Sashe 100
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba kowa saman gadon,tabi shimfidar gadon da kallo a hankali. Komai a yamutse yake,wasu pillows din sun fado qasa sun zube daga gefe. Idanunta ta dauke a hankali,wannan gadon bai kama da mutum daya bane kawai ya kwanta,yanayinsa kamar anyi dambe ko yara ne sukayi bacci akai suka tashi.
Idanunta ta maida qofar bandaki sanda take budewa. Akhnan ce,sanye da doguwar riga cotton me laushi sosai data saukar mata har qasa. Ta sani,bada rigar ta kwanta bacci ba,kaman yadda gashinta ke a hargitse ba kaman yadda ta ganshi dazu data shigo ta kashe mata wuta ba.
Qasa akhnan tayi da idanunta,haka kawai tana jin wani faduwar gaba dakunya suna saukar mata. Gani take kaman nanay tana ganin komai,yadda ya kwana tsakanin qirjinta,yadda ta farka fuskarya saman lallausan gashin kansa,yadda ta sake bude idanu ta tarara yana tsaye yana qare mata kallo,sumarsa na digar da ruwan da take da tabbacin wankan ibada yayi. Ya yarfa mata ragowar ruwan hannun nasa a tausashe yana sakin lallausan murmushi.
Ta bashi wani abu da ake kira da suna NUTSUWA wato peace inji bature. A yau yasan yayi wani irin bacci daya amsa sunansa,kalar baccin da bai taba irinsa ba kaf rayuwarsa.
"Gate up......ko kina so nanay tazo ta sameki a haka?" Duvet din data boye fuskarta ta janye kadan,tanason dubansa amma ta kasa,ta ganta a haka kaman yaya?.
Daga ido tayi karo na biyu,caraf ya riqe idanun cikin nasa,ya mata nuni kuma da jikinta,takai hannunta a hankali tana tabawa. Ya rabata da komai sai a sannan ta tuna,ta cure guri daya tana duba lokaci,shirye shiryen sallar asuba akeyi.
"Ruwan wanka yana ciki yana jiranki".
" Ni bazanyi wanka ba" Ta fada tana tura baki kunya kaman ta kasheta. Karon farko ra yuwarta da taji sautin siririyar dariyarsa,ya tako a nutse yana isowa dab da kanta ya sunkuya kadan.
"Ba zaki wanka ba.....amma awannin dazu kike fadin....." Sai ya sassauta muryarsa yana maimaita mata maganganun da ko daya a ciki ba wanda tasan tayi.
"Wayyo Allah na bappi.....zai lalatamin kunnuwa na" Ta fada da siririyar muryar nan tata dake kasheshi,musamman duk sanda tayi magana da sautin shagwaba.
Baya yaja a hankali sautin siririyar dariyarsa yana fita,wani abu daya zowa akhnan da wani sabon yanayi.
"Ba sharri na miki ba,pillows din dake nan da suna magana zasu fada"
"Nidai ka fita" Ta fada hawaye na tarar mata a idanu. Ya akayi ta bari ya yaudareta har haka yaji wadannan kalaman a bakinta?. Banda tasan baya qarya zata iya tsinewa kanta ita ba ita ta fada ba.
Yana sakin qasaitaccen murmushin nan nasa dake gaya mata,ba abinda ta furta kawai ba......tuna komai daya shude cikin awannin dadi yake masa,ya koma private musallah din,ya shimfida tattausar daddauma ya tayar da salla abinsa hankali kwance,kaman baya duban lokaci,kaman baya tsoron wani ya shigo ya ganshi.
Tayar da sallarsa ya bata cikakken daman wucewa bathroom din kai tsaye a gurguje,ta samu ya hada mata komai,hatta da towel da zatayi amfani dashi,kaman yadda birra ke mata. Sanda ta fito taga dakin wayam,batasan sanda ya fita ba,sai ta sauya kayanta kawai wanda tana kammalawa ta koma bandakin don daura alwala,fitowarta ne a yanzun sukayi kacibus da nanay.
Idanunta kawai ta janye nanay din,jikinta yana bata akwai wani abu da yake ba daidai ba,saidai bata nunawa akhnan din komai ba tace
"Alhamdulillah,kin tashi kenan".
"Eh na tashi" Ta amsawa nanay wadda har takai bakin qofa a sannan.
"Zenebe zata shigo zata ganki" Abinda tace kawai kenan tana fita daga dakin.
Kawai juya abun take cikin ranta,tana tafe tana amsa gaisuwar hadimai da ma'aikatanta cikin girmamawa kaman yadda ta saba. Can qasan ranta take maido da yanayin dakin da qamshin haisam da taji,kadafa su bata kunya.....karfa ya sake maimaita wani abun kamar yadda motii ke fada mata.
"Bayan na kwanta,akwai wanda aka sake budewa sassan nan ne?" Ta tambayi saamiyaa wadda keda alhakin kula da shige da fice na cikin dare.
Qasa kadan tayi da kanta,tana jin nauyin fade,duk da ya wuce abinsa ne kai tsaye bayan ya tambayeta nanay din ta kwanta?,ba tare da yace mata komai ba.
"Saamiya" Ta kira sunanta tana juya daffaffiyar madarar hannunta.
"Eh......yarima haisam ne ranki ya dade" Shuru nanay tayi,ta gyada kai a hankali,kawai sai taji dariya nason qwace mata.
Karo na farko......karo na farko kenan data taba shata iyaka da layi akan abu amma haisam ya tsallake. Ta yarda da maganan motii,ta kuma yarda duk wanda ya rigaka kwana zai rigaka tashi. Namiji baida amana akan mace da gaske ne,kota yaya ne zai samawa kansa ita. Ta sake gyada kai tana godewa Allah da tunda asuba aka gaya mata isowar saqon,kuma duka a yau zata iya yiwa akhnan amfani dasu,iyaka dai kawai ta barta subi jikinta na kwana uku kawai shikenan ta miqa masa matarsa.
Yinin ranar ta sani za'a iya samun yaiwatar zirga zirga da jama'a. Saboda walimar da hussam ya shirya zaiyiwa haisam din. Nanay din tana jinsa yanata mita.
"Karma kaje kayi abinda ba zai burgeshi ba.....shigar jubah zamuyi,kowa ya saka thobe kawai" Ya fada yana ya mutsa fuska,tana jinsa ya bada kalan shigan da za'a yi na jallabiyya,color kowa ya zabi favourite colour nasa.
Breakfast kawai akhnan din tayi,zenebe da wata mata da ba zata iya tantance qabilarta ba,sukazo suka dauketa saboda gyaran jiki na qarshe da zasuyi mata,suka zagaya da ita baya inda nanay tasa aka kebance wani guri na musamman don suyi komai acan.
*H A I S A M*
Ya kammala shirinsa gaba daya na tafiya a yau din,wuni guda yana kai kawo bai zauna ba na hada sauran takardu da komai da zaya buqata,saidai ko sau daya bata bar tunaninsa ya huta ba.
Baisan me yasa baya samun wayarta ba,saidai abinda bai sani ba nanay ta karba ta kashe. Can qasan ranta tanaso yayi missing akhnan dinne,tanaso yaji ya matsu da ita da gasken gaske,sannan kuma tana tsoron abinda ta gani a idanun akhnan din. Rauni da wata irin QAUNA data fara hange ta bata tsoro,kada ya hure mata kunne ya bata shirinsu na kwanakin data tsara.
Zuwa yammaci aka soma gudanar da walimar. Cikin wani irin ba zata da bai zata ba saiga team dinsa dukkaninsu.
Naseeb.....mutallab.....amjad......khadeem sai omar. Maleek kam yana can ya maqale,yace har yanzu honeymoon yakeci.
Yayi mamakin ganinsu,saboda dukkaninsu zasuje bikin bude company a dubai nan da kwana biyar din daya rage,saidai kuma mamakinsa baiyi yawa can ba,don dukkaninsu suna dasawa da hussam. Baisan me yasa sukeyin hussam din ba,ko don zubin vibes dinsu yana zuwa daya dasu wani lokaci,saidai dukkaninsu a ranar kowa zai koma bakin aikinsa,tunda tafiya ce ta jirgi.
Daga cikin gidan ma still wani walimar ne da Aanani da rumaisa suka shirya,harda noorah. Ita kanta nanay batasan sun shirya kayarsu ba. Daya daga cikin dakunan taro na gidan suma sukasa aka shirya musu shi da sauran qawayensu,dukkaninsu kuma shiga ce sukayi ta gargajiya,ta aninihin tufafin yaren oromo da suturarsu da yake zuwa kaloli biyu
(Zan saka a status dina na watsapp in sha Allah,kusan tafiyar namu gani da jine😄).
Ranar sai gidan ya zama hidima kawai akeyi,hakan ya yiwa nanay daidai,itama taga kawai gwara a kammala komai ta bashi matarsa kafin yakai ga fada mata gaba da gaba. Saidai nanay din batasan kalan tsiyan da yake qullawa ba.
Da yammacin dab da faduwar rana kayan da suke nuna girmamawar ango zuwa ga amaryarsa a qabilar oromo suka iso. Koda ba'a gayawa kowa ba zakasan kayan mene tunda an riga an saba. Ya sameta a cikakkiyar mace da takai budurcinta.
(Don samun littafin lu'u lu'u 08187255862)
(A kowanne yare.....a kowacce al'ada,a kowacce qasa.....a kowanne gari BUDURCI abune me muhimmanci....kada ki yarda.....karki kuskuren da zaki rasa baki a banza a wofi,ki tabbatar duk runtsi duk wuya duk gwagwarmaya kin kai naki dakin mijinki,mijin nan da yasan darajarki,yabi dukkan matakai ya biya sadakinki,wallahi ba wani abu.....ba wani gyara da za'a miki a rudeki ace budurcinki zai dawo,qarya ce wallahi wallahi tallahi,ko waye ya gaya miki ya yaudareki,hajiya kayan kamfani daban daban dana shago,ba wanda ya isa ya halicci wani abu da yayi daidai da wanda ubangiji ya halitta tun asali tun haihuwa,Allah ya bamu ikon kai zukatanmu nesa ameen summa ameen).
Jikinta yana tururi da wani sample na ruwan wanka da turare da aka bata a daren tayi wanka dasu bayan an tashi walimar ta fito daga bandakin,saidai qarar shigowar saqo wayar da yanzu yanzu aka kawo mata ita ya sanyata dakatawa daga tsane jikinta da tayi ta dauki wayar tana dubawa.
_"Wear something comfortable_ tomorrow morning
_And don’t ask questions yet_
_Haisam_
Juya wayar ta dinga yi kawai ba tare data fahimci komai ba. Shigowar Aanani da murmushi tana ajiye mata sauran gifts din da suka kusan cike rabin dakin ya sanyata sauke wayar
"Na gaji giifii.....ko na sanya su obsa su qarasa shigo dasu da safe?". Idanu waje kadan akhnan ta fidda.
"Wai baki gama ba?"
"Da ragowa" Ta amsa mata tana daidaita zaman wani kwali.
"Ki huta sistern captain obbo.....sai goben" Dariya sosai Anaani tayi.
"Da zaijiki kuwa zaice....wannan me kunnen qashin?,noorah ce tawa" Da murmushi ta bita da kallo harta fice,sai taji inama itace su,gasu cikin rayuwar da suka tashi tsakanin qannensu da yayyensu. Akwai wani irin so qauna da respect da suke bawa junansu,musamman haisam din. Ta karanci wani irin so kowa cikin 'yan uwanshi yake masa,saita ture komai ta soma shafa mai tana jiran birra ta qaraso ta bata rigan bacci.
Tabi tarin kyaututtukan da kallo,qawayensu da abokan hussam ne kawai suka hada mata uban kaya haka. Mamaki takeyi na yadda suke da kyakkyawar mu'amala da mutane da yawa. Kaman girma da qarfin iko na masarautarsu bai daukesu ya d'ad'asu da qasa ba. Suna wani rayuwa simple,izzar ke magana da kanta basu ke qoqarin gwada ikonsu ko nunata ba.
Sanda dare ya fara nisa sai bacci ya gagareta. Daren jiya take tunawa,kowanne moment daya shude,kowanne second minti da awa da suka qarar ita dashi,sai ta kuma samun kanta da jin kamar motsinsa,kamar takunsa da tafiyarsa,ta runtse idanunta sannan ta sake budesu a hankali,bashi ba alamunsa. Duka baccin sai taji yana neman qaurace mata,ta samu kanta da tuhumarsa.....me yasa baizo kaman jiya ba?,sai kuma dariya ta subuce mata sanda zuciyarta kece mata.