fada da wata irin raunanniyar murya.

"Don Allah.....amana nanay ta baki.....na tabbatar nanay tace ki kula dani" Ya sake fadi yana qara matse cinyoyinta zuwa mazaunanta tare da nutsa kansa sosai cikin cinyarta kamar zai narke ya zama daya da fatar jikinta.

(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)

Yadda yayi maganan.....yadda ya fada din sai ya kasheta jiki gaba daya,saita samu kanta da tura yatsun nata kamar yadda ya buqata a hankali da wani irin yanayi da batasan zai haifar masa da komai ba.

"Biftuuu" Ya kirata a nutse yana karya shurun daya ratsa tsakaninsu,idanunsa suna lumshewa da budewa gami da sake jirkicewa daga launin kalarsu.

"Na'am" Ta fada a hankali tana zare hannuwanta saboda wani irin bugawa da taji zuciyarta tana yi daga cikin qirjinsa dake kwance saman cinyoyinta.

"Akhnaaan" Ya sake kiranta,wannan karon kiran daya mata har yafi ka dazun,a daburce tace.

"Shayinka ya huce"

"Na sani" Ya fada da birkitattun idanunsa daya daga yan kallonta. Kallon ya mata nauyi,kashe mata jiki yake sosai....kwarjininsa narkata yakeyi,saita kau da kanta gefe tana jin kowacce gaba ta jikinta tana amsawa.

"Zakasha magani......ka bari na dauko maka kasha.....don Allah" Ta qarashe roqo,don neman inda zata kufce takeyi.

Kamar bazai janye ba,kamar ba zaice komai ba,sai taji yana zare hannuwansa a hankali daga jikinta yana binta da wani sassanyan kallo.

Rawa hannunta yake sosai sanda take zuba masa tea din a cup. Nisan tunanin da tayi ya sanya cup din ya kusa cika bata sani ba. Gigicewa tayi,saboda wani abune da bata saba ba. Hannunta na rawa takai hannunta kan makashin,wallahi takai ga dannawa taga dogon yatsansa me wasu irin fararen farce tamkar baisan wani abu da ake kira da dauda ba ballantana qura.

Janye hannunta tayi,saita daga idanunta suna hada ido dashi. Girarsa daya ya dage mata,ta kauda kanta da sauri tana neman hanyar da zata zame,saboda ya tazarar dake tsakaninsu duka duka bai wuce taku hudu ba tsakani.

Daga nan tana iya jin saukar sassanyan numfashinsa. Daga nan tana iya jin qamshin jarababben turarensa da ya manne mata jikin kayanta gaba daya kaman yadda ya game jikinsu gaba daya

"Ki bani" Ya furta a shagwabe da wani irin laushi yana qare mata kallo tamkar Allah ya aikoshi. Tadan kalleshi kadan a sace tana mamaki. Gashi ga tea din,asalima shine ya kashe maker din amma ya dauka baze iya ba.
Chapter 78 · 0% Book details