Sashe 123
LUu Luu Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Karku kuskura.....karku soma sanya wadannan qarafunan a hannun sarkinmu na gobe!" Kaman an watsa musu ruwan sanyi haka karsashin kowa a cikinsu ya ragu,sai suka dakata suka tsaya cak da abinda suke shirin yi din.
"Ku tafi dashi cikin girmamawa......jinin sultane ya wuce qasqanci.....gobenku zatazo muku dashi a matsayin sarkinku.....sarkinku na agadez.....kada ku manta da wannan" Ta qarasa maganan tana zube idanunta cikin idanun mammina.
Wani kallon kallo ne ya wanxu tsakaninta da ita,tamkar tana bawa mammina tabbacin INDE INA RAYE BA ZAKI CIMMA NASARA BA. Yayin da mammina ke fadin MAMAKIN QARFIN HALI DA TAURIN KAI IRIN NAKI SAFIYYA!.
Kuka falaak ta saki wanda ya gauraye ilahirin hall din,akhnan tayi yunqurin miqewa zuwa ga d'an uwanta itama sanda guard ke zagayeshi. A tausashe haisam ya jawota zuwa jikinsa yana mata wani kyakkyawan riqo.
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" Ya fada rada mata a kunnenta,abinda ya sanya jikinta dukka ya sake da wani irin kuka da laushi da zuciyarta tayi,tayi luf a qirjinsa tana jin sautinnan nasa yana ratsa kunnenta,zuciyarta kuma tana mata zafi na yadda yaqi yin komai akan tafiya da ahmad din.
Matsowa gabansa tayi kadan,boyayyen murmushin nan da shi kadai yake iya ganinsa ta saki.
"Thank you for respecting the law of this palace". Ta fada ne da yaren oromo,a yau din,kanta tsaye,muraran ba tare da tsoro boyewa ko shakka ba. A yau ta amsa ta yarda ita din 'yar qasad Ethiopia ce.....a yau ta karbi wannan
"WATA BABBAR NASARAR" ya furta a hankali yana aika umarnin datse wannan sautin cikin muryarta da yaren oromo.
*B A Y A N A W A H U D U*
Abubuwa da yawa suka faru cikin masarauta a wadannan awannin hudun da sukazo masa da tarin matsi da wahala. Bawai wahalar aiki bincike tattara bayanai da hujjoji ba....aah....sam. Hasalima komai wahalan aiki yana samun wani karsashi da qwarin gwiwa wajen aiwatar dashi.
Abu daya da ya sanya wannan gajiyar da wahalar shine. Tarin tuhuma da zuciyarsa keta aike masa kan HAWAYEN AKHNAN. Me yasa baiyi komai akai ba?,zuciyarsa ke tuhmarsa. Me yasa zaibar hawaye masu nauyi cikin idanunta?.
Duk inda ya jefa idanunsa sai yaga masarautar kamar ta hargitse. Ba kuma kamar bane....a hautsine din take,ba wai don yawan jama'a ba.....aah. Hasalima ba wani baqo da aka sake bari ya shigo masarautar tun bayan wadancan awannin. An kammala sadakar ukun sultane......mammina kuma tace a dakatar da zuwa karbar gaisuwa ya isa hakanan. A yanzu lokacine na iyalinsa,lokacin iyalin daba wanda ya fahimci me take nufi da hakan,don bayan tsare yarima ahmad wanda labarin ya matuqar girgiza masarautar saidai ba wanda ya isa ya magantu.....ta tsare WAZEER an kuma kama mutanen da suke da fada a ciki cikin fada sun kusa su goma. Shi ya hana maleek shigowa cikin masarautar gaba daya,duk da yace bazai fita daga agadez yabar matarsa ba.
"Na maka alqawari.....bakin rai bakin fama. Zan kula da falaak kamar yadda zan kula da akhnan,ba falaak kawai ba.....dukka jinin sultane da iyalinsa gaba daya sun rataya a wuyana" Yasan waye haisam.....ya kuma gasgatashi ba na jiya ko yau ba. Idan yace zaiyi IN SHA ALLAH kaman yadda ta zame masa jini cikin dukka maganganunsa.....to zaiyi din. Idan yace bazaiyi ba.....zai wahala wani abu ya sauya matsayinsa akan wannan.
Ko a yanzun da yake takawa zuwa cikin gidan,dab da magariba ne da yanayin yammacin ya sake sanyayar da masarautar dama jikin dukka wanda ke rayuwa a cikin ta. Saidai akwai mutanen da idanunsa suke nuna masa. Ba wannan kamannin sam a tattare dasu,mutanen da ya sanyawa kowanne d'aya daga cikinsu jan fenti.
"Abeer......hold on" Ya fada a nutse yana zurfafa kallonsa tsakanin wasu shuke shuken dogon yaro masu tsaho sosai,inda yaga gilmawar wani motsi. Motsin da tuni yayi marking nasa......kuma ya fahimci akwai wani ta gurin.
Cikin jarumta da dakewar zuciyar nan tasa yake matsawa gurin,dab da zai isa ya dakata yana ci gaba da zubawa gurin idanu,yadan dauke kansa yana jan numfashi.
"Fito" Ya fada calmly,yana kuma sauke maganansa ta bayyana.
Tafisu ce,saidai bada wannan shigar tata ta asali ba,da wani launin kayan na daban,fuskarta a lullube da yanayin da ba lallai ka gane ita bace,amma shikam,ba wani motsi ko gilmawar mutumin daya sani da zata boye masa.
"Ta shirya korar nannie daga masarauta a daren yau da mafi munin sharri....." Shuru yayi yana zubawa tafisu idanu,hannunsa zube a aljihunsa. Cikin nutsuwar nan daba abinda ke girgizata ya motsa labbansa
"Yayi kyau.....yayi daidai,na gode,zaki iya komawa....amma haduwa ta gaba.....a wani gurin daban,ba cikin masarautar nan ba" Qasa tayi da kanta ba tare data iya dagowa ba,har zuwa sanda ya juya yana shigewa ciki.
"Abeer" Ya kirashi softly.
"Ranka ya dade" Ya amsa masa a girmame.
"Nannie zata bar masarautar nan,daga yanzu zuwa kowanne lokaci,a shirya mata sashenta itama.....a shirya mata gurin zama"
"An gama".
"And then....." Ya fada da yanayin daya karkato da hankalin abeer din.
"Sir...." Ya fada don nuna alamun yana saurarensa.
"....don't let anyone suffer"
"Done sir" Ya fada da girmamawa.
"Ina jabeer?"
"Yana online".
" Cut the connection abeer.....jabeer ina jinka" Ya fada yana ci gaba da nufar sassansa. Nufar da yakeyinta amma yana jin kamar ba tafiya yake ba. Yana buqatar sirri,dole yayi maganar akan hanya ba cikin daki ko wani gida ba. Ya saba idan yana aiki irin wannan.....koda katangu da bishiyoyi baya amanna dasu,yafi ganewa yawo cikin iska har zuwa mission dinsa zai kammala.
"She started already sir......" Jabeer ya fada dukka muryarsa tana nuna bacin ransa. Yasan bacin ran jabeer qwarai,wannan ya sanya aikinsu na farko da yasan yana buqatar haquri.....da daukan dogon lokaci kafin bincike ya kammala sai bai sanyashi ba.
"💎 *L U'U L U'U*
*_(The diamond)_*💎
*H U G U M A*
*BOOK 03///PAGE 111*
Jabeer" Ya kirashi da wata murya me taushi cike da tarin nutsuwa,tamkar ba shine yake fuskantar abu irin wannan ba.
"Don't forget jabeer.....karka manta" Ya tuna masa da yarjejeniyarsu,alqawarin danne fushi da janye dabi'arsa ta gaggawa cikin aikin kafin ya aminta ya shigo dashi ciki
"In sha Allah sir...." Ya fada a hankali. Shuru ya ratsa tsakani,ya kuma bawa jabeer dinne space ya shaqi iskar nutsuwa.
"Zaka iya ci gaba?" Ya tambayeshi a nutse.
"Yes sir....."
"Ehnnnn.....what did she take?" Haisam ya tambayeshi idanunsa suna kallon shimfidaddun duwatsun gurin kamar meson tantance nau'in wanne dutse aka fasa aka samar dasu,iskar yammacin me cakude da sanyin hamada da Sahara da ruwa ya jiqa tana busowa.
"Treasury access.” sai ya dakata kamar fadin kawai ciwo yake masa.
"Archive wing too.” idanunsa haisam ya dauke daga kan duwatsun a hankali yana duban gabansa. Ba wani mamaki saman fuskarsa,kaman dama yasan zata aikata hakan. Already ya riga yaga alamun faruwar hakan,tun a jiya.
“Should we interfere?” jabeer ya tambaya cikin zaquwa. Kai haisam ya girgiza masa a nutse.
"No" Ya amsa masa a hankali. Da sauri jabeer din yace.
"But if she gains control over the palace records......".
" She thinks power is in keys....." Ya fadi wani kasalallen murmushi yana subuce masa.
"Let her" Ya fada da wani irin confidence a muryarsa..
"The more confident she becomes…” ya sauke numfashi.
“…the more careless she’ll be.” wata nutsuwa ta saukarwa jabeer,sai ya gyada kansa sosai. Sai yanzu ya fara fahimtar ogan nasa..... isn't defending......he's trapping.
Ya murda handle na qofar bayan ya wuce dukka faluka,ya kuma duba duk inda ya kamata ya duba din.
Ya sallami birra a falon qarshe bayan ya karbi record na awanninta tare da akhnan din.
A kwace take kawai,saidai bata banbamce a wacce duniyar take rayuwa a yanzu?.
Ba abinda ke mata yawo a yanzu cikin zuciya da idanunta sai yadda aka wuce da ahmad zuwa prison. Prison fa?......abun yana mata nauyi da yawa. Yayin da zuciyarta ta cika da mamakin data dinga ji kamar zai hallakata akan mammina.
"Me yasa ta koma haka?,me ya sauyata?" Ta dinga maimaitawa cikin kanta.
Maganganunta.....kallonta.....ayyukanta dama idanunta.
"Ko ta qullaceni ne?,ko tana jin haushina ne shi yasa take shirya komai?,shi yasa ta shirya hucewa akan ahmad?,saboda me?,me nayi?,don naqi bin tsarinta ne?,don naqi bin umarninta ne?,don na karbi zabin sultane hannu bibbiyu?,me yasa ta zabi ta zama haka?,me yasa ba zatayi komai a kaina ni daya ba?". Sai ta runtse idanunta da gaske tana sake dawo mata da komai akan mammina.
Sai kuma ta soma girgiza kanta. Abinda take gani a idanun mammina ya d'ara wannan......abinda take gani a fuskarta yana gaya mata ba iya wannan bane.....ba iya matsalar kenan ba. Idan iya itace ina ruwan wazeer daba ahalin gidan ba?,ina ruwan sauran mutanen da aka gayawa morsa dazu suma an kamasu?. Ta sake rufe idanunta tana dawo da fuskar mammina.
Fuskar babban MAQIYI take gani yanzu shimfide a tare da ita.
"Me yake shirin faruwa?" Ta tambayi kanta tunaninta yana hargitsewa,ta kuma yi tambayar daidai sanda haisam ya buda qofar da sallama a nutse.
Idanunta ta maida ta kulle a hankali. Zafinsa take so taji.....haushinsa take so taji koda d'an kad'anne amma zuciyar taqi karbar wannan yanayin.
"Me yasa ba zakiji haushinsa ba.....me yasa?" Ta tuhumi kanta,idanunta a lumshe amma tana jin takunsa da sake kusantotan da yakeyi a rubuce cikin zuciyarta. Duk da idanunta a lumshe suke....amma tana jin hakan a qasan zuciyarta.
"Assalamu alaikum warahmatullah" Ya sake maimaitawa bayan wadda yayi da farko bata amsa ba,ya sake maimaita sallamar a sanda ya iso dab da bakin gadon inda take kwance,ya kuma tsugunna a gaban gadon saitin kanta.
Bata motsa ba,bata kuma amsa masa ba,sai ya miqe tsam yana isa ga tarin jerin abincin awannin duka da aka ajjiye mata. Suna nan kamar yadda birra ta gaya masa,daidai da ruwa kadan tasha.
Ya waiwaya ya sake kallonta,ko motsi har yanzu batayi ba,ya sani....idanunta biyu,ba wani motsi nata da zai boyu a idanunsa.
"You didn’t eat.” ya fada softly bayan ya dawo gefan bedside drawer ya zauna daf da ita.
Zuwa sannan zuciyarta ta game matsewa guri daya. Zuciyarta tana gaya mata bai kyautu taqi kulashi ba....bai kamata taqi amsa sallamarsa ba.
"Ka damu ne?.....tunda ka bari suka tafi dashi" Ta fada da raunanniyar muryartan nan dake kakkarya masa zuciya da katse masa duk wata jijiya me amfani dake jikinsa.