← Book details LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 171 OF 176

Sashe 171

LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Itama don dai kawai ba'a manta asali.....kuma ba'a manta gida. Amma saura qiris a lokuta da danma ta zabu jimma sama da agadez. Garin yana da wata irin albarka,hakanan yana da wani irin weather dake sanyaya zuciya. Irin weather din da yawancin zukata da gangar jiki sukeso,irin yanayin nan me sanya nishadi a zukata.

Akhnan ce,tsaye bakin glass railing din tana riqe da cup din tea dinta. Ta zama wata irin mayyar tea har abbee(haisam) yana tsokanarta a gaban yara su kuma suna tayashi.

"Mun maidata 'yar jimma....cikakkiyar yar Ethiopia....mun mantar da ita agadez gaba daya"

Daga qasa...dariyar yara ta cika garden din. Ta sauke idanunta a kansu tana kallonsu daya bayan daya.

Ba ashraf bane.....ba asif bane....ba afeef bane. A yanzun....wasu yaranne na daban.....wasu saitin 'yan ukun daban......da wani set na 'yan biyun da suka zama haihuwarta na qarshe da tayi shekaru biyu baya.

Ahsan.....ahlaam......da ajmal.....sai 'yammatan da suka kasance twins su biyu masu tsananin kama da akhnan din kamar kakinsu tayi ta ajjiye. Safiyya da safeena.....wanda nanay tayi kawaici tace sunansu ya kamata ya saka ita ta yafe. (YUMNA DA YUSRA).

Yumna ce ke gudu tana qoqarin kaucewa kubuta daga hannun ahsan wanda yakeso lallai sai ya riqeta kada ta fadi,yayin da nannynsu ruqayya yarinyar da bata haura shekara sha uku ba ke binsu cikin dariya.

Murmushi ya bayyana a fuskar Akhnan ba tare da ta shirya ba. Years ago...... da wani ya gaya mata cewa zata taba samun irin wannan rayuwar,da bata yarda ba.

Ba wannan mutumin ba...yarima sheikh Muhammad hausam. Ba wannan gidan ba......ba wannan nutsuwar ba.

Mafarkinta yayi nisa akan ta rayu ita kadai kawai. Mafarkinta yayi nisa yana gaya mata lallai akwai rashin 'yanci da takura gurin rayuwa tare da d'a namiji. Ashe dai saidai ga wadda bata dace ba.

D'A NAMIJI.....KUMA MALAMIN data raina.....shi ya zame mata wani tsani na kaiwa wani mataki da bata taba mafarkin kaiwa ba kaf rayuwarta. Malamin dai.....shine ya kama hannunta ya sanyata ta san ma mene addininta haqiqanin sani. Ya sanyata ta sauke litattafan addini da dama. Ya sanyata ta gyara lahirarta ta hanyar yin karatun litattafan addini masu yawan gaske daga bango zuwa bango. Ta sauke hadisai masu yawa,litattafan fiqhu dana sira. Tasan rayuwa a haqiqanin zahirinta. Tasan mutuwa hisabi da kwaciyar kabari sanin da bata taba kaiwa koda gefansa ba. Ya sanyata da kudinta da abinda ta mallaka takewa kanta mahaifiyarta da morsa safiyya sadaqatul jariya. Harda wadanda ta manta. Yawan sadaqar ya sanyata take mafarkin mahaifiyarta cikin ni'ima a mabanbatan lokuta. Allah ya nuna mata a mafarki yadda sadaqatul jariya dinta ke isa ga mamminta.
(Iyayenki sun mutu?,amma kina da dubu hamsin,dubu dari da zata isa gina rijiya......siyan qur'ani kikai masallaci......gyaran hanyoyin unguwarku ko yin cikon hanya amma ki kasa yi musu wannan kice ladan Allah yakai kabarinsu?).

Sharrin mammina bai hanata roqa mata yafiyar Allah ba....sharrinta bai hana mata yi mata sadaqatul jariya ba tunda bata da wanda zai mata. Tana fatan wannan ya sanya ta samu sassauci a gurin Allah.

(A duk sanda bawa ya maka sharri,kai kuma idan ka samu dama akansa gwada masa alkhairi. Yi masa alkhairi har sai ya kasa kallon idanunka,Allah kasa mufi qarfin zukatanmu....kasa mu shuka alkhairi don mu girbeshi ranar gobe qiyama).

Tayi nisa a tunaninta sai ta ji motsin qofa a bayanta.

Ba sai ta juya ba kafin ta san shi ne. Presence dinsa har yanzu yana nan quiet power. calm danger. the same man.......prince sheikh muhammad haisam.

Wannan kamannin.....wannan lallausan kyan....wannan charisma din.....haiba,kwarjini,kamala dukkansu suna nan tattare dashi,sai ya zamana kamar an ninkasu ne ma.

Da tarin nutsuwar nan tasa ya tsaya bayanta cikin dark suit dinsa,ya zube hannayensa a aljihun suit din,saidai hakan bai hana bayyanar agogon hannunsa dake kyalli qarqashin hasken safiyar ranar ba.

“Kika gudu kika barni da su.” ya fada a tausashe da wannan husky voice din tasa me zurfi,wadda idan yayi magana take kai mata kowanne sashe na jikinta.

Ta yi murmushi tana kallon garden,har yanzu anata artabu da yumna. Kuzari tafi kowa a gidan?,ko rashin ji?,itadai ba zata ce ba.

“They like you more.” ta amsa masa da muryarta dinnan da bata sauyawa

“A’a.” ya fada a tausashe,sannan a nutse ya tako ya qaraso kusa da ita yana aza hannunsa jikin makarin silver din.

“They fear me more.” Tayi qaramar dariya tana duban idanun nan nasa da kowacce rana yake sake narkar da ita.

"Abbee....yaran nan wani lokaci abinsu baya tashi ma sai sun ganka fa" Murmushi ya saki a hankali,ya miqa hannunsa yana dan ja hancinta da yaga ya bude kadan.

*zaki samu daman karanta wannan QASAITACCEN LABARIN ta hanyoyin siyan tikitinki kamar haka da naira (1000) kacal*

*Lambar asusu:- 6019473875*
*Safiya musa abdullahi*
*Keystone bank*

*KI TURA SHAIDAR BIYA TA NAN*

08187255862

*Al'ummar qasar nijer 🇳🇪*

*2349166221261*
*Safiya musa abdullahi*
*NITA*
*CFA 1,000*

*SAIKU TURA SHAIDAR BIYA TA LAMBAR DAI*

08187255862

*GA WADANDA ZASU SAKA KATIN WAYA NA MTN SUMA NUMBER DUKA DAYA CE*

*MTN CREDIT 1000 ZUWA GA*
09166221261

*SHAIDAR BIYA*
08187255862

*_TAFIYAR 'YAR GASKE CE........LABARIN QASAITACCIYAR MACE CE KAWAI KE IYA SIYANSA_*

*QASAITA👑*

*HUGUMANKU CE*✍🏽💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎

*H U G U M A*

*BOOK 03///PAGE 158*
__________________________
*_Amintaccen gurin siyayya_*

*_ingantattun kaya akan ingantaccen farashin da ba irinsa a kasuwa_*

*_BONONZA DA PROMO akai akai_*

*dukka sai a HUGUMA CLOSET*

*Duniyar kayan yara,mata,maza,dukka*

*shaddodi,atamfofi,laces,abayas,jakankuna,takalma,agogo,sarqoqi,English wears,night wears,under wears,da duk wani nau'in sutura babba da qarami*

*_Karki yadda ayi babu ke.....leqa kiga yadda closet din HUGUMA kullum ke cike da kaya akan farashi me kama da KYAUTA_*

*_YAN SARI....YAN REPOSTING.....DA SARAKAN ADO MASU SIYA DON KANSU....DUKKA INA MUKU MARABA_*🤝🤝🤝🤝

https://chat.whatsapp.com/FrqgC0YmUWP4FPmUzYuLJX
___________________________

Akwai shaquwa da sabo da sakewa sosai tsakaninsu sama da yadda suka sake da mamansu..... Amma akwai wani tsoro da respect a tsakaninsu. Wani shakkarsa suke....musamman idan kasan kayi ba daidai ba. Amma kuma idan kaga yadda suke rayuwa dashi zaka dauka abokinsu ne ba uba ba.

"Hancina ko abbee" Ta fada taba dan tsuke fuska. Ido ya zuba mata sosai kaman bayason ya daina kallonta. Itama kallonsa take tana sake ganin yadda kyansa ke sake fitowa yana cakuda da shekaru wadanda ke sake qara masa kwarjini. Mutumin da duniya ke tsoro… ita ce kadai take jin yadda zuciyarsa take samun wata cikakkiyar nutsuwa idan yana gida.

"No" Yace yana danne murmushinsa. Rau rau tayi da idanu tana dubanshi.

"Kaji tsoron Allah ka fadi gaskiya" Ta fada muryarta tana raurawa kaman zata sake masa kuka,abinda ya tilasta dariyanshi fita gaba daya. Siririn kuka ta sake masa,amma kuma da gaske abun mamaki qwalla take fitarwa,ya dan zaro ido yana mamaki.....saidai kafin yace komai,sai qaramar muryar yusra ta taso daga qasa.

“abbeee!" Ya sauke idanunsa sanda take rugowa qofar da zata sadata da inda suke tsayen kafin ruqayya ta kai ga kama ta.

Idanunsa ya maida kan akhnan yana narke idanunsa shima.

"Ki rufan asiri ammee...(sunan da yaran ke Kiran ta?,kinga dai banyi miki komai ba...hasalima yau ni aka yiwa laifi,da asuba akaqi sanmin abun arziqi. Yanzun yusra zata shigo,idan taga qwalla a idonki tace me na yiwa ammeenta?" Banda bacin rai kadan da takeji wanda batasan asalinsa ba,tabbas data qyalqyale da dariya. Saboda haisam din wani irin mutum ne da sam bayaso yaranta suga alamun ya bata ran mamansu. Ya taba bata amsa da cewa.

"Inaso su taso da tausayin iyalansu suma a gaba,dole sai ina kwatantawa. Yaro kuma baya mantuwa,komai a kansa yake zama,inaso su samu memory me kyau....inaso su tashi da yiwa rayuwar aure kyakykyawan zato,adadin kulawa nutsuwa da kwanciyar hankali da kuma soyayyar da yaro ya samu,adadin yadda zai dinga mu'amala da kowa a waje. Da taushi,da nuna qauna da soyayya ga kowa,ba tare da musgunawa ba" .ta gamsu da hakan dari bisa dari,don tana ganin tasirinsa tattare da yaran.

"Ba kaine ba.....dariya kakewa hancina".

" Na tuba.....na tuba giiftii din jimma" Ya fada yana hade hannayensa guri daya. Daidai lokacin yusra ta iso.

Yusea me sleepy eyes ta bayyana bakin qofar gurin tana kallonsu duk sy biyun. Sai dukkaninsu suka bude mata hannayensu,da gudu ta rugo,amma sai ta zabi fadawa jikin haisam. Dan ihu ya saki yana dariya wa akhnan din. Murmushi kawai ta saki,don dama tasan hakan na iya faruwa,bata sanya rai da yawa tazo gurinta ba.

Dagata sama yayi yana zagaye gurin da ita yana mata wata waqar larabci da yakan rera musu tun suna jira jirai idan suna kuka.

Burgeta kallonsu yakeyi......haisam.....mutum na musamman a duniya. Bata gajiya da fadin hakan. Idan ka ganshi cikin iyalinsa ba zakace shine wanda kullum manyan attajirai da manyan shuwagabannin duniya ke jiransa ba.

Yadda yusra ta kwantar da kanta a kafadarsa kawai ya isa ya gaya maka ita kanta ta gamsu tana da amintaccen uba a duniya. Yadda hannun Haisam ya riqeta instinctively. Yadda cold din mutumin nan yake narkewa a gaban iyalinsa kawai,sai idanunsu suka hadu da nata.

Na wani second guda… duk memories suka dawo mata. hamadar agadez,tsoron da suka fuskanta a tare,jarrabawar rayuwarsu da mammina....soyayyar da ta firgita ta. Da kuma daren da ta taba tunanin bazata iya rayuwa cikin duniyarsa ba. Yanzu kuma…ita ce duniyar tasa.

Haisam ya kalleta cikin nutsuwa irin tasa muryarsa a qasa yadda yusra ba zata fahimta ba.

“Why are you looking at me like that?” Ta girgiza kai a hankali.

“Just thinking.”

“Dangerous.”Ta yi murmushi,still him. Amma taqi bashi amsa. Ta sani tsaf zai qarar da duka lokacinsa a gurin,bayan tun a jiya tasan fitar yau me muhimmanci ce.

"Zaka wuce ne?" Ta tambaya kaman me masa tuni.

Ya sani.....meeting dinsa na jiransa. Phones suna ta vibrating tun safe. Duniya tana jiransa kamar kullum.
Amma sai ya kalli matarsa......'Ya'yansa.....gidansa sannan calmly yace

“No.”

Akhnan ta dan daga idonta a kansa.

“Your meeting?”

“It can wait.” ya furta yana rage tazarar nisan dake tsakaninsu. Sai ya qaraso gare ta,ya tsaya kusa da ita yusra na rungume a jikinsa.

A wajen balcony din… ,wata irin iska mai sanyi da dadi ke ratsasu. Garden din na cike da tsirrai dake bada iska me dadi har nan inda suke tsaye,shi yasa aka gina gurin daura da garden din. Rana mara haske da qarancin zafi tana haskaka gidan kamar wata sabywar rayuwa.
Chapter 171 · 0% Book details